SANGARTA COMPLETE

By ZulayheartRano89

120K 6.6K 88

labarin soyayya da ban tausayi More

part 1
BABI NA BIYU
BABI NA UKU
BABI NA HUDU
BABI NA BIYAR
BABI NA SHIDA
BABI NA BAKWAI
BABI NA TAKWAS
BABI NA TARA
BABI NA GOMA
BABI NA SHA DAYA
BABI NA SHA BIYU
BABI NA SHA UKU
BABI NA SHA HUDU
BABI NA SHA BIYAR
BABI NA SHA SHIDA
BABI NA SHA BAKWAI
BABI NA SHA TAKWAS
BABI NA SHA TARA
BABI NA ASHIRIN
BABI NA ASHIRIN DA DAYA
BABI NA ASHIRIN DA BIYU
BABI NA ASHIRIN DA UKU
BABI NA ASHIRIN DA HUDU
BABI NA ASHIRIN DA BIYAR
ASHIRIN DA SHIDA
ASHIRIN DA BAKWAI
ASHIRIN DA TAKWAS
ASHIRIN DA TARA
TALATIN 30
TALATIN DA DAYA
TALATIN DA BIYU
TALATIN DA UKU
TALATIN DA HUDU
TALATIN DA BIYAR
TALATIN DA SHIDA
TALATIN DA BAKWAI
TALATIN DA TARA
ARBA'IN
ARBA'IN DA DAYA
ARBA'IN DA BIYU
ARBA'IN DA UKU
ARBA'IN DA HUDU
ARBA'IN DA BIYAR
ARBA'IN DA SHIDA
ARBA'IN DA BAKWAI
ARBA'IN DA TAKWAS
ARBA'IN DA TARA
HAMSIN
Complete

TALATIN DA TARA

2K 114 2
By ZulayheartRano89

*SANGARTA*

  
                        ©
           *ZULAYHEART RANO*
My Wattpad username
*ZulayheartRano89*


    *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

                      *38*

    "Au dama Dr Asmad ne ya yi maki wannan walak'ancin?"

     "Eh! Abbana." Meesha ta bashi tabbaci.

     "Ai ko sai na nuna masa kurakuransa tunda ya taɓa min uwata."

    "Yawwa Abba wallahi ka nuna masa kurakuransa, har yau idan na tuna marin raina yakan ɓaci, kuma fa shi ne sanadin da na daina zuwa sahad yanzu."

      "Yi hakuri 'yar Abbanta tabbas Dr bai kyauta ba, don haka zan dau mataki, tashi ki ci abinci."

     "Bari na je na yi wanka tashina daga bacci kenan ko wanke baki ban yi ba."

    "A fito lafiya, amma don Allah Mamina a daina baccin yamma."

Dariya sosai Ameesha ta yi jin yadda Abba ya yi maganar, kamar wani marayan yaro

      "Na daina in sha Allah."

    "Allah ya yi albarka, je ki fito ina nan tare za mu yi dinner."

Amsawa ta yi tana tattaka matakalar benen. A jiyar zuciya Ummi ta saki, domin tun ɗazun ta suma da jin maganganun Abba da 'yarsa, gyara zama ta yi tare da maida hankali kan Alhaji Taheer ta ce

    "Alhaji da gaske mataki zaka ɗauka kan Dr Asmad?"

   "Me kika gani?"

   "Na ji  kana tabbatarwa da Auta ne, to wallahi Allah tun wuri ka sake tunani, wannan SANGARTAR da kake nunawa Auta sam ba abin arziki ba, kai yanzu ko shawara aka baka sai ka ɗauka Alhaji?" Cikin sanyi take maganar.

Murmushi ya yi irin tasu ta manya ya ce

    "Haba Halima! Ai karen hauka bai cijeni ba, da har zan ce zan ɗauki mataki akan Dr Asmad, ba Dr ba wallahi ko wanine babu abin da zan masa, kin san menene hikimar amsa mata zan dau mataki?"

