WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)

By PrincessAmrah

52.1K 3.5K 52

Zazzafar shari'a ce a cikinsa, wacce take kunshe da rikici da tashin hankali. Me ya sa rashin 'yancin kai ya... More

01 Soyayya
02 Boyayyen al'amari
BABI NA UKU
BABI NA BIYAR
BABI NA SHIDA
BABI NA BAKWAI
BABI NA TAKWAS
BABI NA TARA
BABI NA GOMA
BABI NA SHA DAYA
BABI NA SHA BIYU
BABI NA SHA UKU
BABI NA SHA HUDU
BABI NA SHA BIYAR
BABI NA SHA SHIDA
BABI NA SHA BAKWAI
BABI NA SHA TAKWAS
BABI NA SHA TARA
BABI NA ASHIRIN
BABI NA ASHIRIN DA DAYA
BABI NA ASHIRIN DA BIYU
BABI NA ASHIRIN DA UKU
BABI NA ASHIRIN DA HUDU
BABI NA ASHIRIN DA BIYAR
BABI DA ASHIRIN DA SHIDA
BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI
BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS
BABI NA ASHIRIN DA TARA
BABI NA TALATIN
BABI NA TALATIN DA DAYA
SHARHI

BABI NA HUDU

1.9K 129 0
By PrincessAmrah

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)
               
                   {~11-20~}

Yau ta kasance Friday ne, dan haka tun k'arfe sha biyu Umar da Sultana suka tashi daga aiki,
   Kai tsaye suka wuce Gobarau Academy suka d'auko Hafsa sannan suka wuce gida.
    A cikin motar Hafsa tace "Abbah yau ina cikin Class Teacher Nasir ya kirani, bayan naje yace min wai wani mutumi ne yazo nemana amma bazai barni in tafi wurin mutumin ni kad'ai ba dan kar aje wani abu ya sameni kuma laifinsu ne, shine na bishi mukaje wurin mutumin a bakin Head Master's Office,
   Na gaisheshi ya dafa kaina yace min "kece Hafsa ko?",
    "Ehh nice Hafsat Umar Muhammad" na bashi amsa,
    Shine yace min wai dama sak'one zai bani wurinku,
    "Hafsa ki jaddadawa iyayenki cewa taimako yanada matuk'ar muhimmanci, idan Allah ya baka damar taimako to kayi k'ok'arin aikatashi tun kafin damar ta kufce maka" ya kuma ce min "karki manta ki fad'a masu wannan sak'on".
   Yana gama fad'in haka English Teacher d'inmu yazo harda bulala a hannunshi
   "Hafsa you are speaking vanacular ba? Hmm!" Naji tsoro sosai Abbah dan nasan sai ya bani kashi idan na koma class,
   Abbah abun mamaki ashe wannan mutumin wanda ya bani sak'o wurinku ya iya turanci sosai,
   Aikuwa ya taimakeni ya fad'awa Teacher'nmu cewa ba Hausa nakeyi ba turancine, harda cewa yayi wai yaji dad'in yanda ya jini ina speaking kamar ba 'yar Nigeria ba, kuma sak'o yake bani wurin parents d'ina, daga nan kuma sai ya tafi" ta gama basu labarin hankalinta kwance tana bud'e dash board dake side d'inta.

     Juyowa Umar yayi ya kalleta taci gaba da wasanta,
     Bai tanka mata ba, haka Sultana ma batace mata komai ba,
    "Abbah da Momy kunyi shiru, nidai babu ruwana idan ya tambayeni nasan na fad'a maku sak'onshi".

    Shiru sukayi har suka isa gida,
    Bayan Umar ya shiga d'aki ne Sultana ta juyo ga Hafsa tace "mutumin da yayi miki maganar ya yake?",
    "Momy nifa ban sanshi ba, kawai dai nasan ya iya turanci kuma yanada fara'ah" ta bata amsa.

*****

    Washe gari.

Da sassafe Sultana ta tashi, ita dama  haka tsarinta yake kullum ita ke rigar Umar tashi, sai ta gama ayyukanta kaf ta bad'e gidan da k'amshi sannan ta tasheshi yayi wanja, idan yayi wanka sai su karya tare lokacin itama ta shirya kuma ta gyara Hafsa da Haydar.

    Bayan sun zauna kalaci ne Sultana tace "Abbah yau kuwa ina son fita ko zuwa da yamma ne insha Allahu".

    Gyaran murya yayi yace "dama kinga nima inason fita, ina zakuje ne sai mu fita tare?".
    Ido ta ringa zarowa dan batasan kalar k'aryar da zata masa ba,
    "Gudan Hauwa nake son zuwa, kwana biyu bamu gaisa ba",
    "Ehh kuma dama jiya ta kirani ni nama manta, tace ince miki Zarah batada lafiya saima yanzu na tuna wallahi, afuwan".

