SILAR AJALI

By Ummu-abdoul

65.5K 7.6K 2.1K

Duk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabb... More

Babi Na Daya
Babi Na Biyu
Babi Na Uku
Babi Na Hudu
Babi Na Biyar
Babi Na Biyar (cigaba)
Babi Na Shida
Babi Na Takwas
Real Babi Na Takwas
Babi Na Tara
Babi Na Goma
Babi Na Goma Sha Daya
Babi Na Goma Sha Biyu
Babi Na Goma Sha Uku
Babi Na Goma Sha Hudu
Babi Na Goma Sha Biyar
Babi Na Goma Sha Shida
Apologies
Babi Na Goma Sha Bakwai
Babi Na Goma Sha Takwas
Babi Na Goma Sha Tara
Babi Na ASHIRIN
Open Letter 2 Ol
Babi Na ASHIRIN Da DAYA
Babi Na ASHIRIN Da Biyu
Babi Na Ashirin Da Uku
Babi Na Ashirin Da Hudu
Babi Na Ashirin Da Shida
Babi Na Ashirin Da Bakwai
Babi Na Ashirin Da Takwas
Babi Na Ashirin Da Tara
Babi Na Ashirin Da Tara
Babi Na Talatin
Kururuwan Sheɗan

Babi Na Ashirin Da Biyar

1.6K 188 85
By Ummu-abdoul

IMRAN...

Tun da ya sauke wayar Salman ya shiga tashin hankali, hawaye ya fara zuba a idanunsa, takaicin kansa da RAHANATU ya cika shi. A sanyaye ya karasa sashinsa inda yake zaune da amaryar sa Aisha,

"Sannu da dawowa" tace da shi tana mai murmushi, ganin yanayinsa ya sa ta shan jinin jikinta. Zama yayi gefenta yana mata murmushi da ya fi kuka ciwo,

   "Na faɗi jarabawar da Allah ya min na matsayin uba" Ya faɗi a cije, sai hawaye kuma shar! Tsam ta tashi ta kawo masa ruwa mai sanyi ya sha, ya saki ajiyar zuciya,  a hankali ta ke tausa masa kafafunsa lumshe idanu yayi, hawayen ya tsaya amma sai sakin ajiyar zuciya.

Sun fi karfin minti talatin a haka, can ta tashi ta kai masa ruwa yayi wanka, ya fito nan ne ya ji kamar ana sauke masa nauyin da kansa yayi. Zaman da yayi kusa da ita haɗe da cire mata tagumin da tayi ne ya ankarar da ita dawowa shi. Murmushi ta sakar masa ta kauda fuska.

"in karo maka ruwa kasha ko? Ta tambaya idanunta cikin nasa tana mai aika masa sakonni wanda yake ji tun daga kwanya har tafukan kafarsa. Janyo ta yayi jikinsa ya raɗa mata abu a kunne yana shafo cikinta da ya turo riga. Dariya tayi tana ɓoye fuska a kirjinsa. Shi ɗin ma taya ta yayi. Sannan yace

"ɗan ki ne ya kira ni, wai ashe Salmah bata da a lafiya ina matsayin ubanta ban nema mata lafiya ba. Har ya kai ga an mika ta asibitin mahaukata duk da ciwon ta jinnu ne"  Ya faɗa muryar sa na nuna tsantsan haushin da yake ji.

"Subhanallah, inna lillahi wa wa inna ilaihi rajiun, mahaifiyarsu fa?"

"shi ya sa Allah ya ce mu nema ma yaranmu uwa ta gari kuma ku nema masu uba na gari, wannan hakkinsu ne da in ka kasa za'a muku hisabi akai ranar gobe kiyama, da ga ni har ita mun gaza anan. Bata zaɓa musu ba nima ban zaɓa musu ba" Ya karasa yana mai kukan da yafi jini ciwo.

