RABI'ATU

595 19 0
                                    

❤💕❤💕❤💕❤
       *RABI'ATU*



STORY & WRITTEN BY BILLYLOSH❤






® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*


(ฬє ๔๏ภ't ๏ภly єภtєгtคเภ คภ๔ є๔ยςคtє,๒ยt ฬє t๏ยςђ tђє ђєคгt ❤๏モ гєค๔єг'ร 📚)_





#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/
PML_-Writers-
FANS-4525671123035
#http://maryamsbello.blogspot.com




Follow me on wattpad @ Billylosh1






*AUNTY SIS💞*






*NEED YOUR DU'A*❤





3⃣3⃣➡3⃣4⃣

    



     Ihu ta t'sandara mai sauti sai ga Baba Baraka da  Inna sun fito domin ganin abinda ke faruwa, suna isowa sukaga Abdoulra'uf at'saye da miya ajikin shi gefe kuma Rabi'a ce tsaye tana kallon shi, Baba Baraka ce ta wankawa Rabi'atu wani bahagon mari sai da taga taurari tace " in banda dabbanci yaza ayi ki watsa mai miya mahaukaciya ce ke? Maza tattara min guri" a duburburce  Rabi'atu ta k'unce zanin jikin ta ta fara goge jikin Abdoura'uf da sauri ya hankad'a ta ta fad'i k'asa ya jefe ta da wani mugun kallo na bak'in ciki sannan ya juya ya fita.
    Baba Baraka ranta ya k'ara baci ta haura sama tana kunk'uni, Abdoulra'uf tunda ya fita ranshi a b'ace yaji ya t'sani Rabi'atu gata da shegen k'azanta, a haka ya isa gidan shi cikin b'acin rai.

   
  Watan sa d'aya rabon shi da gidan Baffa Bala saboda bayason yaje ya tarar da Rabi'atu sabonda k'azantar ta, ya cigaba da normal duties d'in shi, Baffa Bala kuwa komai ya tsaya masa babu kudi kayan abinci ma sunyi k'asa, Baba Baraka duk abin duniya ya dameta ga sha'awar Abdoulra'uf ga Baffa Bala ya dameta da babu. ahaka ranar tad'au aniyar babu mai hanata cimma burinta duk ranar da Abdoulra'uf ya shigo.

   saida yayi 2month baije gidan ba, ya shirya tsaf cikin farar shirt  da chinos white ya fito ya info gidan ya shiga suka gaisa da maigadi sannan ya k'arasa cikin gidan, ya shiga palour ya zauna saiga Inna ta fito da taji sallama tazo suka gaisa sannan ta juya kitchen tace ma Rabi'a ta kimt'sa ta kawo masa abinci da ruwa sai ta nufi sama ta sanarda Baba Baraka dasauri ta mike akan gadon saboda farin ciki kamar an mata kyautar kud'i ta ce ma Inna inya gama cin abinci ta ce masa tazo d'akinta tana nemansa.

    Nan Inna ta fita, Rabi'a kuwa ta d'auko abinci ta kawo masa ta komata d'auko mug da mini flask ta zauna a k'asa kusa dashi ta sosa kan ta hannun nan fal k'wark'wata sannan ta tura hannun acikin mug din don share k'ura sannan ta zuba mishi tea tasaka sugar zata juya shi kennan taji hancin ta  na k'aik'ayi tasaka d'an yat'sa aciki ta k'wak'ulo tasono sannan ta saka d'an yat'san acikin tea din domin cire mishi abin ganyen tea,sai ta mot'sa mishi ta mik'a mishi, da gudu ya bug'e cup din ya tashi sai amai haka ya ringa kwararawa, sai ga Inna ta sauko jin mutum na amai a waje hakan yasa ta nufi wajen taje ta sameshi ta kawo masa ruwa ganin ya lafa ne ta sanar dashi cewa Baba Baraka tana kiran shi a sama.

    D'agowa yayi da mamaki jin maganar Inna, hakan yasa ya koma parlour ya hau stair case ya nufi d'akunan gurin yana binsu da ido ganin wani d'aki a bud'e ne yasa yayi sallama a kofar  d'akin, jin muryar Abdoulra'uf yasa ta karya murya ta amsa cikin sigar shagwaba ta k'ara da shigo.

   Shiga yayi kansa a k'asa har tsakiyar d'akin, batare da ya lura da shigar dake jikin ta ba, ta taho ta bayansa ta fad'a jikinsa da sauri ya juya tare da hankad'a ta yayi hanyar fita da gudu Baba Baraka ta isa gurin k'ofar ta rufe ta da key ta juyo ta kashe masa ido d'aya sannan ta  kama hannun shi zuwa kan gadon ta Abdoulra'uf dai ya kasa magana saboda kid'ima ga wata tsinanniyar riga da Baba Baraka tasaka light pink transparent ko gwiwa bai kai ba komai na jikin ta a bayyane yake ak'alla zatakai shekaru arba'in da biyar 49yrs a duniya,  bai ankara ba yaji tana kokarin cire mishi riga nan ya ringa kok'arin tureta, dambe suka ringa yi rigarta duk ta yage, har ta samu nasarar kama bakinshi ta fara kissing d'inshi, wani mahaukacin mari ya saukar mata a fuska ta tare da goge bakin sa , ta rike gurin tace "Abdoul ni ka mara? Toh wlh ko ka yarda da buk'atata ko na salwantar da rayuwarka na hanaka sukuni kuma nayi maka k'azafin da baza ka iya wanke kanka ba"

RABI'ATUWhere stories live. Discover now