SANGARTA COMPLETE

By ZulayheartRano89

122K 6.6K 89

labarin soyayya da ban tausayi More

part 1
BABI NA BIYU
BABI NA UKU
BABI NA HUDU
BABI NA BIYAR
BABI NA SHIDA
BABI NA BAKWAI
BABI NA TAKWAS
BABI NA TARA
BABI NA GOMA
BABI NA SHA DAYA
BABI NA SHA BIYU
BABI NA SHA UKU
BABI NA SHA HUDU
BABI NA SHA BIYAR
BABI NA SHA SHIDA
BABI NA SHA BAKWAI
BABI NA SHA TAKWAS
BABI NA SHA TARA
BABI NA ASHIRIN
BABI NA ASHIRIN DA DAYA
BABI NA ASHIRIN DA BIYU
BABI NA ASHIRIN DA UKU
BABI NA ASHIRIN DA HUDU
BABI NA ASHIRIN DA BIYAR
ASHIRIN DA SHIDA
ASHIRIN DA BAKWAI
ASHIRIN DA TARA
TALATIN 30
TALATIN DA DAYA
TALATIN DA BIYU
TALATIN DA UKU
TALATIN DA HUDU
TALATIN DA BIYAR
TALATIN DA SHIDA
TALATIN DA BAKWAI
TALATIN DA TARA
TALATIN DA TARA
ARBA'IN
ARBA'IN DA DAYA
ARBA'IN DA BIYU
ARBA'IN DA UKU
ARBA'IN DA HUDU
ARBA'IN DA BIYAR
ARBA'IN DA SHIDA
ARBA'IN DA BAKWAI
ARBA'IN DA TAKWAS
ARBA'IN DA TARA
HAMSIN
Complete

ASHIRIN DA TAKWAS

2.1K 127 1
By ZulayheartRano89

*SANGARTA*

                      ©
            *ZULAYHEART RANO*
My Wattpad username *ZulayheartRano89*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

_*Wannan page din sadaukarwa ne ga NAFEESA ANKERH (mr korafi) na sadaukar maki da shi ki yi yadda zaki yi dashi idan ma kika ce kar kowa ya karanta wannan ikon ki ne, ni dai kawai a barnin in inke yin typing a time da na samu dama hhhhhhhhh!, Fatan Alhairi a gareki Zulayheart Rano tana yinki sosai*_ 😍😍

                       *28*

Daddaɗar muryarta ne ya ratsa kunnuwansa, musamman yadda ta faɗin sunan sai ya ji ta saukar masa da kasala, dadingushi kuma yadda ta lafe a jikinsa, sai wani feeling wanda tunda yake da Meesha duk fadawa jikinsa da ta keyi, bai taɓa jin irin saba, gyara mata zama ya yi a maimakon da da yake zameta daga jikinsa ya ce

"My Meesha ya ki ke?"

Bata ce komai ba sai lumshe ido da ta yi, fuskarta har yanzu da murmushi, Meena kam tsayawa ta yi tana kare masu kallo don yadda Dr ya yi ko wanda bai san SO bane ya gansu to zai iya shaida su ɗin masoyan junane, murmushin farin ciki ta yi a ranta tana faɗin

"Alhamdulillah! Ashe Dr ma yana son Meesha Amma wannan abu ya min daɗi."

Ganin hankalin Dr yana ga Ameesha bai masan da wata Meena ba sai ta ɗan gyaran murya ta ce

"Dr ina wuni! An daura aure lafiya?"

Wata kunya ce ta kamashi, don da farko yaga lokacin da suka shigo tare da Meena ɗin, amma tunda Meesha ta matsa inda yake sai ya manta da komai ya maida hankalinsa kan Ameesha.

"Lafiya lau Meena ya kuke?"

"Duk muna lafiya." Ta bashi amsa tana tafiya.

Meena tana wucewa ya maida hankali kan Meesha da ke ta daddana wayar Dr ɗin. Ya ce

"My Meesha zaki bini gidanmu?"

Da sauri ta daga kai alamar "eh!"

Murmushi ya yi ya ce "to bari Abba ya dawo, sai na kaiki wajen Nenne ku gaisa." Ya ida maganar dai dai da zuwan Meena, abin motsa baki ta shiryo masa.

"Thanks Meena sannu da k'ok'ari."

"Your are welcome!" Ta faɗa tana tafiya. Shi Dr tunda Ameesha ta wanzu kusa da shi sai ya nemi yunwa ya rasa, don kasancewarta kusa da shi ba karamin farin ciki ne a gare shi ba.

Kallon ta ya yi tana ci gaba da danna wayarsa, cikin zuciyarsa fadi yake

"Ina ma ace Ameesha tana cikin tunanin ta aka daura masu aure! Lallai yasan da ace tana tunanin ta, to yau da abin ya fi masa jin dadi, amma a haka ma yana farin ciki, yana godiya ga Allah."