"ai ba kuka zaka yi ba, akwai masu magani da dama a nan, yanzu dai ka shirya dawowarta, in ta zo sai a nema mata magani a aurar da ita, ka ga shi kenan yar ka ta dawo kusa da kai. Ko a cikin yan uwa ba za'a rasa ba. Don Kaga akwai masu ilimin zamani ma a cikinsu. " haka ta cigaba da karfafa masa gwiwa tana nuna masa ai gara ya dawo da yar sa kusa da shi don sauran dole su nemi dangin su kasancewar su maza.

A ranar ya cika da alfaharin samunta a matsayin mata, don shi ya san so ɗaya ne kuma rahanatu yake ma wannan so ɗin.
                                ***
Tun da suka tsaida maganar dawowar Salmah Sudan ya shiga bincike akan malamai da zasu mata maganin jinnu, da ya tabbatar da ya samu ingantacce ba mai tsubbu ba a Unguwar Ma'amoorah. Gini nai ya ji gini na asibiti mai tsada, amma duk magungunan musulunci suke badawa. Nan ya shiga ya tambayi yanda abin yake suka masa bayani kuɗaɗen da irin magungunar.  Bai bar asibitin ba sai da ya yi booking.
    Washegari ne ya kira Salman ya tura masa kuɗin da zasu shirya ma Salmah tafiyar. Sannan ya faɗa ma iyayensa da sauran yan uwa Salmah na tafe. Nan murna ya karade zuriar, take aka fara shirye, ana aika ma yan uwa na nesa da na kusa.

                           ***
Ranar da aka kira shi kan cewa jirgin su Salmah ya taso nan ya cika da murna. Yar da rabon da ya ganta tun tana da shekara hudu zuwa biyar ce zai gani a yanzu. Can ya tuna da rabuwar su da RAHANATU, take zuciyar sa ta tunatar da shi kalaman su na karshe ga junansu. Take ya zaro waya ya danna lambobinta. Kara na uku ta ɗaga, zazzakar muryarta na masa sallama.

                        ***
RAHANATU...

Zaune take, ta dawo daga wani taro da aka yi na yan asalin Kasar Nijeriya da suke zaune a Kasar Saudiyya. Hankalin ta ya tashi saboda wanda ta gani a wajen hakan ya sa ta barin wajen ba don ta shirya ba.

    Suna zaune kamar an ce ta ɗaga kai nan ta haɗa ido da shi. Bata wani saba da shi ba ko san da ya ce yana son ta, amma ko ya siffansa ya chanza ba zata taɓa manta fuskar da ta ɓata mata rayuwa, fuskar da kan zo mata cikin kashi a 70% na Barcin ta tun faruwar abin. Fuskar da mamallakin sa ya zama SILAR AJALIn mahaifinta da ta fi so duk duniyar nan. Fuskar da ta hana ta tausayin ya'yan ta lokacin da suka fi kowa bukatar ta. Take ta ji ta tsani zaman Saudiyya, bata kai ga tantance abin yi ba taji muryar sa na faɗin.

"wasu a suna ne kawai suke zaune a Kasar nan bisa ka'ida amma in da mahukuntar Kasar Saudiyya ta san ɓarnar da suka yi a kasashensu da su suka kada ba tukuri ba. Wasu ya'yan su na chan ba gata, suna rayuwa a kauyukan mu na Nijeriya mai cike da talauci amma suna rayuwa da fiye da dala miliyan a Kasar nan. Wasu matan Tsabagen son abin duniya suna zaune su ba muharramai ba, su ba mazaje ba, su din kuma suna da yaya a wahalce a Kasar Nijeriya, wata ma anan yayanta Bara su ke. Wasu mazan sun bar iyalansu a can ba sa zuwa sai shekara shekara. Babu ruwan su da hakkin matansu da ke kansu na biyan bukata, in tayi magana ace jarababbiya in Shaiɗan ya rinjaye ta ga aikata zina a ce yar iska. Mu ji tsoron Allah mu san duk wanda ya ke zaune anan ba tare da iyalinsa ba ya je ya dauko su ko kuma ya koma gida da zama. "

