SANGARTA COMPLETE

By ZulayheartRano89

122K 6.6K 89

labarin soyayya da ban tausayi More

part 1
BABI NA BIYU
BABI NA UKU
BABI NA HUDU
BABI NA BIYAR
BABI NA SHIDA
BABI NA BAKWAI
BABI NA TAKWAS
BABI NA TARA
BABI NA GOMA
BABI NA SHA DAYA
BABI NA SHA BIYU
BABI NA SHA UKU
BABI NA SHA HUDU
BABI NA SHA BIYAR
BABI NA SHA SHIDA
BABI NA SHA BAKWAI
BABI NA SHA TAKWAS
BABI NA SHA TARA
BABI NA ASHIRIN
BABI NA ASHIRIN DA DAYA
BABI NA ASHIRIN DA BIYU
BABI NA ASHIRIN DA UKU
BABI NA ASHIRIN DA HUDU
BABI NA ASHIRIN DA BIYAR
ASHIRIN DA SHIDA
ASHIRIN DA BAKWAI
ASHIRIN DA TAKWAS
ASHIRIN DA TARA
TALATIN 30
TALATIN DA DAYA
TALATIN DA BIYU
TALATIN DA UKU
TALATIN DA HUDU
TALATIN DA BIYAR
TALATIN DA SHIDA
TALATIN DA BAKWAI
TALATIN DA TARA
TALATIN DA TARA
ARBA'IN DA DAYA
ARBA'IN DA BIYU
ARBA'IN DA UKU
ARBA'IN DA HUDU
ARBA'IN DA BIYAR
ARBA'IN DA SHIDA
ARBA'IN DA BAKWAI
ARBA'IN DA TAKWAS
ARBA'IN DA TARA
HAMSIN
Complete

ARBA'IN

2.6K 129 0
By ZulayheartRano89

*SANGARTA*


                     ©
         *ZULAYHEART RANO*

       *Sadaukarwa ga khadija s Muhammad My Besty*

 
                  *40*

Bedroom ɗinsa ya nufa, sai da ya soma rage kayan jikinsa sannan ya faɗa toilet ruwa ya watsawa jikinsa, bayan ya fito ya gabatar da sallah, jikinsa ya shafe da mai tare da feshe ko ina da turarr, kayan bacci ya sanya sai ya bi lafin gado bakin sa dauke da addu'a, bai wani dade ba bacci ya yi a won gaba da shi, mai cike da mafarkin Ameesha. Kiran sallar asuba ya  farkar da shi, mika ya yi tare da addu'a kana ya nufi toilet ya dauro alwala, bai ta yar da sallah ba sai da ya je dakin Ameesha wacce ke sharar bacci, a hankali ya matsa inda take tare da kai lallausan hannunsa  fuskarta yana mata waiwayi.

Buɗe idonta ta yi mai cike da bacci, ta zuba su bisa fuskar Dr.

"Lokacin sallah ya yi tashi ki yi."

Mika ta yi tare da hamma alamar dai bacci bai isheta ba, ta amsa da

"To."

Yana zaune har ta  shiga ta fito, sannan ya jasu sallah suna idarwa Ameesha ta sanyaya murya ta ce

"Ina kwana Dr!"

"Lafiya lau Heartbeat fatan kin tashi lafiya ya sabon waje?"

Murmushi ta yi kanta a kasa ta ce "Alhamdulillah!"

"Madallah! Yanzu dai nasan kina da buk'atar hutu, je ki kwanta ki huta zuwa anjima."

Mik'ewa ta yi ta nufi gadon, shima Dr gadon ya nufa ya kwanta cikin hikima ya jawota jikinsa tare da rungumota, kamar zai mai da ta ciki duk da son jiki irin na  Ameesha amma ganin yadda Dr ya cusata jikinsa sai ta fara k'ok'ari janye jikinta, shi kuma ya ki barinta, gajiya ta yi ta barshi  a haka bacci ya kwashe su.

Basu farka ba sai karfe tara, Dr ne ya soma tashi sannan Ameesha bed ɗinsa ya nufa don yin wanka, shaf shaf Dr ya yi wanka ya fita, kai tsaye bangaren Aneesa ya nufa.

A hakimce ya ganta zaune kan kujera, ko sallamar da ya yi kin amsa masa ta yi

"Kin tashi lafiya?"

