SANGARTA COMPLETE

By ZulayheartRano89

122K 6.6K 89

labarin soyayya da ban tausayi More

part 1
BABI NA BIYU
BABI NA UKU
BABI NA HUDU
BABI NA BIYAR
BABI NA SHIDA
BABI NA BAKWAI
BABI NA TAKWAS
BABI NA TARA
BABI NA GOMA
BABI NA SHA DAYA
BABI NA SHA BIYU
BABI NA SHA HUDU
BABI NA SHA BIYAR
BABI NA SHA SHIDA
BABI NA SHA BAKWAI
BABI NA SHA TAKWAS
BABI NA SHA TARA
BABI NA ASHIRIN
BABI NA ASHIRIN DA DAYA
BABI NA ASHIRIN DA BIYU
BABI NA ASHIRIN DA UKU
BABI NA ASHIRIN DA HUDU
BABI NA ASHIRIN DA BIYAR
ASHIRIN DA SHIDA
ASHIRIN DA BAKWAI
ASHIRIN DA TAKWAS
ASHIRIN DA TARA
TALATIN 30
TALATIN DA DAYA
TALATIN DA BIYU
TALATIN DA UKU
TALATIN DA HUDU
TALATIN DA BIYAR
TALATIN DA SHIDA
TALATIN DA BAKWAI
TALATIN DA TARA
TALATIN DA TARA
ARBA'IN
ARBA'IN DA DAYA
ARBA'IN DA BIYU
ARBA'IN DA UKU
ARBA'IN DA HUDU
ARBA'IN DA BIYAR
ARBA'IN DA SHIDA
ARBA'IN DA BAKWAI
ARBA'IN DA TAKWAS
ARBA'IN DA TARA
HAMSIN
Complete

BABI NA SHA UKU

2.1K 139 1
By ZulayheartRano89

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*(NWA)*

                 *SANGARTA*

                        ©
            *ZULAYHEART RANO*

       *Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah*
                      *13*

" Lafiya kuwa?"

Daga can ɓangaren Aneesa ta ce

" Hamma ina yini?"

"Lafiya."

Ya yi maganar fuskar sa ba yabo ba fallasa.

" Ehm daman..." Sai kuma  ta yi shiru.

" Aneesa ina jinki akwai matsala ne?"

Dan murmushi ta yi ta ce

"Dama so nake na ce muna da buk'atar kuɗi, wanda zamu yi amfani da shi."

"Ok"

Shi ne kaɗai abin da Asmad ya faɗa ya katse kiran.

Aneesa kuwa sororo ta tsaya da waya a hannu, tana mamakin Asmad ɗin , sai kuma ta saki murmushi da ta tuna kwana kaɗan ya rage su kasance matsayin miji da mata, tana alfaharin kasance wa da Asmad a matsayin miji.

Da wannan tunanin ɓacin ran da ya ɗan sa mata ya gushe.

Asmad kuwa falon ya koma inda iyayen sa suke, zama ya yi tare da kallon Bobbo ya ce

" To Bobbo yau she za'a buɗe asibitin?"

Asmad ya yi tambayar yana kallon Alhaji Abubakar.

" Ranar ɗaurin Aure ina kamar zai fi."

Bobbo ya bashi amsa.

" A'a ko dai washe gari, don kasan fa kafin a dawo gida za'a daɗe a hanya."

Nenne ta faɗa.

" Tom a barshi haka ɗin, tunda muna da buk'atar mutane."

Allah ya sa albarka ya taimaka, Ubangiji ya ida nufi ka kula da kyau Asmad ka taimaki bayin Allah, domin kaima Allah ya taimake ka ."

"Insha Allah Nennena zanyi yadda kika umurta, kudai ci gaba da yi mana addu'a."

Kullum muna yi maku Allah ya yi albarka.

********************************

" Abba wai ni kam sai yaushe za'a sallame ni?"

"Ina zan sani uwata? Ki bari dai har ki kara samun sauki."

"Nidai gaskiya na gaji, shi mutumin nan tunda ya aje mutum babu wanda ya kuma ganin shi."

Ameesha ta karasa maganar kamar zata yi kuka.

Harara Ummi ta watsa mata ta ce

"To ai ko yanzu kina iya tashi ki wuce, tunda ke kamar karamar yarinya ki ke ji."

"A'a Hajiya me kuma na harara? Baki ganin ba lafiya ne da ita ba?"

Kai Alhaji sai kayi ta goyon bayan Ameesha, duk maganar da taga dama shi take yi, yanzu don Allah ina laifin yaron nan?"