Nan take ta ji bata taɓa muzanta irin yau ba. Wato bayan ya illata mata rayuwa, har yan da bakin da zai aibace ta, bata jira ya kammala ba ta ja kayanta zuwa gida. Ta zauna kenan wayarta ta hau tsuwa. Kallon Numb ta yi, tabbas lambar Sudan ne.
" kar dai ace mutumin nan ya rasu me zan ce da yaran nan" Ta faɗa a bayyane yana mai ɗaga wayar. Tun da ta samu labarin ya bar Kasar bata ji daga gare shi ba

"Assalamu Alaikum warahmatullah" Ta faɗa gaban ta na faduwa,

"umm Salman" ya ce bayan ya maida mata da sallama.
Gaida shi tayi duk da tana jin muryar sa ne, amma a tsorace take, maganar da ya mata ya katse ta.

"Insha Allah nan da awa biyu zuwa uku Salmah zata iso Sudan. Ban sani ba da ranta ne ko gawar ta za'a kawo, na dai san sun tuna ba su gatan da ya wuce nan shi ya sa suka ga ya kamata ta iso nan ne bayan sun kuɓito da ita daga asibitin mahaukatan da marasa tunani suka kaita don su karasa haukatar da ita" bai jira amsar ta ba ya kashe wayar.

Hannu ta sa akai, yau da wani irin sa'a ta tashi da aka tozarta ta sau biyu a tare." Su din basa duba matsala ta ne, ba su damu da damuwata ba" Ta faɗa cikin kuka.

Wayar Salman ta fara nema, bata samu ba, nan tai tunanin aika masa sako ta WhatsApp, kunna data dinta ke da wuya sako ya shigo mata ta hanyar akwatin sakon gmail. Hannun ta na rawa ta buɗe ganin daga kamfanin da suka bata aikin ta ne. Wasikar dakatarwa ce daga aiki ne. Sun kuma bata awanni 48 ta dawo musu da duk wani abin da take rike da shi na kamfanin su sannan sun daskarar da akawun dinta na banki da duk bin da ta mallaka. Kuka ta saki, har da gunjin ta. Sai da tayi mai isar ta sannan ta tashi ta fara baza kaya

"zan koma in rungume ya'yana, Imran kayi kaɗan ka kwace min su" tana kuka tana fadi kamar wata sabon kamu.

Abeg  yan uwa yan Sudan ku agazo min, turomin numb ki ta safiyyahjibril@gmail.com akwai inda zaku dan cincida ni, wacce nake da wayarta ya lalace... Thnx

Ummu-Abdoul

Continue Reading

You'll Also Like

16.5K 1.9K 12
Sau da yawa hotunan mu kan shiga kafofin sadarwa, tare da lbr mabambanta haɗe da hotunan wanda hakan kan iya zama Qaharu.
133K 14.9K 116
💥New BL ဒါဒါတို့ရေ... ရှေးခတ်ကျေးလက်တောရွာကို ကူးပြောင်းမှ ကြိုက်ပါတယ်ဆိုတဲ့ဒါဒါလေးတို့အတွက် အသစ်လေးလာပါပြီ .... ရှားပါးတဲ့ MC Gong ပါနော် Gp လေးက...
129K 12.3K 36
အိပ်မက်ရှည်ကြီးတစ်ခုမက်တယ် ။ ကျောခိုင်းထားတဲ့နောက်ကျောပြင်တစ်ခုကို ငါက တစ်ဖက်သတ် ဖက်တွယ်ဖို့ကြိုးစားနေခဲ့တာတဲ့ ။ ဟင့်အင်း.. မင်းငါ့ကိုမချစ်ဘူး ။ ...
102K 7.4K 48
It's all about heart touching love story,betrayal & hot love💗............ Karku sake abaku labari