RABI'ATU

By Billylosh1

18.8K 732 37

The irresponsible woman More

RABI'ATU
RABI'ATU
RABI'ATU
RABI'ATU
RABI'ATU
RABI'ATU
RABI'ATU
RABI'ATU
RABI'ATU
RABI'ATU
RABI'ATU
RABI'ATU
RABI'ATU
RABI'ATU
RABI'ATU
RABI'ATU
RABI'ATU
RABI'ATU
RABI'ATU
RABI'ATU
RABI'ATU

RABI'ATU

723 31 5
By Billylosh1

❤💕❤💕❤💕❤
       *RABI'ATU*



STORY & WRITTEN BY BILLYLOSH❤






® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*


(ฬє ๔๏ภ't ๏ภly єภtєгtคเภ คภ๔ є๔ยςคtє,๒ยt ฬє t๏ยςђ tђє ђєคгt ❤๏モ гєค๔єг'ร 📚)_





#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/
PML_-Writers-
FANS-4525671123035
#http://maryamsbello.blogspot.com




Follow me on wattpad @ Billylosh1




*AUNTY SIS💞*




2⃣8⃣➡3⃣0⃣



     "Ciki"?

Rabi'a tace "ciki likita, anya kuwa"?

Inna ce ta gwabje mata baki tace  " sakaryar banza kawai tashi mu tafi"

Mik'ewa tayi jiki babu kwari suka karbi takardar suka fito, Inna ta juyo tace mata " Dan ubanki zaki sanar dani a ina kika samo cikin sati biyu"  Rabi'a tace "walla...... Bata k'arasa ba taji saukar wani rikitaccen mari a fuskarta har sau uku. Abinda ko duka inna bata taba mata ba ballantana mari ta rike kumatunta tana dirzar kuka mai cin rai, ita bama cikin ke sata kuka ba marin da Inna tayi mata ne ya sata kuka.

   Adaidaita suka hau suka Rabi'a bata daina kuka ba aranta tana tunanin a ina ta samu ciki? Waye ya mata ciki? Yaushe? Tambayoyi ta ringa jerowa zuciyarta amma bata da amsoshin su.
       ahaka suka nufi wani asibitin amma result d'aya yake nunawa wato 2weeks pregnant, sai da suka zagaya asibitoci shida suna tarar da result d'aya alokacin ana kiraye-kirayen sallar magrib sannan suka wuce gida..




   Abdoulra'uf har ya gaji da jiranta bata dawo yana kwance a d'akin shi ya fara  tunanin rayuwar shi ta baya................

30yrs⏮


    Yaro d'an shekara tak'was 8yrs na gani a bakin k'ofar parlour yace "Assalamu Alaikum" shiru ya k'arayin sallama amma shiru kakeji hakan yasa ya bud'e labulan parlour ya shiga amma ga mamakin sa sai yaga Baffa Bala  da matarsa Baba Baraka ta hard'e k'afa d'aya kan d'aya, t'sugunnawa yayi har k'asa ya gaishe su  ko kallonsa basuyi ba ballantana su amsa masa yace

    "Baffa yunwa nakeji a sammin Abinci inci tun gayan  tuwon jiya har yanzu da dare yayi bansa komai a baki na ba dan Allah ko wani guntun tuwo ne abani in ci"

    Baba Baraka ce ta d'amk'o wuyar rigarsa ta sharara masa mari ta k'ara sharara masa wani ta rik'e kansa ta buga a jikin bango har sai da ya daina gani saboda azabar da yasha ya fad'i k'asa yana kuka yace "Baffa ka cice ni zan mutu Baffa abinci kawai na rok'a"  gyaran murya BaffaBala yayi sannan yace

    " Abdoulra'uf  wallahi zanci ubanka da wannan shegen iyayin naka toh uban waye zai baka abincin, ay masu gata suke cin abinci kaikuwa da baka da iyaye sai dai ka kwana da yunwa kuma bari kaji shinkafa da tuwo sunfi k'arfin ka saidai dawa da gero ko k'anzon tuwo yafi karfin ka shegen yaro mai idon mayu kawai, tashi ka bani guri ko in taka maka ruwan ciki"

  Haka ya tashi ya tafi, harya fita Baba Baraka ta mike tace " kai mai idon mayu zo nan"

   juyowa yayi yazo gabanta ya t'sugunna

   tace "wanki kaya zan baka da bargo kanaji na" 

  "Eh"

Wucewa tayi d'aki ta kwaso kayan dayawa wanda tasan cewa sarai bazai iya wanke wa ba sannan ta bashi bargo ,

  tace " d'auka ka tafi dukka nakeson ka gama wankesu kafin gari ya waye kana jina"  d'aga mata kai yayi alamun "eh " matsowa tayi kusa dashi ta rike kunnenshi ta murde sannan tace "idan ka kuskura kayi barci wallahi sai na kashe ka kaima kabi iyayen ka" yace "in sha Allah zan wakesu "

  K'afa tasa tayi ball dashi saida ya buge kansa da bango da sauri ya k'washi kayan ya fita dasu duk da zafin da yakeji akansa.

