WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)

By PrincessAmrah

52.1K 3.5K 52

Zazzafar shari'a ce a cikinsa, wacce take kunshe da rikici da tashin hankali. Me ya sa rashin 'yancin kai ya... More

01 Soyayya
02 Boyayyen al'amari
BABI NA UKU
BABI NA HUDU
BABI NA BIYAR
BABI NA SHIDA
BABI NA BAKWAI
BABI NA TAKWAS
BABI NA TARA
BABI NA GOMA
BABI NA SHA DAYA
BABI NA SHA BIYU
BABI NA SHA UKU
BABI NA SHA HUDU
BABI NA SHA BIYAR
BABI NA SHA SHIDA
BABI NA SHA TAKWAS
BABI NA SHA TARA
BABI NA ASHIRIN
BABI NA ASHIRIN DA DAYA
BABI NA ASHIRIN DA BIYU
BABI NA ASHIRIN DA UKU
BABI NA ASHIRIN DA HUDU
BABI NA ASHIRIN DA BIYAR
BABI DA ASHIRIN DA SHIDA
BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI
BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS
BABI NA ASHIRIN DA TARA
BABI NA TALATIN
BABI NA TALATIN DA DAYA
SHARHI

BABI NA SHA BAKWAI

1.4K 96 0
By PrincessAmrah

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

               
                   {~69~}

       Washe gari da sassafe suka kama haramar zuwa aiki kamar yanda suka saba,
     Kai tsaya Gobarau academy duka zarce sukayi dropping d'in Hafsa sannan suka wuce nasu aikin.

    Kasantuwar weekend akayi aiki ya taru masu sosai a Office musamman ma Umar, hakan yasa bai shigar da maganar ba sai washe gari,
     Safiyar talata kam babu b'ata lokaci ya shigar da case d'in su Ummimah, aka kuma ce nan da sati d'aya za'a shiga kotu.

   Sosai Sultana taji dad'i ta kuma shirya ta tafi gidan su Ummimah dan ta shaida masu halin da ake ciki.

    Masinjan kotu aka aika gidansu Gentle dan yakai sammaci, saboda koda aka fad'i sunanta da sunan iyayenta  kowa ya ganeta, saboda babanta sananne ne sosai kuma yanzu haka ya fito takarar d'an majalissar tarayya.

   Kai tsaye gidan Alhaji Abu Abu ya dosa,
   Sallamah yayi a tangamemen gate d'in gidan amma shiru ba'a amsa ba,
   Saida yayi sallamah sau uku sannan mai gadin gidan ya fito yana taunar asuwaki,
   Hannu masinjan ya bashi suka gaisa sannan yace
   "Meke tafe dakai bawan Allah?",
    "Sak'o ne daga kotu, sammaci ne akace a kawowa masu gidan nan".

   Cike da mamaki mai gadin ya karb'i takardar,
    "Sammaci?" Ya tambayeshi.

   "Ehh sammaci ne, dan Allah a tabbatar da anbawa masu gidan wannan takardar" masinjan ya fad'a tare da juyawa ya tafi.

     Kai kawai mai gadin ya kad'a sannan ya zarce cikin gidan domin ya basu takardar.

    Bayan yayi sallamah yaga Ladi mai aiki tana mopping, mik'a mata takardar yayi yace 'ta bama yallab'ai' sannan ya tafi.

      Saida suka fito karyawa sannan tace
    "Hajia wai ga wannan mai gadi ya kawo yace a bama yallab'ai",
   Bayan ta karb'a tace
   "Alhajina gashi",
Murmushi ya mata yace
   "Bud'e ki karanto min inji".

   A zahiri kuwa ta karanto cewa 'sammaci ne daga kotu ankai k'arar 'yarsu Salmah bisa laifuka da dama'.

