SANGARTA COMPLETE

By ZulayheartRano89

120K 6.6K 88

labarin soyayya da ban tausayi More

part 1
BABI NA BIYU
BABI NA UKU
BABI NA HUDU
BABI NA BIYAR
BABI NA SHIDA
BABI NA BAKWAI
BABI NA TAKWAS
BABI NA TARA
BABI NA GOMA
BABI NA SHA DAYA
BABI NA SHA BIYU
BABI NA SHA UKU
BABI NA SHA HUDU
BABI NA SHA BIYAR
BABI NA SHA SHIDA
BABI NA SHA TAKWAS
BABI NA SHA TARA
BABI NA ASHIRIN
BABI NA ASHIRIN DA DAYA
BABI NA ASHIRIN DA BIYU
BABI NA ASHIRIN DA UKU
BABI NA ASHIRIN DA HUDU
BABI NA ASHIRIN DA BIYAR
ASHIRIN DA SHIDA
ASHIRIN DA BAKWAI
ASHIRIN DA TAKWAS
ASHIRIN DA TARA
TALATIN 30
TALATIN DA DAYA
TALATIN DA BIYU
TALATIN DA UKU
TALATIN DA HUDU
TALATIN DA BIYAR
TALATIN DA SHIDA
TALATIN DA BAKWAI
TALATIN DA TARA
TALATIN DA TARA
ARBA'IN
ARBA'IN DA DAYA
ARBA'IN DA BIYU
ARBA'IN DA UKU
ARBA'IN DA HUDU
ARBA'IN DA BIYAR
ARBA'IN DA SHIDA
ARBA'IN DA BAKWAI
ARBA'IN DA TAKWAS
ARBA'IN DA TARA
HAMSIN
Complete

BABI NA SHA BAKWAI

2.1K 136 0
By ZulayheartRano89

*SANGARTA*

                        ©
       *ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad my Besty*

_*Ina taya dukkan Musulmai murnar sallah, Allah ya amsa ibadunmu Ubangiji ya sa muna cikin yantattu da wadinda aka yiwa gafara Allahumma amin*_

_ina cigiyar Baseera Sabo Nadabo! Please baiwar Allah ina kika shiga haka?_

*My Besty ke kam dama ta dabance, a lokuta da dama har rasa kalmar da zanyi amfani da ita yayin nuna maki  zallar farin ciki da kulawar da kike min nake yi, amma duk da haka ina maki fatan alheri, Allah ya baki miji na gari Ubangiji ya nuna min auran ki muzo mu kwashi shokiiii*

''' Happy sallah Uncle HASSAN ATK & Uncle HUSSAIN ATK''' inji Sweet *SAFWAN* fatan kunyi sallah lafiya Allah ya maimaita mana na baɗinbaɗaɗa

                 *17*
Zuru Ameesha ta yi tana kallon sa.

Shima Asmad ɗin zuba mata ido ya yi cikin wani irin yanayi.

A hankali ya girgiza kai, a zuciyar sa  yace " *Lossing memory?* " Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un. Ashe maganar a bayyane ya yi ta sai jin muryar Meena ya yi ta ce

"What Dr Meesha tayi lossing memory? Hasbinallahu wani'imal walkil, Inna lillahi!

Haɗa rai ya yi yace " Please Meena kiyi shiru domin ban tabbatar ba."

Faɗin haka ke da wuya, sai ya nufi kofa da niyyar fita, zuciyar sa cike da tausayin halin da ta tsinci kanta a cikin.

Bai ko kalli su Abba ba, ya ce

" Alhaji bari na ɗauko wani abu a office."

Ita ma Ameesha maimaitawa ta yi, tana mik'ewa tsaye da sauri ta isa inda Asmad yake tayi saurin rik'o hannunsa  ta kankame, sai kuma ta bata fuska.

"Cike da mamaki, haɗe da mutuwar jiki, Alhaji ya bi Ameesha da kallo, saboda yadda yaga ta kamkame hannayen likitan. Wannan bakon al'amari ne a rayuwar."

A hankali Dr ɗan fullo ya zame hannayen sa daga rikon da ta yi masa, ya zaunar da ita bisa gadon ya kalleta zuciyar sa  a karye kamar zai zubar mata da hawaye "Zauna ina zuwa kin ji ko? Ya faɗa a hankali cikin dakin fuka. Ita dai kallon da ta yi wannan karon bata yi magana ba.

Wani murmushi ya saki, aiko sai ita dinma ta yi murmushin, kallon su Abba ya yi ya kuma maida kallon sa kanta, in har ya fahimta dai dai to Ameesha yunwa take ji, don haka sai ya ce

"Meena taimaka mana da tea please! Dr Asmad ya faɗa.