Girgiza kai Ummi ta yi idonta na kan fuskar Alhaji Taheer.

    "Saboda yanzu uwata ta zama hukuma sai da lallashi, yanzu da ace ba haka na ce mata sanin kanki ne da yanzu bata bar kuka ba, to kin ji dalilin amsa mata, ai  kaf duniya uwata bata da wani miji sama da Dr Asmad."

Murmushin nasara Ummi ta yi ta ce

     "Madallah! Da maigidana abin alfahari na, tunanin ka abin sone ga kowa, Allah ya tabbatar da Alhairi."

     "Hhhhhhhhh! Tunanina? Ko tunaninki? Ai yanzu duk wani abu da nake aiwatarwa ke ce SILAH, a da bana gane karatun da ki ke min amma yanzu Alhamdulillah! Allah ya maki albarka."

    "Amin." Ummi ta amsa sannan suka ci gaba da hira, a haka Meesha ta same su, kai tsaye dining suka nufa domin yin dinner, sai a time ɗin Haydar ya dawo gida.

Bayan sun gama cin abinci, Ameesha suka ci gaba da hira ita da Abba rabi duk nusiha ne, ta yadda zata kula da Dr, domin cikin hikima da basira Abba ya tabbatar mata da aurenta da Dr babu fashi, domin dai Dr Alhairi ne a gare su.

Bayan duk ta gama jin bayanin Abba, sai ta mik'e cikin zallar SANGARTAR ta fashe da kuka,  harda bubbuga kafa kamar dai wata karamar yarinya, da gudu ta kwasa ta yi sama cikin fushi.

Duk yadda Abba yaso ya shawo kanta abin ya gagara sai kawai ya barta.

Da niyyar da safe zai lallasheta

****

Yanzu dai zaman Dr da Aneesa sai madallah, domin tana kokarin yi masa duk wani biyayya, wannan duk aikin Rukky ne, a cewar ta ta haka ne zata samu Dr a hannu kafin Ameesha tazo.

Dr kansa ya ji dadin haka, domin ranar suna zaune bayan sun gama love dinsu, Aneesa tana jikinsa sai shagwaɓa take zuba masa, sai ya ɗago da fuskarta ya manna mata kiss ya ce

    "My Anne don Allah Yanzu baki jin dadin zaman da muke yi?"

Wani murmushi ne ya bayyana akan fuskarta ta ce

     "Ni kam ke ji, yanzu ko da yaushe ina tare da mijina mu yi bacci tare mu ci abinci tare, kana nuna min soyayya komai duk wani hakki nawa kana kokarin saukewa, nikam a duniya mai ta kai min wannan daɗi? Wallahi Hamman ba bi shi."

    "To kinga wallahi kaf duniya zaman lafiya ya fi komai, don haka Please mu zauna lafiya da juna ko da abokiyar zamanki ta zo a daure a rika kai zuciya nesa."

  Wani irin faduwar gaba ta ji da ya ambato abokiyar zama, ita da har ta manta da wata matarsa, sai yanzu da ya tuna mata, da kyar ta iya tattaro nutsuwarta ta ce

  "Karka damu Hamman baza'a samu matsala ba da yaddar Allah."

  "Allah ya maki albarka matata."

    "Amin." Ta amsa tana sauka daga jikinsa, toilet ta faɗa sai da ta sha kukanta kafin ta yi wanka ta fito, tana fitowa ya shiga ko kafin ya fito, har ta gama shafe-shafenta ta kwanta kamar mai bacci, alhalin kan ba bacci take ba kishi ne ya motsa.

Magana ya yi mata, tunda ya ji ta yi shiru sai kawai ya kwanta a bayanta, tare da rungumota jikinsa a haka bacci ya yi awon gaba da shi.

Ta daɗe tana takaici kafin bacci ya kwashe ta.