Dr ya manta da komai ya dauki lokacin da kacokan ya dankawa Ameesha, sam ya manta a gidan surukai yake, soyayya kawai yake nuna mata irin mai tsayawa arai dinnan, ya yin da ita kuma ta wani lafe a jikinsa kamar wani ya ce zai raba su, bai tashi farga ba sai da ya ji kiran sallar magriba, ɗago da ita ya yi yana faɗin

"Meesha time for prayer, zan je masallaci."

Da kallo take binsa don bata fahimci inda maganar sa ta dosa ba, ganin zata bata masa lokaci har ya rasa jam'i yasa ya kira Meena yana sanar mata to zo ta tafi da Meesha, babu bata lokaci sai gata, da wayau Dr ya samu ya guje mata.

****

Aneesa kam tana shiga dakin wani sabon kuka ta fashe da shi, zuciyarta tana wani irin zafi tana jin kishin Dr fiye da komai, zata iya yin komai don ta hana Dr zama da amaryar sa, yadda take kukan Ni kaina sai da na tausaya mata, don *kishiya ko ta kashin dankali ne babu daɗi*  balle wacce aka auro don ku zauna a karkashin inuwar mutum ɗaya.

Ganin kukan ba shi ne solution ba sai ta jawo wayarta tare da dannawa Rukky kira, bugu biyu kuwa Rukky ta amsa

"Hello k'awata!" Rukky ta faɗa tana gyara wayar a kunnenta.

Shiru Aneesa ta yi har sai da Rukky ta yi magana sau uku kana ta iya sauke nannauyan ajiyar zuciya ta ce

"K'awata babu lafiya fa!"

Zaro ido Rukky ta yi kamar Aneesa tana kallonta baki har yana rawa ta ce

"Mai ya faru? Da ga jin muryar ki nasan babu lafiya faɗa min mai ya sameki?"

"Dr ya yi aure." Ta yi maganar cikin rawan murya.

"Aure! Kan uban... Rukky ta mulmulo wani katon ashar, ke Aneesa anya kuwa kin san me kika faɗa min?"

"Ce maki na yi Dr ya yi aure." Wannan karon tare da hawaye maganar ta k'arasa fitowa.

"Amma kuwa an yi mara mutunci, yanzu don Allah duk son da kike masa shi ne zai saka maki da kishiya? Lallai na yarda da ake cewa *namiji dan kunama* to ke yanzu wane mataki kika ɗauka?"

"Hmmmm! Wane mataki zan ɗauka kuwa, Nenne ce fa da bakinta ta sanar min da maganar, abin takaici ma wai har yau kwana biyu da ɗaurin auren fa, saboda ranin hankali wai bai san an yi masa auren ba, ki ji fa kamar shi ɗin yaro ne da za'a masa dole."

Mtsss Rukky ta ja tsaki ta ce

"Kina nufin haka zaki zuba masa ido?"

"To ya zan yi Rukky? Kuka kawai nake yi, amma mutumin nan haka ya tsallakeni  ya yi tafiyar sa wajen ta."

"Allah ke Aneesa wani time gaki kamar  wayayya ashe ba haka ba ne. To bari ki ji wallahi da Ni ce ke sam bazan damu da lamarin sa ba, balle har in damu da lamarin aurensa, domin kuwa kamar wata dama na samu in yi yadda na ga dama da rayuwata." Rukky ta yi shiru don jin me Aneesa zata faɗa.

"In fita harkar Asmad hmmmm! Gaskiya wannan ne da kamar wuya gurguwa da auren nesa,  kince na samu dama ban gane nufin ki ba? Wacce irin dama kenan?" Aneesa ta yi tambayar cike da rashin fahimta.

"Dallah ke wallahi kina da matsala fa."

"Gidan haya ce Ni." Aneesa ta bata amsa cikin jin haushi da maganar Rukky din.

"Ki bari zan shigo Kano rana ita yau, wannan maganar tafi gaban yinta a waya, fatan kina ci gaba da shan mugungun nan?"

"Suna nan ina sha, duk da dai zubar da ciki bai min rana ba, ina gudun na tsufa da wuri, sai gashi tun ba aje ko ina ba an samu matsala."

"Karki damu fa komai zai warware, matuk'ar dai muka bishiyoyi a sannu, ki tattara lamarinsa ki watsar nan da sati biyu, zaki ga canji ita ɗin banza."

"Kai wallahi Rukky bana jin zan iya barin ma wata Hamma, domin shi ɗin ba fa irin sauran mazan da kika sani bane, bazan iya barin Hamma."

"To na ji karki rabu da shi amma ki ɗauki shawarata ki rika tada masa hankali sam karki raga masa sam."