To kawai Meena ta amsa sannan ta soma haɗawa, cikin kankanin lokaci ta mika masa, shi kuma ya mikawa Meesha, ita dai Ameesha zubawa cup din ido tayi tana kallo don bata san ya zata yi da shi ba. Kamo hannunta ya yi yasa mata cup din ya ce

"Princess sha tea kina jin yunwa ko?

Cup din ta rike sannan ta maimaita abin da ya faɗa ɗin. Ita bata sha ba kuma bata aje ba.

Wani tunanin ya yi sai ya ce "Meena haɗa wani tea din ki zauna kusa da ita, sannan ki fara sha."

Yadda ya ce kuwa haka ta yi tana sanya cup din sai itama Ameesha ta kai baki, ta kurba sai ta aje shi a baki ta kasa haɗiyewa, don bata masan haɗiyewar ake yi ba.

"Meena ki kuma kurba sai ki hadiye ta gani." Dr ɗan fullo ya yi maganar.

Cikin ikon Allah kuwa sai Ameesha ta yi yadda Meena ta yi har saida ta shanye tas ta saki gyatsa. Sai ga zufa ya soma keto mata.

Murmushi ya yi irin mai nuna farin ciki.

Ji yowa ya yi ga su Ummi wanda suka yi jugum, suna kallon ikon Allah.

"Alhaji ku sameni a office yanzu."

"To" suka amsa, shi kuma ya nufi fita, ai kuwa sai Meesha ta mike ita a dole binsa zata yi, ita fa a nata tunanin duk inda Dr ɗan fullo ya yi shi zata yi.

"Jira ni yanzu zan dawo."

Still dai ta maimaita yadda ya ce, ganin tana don bata lokacin sa ga Aneesa tana ta kiransa sai kawai ya yi tunanin yin mata allurar bacci.

Wani dogon ajiyar zuciya ya sauke, tare da kuma duban Ameesha wacce ta zuba masa ido.  Bai ɓata lokaci ba ya haɗa allura kawai ya yi mata, cikin zuciyar sa yana addu'ar Allah yasa ta farka lafiya ba tare da wannan lalura ba.

"Lafiya kuwa Dr me hakan ke nufi?" Muryar Alhaji Taheer kenan.

"No Abba kayi hak'uri ku dai sameni a office dina, nayi mata allurar ne don tana bukatar hutu."

"Tom Allah ya bata lafiya! Amma Please Dr ka taimaka kar wani abu ya sameta wallahi ita ɗaya ke gareni."

"Ku kwantar da hankalin ku insha Allah komai zai zo da sauki." Yana gama faɗin haka ya yi waje domin shi kansa yana da buk'atar ya samu nutsuwa har ya yi tunanin matsalar Ameesha.

Yana fita Ummi ta matsa inda Abba yake, sam bata cikin nutsuwa don gaba daya ta canza sosai hankalinta ya tashi da ganin yadda Ameesha ta koma, musamman maimaita maganar da ta yi a ɗazun abin ya tsaya mata a rai.

"Alhaji wallahi ina tsoron kar wani ciwon ya samu Ameesha, gani nake fa kamar hauka take yi fa!

"Inna lillahi! Ya yi saurin faɗa a zuciyar sa, don shi ɗin ma ya yi tunanin haka, domin kuwa yaji Dr ɗazun ya ce lossing memory, kenan ta manta komai? Kai ina hakan ba zai faru ba. Amma a fili sai ya ce "karki damu kiyi addu'a Hajiya babu wani abu da zai faru face da sanin Allah, don haka kawai kiyi hakuri ki barwa Allah."

"Na bar masa, amma gaskiya dai na firgita da wannan lamarin.

Alhaji Mansur dake gefe yana sauraron su, in ka kalli fuskarsa sai ka yi tunanin zallar tausayin Ameesha ya ke, amma ina a cikin zuciyar sa sai cewa ya yi "Allah na gode maka da haka ta faru, na samu hanyar raba ta da  ɗana kenan, kai kuma Taheer sai a yi ta fama da biyan kudin magani tunda yartaka ta haukace."  Ya karasa maganar tare da sakin wani mugun murmushi.

********************

A office Abba ne da Ummi zaune suna sauraron bayanin Dr, gyara zama ya yi cikin nutsuwa ya soma yi masu bayani yadda ciwon Ameesha ya ke.

