WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)

De PrincessAmrah

51.5K 3.5K 52

Zazzafar shari'a ce a cikinsa, wacce take kunshe da rikici da tashin hankali. Me ya sa rashin 'yancin kai ya... Mais

01 Soyayya
02 Boyayyen al'amari
BABI NA UKU
BABI NA HUDU
BABI NA BIYAR
BABI NA SHIDA
BABI NA BAKWAI
BABI NA TAKWAS
BABI NA TARA
BABI NA GOMA
BABI NA SHA DAYA
BABI NA SHA BIYU
BABI NA SHA UKU
BABI NA SHA HUDU
BABI NA SHA BIYAR
BABI NA SHA SHIDA
BABI NA SHA BAKWAI
BABI NA SHA TAKWAS
BABI NA SHA TARA
BABI NA ASHIRIN
BABI NA ASHIRIN DA DAYA
BABI NA ASHIRIN DA BIYU
BABI NA ASHIRIN DA UKU
BABI NA ASHIRIN DA HUDU
BABI NA ASHIRIN DA BIYAR
BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI
BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS
BABI NA ASHIRIN DA TARA
BABI NA TALATIN
BABI NA TALATIN DA DAYA
SHARHI

BABI DA ASHIRIN DA SHIDA

1.2K 93 2
De PrincessAmrah

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

                

                   {~78~}

_wannan shafin tukuici ne gareki my dear *Ummu Shureym,* hak'ik'a ke masoyiya ce ta gaske, Allah yabar soyayya da k'auna ya raya mana Shureym bisa tafarkin sunnah. Amrah LYSM #Onelove#_

*****

      Mamaki fal a fuskar Umar yake kallon mutanen dake cikin matrix d'in,
   A hankali mutumin ya fito bayan ya kashe motar,
   Murmushi yayi tare da mik'a masa hannu yace
    "Assalamu alaikum",
   Shima hannun ya mik'a masa amma kuma bai amsa sallamar ba saidai kallo kawai da yake binsa dashi.

     "Ka daina mamaki Barr. Umar, nine d'in dai Dr. Rafiq wanda kukayi dashi zaije kotu ya bayar da shaida sai kuma wani dalili ya hana, amma yau a shirye yake daya bayarda shaidar duk abunda ya sani kuma tsakaninshi da Allah".

    Murmushi Umar yayi yace
   "ina ka shiga Dr. Rafiq? Aimu munyi zaton ko kaima sun siyeka da kud'i ne, tuni aka yanke hukunci amma mun d'aukaka k'ara, yanzu haka shirin tafiya kotun muke saboda yaune zamu fara zama".

   Muryar mace ya jiyo tace
   "Ba za'a tab'a siye Rafiqu da kud'i ba d'an nan, shari'ar nan tana ransa kawai dai an nuna anfi k'arfinsa ne..." Umman Rafiq ta kwashe duk abunda ya faru ta fad'awa Umar,
   Sultana ma tana tsaye tana saurarensu wani irin dad'i taji a ranta,
   Itakam dama tayi mamakin rashin zuwansa kotun, ta tabbatar da akwai wani babban dalili daya hanashi zuwa lokacin da ake buk'atar ganinshi.

   Har k'asa ta duk'a ta gaishe da Umman Rafiq sannan ta gaishe da Rafiq d'in ma,
      Motarsu suka koma Sultana ma ta koma ta shiga tata wadda su Ummimah ke ciki suna hangen  duk abunda yake faruwa amma kuma basu san kome ake fad'i ba.

   Bayan ta shiga ta labarta masu duk abunda ya faru, hamdala Mama tayi sannan tace
    "Allah majik'an bawa, dama shaidarshi ake nema kuma gashi Allah ya kawoshi, Allah dai ya kawo mana k'arshen wannan shari'ah ya bawa mai gaskiya nasarah",
    "Ameen" su duka suka amsa dashi sannan Sultana ta tayar da motar,
   Umar ne gaba sai Dr. Rafiq a bayanshi,
  Sultana kuma a bayan Rafiq, a hankali suke tafiya har suka isa court of apeal.

     Sun samu motoci da yawan gaske a pake, hakan ya tabbatar ma Umar da cewa su kad'ai ake jira,
   Savoda tun k'arfe takwas akace suzo za'a fara shari'ar yanzu kuma gashi har takwas da rabi ta wuce.

   A hanzarce suka zira rigunansu sannan suka shiga,
    Wuri d'aya su Sultana suka zauna da Umman Rafiq da k'annenshi biyu,
   Sultana da Umar kuma suka tafi inda aka tanada domin zaman lauyoyi.

    Bayan sun zauna baifi da minti biyar ba alk'ali ya iso,
   Mazauninsa ya zauna sannan mai gabatar da k'ara ya tashi ya gabatar.

     "Kotu tana son ganin Aishatu Abubakar wadda ta kawo k'ara da kuma Salmah Abubakar wadda ake k'ara" alk'ali ya fad'a tare da yin d'an rubutu a takarda.

