SILAR AJALI

SILAR AJALI

53.5K Reads 6.2K Votes 35 Part Story
Safiyyah Ummu-Abdoul By Ummu-abdoul Completed

Duk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani dan adama bi ta hanyar.... Saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi'arta ce zuwa makaranta, duk wani matashi dake kauyen da makwabtan kauyukan sun shaidata ne a matsayin daliba mai zuwa makarantar boko.

Iyayenta basu da kudi, basu mallaki komai ba sai ita da kanwarta AMINA, daga su sai gatarin faskaren da mahafinta malam TANKO ya gada a wurin kawunsa, daga nan sai tukunyar da Rahanatu ta sani da ake dora musu abinci ba kullum ba. 
Kullum bata manta maganar babanta
"karatun ki shine hanyar ceton mu, ke kamar gona ce da muke shuka muke fatan girban albarkacin noman mu anan gaba, karatun ki ne zai sa mu san dadin cire kudi mu biyawa kanmu bukata, karatun kine zai sa wata rana mu daina lissafa abincin da muke ci, karatun ki ne zaisa wata rana mu iya siyan sutura har mu manta adadin wadda muka mallaka, karatun kine zaisa a rika tunawa damu a matsayin masu rufin asiri. Dan haka kada kiyi wasa da karatun ki rahanatu"
ba zata yi ba, saboda tana so taga iyayenta sun fita daga talauci. Ta sha alwashin haka. Sai dai a hanyar ta ta zuwa makarantar taci karo da shaidanin yaro HADI ALJAN. Yaron sarkin garin, yaci alwashin lalata rayuwarta koda ta hanyar fyade ne, bata bashi goyon baya ba, amma kuma ba zata iya hana shi ba 
Ba zata fadawa iyayenta ba saboda kada hankalinsu ya tashi
Kota fada musu ba zasu iya komai ba babansa ne sarki.
Ba zata kuma daina zuwa makaranta ba saboda canne fatansu yake.
Ba zata iya salwantar da rayuwarta ta yarda dashi ba dan zai lalata rayuwarta.
A haka ba yadda zata iya, yayi mata fyade.
Ba zata iya fadawa iyayenta ba, duk da saida ta wuni a cikin gona cikin jinni, aka samu mai taimaka mata ta ceceta.
Cikin da ya bayyana a jikin rahana shine ya zama silar tarwatsewar iyayenta da ita. Har ta tsinci kanta a birni.... A cikin tarragon rayuwa mai tsananin daci da burin daukar fansa...

 • forced
 • hausa
 • love
 • mariage
 • pregnancy
 • revenge
 • saudiyya
 • sudan
 • teen
meeteelabo meeteelabo Jan 25
🤣🤣🤣🤣 su baba ashe an san Allah da mazon sa (صلّى الله عليه وسلّم)
aminabello96 aminabello96 Sep 23, 2017
Ya burge ni da bai sanya sun yi bara ko rokon kowa ba! Thumps up Salman I 👍
meeteelabo meeteelabo Jan 25
Ka dai ji kunya. Da wane idon zaka kallet a da rana? 😏😏
aminabello96 aminabello96 Sep 23, 2017
Karya kike Salame, musulunci baya tauye ma kowa hakki, sai wanda ya bari a dalilin jahilci ko tsoro ko fin karfi
maryamsiddeeq maryamsiddeeq Jan 18, 2017
Allah yaqara basira wannan yanacikin babban qalubale da mata suke fuskanta arayuwa (tauye haqqi)
               Allah yakawo mana dauki
lamtana lamtana Jan 22, 2017
Dan wulaqamcin wattpad dinnan yaki kar6ata a Bingel mita, sai Lamtana ummu.