   Bakin tap yaje ya ajiye kayan ya kunna tap din ya tara bahon wanki sannan ya samu guri ya zauna yayi tagumi hawaye nabin kumatushi yana tuna rayuwar sa da Iyayen sa da irin jin dadin da yake ciki a wannan lokacin, sai abinda yakeson ci ake dafawa agidan amma yanzu wai shi yake neman k'anzo rayuwa kenan nan yake tuno da abinda Mamy shi kullum take fad'a mishi "Abdoul karka kasance  daga cikin  masu shagala da rayuwar duniya ka manta da cewar akwai mutuwa kasa aranka zaka iya rayuwa babu mu, ka kasance mai juriya da hakuri kasan mahak'urci mawadaci kuma aduk irin rayuwar daka tsinci kanka ka kasance mai godiya ga Allah karka dogara da abin wani ko da wani ka tashi ka nemi na kanta karkaci Haram dan bamu ginaka dashi ba aduk irin wahalar rayuwar da ka kasance toh addu'a itace maganin komai ka kasance mai yawan Addu'a akoda yaushe karka zama mai sakaci da ibada dan duniya ba matabbata bace" share hawaye yayi in a low voice yace " Mamy na meysa kika tafi kika barni gashi ina shan wahala abinci ma bana samu" muryar Baba Baraka yaji tana cewa " Dan ubanka baza kazo ka dauki sabulun ba" da sauri ya goge hawayen ya mike yaje ya karba ya fito.

    Kayan ya jik'a ya fara wankewa gashi wani irin sanyi akeyi saboda k'arshen shekara ta zagayo haka ya ringa dirzar wankin  nan ga sanyi hak'oransa har hadewa sukeyi saboda karkarwar sanyi.

    Haka ya kwana yana dirzar wanki tunda ba yau ta fara bashi ba, ko rint'sawa bai yi ba saboda irin azabar da zai shiga idan bai gama ba ana kiraye-kirayen sallar asuba ya gama wanke kayan ya d'auraye ya shanya sannan ya jik'a bargon ya fara wankewa dayake Baffa Bala  ba zuwa sallah a masallaci yake ba  haka sai da gari ya waye wuraren tak'was na safe sannan Baba Baraka ta tashi ta fito ta sameshi yana dauraye bargon amma ya gagara matsewa kallonshi tayi a wulak'ance tayi t'saki ta shiga kitchen ta barshi a gurin. Shikuwa Abdoulra'uf  ya jigata ya fara fita hayyacinsa  gashi ya kasa matse bargon ballantana ya shanya shi nan ya t'sugunna yana rike ciki yana sai amai nan ya ringa k'warara amai kuma ruwane kawai yake amayarwa,  Baba baraka tana jinshi yana kwarara amai amma ko abakin d'ank'walinta illa ma aikinta data cigaba,haka ya ringa aman nan harya rasa abinda zai amayar ya suma a gurin. Saida ta gama aikin breakfast sannan ta fito ta nufi parlour jin sallamar almajirinta ne yasa tace mishi ya shanya mata bargon, yazo yana tashin Abdoul dake kwance abakin rariya, fitowa tayi da sauri ta kama Dan Almajirin ta tunkud'a keyarsa waje tace ta sallameshi dan bazata ajiye wani acikin gidannan ba wanda zaiji tausayin Abdoulra'uf ba, ruwan da aka d'auraye bargon dashi ta k'warawa Abdoulra'uf a jiki firgigigit ya bude ido saboda azabar sanyi ta harare shi ta koma ciki, tashi yayi ya tattara robobin wankin sannan ya tafi d'akin shi dake soro, ko leda babu ad'akin sai tulin k'asa sai wata 'yar yaloluwar katifa da ta gama cinyewa ya k'wanta yana karkarwar sanyi haka ya wuni da zazzabi ranar ba tare da kulawar kowa ba .