   A hankali Ummimah ta taso ta tsaya cikin akwatin tuhuma,
   Salmah ma tasowar tayi ta tsaya itama a cikin akwatin tuhuma wanda ke kusa dana Ummimah.

    "ba sai an tsaya wani dogon bayani ba, kamar yanda kowa ya sani cewa wannan k'ara ce aka d'aukaka, dan haka zamu so wanda suka kawo k'arar su tashi suyi bayanin dalilinsu na d'aukaka k'arar sannan su bamu hujjarsu ta farko".

     Cike da natsuwa da kamun kai Sultana ta tashi tsaye,
   "Sunana Barr. Sultana Saddam Bakori, a tare dani akwai Barr. Umar Mohd Bashir, mune wanda muka d'aukaka k'ara,
   Dalilinmu na d'aukaka k'ara kuwa shine; an yanke hukunci a zamanmu na kotun daya gabata wanda kuma hukuncin bai mana ba,
   Shine muka d'aukaka k'ara a wannan kotu mai adalci tare da hujjojinmu wanda muke fatan kotu zatayi masu duba ta yanke hukunci ga mai laifi".

    "Kotu ta gamsu da dalilinku na d'aukaka k'ara, tana jiran hujjarku ta farko" alk'alin mai cike da dattako ya fad'a yana kallon Barr. Sultana.

    A kotun data gabata, akwai likita wanda yake shine ya duba Ummimah a lokacin da aka kaita, shine ya tabbatar da fyad'e aka mata,
   Munyi dashi cewa zaije ya bayarda shaida, sai kuma mukajishi shiru baizo ba, kasantuwar dama dashi kad'ai muka dogara yasa aka yanke hukunci bamuda wata hujja,
   To yanzu dai yana kusa kuma ya halarci kotun nan,
   Zanso kotu mai adalci data bani dama domin gabatar dashi dan aji ta bakinshi".

    Kai alk'alin ya jinjina kafin yace
    "Kotu ta baki dama Barr. Sultana".

    Tasowa Dr. Rafiq yayi ya iso inda aka tanadar dominshi,
    Tunda ya taso Gentle ke binshi da kallon mamaki, itakam sam batayi tunanin zaizo ba,
  Hankalinta kuwa ya matuk'ar tashi dan tasan zayyi bayanin duk abunda ya faru.

    Qur'ani aka bashi ya dafa tare da fad'in
    "Nayi alk'awarin zan fad'i gaskiya tsakanina da Allah".

       Sultana ta matsa inda yake tace
    "Dr. Rafiq inaso kayiwa kotu bayanin tun dawowarka daga Lagos ina kaji? Sannan kuma me ya hanaka zuwa kotu domin bayarda shaida?",
    "Ranar dana dawo daga Lagos shine ranar jumu'ah, ko a ranar munyi waya da Barr. Umar kuma na k'ara tabbatar masa da zanzo,
    Kwatsam ina shirin tahowa da rana tsaka wasu mutane suka shigo mana manya manya abun tsoro,
     Cike da fargaba na tambayesu 'me sukazo yi?',
   Basu bani amsa ba saa d'aukeni da mari da babban cikinsu yayi,
    Fitowa sukayi dani daga d'akina, a parlor na tayar sun nannad'e  Ummana da igiya sannan sun nad'e mata bakinta da selotape,
   A lokacin k'annena basu nan,
   Tafiya sukayi damu bayan sun nad'e mana fuskoki dan kar musan inda zasuje damu,
   A wani d'aki suka jefa Ummah ni kuma suka barni a tsakar gida,
   Saida muka kwana biyu a haka sannan suka min bayanin dalilin kamomu da sukayi,
   Sukace 'inhar na kuskura na sake ko waiwayarku barin har inyi tunani bayar da shaida sai sun kashe Ummana',
   Na masu alk'awarin ba zanyi ba, bayan mun dawo gida shine Ummah tace 'kome zai faru saidai ya faru amma sai na bayar da shaida ta amince, tun a ranar mukayi niyyar tafiya amma saboda mun san ana bibiyarmu yasa muka jinkirta vamu taho ba sai jiya,
   Tun jiyan muke neman gidan Bar Umar muka rasa,
      Sai daga baya bayan mun sauka hotel muka tambayi wani mutum shine ya mana bayanin gidan,
    Da safen nan myka nufi gidan shine Allah ya had'amu dasu a hanyarsu ta zuwa nan kotu".

    Cike da gamsuwa alk'ali ya d'aga kanshi.
   Sultana tace
   "Kotu zata so ka fad"a mata duk yanda abun ya faru bayan an kai Ummimah clinic d'inka,
   Sannan kuma abokin aikinka Dr. Khalid ya tabbatarwa kotu a baya cewa clinic d'insa ce kawai dai ya d'aukeka aiki ne, shin ya abun yake?"