Dan murmushi yaja ya ce

"To naji amma dai lallaɓata ya kamata kiyi."

Su Alhaji Mansur ne su ka yi sallama, shi da matarsa fara'a sosai Alhaji Taheer ya saki da ganin abokin nasa.

" Sannu da zuwa Alhaji ku ne a wannan lokacin?"

Faɗa ɗa murmushi Alhaji Mansur ya yi ya ce

" wallahi mune muka ce yau dai tunda mun samu lokaci bari muzo mu duba mai jiki."

" Masha Allah ai mai jiki ma ta samu sauki sosai."

Zama su ka yi kafin aka hau gaggaisawa, Ameesha dai kanta a kasa ta kasa ko da kallon su, wani karin haushi ya rufe Alhaji Mansur, ganin yadda ya tasa Ameesha a gaba sai *sangarta* take masa ga uban kaya da ya zuba a ɗakin na kwaɗayi, kamar ba asibiti ba " yanzu da nine bani lafiya sai dai yazo gaishe ni, zanyi maganin ka"

( "Kai dai Alhaji Mansur hassada ta yi maka yawa, baka san hassada kan meshi ya  ke komawa ba? Ubangiji ka rabamu da hassada don bata yi ba a rayuwa")

Hajiya Salaha wato mahaifiyar Najeeb ita ce ta kalli Ameesha da murmushi ta ce

"Daughter ya jikin?"

"Da sauki." Ta bata amsa.

Sun ɗan daɗe a asibitin kafin su ka yi sallama.

Asmad ne zaune ya jingina bayansa a kujerar da ke office ɗin sa , zuwan sa kenan daga gida, tunanin Ameesha ne ya addabe shi har ya kasa jurewa , yana son ya bata sallama sai dai kuma bai gaji da ganin ta ba.

Sannan yana jin haushin yadda yake ganin ta tare da Najeeb, domin ko da yaushe yana shigowa asibitin sai dai baya zuwa ɗakin da take, da yake ɗakin nata na musamman ne, ya kula kuma Najeeb ko da yaushe yana cikin asibitin.

Tsaki yaja a karo na barkatai ya faɗa a fili

" Ya zama dole na sallame ta domin gobe ne zan tafi Adamawa don jibi daura aure,  kuma idan na bar asibitin a yau ni da kaina ban san ranar da zan dawo ba."

Da wannan tunanin ya mik'e ya nufi hanyar ɗakin da take, tun da ya doshi wajen ya hango motar Najeeb, sai ya ji wani kululun bak'in ciki ya tokareshi a zuciya , tabbas yasan yana cikin ɗakin yasa ta a gaba tana masa murmushi.

A kofar shiga ɗakin ya haɗu da Meena gaisuwar mutunci su ka yi ta ce

" Dr mukam yau she za'a bamu sallama? Mun gaji da zaman asibitin nan fa?"

Murmushi ya yi ya ce

" Yanzu zan baku sallama ku kwantar da hankalin ku, bari na shiga na kuma dubata."

Ya ida maganar yana shiga ɗakin .

Sai da suka gaisa da Ummi da Abba sannan ya dubi inda take kwance.

Najeeb ne zaune kusa da Ameesha suna hira kasa kasa,sai ka saurara da kyau za ka ji abin da suke faɗa, wani kallon ya yi wa Najeeb mai cike da ma'anoni daban daban, Malam ɗan bani waje zanyi aiki."

"  Tom"  Najeeb ya faɗa tare da tashi ya ce

" Babyn Ummi ina tunanin na tafi, idan an sallame ki tom sai nazo gida."

Gyada kai tayi kawai, don tunda taga Dr ɗan fullo ya shigo ta rasa nutsuwa, don haka sai ta kasa masa magana.

Bayan fitar Najeeb ɗin sai Dr ɗan fullo ya watsawa wa Ameesha harara ,wanda akayi sa'a tagani

" Ashe daman rashin lafiyar karya ki ke yi?"

" Bangane ba?" Tayi tambayar tana murguɗa baki.

"Ai dama ba zaki gane ba, tunda fa kinsa wannan k'aton a gaba kina masa dariya taya za ki gane?"

Mamakin maganar nasa take yi, don bata fahimci me yake nufi ba... Bata gama tunanin ba sai ta kuma tsinkayar maganar sa

" Bari na sallame ki don nan asibiti ne ba gidan love ba, don naga alamar ke baki da ta ido, a gaban iyayen ki sai ki zauna kina wa wani k'ato murmushi, ku ala dole ga masoya ko? To kuje gida can kuyi soyayyar."