Da asbah kusan a tare suka farka, Dr toilet ya shiga ya dauro alwala sannan ya wuce masallaci, Aneesa kam bedroom ɗinta ta koma, sallah ta gabatar sannan ta koma bacci, sam ta ji bazata iya haɗa masa abin break ba, domin da takaicin sa ta kwana.

Bayan ya dawo masallaci, karatun Alkur'ani ya yi, ko da ya kammala sai ya dan kwanta  domin dai ba zai fita office da wuri ba, nannauyan bacci ya kwashe shi, bai farka ba sai 9:30 shi din ma wata mahaukaciyar yunwa ta tayar da shi.

Wanka ya yi ya yi shirin fita, falo ya fita babu kowa ya duba dining babu komai akan dining din, sai ya nufi bedroom a kwance ya hango ta ta yi dai dai tana ci gaba da sharar bacci.

Cikin takaici ya girgiza kai tare da fita daga gidan gaba daya, gidan Nenne ya nufa don yasan can suna da komai, bayan sun gaisa ne ya ce

     "Nenne yunwa ta biyo dani nan gidan fa."

     "Yunwa ina Aneesar?" Nenne ta tambaya cike da mamaki.

     "Wallahi Nenne bacci take yi kamar dai bata jin dadin jikinta ne." Ya ɓoye don kar Nenne ta fahimci wani abu.

     "Allah ya bata lafiya." Shi ne abin da Nenne ta faɗa tana nufa dining, mintina ƙalilan

Nenne ta kawo masa break, yana ci suna hira har suka sauka kan na Ameesha gyara zama Nenne ta yi tana fuskantar Dr ta ce

    "Wai kuwa Asmad ka koma gidansu Ameesha?"

   "Ban koma ba Nenne." Kai tsaye ya bata amsa.

   "Menene dalili?"

   "Bana son ta kuma bata min rai."

   "Kai bana son shashanci, ko ka manta matarka ce Ameesha, dole sai kana mantawa da wasu abubuwan kuma ai ɗan Adam ajazi ne, tana da hakki akan ka, don haka ya zama wajibi ka kula da hakkin ta."

    "To Nenne in sha Allah, yau zan biya idan na dawo." Yana maganar ne bayan ya mik'e tsaye.

   "Allah ya yi albarka."

Daga haka Dr ya bar gidan, ko da ya isa office bai wani jima ba, domin babu wani aiki tunda ranar ta ƙkasance asabar ne, da ya bar asbiti, wani mall ya biya ya yiwa Ameesha shopping don yasan ta da shan kayan zaki, yana fita  diret gidan Alhaji Taheer ya nufa, ya yi hon maigadi ya buɗe masa, ya faka motar sannan ya daga waya ya kira number ɗinta.

Lokacin tana zaune ta yi nisa cikin tunaninsa, sai yanzu take dana sanin abin da ta masa ga shi   rabon ta da shi tun ranar da ya bar gidan cikin zuciya babu mamaki ma fushi ya yi da ita.

Wayar ta ce dake kusa da ita ta fara ruri, a zabura ta kalli wayar, har murza ido ta yi don son ta gasgata abin da ta gani tabbas Number Dr Asmad ne, cikin sanyin jiki ta ɗauki wayar tare da karawa a kunne

      "Assalamu Alaikum." Ta furta cikin siririyar murya.

   Daga ɓangaren Dr sai da ya saki ajiyar zuciya jin muryar Ameesha

      "Wa'alaikumus salam, ki fito ina jiran ki domin sauri nake." Abin da ya faɗa kenan ya kashe wayar.

Jiki a sanyaye ta mik'e ta kudirta sai ta ba Dr haushi tunda haka yake faɗa mata,  sai da  ta gyara fuskarta, ta nufi bedroom din Ummi, sanar mata ta yi da zuwan Dr ya ce

      "Yana jirana."