      Cikin mamaki Dr. Rafiq ya kalli Barr. Sultana yace
    "Ba gaskiya Dr. Khalid ya fad'awa kotu ba,
    Asibiti dai tamu ce ni da shi muka had'a k'arfi da k'arfi muka bud'eta,
     Ya zuba dukiyarshi nima kuma na zuba tawa, a lokacin ma ni kad'ai nayi niyyar bud'eshi sai ya rok'eni akan yana so mu bud'e tare,
   Saida Ummana ta musa hakan amma daga baya ta amince saboda taga yanda muka shak'u dashi,
   Na amince masa muka bud'e asibin saisa muka saka mata *'KADRAQ CLINIC'* inada hujjar hakan saboda ina tafe da takardun asibitin baki d'aya, wanda shima kuma Dr. Khalid d'in yana dasu, idan ya musa wannan bayanin da nayi sai ya kawo nashi wanda suka tabbatar da cewa clinic d'inshi ce shi kad'ai" ya duk'a k'asa ya d'auko 'yar jakarsa,
    A hankali yake d'aga takardu har yakaiga ta asibitin,
   Mai gabatar da k'ara ya karb'i takardar tare da isar da ita ga alk'ali.

   Bayan ya karb'a ya dudduba yayi rubutu a takardarsa sannan ya dawo da ita ga Sultana,
    "Wannan bayanin da hujja da Dr. Rafiq ya kawo kad'ai ya isa ya tabbatarwa kotu da cewa Dr. Khalid mak'aryaci ne, idan kuwa shi mai gaiskiya ne nasan yana kusa, zai iya kawowa kotu takardar da zata tabbatar da asibitinsa ce ita kad'ai".

    "Objection my lord!" Barr. Sa'eed ya fad'a,
    "Barr. Sultana tana k'ok'arin ta canja salon shari'ar nan, bayan kuma ba akanta muke ba, tana k'ok'arin tozarta Dr. Khalid ta hanyar k'aryatashi".

   "K'orafi bai karb'u ba, savoda Barr. Sultana k'ok'ari take dan tabbatarwa kotu da gaskiya ne Dr. Rafiq ya fad'a wanda ta wannan hanyar ce kotu zata san ganskiyar wannna lamari, Barr. Sultana kici gaba" ya miyar da kallonshi ga Sultana dake murmushin jin dad'i.

     "Ko zan iya ganin Dr. Khalid da takardarshi wadda sata tabbatar da cewa asibitinsa ce?".

    Cikin raba ido Dr. Khalid ya taso har ya iso kusa da Dr. Rafiq,
    "Kotu tana buk'atar ganin takardar kamar yanda na fad'a a baya" Sultana ta fad'a tana kallon Dr. Khalid.

    Cikin in ina yace
    "Nn.nn...banzo da ita ba, sssaboda banyi zaton za'a tambayeni ba",
    "Ka kwantar da hankalinka ka daina wannan in inar Dr. Khalid,
   A ina rakardar take yanzu?",
     "Tttttana can gida banzo da ita ba" ya bata amsa,
     "Kotu zata so ganin wannan takarda kuwa" ta jiya ga alk'ali tace
    "Ya mai girma mai shari'ah, ina neman alfarma da kotu ta d'aga wannan shari'ah zuwa goma ga watan biyu shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai, a wannan ranar muke buk'atar Dr. Khalid ya kawo mana wannan takarda, nagode ya mai shari'ah".

     Rubutu alk'alin yayi mai d'an tsawo kafin ya d'ago kanshi yace
    "Kotu ta yarda da alfarmar da Barr. Sultana take nema,
  Ta d'aga wannan shari'ar har saa gima ga watan biyu shekara ta dubi biyu da goma sha bakwai, koooootu!" Ya buga guduma tare da mik'ewa ya fice.





  _gaisuwa gareki *Basman mai sanyinta,* nagode da kulawa sosai, Allahu yabar zaman tare. ILYSM._



°•°AKA°•°Princess Amrah😘
                  NWA

Continue lendo

Você também vai gostar

18.7K 732 31
MAFIA STEP - SISTER OF BANGPINK
50.1K 1.4K 81
"𝐻𝑎𝑛𝑠𝑒𝑜𝑘𝑎𝑎,𝑎 ℎ𝑒𝑎𝑟𝑡𝑙𝑒𝑠𝑠 𝑝𝑠𝑦𝑐ℎ𝑜𝑝𝑎𝑡ℎ 𝑙𝑖𝑘𝑒 𝑦𝑜𝑢 𝑑𝑜𝑒𝑠𝑛'𝑡 𝑑𝑒𝑠𝑒𝑟𝑣𝑒 𝑡𝑜 𝑓𝑒𝑒𝑙 𝑙𝑜𝑣𝑒 𝑤𝑖𝑡ℎ 𝑠𝑜𝑚𝑒𝑜𝑛�...
17.8K 198 21
⚠️رواية منحرفة خاصة للبالغين⚠️ وَقَعْتُ بِحُبِ رَجُلٍ ثَلٰاَثِينِيٖ قَاٰمَ بِتَرْبِيَتِيٖ إِنَكَ مُتَزَوِجْ يَاسَيِدْ جُيُوٰنْ قَتَلَ كُلْ مَنْ حَا...
628K 9.7K 48
Lost, Lose (Loose Trilogy #1) She's a girl of hope, Lisianthus Yvonne Vezina. A teen-year-old girl who focused on her goal... to strive. But everyth...