WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)

By PrincessAmrah

51.5K 3.5K 52

Zazzafar shari'a ce a cikinsa, wacce take kunshe da rikici da tashin hankali. Me ya sa rashin 'yancin kai ya... More

01 Soyayya
02 Boyayyen al'amari
BABI NA UKU
BABI NA HUDU
BABI NA BIYAR
BABI NA SHIDA
BABI NA BAKWAI
BABI NA TAKWAS
BABI NA TARA
BABI NA GOMA
BABI NA SHA DAYA
BABI NA SHA BIYU
BABI NA SHA UKU
BABI NA SHA HUDU
BABI NA SHA BIYAR
BABI NA SHA SHIDA
BABI NA SHA BAKWAI
BABI NA SHA TAKWAS
BABI NA SHA TARA
BABI NA ASHIRIN DA DAYA
BABI NA ASHIRIN DA BIYU
BABI NA ASHIRIN DA UKU
BABI NA ASHIRIN DA HUDU
BABI NA ASHIRIN DA BIYAR
BABI DA ASHIRIN DA SHIDA
BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI
BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS
BABI NA ASHIRIN DA TARA
BABI NA TALATIN
BABI NA TALATIN DA DAYA
SHARHI

BABI NA ASHIRIN

1.4K 103 1
By PrincessAmrah

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

               
                   {~72~}

    Cikin izzah da tak'ama Barr. Sa'eed yace
    "Aishatu shin a cikin kalaman da Salmah tayi ko akwai maganar data fad'a wadda kike da ja akanta?",
    Da hannunta ta share hawaye jikinta ya fara rawa saboda yanda taga an tsura mata ido,
    "Ehh...ehh a..akwai" ta fad'a cikin rawar murya.

   Murmushi Barr. Sa'eed yayi yace
    "Ki kwantar da hankalinki ki daina rawae murya indai da gaske kinada gaskiya ba k'arya zaki fad'a ba".

     "Objection my lord!" Barr. Sultana ta fad'a k'ufule,
     "Bai kamata Barr. Sa'eed yana fad'in wannan kalaman ga Aishatu ba, ya kamata yayi la'akari da yanayin yawan mutanen wurin nan ne yasa take rawar jiki da rawar murya",
     "Barr. Sa'eed a kiyaye" alk'ali ya fad'a yaci gaba da kallonsu.

    "uhm, kr nake sauraro" ya fad'a a hankali.

    "Kusan duk maganganun data fad'a k'arya ne, nasan dai tana yimin wasu abubuwan idan taga inada buk'ata, amma maganar da tace ita ke d'aukar nauyinmu wallahi k'aryane, babana bai rageni da komai ba, kusan duk wata ko baya da kud'i sai ya ranta ya turo min, sannan kuma da tace na canja hali wannan duk halayenta ne, babu inda nake zuwa, idan ma na fita daga room d'inmu to bazan wuce room na kusa da namu ba inda k'awayena Zarag da Rabiatu suke ba".

     "Ina su k'awayen naki suke a halin yanzu? In da gaskene ai ya kamata ace sunzo nam kodan su bada wannan shaidar ga k'awarsu".
    Jikin Ummimah ya hau rawa saboda rashin halartar su Rabiatu kotun, tasan ba lallai bane a yarda da maganarta.

    "Gamu" Zarah da Rabiatu suke fad'a daidai lokacin da suka shigo cikin kotun.

    Ajiyar zuciya ta sauke farin ciki bayyane a fuskarta, hamdala tayi ga Allah a lokacin da suka iso inda ake son ganinsu.

     Qur'ani aka basu sukayi rantsuwa da zasu fad'i gaskiya sannan cikin rashin jin dad'in zuwansu Barr. Sa'eed yace
    "Kune k'awayen nata?",
    "Ehh mune"  suka had'a baki wurin fad'i.

     Baki d'aya yama rasa tambayar da zayyi masu, saboda sam bayyi tunanin zasuzo ba, dan saida ya tabbatar da babu su a cikin kotun sannan ya nemi yana son ganinsu.
    Sai daga baya wata fasaha ta fad'o masa yace
    "Wai da gaske wurinku Aishatu take zuwa wani lokaci?",
    "Ehh da gaske wurinmu take zuwa duk lokacin da Gentle ta fita tayi dare, wani lokacin ma a d'akinmu take kwana saboda tace ba zata iya kwana ita kad'ai ba" Rabiatu ta bashi amsa.