      "To ki shigo da shi falo mana, ke kamar wata mara wayau ki ke." Ummi ta faɗa cikin takaici.

"To." Ta amsa tana nufa waje.

Jingine yake jikin motarsa, ya zubawa hanyar da Ameesha zata fito ido, can yaga ta nufo wajensa cikin takunta mai daukar hankali, sosai ta tafi da hankalinsa har bai san time da ta iso wajen ba, sai jin sansanyar kamshi turarenta da ya gauraye wajen, dogo da kai ya yi tare da zuba mata ido.

"Sannu da zuwa." Ta faɗa tana kauda kai gefe.

"Yawwa."

Ya amsa a dakile, shiru ne ya ratsa na yan dakiku, sannan yasa hannu cikin mota ya dauko mata ledar da ya shigo mata da shi, yana tambayarta

"Ga wannan ki yi amfani da shi, baki jin komai a jikinki ko?"

"Eh!" Ta bashi amsa. Bata da niyyar amsan ledar.

"Princess ke fa nake mik'awa?"

"No! Dr ka barshi kawai na gode."

Da mamaki ya kalleta, cikin zuciyarsa ya ce "lallai yarinyar nan, Ni kikawa laifi amma kuma ke kike jin haushi na, aikam sai kin gane kuranki.

A fili kam sai ya ce "amsa ki kaiwa Meena, tunda ke baki buk'ata."

Babu musu ta amsa, Dr dai kuma kallonta ya yi ya ce

"Dama nazo dubaki ne tunda babu matsala zan wuce." Ya ida maganar yana buɗe kofar motar

"Ina son zuwa gidan Nenne."

"Allah ya dawo da ke lafiya, amma ki sani karki kuskura ki tuka mota da kanki." Yana maganar ne yana kunna motar, ko kafin Ameesha ta yi magana sai ganin motar Abba suka yi.

Cikin sauri Dr ya fito yana gaida Abba cikin yanayi me nuna alamar jin kunya, Abba ya amsa cikin sakin fuska yana tambayarsa su Bobbo

"Duk suna lafiya." Dr ya bashi amsa, kanshi a kasa.

"Naji daɗin zuwanka domin tun jiya naso kiranka, akan ka fara shiri uwata ta tare a ɗakinta, zamanta haka babu amfani, kamar yaushe kake ganin zata tare ɗin?"

Shiru Dr ya yi, har yanzu kanshi a kasa, bai nuna alamar zai yi magana ba. Duk dai a zuciyarshi
Sosai  ya ji dadin maganar Abba, don dama haka yake so kuma ga damar ta samu.

"Ko akwai matsala ne?" Abba ya tambaya gani shirun ya yi yawa

Har yanzu kanshi a kasa yake, yayin da ya kai hannunshi yana shafo kanshi

"To Abba, amma akwai wasu yan gyare-gyaren da zan yiwa bangaren ta, nan da sati biyu zafi kyau a bari har na k'arasa." Cikin ladabi ya yi maganar.

"Allah ya kaimu." Daga haka suka yi sallama.

_*YAR MUTAN RANO*_

Continue Reading

You'll Also Like

7.2K 156 24
It's classification day for Riley. he is finally 18 but when he gets his results things turn for the worst quickly when he has to stay with his broth...
16.2K 2.5K 19
ආදරේ කියන්නෙ හුත්තක්. එච්චරයි __සිතුම් ආකාෂ් ෆ්‍රනෑන්ඩෝ
42.6K 995 6
Hiroki has recently discovered that the four women he once knew and loved, his girlfriend (Nao), sister (Kanoko), best friend (Ayumu), and mom (Kaede...
8.3K 272 56
WOC SERIES SAMPINGAN XAVIER ADREAN X DAHLIA ARYANA Dahlia Aryana. Dipaksa bekerja di kelab malam oleh ibu kandungnya sendiri. Berhari-hari dipaksa me...