    "Amma dai honey ka cika mantuwa da yawa, yanzu inda ace bance zanje ba kenan da bazaka fad'a min ba, saidai ta ringa kallona da abun ko? Ai babu dad'i ace yarinya batada lafiya banje na ganota ba",
    "Nidai kiyi min hak'uri tunda gashi na fad'a miki, anjima d'in kinga sai mu tafi tare nima in dubata da jikin".

   Damm! Gaban Sultana ya fad'i sai raba idanuwa take saboda bata son ya bita,
    "A'a kafa san dama ba tare dakai nake zuwa gidan Hauwa ba, bana son inje ka azalzaleni sai na tashi mun tafi gida, ni kuma ina son in zauna muyi fira sosai barin yanzu mun dad'e bamu had'u ba".

    "To naji uwar son fira, kije yau ni kuma gobe sai inje, kuma inji kince zaki bini yawon gobe in kurta miki rashin mutunci" cike da soyayya yakeyin maganar.

    "Ehh naji dai babu komai, nima kuma daga can sai mu wuce yawonmu ko Hafsa?"
    "Ehh Momy, har ki kaini Royal Bakeries ki siya min shawarma da ice cream" Hafsa ta fad'a tana murmushi.
    "Karki damu ai yawo zamusha sosai cikin garin nan, harda inda wani bai tab'a zuwa bama sai munje ko?"
    "Ehh momy zanje, shi kuma Abbah sai mu barshi da Haydar ko?"
    Kwakkwab'e baki Haydar yayi alamar zayyi kuka,
    "Ni ba jakuje daniba ko? Appa kaji wai bajacu tafi dani loyal ba nima insha ayish kilim",
    "Woiii Haydar bai iya magana ba, wai ayish kilim, yaro kazo in koya maka magana" Hafsa ta fad'a tana mishi gwalo.

    Kukane ya fito da k'arfi ya fasashi, yanayi yana kallon Umar dan yaji abunda zai fad'a,
    "A'a fa Hafsa, wallahi idan kikaci gaba da samin yaro kuka duka ma sai in hanaku fitar, ni kuma gobe muyi tafiyarmu nida d'ana Haydar" Umar ya fad'a yana rarrashin Haydar d'in.

    "A'a fa wasa take masa, nidai ka barmu mu fita ai hardashi zamu tafi amma fa sai idan yayi shiru da kukan nan",
    Saurin goge hawayen yayi yace "nayi shilu momy, jaki tafi dani?",
   "Ehh zan tafi dakai yarona" sukayi murmushi su duka ukun.

    Ranar tunda wuri Sultana ta d'aura abincin rana, dambun cous cous da sauce d'in hanta ce tayi, cikin lokaci kad'an kuwa ta gama komai ta saka a food flask,
     Dining suka zauna suka shari abincinsu, Umar harda santi ya ringayi.

    Ta sake yima Hafsa da Haydar wanka ta shiryasu sannan ta umurci Safiyya ma da ta shirya su tafi tare.

    K'arfe uku daidai suka fita, motarta k'irar vibe ja suka shiga, Hafsa ce gaba sai Safiyya da Haydar a baya,
     Basu wani d'auki lokaci a hanya ba suka isa gidan Hauwa kasantuwar babu nisa sosai unguwar.

      Sosai Hauwa tayi farin cikin ganinsu,
Sunsha fira sosai kafin Sultana tace "zanje in dawo yanzu insha Allahu",
    "Daga zuwa kuma? Ina zakije ne?" Hauwa ta tambayeta,
     "Ehh zan dawo ai anan zan bar su Hafsa, Tudun wada zanje yanzu bazan dad'e ba ai".
     "Momy kince fa zaki tafi damu musha ice cream, ya kuma zaki tafi ki barmu?",
    "Ai yanzu zan dawo Hafsa, ga Zarah nan kuyi wasa kafin in dawo sai mu tafi royal d'in ku zab'i duk abunda kuke so",
    "Yauwa momy na sai kin dawo",
    "Ok sai na dawo, Safiyya ki kula da Haydar kin sanshi da b'arna da kuma yawo"
    Tana gama fad'ar haka ta d'auki hand bag d'inta ta nufi hanyar fita.

   Kai taaye Tudun wada ta wuce,
   Wayarta ta fiddo daga cikin jaka ta sake duba text message na address d'inda aka turo mata,
    A hankali ta ringa driving tana k'ara duba message d'in,
    Daidai gaban gidan da yake kallon masallacin kuwa tayi parking kamar yanda aka rubuta mata,
     Bayan ta rurrufe motar ta fito tana rik'e da jakarta.

    "Assalamu alaikum" Sultana ta fad'a bayan ta zare medical glasses d'inta daga ido.
    Shiru taji ba'a amsa sallamar ba, hakan yasa ta sakeyin wata sallamar amma har yanzu shiru ne,
     Sallamah ta sakeyi a karo na uku sannan wata murya ta amsa sallamar.
    A hankali tayi taku hud'u zuwa biyar ya sadata da cikin gidan.