Yana maganar tana aika masa harara, cikin zallar rashin kunya.

Yana gama faɗin haka ya mik'a mata takaddan da ya rubuta mata sallamar, sannan ya yi sallama da su Ummi ya yi gaba, ita kam banda juya maganar da ya faɗa mata babu abin da ta ke yi, gaba daya ta kasa gane inda maganar ta dosa .

" Auta ya ce ya sallame ki ko?"

" Eh Ummi ga takardan da ya bani."

" Ok to bari mu tafi kenan, dama ɗazun na rage wasu kayan."

Dan danan suka tattara kayan su suka koma gida.

Yau dai rana bata karya a yau asabar aka ɗaura auren Asmad da Aneesa wanda dubban jama'ar Adamawa suka shaida, shi dai ango a nashi fannin babu kuka babu dariya, baya farin ciki kuma baya bak'in ciki.

Yana cikin abokan sa sai harkan bikin suke.

Aneesa kuwa yau babban burinta ya cika, tunda yau ta kasance matsayin matar *Asmad Abubakar ɗan fullo* ta zama matar Dr ɗan fullo kyakkyawan matashi mai ji da kyau da kuɗi,kai ita kam babu wacce ta kaita sa'a.

Ana gama ɗaura aure suka kamo hanyar kano, inda abokan sa suka shirya masa dinner a  cikin wani haɗaɗen hall mai suna *Zamani* .

Basu isa gida ba sai bayan magriba, don haka wanka kawai su ka yi ta yi tare da salloli, sannan suka soma shiri don karfe goma za'a fara tafiya.

Sosai amarya ta yi kyau na ban mamaki, take aka fara haska bikin cikin gidajen Talabijin, a dai dai lokacin Ameesha ne zaune da Abbanta yana lallaɓata akan ta sha yogurt ɗin da ya shigo mata da shi, don kwata kwata bata son cin abinci  TV Abbanta ya kunna ya kamo tashar liberty , dai dai sanda ake nuno shagalin bikin.

Sam Ameesha hankalin ta bashi kan tv ɗin sai da Abbanta ya ce

"A'a uwata wannan ba shi ne likitan da ya duba ki ba ?"

Gabanta ya yi wani irin faduwa da jin maganar Abba, saurin ɗago kai ta yi tare da watsa idonta akan TV ɗin Dr ɗan fullo ne da wata sun yi mugun kyau, gashi sun da ce da junansu.

"wai dama da gaske aure zai yi?"

Gyada kai ta yi da kyar ta buɗe baki ta ce " eh shi ne" tana gama faɗin haka  ta yi saurin mik'ewa tare da nufa bedroom ɗin ta  hankalinta a mugun tashe.

Ko da ta shiga bed room ɗinta,kuka ta fashe da shi irin mai ban tausayi, wani irin zafi ta ke ji a zuciyarta, ta rasa me ke mata daɗi ta ji takaicin auren Dr tana nan tana fama da ciwon sonsa, ashe yana da wacce yake gashi har an ɗaura aure suna can cikin farin ciki, ita kuma tana fama da ɓaci rai

Ta sha kukan ta inda daga karshe ta rarrashi kanta, Amma ko da safe da ciwon kai ta tashi, don kar ta ɗaga hankalin su Ummi sai kawai ta cije.

Ganin bata iya direvin mota ya sa ta amsa kudi wajen Ummi, sannan ta fita ko tsayawa jiran Meena bata yi ba
***         ***             ***

Kai na gaji Yaseen

Please kuyi min addu'a am not feeling fine 👏

_*Yar Mutun Rano*_

Continue Reading

You'll Also Like

39.9K 5.6K 48
" අහලා තියනවද අශස්....තෝඩු තෑගි දෙන්නෙ උරුමක්කාරයො උනාට මල් තෑගි දෙන්නෙ හිමිකාරයෝ කියලා.... " ආරුල් අයියාගෙ වචන වලට මගෙ බඩේ සමනල්ලු පියාඹනවා වගේ දැනෙ...
12K 408 12
Lily Wilson is in her early 20s. she's a college student who happens to live alone. She's also a little. one day after her friend insisted that she...
437K 52.5K 93
ආවා නම් කියෙව්වා නම් කමෙන්ට් එකක් දාලා පලයං...
14.4K 684 77
"ေမာင့္ေျကာင့္ပဲ ငါအျကိမ္ျကိမ္ငိုေျကြးခဲရသလို' ေမာင့္ေျကာင့္ပဲငါခဏခနျပံဳးခဲ႔ရဖူးလို့ ေမာင့္ကိုငါမမုန္းပါဘူး" ...