Banza ta kuma masa, bai yi zuciya ba ya kuma faɗin

"Kin yi break ne?"

Mtsss ta ja tsaki ta ce

"Ina ruwanka da break ɗin na? Kai dai ba kana can tare da matarka ba, kaga kenan rashin yin break na ba matsalar ka ba ce." Tana dire maganar ta yi shigewarta bedroom.

Tsayawa kawai Dr ya yi yana kallon Aneesa, tun yana mamakin halinta zuwa yanzu har ya daina, nannauyan ajiyar zuciya ya sauke tare da kaɗa kai ya fita.

Mota ya ɗauka ya fita, don nemo masu abin da za su ci, bai ta de ba ya dawo, wannan karon ma falonta ya shiga, mika mata tek away din ya yi ba tare da ya ce komai ba ya fita, yana jin lokacin da ja tsaki.

A bangaren Ameesha bayan Dr ya fita itama toilet ta shiga wanka ta sillo daure da towel gaban madubi ta yi masauki, duk ilahirin jikinta ta shafe da mai kafin ta nufi wordrop da niyyar dauko kayanta, sai jin sallamar Dr ta yi take wani irin kunya ta kamata, motsi ma kasawa ta yi don kunya.

"Heartbeat baki gama shiryawa ba?" Shiru ta yi ta kasa ko da ɗago kai.

Ganin taki magana yasa ya karasa inda take yana faɗin

"Kinga Wallahi yunwa nake ji fa kuma nasan kema haka Please bari na shirya ki." Ya yi maganar yana sa hannu cikin wordrop ɗin, kaya ya dauko mata riga da siket da pant and bra, aje su ya yi kan gado tare da riko hannunta.

"Please Dr ka barni zan iya sawa fa." A hankali ta yi maganar.

"No! Bana so ki wahala bari na shirya ki kawai."

"Please.. "

Ko sauraron maganar ta bai yi ba, sai ma fara sanya mata pant da bra, tsaf ya shirya ta har yana shafa mata hoda, ita kam sai turo baki take har da kukan sangarta, hannunta ya ja sai falo a dining ya yi mata masauki, don ya yi masu tek away, tsaf ya shirya masu komai a kan dining.

Da kansa ya zuba mata komai sannan ya soma bata shi ma yana ci, suna ci suna soyayyar su har suka gama, tashi Ameesha ta yi tare da kwashe duk wani kaya da suka bata ta yi kicin da su, bata fito ba sai da ta wanke tare da gyara kicin ɗin. Dr na zaune shi kadai a falon yana jiran ta fito amma ya ji shiru sai kawai ya bita kicin ɗin, zaro ido ya yi cikin mamaki ya ce

"Heartbeat aikin me kike yi kuma?"

Murmushi ta saki ta ce

"Dr gyara kicin nake yi."

"Me yasa baki kirani ba?"

"In kiraka ka yi min me?" Da mamaki ta yi tambayar.

"Aikin mana." ya bata amsa.

"Hmmm! Dr kenan ai wannan ba irin aikinka bane nawa ne don haka na hutace ka." Yadda take maganar kawai abin birgewa ce. Domin har kasala ta saukarwa Dr.

"Ni dai ban yadda da wayonki ba, Heartbeat kullum nafi so ki rika hutawa kinji ko?" Ya yi maganar yana jan hancinta.

Dariya suka yi gaba daya, ta ce

"Na daina Dr."

"Yawwa autar Ummi mu je mu gaida Aneesa."

"To." Ta amsa tana tafiya.

Yana rike da hannunta suka yi sallama a falon Aneesa, Aneesa wacce ke zaune ta buga uban tagumi saurin ɗago da kai  ta yi, tana amsawa  cikin murmushin karfin hali  ganin Dr da Ameesha. Ji ta yi kamar ta tashi ta shake Ameesha, wani irin kishin Dr ke a zalzalar ta, da kyar ta yi control ɗin kanta ta tattaro nutsuwarta ta furta masu

"Sannun ku da zuwa."

"Yawwa."  Yawwa Dr ya amsa  .

Yana zama a kan kujera  Ameesha kuwa a kasa kusa da kafar Dr.

"Hamman ina kwana?"

"Lafiya lau My Anee ya kika tashi?"