"Tabbas haka zan yi ko dan na kwatowa kaina yanci, zan nuna masa ainahin Aneesa." ta bata amsa cikin tabbatar mata da  zata iya aika abin da ya fi haka.

'''(Allah ka shirya mu Ubangiji kasa mufi karfin zukatanmu, Allah ka rabamu da aikin danasani, Aneesa kin yi asara tunda dai ke har kullum idan kika samu matsala kawa kike fara sanarwa, duk shawarar da ta baki shi kike dauka  wata rana da idonki zaki yi hawaye. Allah ya tsaremu ya tsare mana imanin mu.)'''

Karfe takwas da mintina Dr ya koma gida, domin sai da ya biya wajen Hafiz a falo ya samu Aneesa zaune ko sallamar da ya yi kin amsawa ta yi sai hararar da ta rika zabga masa, murmushi kawai ya yi ya wuce bedroom ɗinsa ya canza kaya sannan ya kuma dawowa falon harlau dai tana zaune wajenta ya nufa ya zauna tare da faɗin.

"Sannu da gida kanwata." Cikin tsokana ya yi maganar.

Turo baki ta yi ta juyar da kai gefe, don haushi yake bata

"Allah sarki kanwata fushin ne har yanzu Allah dai ya huci zuciyarki!"

Shiru ta masa har lokacin, ko juyo da kai taki yi

"Ina dai kara bada hak'uri adaure ayi min koda magana ne kila ko baki sanyi." Cikin sigar lallashi yake maganar.

"To ina ruwan biri da gada! Nifa wallahi bana son sanabe kai Hamma kana tunanin akwai sauran abin da zaka faɗa min!" A fusace ta dire maganar.

"Yi hakuri yanzu dai kawo karshen ci abinci?"

"Bana jin yunwa?" Ta bashi amsa a takaice.

"Ban gane mai kike nufi ba, rabon ki fa da abici tun safe baki tsoron wani ciwon ya kamaki?"

"Eh! Ta bashi amsa kai tsaye.

Gyada kai ya yi ya ce "da da kyau gashi kuma nima ɗin yunwa nake ji ya za'ayi da ni?" Ya yi tambayar yana kashe mata ido ɗaya.

Karamin tsaki taja ta ce "kai da ka je gidan amarya kuma mai zai sa kazo kana tambayata abinci?" Cike da tsiwa ta ƙarashe tambayarsa.

Mik'ewa ya yi sannan ya saki  Murmushi mai birgewa ya ce
"Saboda naki na saba ci,  amma wallahi yammata kin haɗu fa,  aikinki yana kyau  ina son irin wannan tsiwar, ya yi maganar yana kai hannu kan bakinta.

Kuka Aneesa ta fashe da shi cikin kunar rai da maganar shi, don a nata tunanin ya maidata wata mara lissafi ne, bai san irin mugun kishin sa da take ji bane shi yasa.  Amma a fili sai ta ce

"Hamma dama don ka riƙa walak'antani ka yi aure? Tun kafin amaryar ta tare har ka soma faɗa min magana, har ka fara nuna baka damu da damuwa ta ba?" Ta yi maganar tana mik'ewa tare da soma tafiya.

Cikin zafin nama ya rikota ta faɗa jikinsa gam ya riketa, hannu saya tare da ɗago fuskarta ya ce

"Sam ba shi ne dalilin aurena ba Aneesa ki yi hakuri kar kisa wannan a ranki har ya zame Mali matsala, insha Allahu ni  ASMAD na dauki maki alk'awari ba zan taɓa walak'antaki ba." Cikin sanyin murya wacce a ke kwantarwa da mutum hankali ya ke maganar.

Sun ɓuro baki Aneesa ta yi ba tare da ta ce komai ba.

Mu je in haɗa  maki te...




_*YAR MUTAN RANO*_

Continue Reading

You'll Also Like

63.3K 4.3K 47
مزيج من المغامرات المختلفة سواء مغامرة حقًا أو مجرد كلمة. " هــاريـكـا " بهدف الاستفادة وليس الاستمتاع فقط، بإذن الله تستفيد حتى لو ٥٠٪ معلومات ديني...
18.3K 507 22
Camden Moore is a referee making waves in the WSL...she has many ups and downs...trying to navigate life...she clashes with a certain blonde arsenal...
107K 4.9K 38
Poonam Chaudhary, a girl from a middle class family got married to the guy who scares her to the core. Kaushal Mishra, husband of Poonam and possesse...
14.4K 685 77
"ေမာင့္ေျကာင့္ပဲ ငါအျကိမ္ျကိမ္ငိုေျကြးခဲရသလို' ေမာင့္ေျကာင့္ပဲငါခဏခနျပံဳးခဲ႔ရဖူးလို့ ေမာင့္ကိုငါမမုန္းပါဘူး" ...