     Haka rayuwa ta cigaba ma ba tareda yana k'in umarnin su ba har aka mallaka musu dukiya ta suka gina katafaren gida a GRA akayimin d'aki irin na maigadin gidan acan bayan gidan kullum sai na bar unguwar nake zuwa wata government school ahaka har na gama makarantar secondary ba tareda kowa yasan halin da nake ciki ba sai Allah . toh anan na fara samun matsala a karatu, result dina yayi kyau nakaiwa Baffa Bala na dukda nasan ba lallai ne ya biyamin kud'in ba amma ban karaya ba na kaimishi da sallama na shiga as usual Basu amsa ba hakan yasa na tsunna na gaishesu sannan na k'arasa gaban Baffa Bala nace  " Baffah wannan ne sakamako na na SSCE kuma na fito da result mai kyau shine nakeso nacigaba da karatu zuwa jam'ia" karbar takardar tayi ba tare da ya karanta ba ya rabata gida biyu ya yayyaga su ya watsamin sannan ya kore ni a parlour,d'aki na nashiga nayi kuka mai isata sannan na tashi nayi nafila tare da addu'oi masu t'sayi na kwanta ina meditating, k'arshe na yanke shawara washe gari da sassafe na tafi gurin masu tura ruwa na siyarwa wato 'yan garuwa na samu ogansu na rokesa daya bani d'aya nima na ringa turawa da k'yar ya bani tareda yarjeje niyar zan ringa biyan naira d'ari duk sati na yadda na karba a lokacin na fara tura ruwa zuwa gida gida kuma  alhamdulillah arana sai in tura kura goma. bayan wata takwas da mai kura yace in bashi nayi magiyar duniya amma yak'i saidaga baya ne naji cewa ya k'wace ne saboda yanda nake ciniki saboda hassada alokacin na tara dubu tamanin da daya 81,000k nan na shiga kasuwar wambai na saro kayan g'wanjo nasamu guri a kasuwar nake kasa nawa kayan tunda na fara kasa kaya customers suke zuwa sai in kwance buhu 2 arana kuma dukka su k'are shekara biyu nayi a harkar g'wanjo haka nan suma y'an kasuwar suka faramin hassada k'arshe nabar kasuwar alokacin na bawa miliyan d'aya baya halin rayuwa yasa nayi sana'oi da dama wanda ada bana tunanin yinsu kuma ayanzu ma banawa wani fatan shiga irin halin da nashiga, sai na sake zana jarabawar SSCE da jamb a lokacin inada shekaru ashirin 20yrs a duniya a jamb na samu 250 ina ta rokon Allah yasa Waec dina tayi kyau ina zuwa masallaci domin d'aukar karatu aranar da. aka sanarda fitowar jarabawa banyi wata-wata ba na tafi cafe domin jin awani matsayi nake, da farko tsoro result din ya bani saboda ganin A' s ci haka makarantar danayi suka nemeni naje suke sanarmin cewa ministry of education suna nemana inyi depending result atsorace na koma gida ranar banyi barci ba na kwana nafilfilu akan Allah ya bani sa'a, da sassafe guraren 7am ta fita tambayoyi suka ringa min ina basu amsa because am so smart they're all surprise haka suka bani short test within sometimes nayi answering sukace gobe zasu kirani atlast akabani scholarship na degree am so happy at that time and jubilating sai kuma hawaye, ban sanarda Baffa Bala ba saboda ina tsoro saida komai ya kammala ana gobe early morning zan wuce sannan da dare naje na samesu nake sanar dasu kamar saukar aradu  haka sukaji abin bai yi masu dad'i ba gashi is too late they can't do anything to stop him, haka ya tashi bayan masifar da suka gama yi mishi na rashin sanar dasu da wuri gari  na wayewa na wuce airport karfe takwas 8am jirgin mu ya d'aga zuwa *INDIA*.......






*BILKISU ARDO CE❤*





❤💕❤💕❤💕❤

Continue Reading

You'll Also Like

44.6K 5.2K 41
ဗုဒ္ဒဟူးနေ့တိုင်း update ပါမည် ကြာပန်းဖြူလေးများ
TPITWOHEF By Aduwei

Historical Fiction

111K 1.6K 200
NOT MY WORK, NOR MY TRANSLATION! For Offline Reading Only The Princess's Inner Thoughts Were Overheard by Her Emperor Father Author(s) 红豆煮水
11.7M 846K 88
Marriage had always been my dream but not to a man about whom I know nothing. The moment my father fixed an alliance of me to a Prince without even t...
6.7M 517K 95
Sitting on the bed, I was waiting for my husband to arrive. It was our wedding Night. I rolled my toes as the visuals of him slowly touching my cheek...