"Lafiya lau."

"Ina kwana?"  Ameesha ta faɗa cikin sanyin murya.

"Lafiya." Shi ne amsar da Aneesar ta bata, bayan ta dauki kusan minti biyar kafin ta amsa tana aika mata harara.

Gyaran murya Dr ya yi, wanda yasa duk suka nutsu tare da maida hankali kansa, godiya ya soma yi ga Allah da ya nuna masa wannan rana, sannan ya soma masu nusiha cikin kwantar da murya akan su zauna lafiya da junansu baya son tashin hankali. Shiru suka masa har ya gama sannan ya tambaye su ko da mai wata matsala

"Babu." Ameesha ta ba shi amsa.

Aneesa kam banza ta masa sai jijjiga kai da hura hanci take yi, ko kallon inda suke bata yi ba.

"Don Allah ku zauna lafiya, matuk'ar kuka zauna lafiya to kwanciyar hankalina ne, haka in akasin zaman lafiya ta samu wallahi tashin hankalina ne, ku rika kai zuciya nesa ku yi koyi da kishin matan Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama."

"Allah ya bamu iko." Cikin siririyar murya ta yi maganar.

Aneesa kam ka sa cewa komai ta yi domin, ji ta yi wani kuka yana shirin zuwa mata, tana son Dr son da batawa kanta tana matukar kishinsa wanda har take jin kamar ba zata iya takwara zuciyarta ba, don haka ganin ya gama sai ta mik'e kamar dai wata kububuwa ta yi shigewarta bedroom

Ameesha kam hamma ta saki, don ta gaji da zaman, kallonta Dr ya yi ya ce

"Ya dai autar Ummi bacci ko?"

Kai ta gyaɗa alamar "eh."

"Ok tashi mu je ki kwanta." Ya yi maganar yana k'ok'arin tashi tsaye.

" *Wai Auta*! Aneesa ta maimaita sunan, wato ma ita ce Auta, sai wani narkewa ta ke masa, hmmmm! Zan yi maganin ku daga ke har shi,  ganin yana niyyar tafiya yasa  Aneesa ta ce

"Hamman ina son zuwa gidan Nenne, domin yau yan Adamawa zasu koma zan je masu sallama." Ta yi maganar ne tana maida kwallar da suke niyyar zubowa.

"Allah ya kiyaye hanya." Ya yi maganar yana mik'ewa tsaye rike da hannun Ameesha.

Kallonsa ta yi cikin wani irin yanayi, hankalinta ya tashi ganin yadda Dr ya mata, don haka suna fita ta saki wani irin kuka mai cin rai, tana bakin ciki da Auren Dr ta kula son da Dr kewa Ameesha ko kwansa baya mata, lallai sai ta mik'e tsaye domin ta samowa kanta yanci.

Dr kam suna fita daga falon ɗaga Ameesha ya yi sama tare da rungumeta, ita kuma sai ciccila kafa take alamar ya sauketa, bai sauketa ba sai ma ci gaba da tafiya da ya yi har suka shiga falonta, a nan ma bai sauketa ba sai juyata da yake kamar wata yar baby.

Kukan sangarta ta fashe masa da shi, ko hawaye babu tana ta bubbuga masa kirji

"Lalala autar Ummi an ya kuwa kina cin abinci?"

"Ni dai ka saukeni gaskiya Dr."

"Allah ba zan saukeki ba, tambayarki nake kina cin abinci kuwa?"

"Ina ci sosai ma, amma m e ka gani Dr?"

"Sam baki da nauyi kamar na ɗauki yar shila."

"Ni dai saukeni." Ta yi maganar tana turo baki.

Bai sauketa ba sai da ya gama shilla sama, sannan ya direta a kan kujera sai dariya suke yi abin su, kara rungumota jikinsa ya yi yana sinsinar sumar kanta, hannunsa na wasa da sassan jikinta jikin Ameesha duk ya gama saki da salon wasannin da Dr yake mata, a haka bacci ya kwashe su kar'ar wayar Dr e ta farkar da su.

Sunan Nenne ya gani a kan screen ɗin wayar, da sauri ya daga tare da sallama.

Bayan sun gaisa take tambayarsa ina Ameesha.

"Gata nan Nenne bari na bata." Da yake ta tashi har ta bude ido.