    "What!?sammaci? 'Yata aka kai sammaci?",
    Itama Hajiyar tsaye ta tashi tace
    "Lallai wannan munafurci ne? Salmah dake makaranta abunta hankali kwance shine dan rainin hankali za'a kaita k'ara?",
    "Ko tantama babu wannan cinne ne daga mak'iyana, suna so inji kunya akan takarar da zanyi ne",
      "Kaga wai Aisha Abubkar sukayi k'ararta, ga sunan nan a jiki" Momy'n Gentle ta fad'a bayan ta mik'a takardar cike da mamakin wannan al'amarin.

   Karb'a yayi yace
   "Wacece wannan? Aisha?" Tun bai rufe bakinshi ba momy tayi caraf tace
   "Na gane ko wacece, k'awartar nan d'iyar matsiyata ce, saisa tun farko na hanata k'awance da ita amma ta nace lallai sai tayi ita dai tana sonta, wato duk alkhairan da Salmah ta mata da wannan abun zata saka mata? Lallai d'an adam abun gudu ne".

     Cike da b'acin rai Alhaji yace
   "Kenan ma 'yar matsiyata ce ta kai 'yata k'ara? Lallai kuwa reshe zai kife da mujiya, saboda duk abunda take nufinta dashi gareta zai koma, wallahi na rantse sai na d'auko lawyer wanda duk k'asar nan babu kamarshi, sai na nuna masu nafi k'arfinsu, su d'in banza!" Ya rofar da yawu bisa center carpet yace
    "Sai kun wulak'anta I promised" ya jefar da takardar k'asa.

    Mamaki sosai uwar keyi ta d'auki wayarta ta latsa kiran Gentle, bayan ta d'auka ne ta shaida mata duk abunda ya faru,
   Taji tsoro sosai amma a zahiri ta nuna al'ajabinta akan al'amarin,
  Harda kukan munafurci tace
   "kinga illar talakawa Momy, ba irin maganar da baki fad'a min akan kar inyi k'awance da Ummimah ba amma na nace sai nayi, kinga abunda ta bini dashi ko momy?" Ta k'ara fashewa da kukan munafurci, da haka suka kashe wayar bayan uwar ta shaida mata cewa sati mai zuwa za'a fara zaman kotu, dan haka ta hanzarta dawowa gida saboda babanta yace zai d'auko mata babban lawyer,
   Dukda hankalin gentle ya tashi amma sai ta samu sassauci jin lawyer za'a d'aukar mata.

    Sosai take mamakin yanda akayi su Ummimah suka samu lawyer wai harma sukayi tunanin kai k'ararta kotu.

   Wani shu'umin murmushi tayi tare da furta,
    "Mugun abunku gareku zai koma maku, wallahi sai kun k'ask'anta, wato na sarara maku kwana biyu shine zaku d'auki wannan matakin ko? Zakuyi regreting" ta katsa kiran d'aya daga cikin 'yan iskanta,
   Umurtarshi tayi da yaje gidansu Ummimah ya k'ona baki d'ayanshi, yanda zasu mutu kuma ba za'ayi zargin kowa ba saidai ace gobara ce sukayi,
   Da wannan shawarar ta kashe wayarta tana ci gaba da muguwar dariya mai d'auke da ma'anini kala kala.

      Shi kuwa Umar sosai ya miyar da hankalinshi ga bincike, yaje Jalingo har asibitin su Dr. Rafiq, amma bai sameshi ba kasantuwar yayi tafiya zuwa Lagos, kuma sai nan da sati biyu zai dawo,
   Dr. Khalid kawai ya tayar, amma bai tinkareshi da maganar ba yafi so yayi da Dr. Rafiq d'in,
    Phone number d'inshi ya karb'a a wurin wata nurse sannan ya juyo zuwa Katsina.