    Shiru ya d'anyi kafin yace
    "To idan da gaske ne mesa wani lokacin idan bata d'akinku kuke zuwa ku tambayi Salmah inda Aishatu taje? Kenan hakan ya tabbatarda ba kowane lokaci kuma d'in kuka san inda take ba".

    Zarah tayi caraf tace
    "So d'aya ne tak hakan ta kasance, kuma ranar ma ta fita neman Gentle ne akan tazo suyo karatu dan exam d'in da zamuyia washe gari mai wahala ce, tun fitar da tayi shine vata dawo ba har mukaje nemanta room d'insu".

     Kallonshi ya miyar ga alk'ali yace
    "Ya mai girma mai shari'ah, da wannan bayanin da k'awayenta sukayi ya isa ya tabbatarwa kotu da cewa ba kowane lokaci ne take tare da k'awayentan da take cewa suna tare always ba, kenan akwai gyara a maganar Aishatu saboda gashi k'awayenta sun fad'a da bakinsu, ta masu k'aryar zataje ta nemi Salmah domin suyi karatu, amma kuma Salmah ta dawo tace ita batama ga Aishatun ba, wannan ya tabbatar da cewa ta tafi yawo kenan"
   Ya juya gasu Zarah yace
    "Zaku iya tafiya ku zauna".

     "Amm kafin su tafi su zauna, ko lauyoyi masu kare wadda take k'ara sunada tambayar da zasuyi masu?" Alk'ali ya tambaya.

    "Ehh akwai ya mai shari'ah" barr. Sultana ta fad'a tare da tasowa cike da natsuwa ta iso inda suke.

     "Bayan kun tambayi Salmah inda Aishatu take, zaku iya tuna amsar data baku?",
    "Ehh zan iya tunawa,
    Saida ta bimu da kallon banza sannan tace 'idan har bamu k'yaleta da tambayar inda Aisha take ba wallahi sai ta saka an mana abunda tasa akaima Aisha', duk da vamu san ko menene ba amma hankalinmu ya tashi, babu yanda muka iya dole muka bar mata d'akin baki d'aya ranmi a dagule yake".

     "Well" Sultana ta fad'a,
    "To daga nan ku kuma wane irin mataki kuka d'auka?".

   Rabiatu tace
    "Babu yanda muka iya duk da tashin hankalin da muka shiga, mun nemeta a duk blocks d'in hostel amma bamu sameta ba, hakan yasa muka koma room d'inmu amma babu wadda ta iya yin bacci a cikinmu,
   Washe gari tun gari bai gama wayeba muka fita waje nemanta,
   Acan muka tsinceta cikin jini nesa da hostel,
  Hankalinmi ya tashi muka d'auketa muka kaita school clinic,
  Bayan sun dubata sukace suma ciwonta yafi k'arfinsu saidai si kaida wata asibiti,
   Tare muka tafi da ita ta dad'e bata farfad'o ba,
     Likitan daya dubata ya tabbatar mana da fyad'e ne aka mata kuma an illatata sosai, yace mana ya rubuta a takarda zai bamu mu tafi da ita idan ta samu sauk'i,
   Amma kuma sai muka shafa'a, shi bai bamu ba muma kuma mun manta bamu karb'a ba,
   Saida aka dawo hutu ne akace wai an koreta, kuma harda gwada mana takardar asibitin anyi amma kuma sab'anin waccan ta farkon wadda bamu san dalilin canzata ba".

    Barr. Sultana zata sake magana kenan alk'ali yace
    "Kotu zata so ganin likitocin da suka dubata a asbitinsu,
   Sannan kuma zataso taga ma'aikatan School clinic d'insu domin su fad'a mana 'mesa sukace ciwonta yafi k'arfisu?' Saboda ta yiwu su abunda suka gani daban, zamuso jin komai daga bakinsu idan suna kusa".

     Cike da ladabi Sultana tace
    "Likitan da yayi mata aikin mun buk'aceshi da yazo amma kuma yayi tafiya zuwa Lagos, ga wannan takardar" ta mik'awa wanda ya gabatar da k'ara domin ya isar da ita ga alk'ali,
    "Takarda ce wadda ta tabbatar da likitan baya nan, yaje wani course ne amma ya tabbatar da yau saura kwana hud'u ya dawo, ranar Friday kenan,
    Sannan kuma bamuyi magana da ma'aikatan School clinic d'inba,
   Muna rok'on kotu mai albarka data d'aga wannan shari'ar har sai zuwa next week, wanda insha Allahu a ranar ma'aikatan zasuzo, shima kuma likitan kafin nan ya dawo".