Mika mata wayar ya yi yana faɗin "Nenne ce ke son magana da ke."

Amsa ta yi ta soma gaidata cikin kunya da ladabi har da tsugunawa, abin da ya kara mata daraja a idon Dr kenan

" 'yata kin tashi lafiya ya bak'on waje?"

"Lafiya lau Nenne."

"Madallah! Fatan babu wata matsala?"

"Eh! Nenne babu komai."

"In har da matsala ki sanar min kin ji ko?"

"In sha Allah! Ameesha ta amsa cikin ladabi. Da haka suka yi sallama ta mik'awa Dr wayarsa suka ci gaba da magana da Nenne, ita kam bedroom ta nufa don yin sallah.

Zata tayar da sallar kenan Dr ya shigo

"Wai har kin yi alwalar?"

"Eh! Zan tayar da sallah."

"Ok jirani na yi alwala." Yana maganar ne yana shiga toilet.

Bayan sun idar suka ci abincin da Dr Asmad ya fita ya sayo masu, sai  suka ci gaba da hira har magriba, wannan lokaci Dr ba a gida ya yi sallar ba domin masallaci ya je, bayan ya idar da sallah ya nufi gidan Nenne don ɗauko Aneesa kuma ya gaisa da bakin gidan, bai su shigo gida ba sai bayan ishsha. Ko a mota Aneesa sai cika take tana batsewa, domin da cewa ta yi gidan Nenne zata kwana, da kyar lallabota ta biyo shi, ko da Dr ya bata take away din da ya yo masu kin karba ta yi, har sai da taga ya nuna ɓacin ransa.

Ita kam Ameesha bayan ta idar da sallar ishsha zama ta yi tare da ɗaukar littafin addu'oi tana karantawa, sallamar Dr ce ta sanyata ɗago kai.

"Sannu da dawowa! Ta yi maganar tana amsan kayan da ya shigo da su.

"Yawwa ya zaman kadaici?"

Murmushi ta yi kawai ta kai kayan ma'ajinsu.

Ruwa ta kawo masa mai sanyi, tas ya shanye ruwan ya aje cup din, zama kusa da shi ta yi tana faɗin

"Dr ka daɗe a masallaci."

"Ki bari kawai na biya gidan Nenne ne bayan an idar da sallar, kin san Aneesa tana can."

"Ok ya Nenne da Bobbo?"

"Duk suna lafiya, ga abinci nan na shigo da shi nasan kina jin yunwa ko?"

"An gode, amma fa ni Dr bana wani jin yunwa."

"Ji beta don Allah wai bata jin yunwa, ko dai baki son cin abinci? Shi yasa kullum baki kiba." Ya yi maganar yana jan kumatunta.

Dariya ta yi tare da daukan kayan ta nufi dining room da su

"Na gama haɗawa fa Dr."

"Ok bari na yi wanka tukun.  Ya bata amsa yana tafiya, bai jima da shiga ba ya fito cikin wasu rigar bacci mai kalar milk, tana ganin sa da kayan ta kauda kai dining suka nufa sai da suka koshi Dr ya suri Ameesha bai zame ko ina da ita ba sai kan fadeden gadonsu, da sauri ta tashi zaune

"Lafiya kuwa?" Cikin mamaki Dr ya yi tambayar.

"Wanka zan yi kuma ban yi brosh ba."

"Mu je na yi maki."

Zaro ido ta yi, cikin sauri ta ce "A'a."

"Please mana My heartbeat."

"Don Allah dai Dr ka yi hakuri."

"Na hak'ura idan kin gama wankan ki dauro alwala." Ya yi maganar bayan ya aje mata kayan bacci a kan gado.

"To." Ta amsa tana shiga toilet, ganin ya fita, ko da ta gama wankan daure da towel ta fito, ganin babu Dr a bed din ta yi saurin isa gaban mirror ta shafe jikinta da mai da turare, jikinta sai fitar da sansanyar kamshi turarenta yake, wajen gadon ta nufa don sanya rigar baccin,

"Inna lillahi! Ta furta a fili ganin irin kayan da Dr ya aje mata, sai juya su take tana tunanin ta yadda zata sanya, a haka Dr ya shigo

"A'a ya baki shirya ba?"

"Dr wannan kayan..."