     Alhaji Abu Abu kuwa yama commisioner na 'yan sanda magana an had'ashi da wani Barrister wanda a duk fad'in k'asar nan babu wanda bai sanshi ba,
   Ya k'ware sosai  a aikinshi, haka kuma fuk shari'ar da zayyi da wasu ba'a winning d'inshi saidai shi yayi winnning mutum,
    Baki d'aya karatunshi ma ba'a k'asar nan yayishi ba, hakan yasa yake da experience sosai akan shari'ah, komai rashin gaskiyar mutum indai ya sakoshi a shari'arshi to sai yayi winning.
   Sosai Alhajin yaji dad'i saboda yasan yanzu kam asirinshi zai rufu, saboda matuk'ar aka kama Gentel da laifin da ake zarginta ti yasan bazai tab'a samun d'an majalisar jiha da yake nema ba.

   Haka Umar ya koma gida ba tare da walwalar kirki ba, saboda jin wai ba yanzu Dr. D'in zai dawo ba, gashi kuma shine kawai hope d'inshi a wannan lokacin, kuma shida dawowa har sai anyi zamab kotu na farko, yasan basuda wani evidence a halin yanzu.
     Zama kawai yayi bisa kujera baki d'aya bashida walwala,
   Kida Sultana ta ganshi haka tasan akwai matsala,
   Inda yake ta zauna tace
   "Sannu da dawowa honey, nasan ka gaji muje kayi wanka kaci abinci",
    Babu musu kuwa ya tashi yabita,
   Ganin a gajiye yake yasa ita da kanta tayi masa wankan,
    Bayan sun fito ta fitar masa da k'ananan kaya jeans bak'i da blue shirt,
   Fita sukayi ta ringa bashi abinci a baki tana faranta masa rai da labarai masu dad'i,
    Saida yayi nat sannan ta goge masa bakinsa  da tissue suka koma d'akinta.

    Bayan taga ya warware sosai tace
    "Honey baka samu likitan bane?",
    Kallonta yayi yace
    "ya akayi kika san haka?".

   Murmushi ta sakar masa sannan tace
    "Wani abu sai bahaushe, ana tambayarshi shima yana tambayarka",
   Shima murmushin ya sakar mata kafin yace
    "wallahi kuwa ban sameshi ba, wai baya nan yaje lagos sai nan da sati biyu zai dawo, gashi kuma kinga saura kwana biyu mu fara zama kotun, ni yanzu damuwata d'aya zamu shiga kuma banida evidence ko d'aya".

   Ajiyar zuciya Sultana tayi tare da cewa
    "Gaskiya kam abun ka damu ne wannan, amma ina ganin ka cire damuwar a ranka, karka cire hope na smaun nasarah tunda ai nasan ba zama d'aya za'ayi ba, sai ka rok'a a d'aga shari'ar har lokacin da zai dawo ku tattauna dashi, kaga duk bayanan da muka samu daga gareshi nasan zasu amfanemu",
    "Ehh hakane wifey, kuma ga lambarshi nan na karb'a so nake sai zuwa dare in kirashi, saboda nasan ta yiwu yanzu he is busy kinsan likitoci, wata k'ila sai dare ne baya komai",
    "To abunma ai yazo da sauk'i, kaga sai kayi magana dashi a waya ka masa bayanin komai, insha Allahu nasan zai taimaka mana sosai,
    Kuma saida ka tafi na tuna da k'awayen nan nata guda biyu, suma zasuyi amfani garemu, ina so inje gidan su Ummimah d'in yanzu sai ta kwatanta min inda gidan k'awayen nata yake".

     Cikin farin ciki Umar yace
    "Good idea, ni ai nama manta da maganar k'awayen nata, ehh kije ki samo bayanin inda suke daga bakinta"
    "Ok yanzu zan tafi",
     Umar yace
     "ni wallahi tunanina d'aya ma karsu d'auko mana lawyer'n da zaifi k'arfinmu",
   Kallo Sultana tabishi dashi kafin tace
    "Bana son jin haka daga bakinka honey, kana tunanin akwai lawyer'nda zai gagareka ne? Kaima fa babbane ko a sahun lawyers",
    "Hakane, amma fa dole sai mun dage da addu'ah, saboda bahaushe yace 'in kanada kyau ka k'ara da wanka'",
    "Barin tafi dai honey, yamma nayi" ta zira hijabinta har k'asa ta d'auki makullin mota ta tafi.