*"Wato Alhaji gaskiya dai Ameesha ta samu matsala sakamakon bigewar mota, kuma dai gaskiya matsalar ta babba ce don ta samu ciwon nan da ake kira da mantau a turance kuma lossing memory amma asalin sunan ciwon (AMNESIA), shi wannan cuta ana samun ta ne musamman ga hatsarin mota, in kan mutum ya bugu cuta dai ta jikin k'wak'walwa.*

*Sannan kuma ita wannan cuta kala biyu ce, 1- akwai wanda in mutum ya kamu da ita zai manta komai na baya sannan kuma ko magana ka gama faɗa masa ba zai taɓa rikewa ba, kai ko hotonsa ya gani ba zay iya shaida ko shi ne ajiki ba, ko ya sha ruwa ko abinci zai iya mantawa yaga kamar bai ci ba.*

*2- shi na biyun yafi sauki, shi ne wanda zaka ga mutum ya manta komai na rayuwar sa na baya, amma kuma duk abin da aka faɗa masa ko aka koya masa zai fahimta har ya aiwatar,  kamar dai yadda ita Ameesha ta keyi a halin yanzu.*

Dr ɗan fullo ya dire maganar sa cikin jimami, musamman yadda Ummi ke tsiyayar da hawaye, shi kansa Alhaji karfin hali kawai yake, amma ko kadan bashi a nutsuwar sa, jin irin ciwon dake damun yar  tasa ba karamin daga hankalin sa ya yi ba.

"Babu komai Dr mun yadda da kaddara! Allah ya bata lafiya shi ne kawai addu'ar mu, amma Dr ita cutar bata da magani ne? In tana da kuma taya ake maganceta?"

"Tana da magani sai dai gaskiya bamu da kayan aikin ta anan Nigeria, amma dai in har mai lalurar ya ga irin abin da ya haddasa masa shiga tashi musamman in ya firgita to yana iya dawowa dai dai, sai kuma a rika tunawa mutum irin abin da yake aikatawa a rayuwarsa ta baya shi ɗin ma zai taimaka wajen dawo da tunanin mai lalurar ."

"Tom yanzu Dr ya kake ganin zamu yi?" Ummi ta yi tambayar hawaye na zuba.

"Ki kwantar da hankalin ki Hajiya, kar da wannan ciwon yasa ki a damuwa insha Allah zata dawo dai dai, don zamu ci gaba da bincike tare da addu'a har Allah ya bata lafiya."

"Allah ya bata lafiya." Iya abin da Alhaji Taheer ya iya fadi kenan ya mik'e.

"Zan baku sallama gobe don allurar bacci nayi mata, sai cikin dare zata farka daga bacci, zuwa safe kuma  sai ku tafi gida, domin dai bata da wani ciwo sai matsalar nan, sai ku tafi gida a ci gaba da addu'a da yawan ziyartar asibitin k'wak'walwa ko za'a da ce."

Daga haka suka fita daga ofis ɗin. Shi ma Dr tattara kayan sa ya yi ya tafi gida domin dai Aneesa ta addabe shi da kira.

Ko da suka koma dakin kowa zama ya yi, tare da buga uban tagumi suka  yi jugum kowa da kallar tunanin sa.

Ameesha kam bacci take sosai bata farka ba sai kusan huɗu da rabi na dare, har a lokacin suna zaune babu wanda ya rintsa, ita ɗaya suke jira su ga farkawar ta ko da ta bude ido bata kalli inda su Ummi suke ba, sai ma lumshe ido ta kuma yi.

A wannan dare babu wanda ya rintsa, har gari ya waye, tunda sassafe Dr ɗan fullo ya diro Asibiti don ganin yadda Ameesha ta kwana, sanda ya shiga bata farka ba don haka sai ya koma ofis.

Bata farka ba sai takwas, batawa kowa magana ba amma idonta a buɗe ya ke.  ganin ta farka sai Abba da kansa ya je ya kira Dr.

Tare suka shigo da Abban, ya yi wa Ummi sannu tun kan ya gama rufe baki har Ameesha ta diro daga gadon ta rungu...

_*Yar Mutan Rano*_

Continue Reading

You'll Also Like

14.7K 1.1K 32
This story is related to brother sister bond. Where brothers are strict yet loving and caring and sister is fully troublemaker and apple of her broth...
190K 20.3K 56
"කේතු දන්නවද මම කේතුට කොච්චරක් ආදරෙයි කියල ?" "හැමතිස්සෙම වචනෙන් නොකිව්වත් සර්ගෙ ඇස් මගේ ඇස් එක්ක පැටලෙනකොට ඒ දිලිසෙන ඇස්වලින් මට පේනවා සර් මට කොච්...
21.4K 690 28
Unicode ငယ်ကိုအရမ်းမုန်းတာပဲလားမမမုန်း သဲငယ် ငါ့ဘဝမှာမင်းကိုအမုန်းဆုံးပဲ တစ်သက်လုံးမုန်းန...
22.3K 699 29
the story takes place in Nevermore where Wednesday meet a tribrid that is Hope's twin sister who was misplaced at birth. her name is Faith Mikaelson...