"Mai suka yi?"

"Ummh! Ban iya sanyata."

"Ok kawo na sanya maki." Ya yi maganar yana nufarta."

"Sorry Dr Please."

"No! Kawo kawai zan sanya maki."

"A'A ka bari zan sa amma ka fita."

"Ba zan fita ba, ki je toilet ki sa kina bata min time fa."

Ganin ya hada ransa yasa ta nufi toilet, sa kayan ta yi ta tsaya tana k'arewa kanta kallo

"Woww." Ta furta ganin yadda kayan suka yi mata kyau, sai dai bata jin zata iya fita a haka don sam kayan basu da maraba da tsirara, riga da wando ne da kadan rigar ta wuce cinya, shi kam wandon har gara babu kalar milk ne, komai a bayyane yake.

Dr kam yana zaune yana jiran ta fito ya ji shiru, don haka sai ya nufi toilet din Yana faɗin

"Heartbeat ki fito ina jiran ki fa. " Da ya ji shiru sai ya tura kofar, nan take ya bude tsaye ya ganta ta rintsa ido.

Kallonta ya yi sosai tare da sakin ajiyar zuciya, hannunta ya riko dogon hijab ya sa mata, kana suka tayar da sallar bayan sun idar ya dafe kanta ya karanto addu'ar da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya umurci ko wane ango ya yiwa amayarsa, yana gama mata addu'oi tare da bata tatacciyar Madara, sannan ya soma tambayarta game da addinin ta, sosai Ameesha ke bashi amsa, ya ji dadin yadda Ameesha ke ba shi amsa, cire mata hijab din ya yi ya ce ta kwanta.

Kwanciyarta babu dadewa shi ma Dr ya hau gadon tare da kashe hasken bed room din, da yake tuni ya kashe duk wani kayan wutan falo, bacci ya soma daukarta kenan ta ji mutum a jikinta, sosai hankalinta ya tashi duk iya kokarin ta na gujewa Dr abin ya faskara, sai ma ji ta yi yana karanta addu'ar saduwa da iyali, tsabar azabar da taji yasata sakar masa kuka ganin abin ba mai k'arewa ba, Dr ma bai san tana yi ba ya dauki dogon lokaci kafin ya maida Ameesha cikakkiyar mace, wahala kam ta duniya ta sha shi, albarka kuwa Dr har ba zai iya fadi adadin wanda ya sanyawa Ameesha ba.

Don sosai ya ji dadin yadda ya sameta, Aneesa Yar uwarsa ce kuma tabbas shi ya soma saninta, amma Ameesha ta daban ce ba zai iya haɗa matsayin ta da ko wacce mace a zuciyarsa ba.

_To sannu Ameesha sangartacciya, yau dai duk ta sangarta ta kare domin kema kin shiga sahun matan aure, Allah ya bada zuri'a dayyaba_ 😍💖💓💗

*YAR MUTAN RANO*

Continue Reading

You'll Also Like

28.3K 1.1K 16
❣️Bản dịch với mục đích phi thương mại, chưa hề có sự cho phép của bất kỳ ai, vui lòng không mang đi nơi khác❣️ Tên truyện chỉ liên quan 1 xíu xìu xi...
13.6K 1.7K 35
" මේ තාක් කාලයක් විදවපු මගෙ ජීවිතේට සතුට අරන් ආපු; මගෙ ආදරේ... මගෙ ජීවිතේ වටිනම වස්තුව... මගෙ මහත්තයා.... මම උබට හරි ආදරෙයි මගෙ මහත්තයෝ..." 🌼❤️ ...
39.7K 5.6K 48
" අහලා තියනවද අශස්....තෝඩු තෑගි දෙන්නෙ උරුමක්කාරයො උනාට මල් තෑගි දෙන්නෙ හිමිකාරයෝ කියලා.... " ආරුල් අයියාගෙ වචන වලට මගෙ බඩේ සමනල්ලු පියාඹනවා වගේ දැනෙ...
14.9K 830 19
ඉතින් ඔයාලා විශ්වාස කරනවද අලුතෙන් ඉස්කූල් එකට ආව sweet , cute ගෑනු ළමයෙක් නිසා එයා වෙනස් වෙයි කියලා..... මේ එයාලගෙ ආදරය කතාව ...