   Shiru alk'ali yayi bayan yayi 'yan rubuce rubuce sannan ya d'ago kanshi yace
    "Kotu ta d'aga sauraron wannan shari'ar har sai ranar litinin, bakwai ga watan d'aya shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai",
   Ya buga tuburonshi da guduma tare da fad'in
     "Kooootu!" Yana mik'ewa kowa ma ya mik'e

***

       Bayan sun fita daga kotu ne Gentle ta ringa watsawa Ummimah harara cike da tsana,
   Zarah da Rabiatu sukayi tsaki tare da fad'in
    "Ta Allah bata mutum ba, kuma insha Allahu sai munyi nasarah, Allah baya goyon bayan azzalumi".

     K'ara k'ufule Gentle sukayi,
    Momy'nta taja hannunta da sauri suka tafi dan tasan halin Gentle tsaf zata iya yin dambe dasu a wurin, kuma idan har tayi to mutane zasu tabbatar da cewa da gaske tasa anyima Ummimah fyad'e duk da yanzu ma wasu sun fara gasgatawa.

    Kallon Rabiatu Ummimah tayi tace
    "k'awayen kun rufa min asiri sosai da kukazo, inda ace bakuzo ba da bansan yanda zanyi ba, banyi tunanin zakuzo ba gaskiya".

    Zarah tace
    "Ai dole ne a garemu muzo Ummimah, an cuceki kuma aka nemi a hanaki kuka,
     Jiya muna Hostel mukaga text d'in lawyer d'inki, ta mana bayanin komai kuma ta nemi in da hali anada buk'atarmu a kotu,
    Kinsan akwai nisa daga Jalingo zuwa Katsina, tun da sassafe muka taso amma bamu iso da wuri ba har akayi nisa da shari'ar, Allah yasa daidai muna zuwa muna ji ana nemanmu".

   Ummimah tace
    "Kuma fa haka kawai na bata number d'inki, saboda kin san yanzu banda waya,
   A wata takardata ce dana tab'a ajiye number'n sanda zan miki call me back,
    Lokacin da zamu baro gida na had'ata cikin jikarmu,
   Ashe da rabon zatayi amfani".

     "Aikuwa dai kin gani".
  Da wannan firar Sultana ta samesu,
     Takardar dubu d'aya ta zaro a jakarta Ta mik'awa Mama tace
        "Mama ku hau  napep da wannan ku tafi gida, ni inada aiki da yawa a Office".

    Karb'a mama tayi tace
    "To mungode sosai Allah yayi albarka,
   Sai kun dawo d'in" suka tafi yayinda Sultana kuma ta koma Office d'inta.

    _ina cigiyar *Sadiya Afka* nikam, ko ina ta shige oho? Gashi ba'a samun lambarta idan an kira, Allah dai yasa lafiya inji Amrah._




°•°AKA°•°Princess Amrah😘
                  NWA

Continue Reading

You'll Also Like

Khalifa By laiba

Mystery / Thriller

2.1M 118K 56
✵ featured ~ ❝Once upon a time in Baghdad, a street girl teaches the Khalifa of the kingdom why a king needs a queen.❞ ✵ Started: June 5, 2021. Comp...
5.6K 268 20
In which flora mikaelson is reborn in to Harry Potter older twin sister Kol mikaelson x fempotter Please leave a comment Love y'all-rose No mine
626K 9.6K 48
Lost, Lose (Loose Trilogy #1) She's a girl of hope, Lisianthus Yvonne Vezina. A teen-year-old girl who focused on her goal... to strive. But everyth...
6.1K 363 6
"𝘿𝙤𝙣'𝙩 𝙩𝙤 𝙩𝙝𝙞𝙨 𝙥𝙡𝙯 , 𝙄 𝙖𝙢 𝙨𝙤𝙧𝙧𝙮" She cried but her 𝙨𝙩𝙚𝙥 𝙢𝙤𝙩𝙝𝙚𝙧 didn't show any mercy and beat her from 𝙄𝙧𝙤𝙣 𝙧𝙤𝙙...