  Washe gari.
Wasu mutanene fuskokinsu sanye da mask k'wayr idonsu kad'ai ake gani,
     Lab'e kawai sukeyi suna sand'o dan basa son a gansu,
    Dukda dare yayi akwai duhu amma suna tsoron a gansu saboda an gargad'esu akan kar su bari asirinsu ya tonu,
    A daidai k'ofar gidansu Ummimah suka tsaya su duka biyar d'in,
    D'aya daga cikinsu hannunshi rik'e da wata jarka babba ya ringa yayyafawa a baki d'aya gidan ta waje,
    Yana gamawa wani daga cikinsu kuma ya k'yasta ashana,
   Take duka gidan ya kama da wuta sosai su kuma suka samu nasarar guduwa.

  Wuta keci sosai babu sassauci har baki d'aya cikin gidanma ya d'auka da duk d'akunan,
     Saida ya k'one sosai ne mutane suka fara kawi d'auki,
   Cike da tausayi aka ringa watsa ruwan omo a ciki amma wutar sai k'ara tashi take,
    Kowa sai karkad'a kai yake saboda sun tabbatar da inhar akwai mutane a ciki tofa babu wanda zai fita da rai, saboda yanda wutar ke tashi sosai duk ta fara cinye katangun dukda na k'asa ne,
    Wasu kuka suke sosai wanu kuka sunyi tagumi suna kallon wannan wuta,
   Daga ganin wutar cinnata akayi ba wai kamawa tayi da kanta ba, saboda da alama daga waje ta fara ci.

     Wani mutumi ne yace
    "Na tabbatar da matar gidan da 'yarta suna ciki, nasan kuwa wuta ta cisu sosai, barin shiga ciki ko Allah zaisa in dace" ya fara nad'e kafar hannunshi data wando yana k'ok'arin shiga ciki,
     Da sauri wani mutumi ya kamoshi yace
     "Kar kayi wannan sayar da ran bawan Allah, kana tunanin akwai mai rai anan ciki ne?",
    Duk mutane suka hanashi shiga saboda sun tabbatar da kowa dake gidan ya mutu saboda katangun da kansu suke fad'uwa tsabar wuta da sukasha.




°•°AKA°•°Princess Amrah😘
                    NWA

Continue Reading

You'll Also Like

224K 4.8K 18
حسابي الوحيد واتباد 🩶 - حسابي انستا : renad2315
248K 48.1K 128
Title - Dangerous Personality Author - Mu Gua Huang MC- Xie Lin x Chi Qing Chapter 161 + 2 extras ထူးဆန်းသည့် ပြန်ပေးဆွဲမှုတစ်ခုအပြီးတွင် ချီချင်းတစ်...
50K 2K 16
Book 2 of the 𝕱𝖎𝖌𝖍𝖙𝖈𝖑𝖚𝖇 series {Duology} 𖤓 𝕾𝖔𝖒𝖊 𝖒𝖊𝖒𝖔𝖗𝖎𝖊𝖘 𝖓𝖊𝖛𝖊𝖗 𝖑𝖊𝖆𝖛𝖊 𝖞𝖔𝖚𝖗 𝖇𝖔𝖓𝖊𝖘. 𝕿𝖍𝖊𝖞 𝖇𝖊𝖈𝖔𝖒𝖊 𝖕𝖆�...
12.3K 1.2K 32
«ឯងជាអូមេហ្កា ដូច្នេះឯងត្រូវធ្វើជាទាសកររបស់យើងពេញមួយជីវិត» មីន យ៉ុនហ្គី «បាទ!» «ពីពេលនេះទៅឯងត្រូវហៅយើងថា "លោកម្ចាស់" ព្រោះយើងជាអ្នកសង្គ្រោះជីវិតដ៏ថោក...