    D'an k'aramin gidane ginin jar k'asa, yana d'auke da d'aki k'waya d'aya tal sai band'aki, daga can gefe kuma kitchen ne aka zagaye da langa langa, k'asan kuwa duk jar k'asa ne.

    "Marhabun, shigo daga ciki mana" matar ta fad'a tana kallon Sultana dukda bata wayeta ba.

    "to mama nagode" ta fad'a bayan ta shiga cikin d'akinda matar ta nuna mata ta shiga.

      "Sannu da zuwa baiwar Allah" Matar ta fad'a har yanzu tana kallon Sultana,
    "Yauwa sannu mama" ta tsuguna k'asa tace "ina yini mama?",
   "Lafiya k'alau baiwar Allah, saidai kuma ban wayeki ba",
    "Ehh gaskiya dama nasan ba zaki wayeni ba dan baki sanni ba" ta zaro ID card d'inta,
    "Sunana Barrister Sultana Saddam Bakori"
     Dafe k'irji matar tayi tace "na shiga uku! Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Allah dai yasa lafiya ba wani abu mukayi ba",
    Murmushi Sultana tayi tace "karki damu mama, lafiya lau ba wani abu kukayi ba, zuwana alkhairine insha Allahu",
     "To ina fatan haka Sultana, Ummimah!" Ta kira sunan a hankali.

   Daga kan gado wata budurwa 'yar kimanin shekara gona sha takwas ta sauko,
   A hankali take tafiya fuskarta bushe da hawaye.
    "Waike Ummimah har yaushe ne zaki hak'ura ki daina wannan kukan? Kukan banza tunda kibsan ba wani magani zayyi miki ba",
    Saurin goge sabon hawayen daya fito mata tayi sannan tace "sannu baiwar Allah".

   Cike da tausayi Sultana ke kallonta tare da fad'in "yauwa Ummimah, ya gida?",
     "Lafiya Sannu da zuwa, barin kawo miki ruwa" ta fad'a muryarta na rawa sosai alamar wani kukan take shirin tayi.
     "A'a ki barshi wallahi bana jin k'ishi",
     "A'a indai kinsan ba k'yamarmu kike ba to kisha ruwanmu" Mamar ta fad'a cikin natsuwa.
    "Hmm! Me zaisa nayi k'yamarku mama?  Kuma fa mutane ne kamar ni, Wallahi kawai dai bana jin k'ishin ne yanzu daga wani gida nake, amma dai Ummimah ki kawo min kad'an zansha".

   Tashi kuwa Ummima d'in tayi sai gata da kofin roba cike da ruwa,
    Mik'awa Sultana tayi aikuwa tajishi da sanyi kamar daga fridge aka d'iboshi,
     Kad'an tasha sannan ta ajiye kofin a k'asa ta fuskanci mama da Ummimah.

      "Nasan baku sanni ba, kuma bakusan dalilin zuwana wurinku ba",
     "Ehh kam hakane, ni a tunanina ma ko kinyi b'atar hanya ne, amma ke nake saurare sai kin fad'a zan tabbatar ko wurinmun kikazo" mama ta fad'a tana kallon Sultana,
     "Wurinku kam nazo mama, Kamar yanda na fad'a maku ni lawyer ce, nazo ne muyi wata magana idan har ba zaku damu ba",
     "Ehh muna jinki Sultana",
   Ta bud'e baki zata fara maganar kenan wayarta ta d'auki ruri, hakan yasa ta ta fasa yin maganar, fiddota tayi daga cikin jaka sannan tayi picking ta kara a kunnenta.

Princess Amrah😘
NWA

Continue Reading

You'll Also Like

THE PARADISE OF LIES By Vanhi

Mystery / Thriller

9.1K 1.3K 78
GENRE : Thriller , drama .......... Vaidehi is a young woman with her own set of dreams and disappointments. She faces a heartbreak when...
248K 17K 29
𝐓𝐇𝐄𝐘\'𝐑𝐄 𝐀 𝐌𝐀𝐅𝐈𝐀.🧠💸🛢️. عالم مُغطىٰ بالذهب الأسود وَ السوَآد . حياة اعيشُها حالكةُ الظُلمِ وَ الظلام . أرواحٌ مــأسـورةٌ في سـرآيا ا...
His burning desire By charmi

Mystery / Thriller

50.6K 3.4K 29
"he was her dark fairytale,and she was his twisted fantasy" 〜⁠(⁠꒪⁠꒳⁠꒪⁠)⁠〜 This is psychopathic Romance novel which is mix of office rom-com+marriage...
223K 4.8K 18
حسابي الوحيد واتباد 🩶 - حسابي انستا : renad2315