TA ƘI ZAMAN AURE...

By KhadeejaCandy

3.4K 292 20

"Ni ma ina da buri, ina da mafarkai irin na kowace mace, sai dai kuma kaddara ta shata min layi, yadda alƙala... More

Chapter 1
Chapter - 2
Chapter -3
Chapter -4
Chapter -5
Chapter -6
Chapter -7
Chapter -8
chapter 9
Chapter -10
Chapter 11
CHAPTER 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Last Free Chapter

Chapter 15

70 4 0
By KhadeejaCandy

Ni da Hana kuka muka sha har muka gode Allah, ni dai sai tunanin ya zame min biyu tafiyar Mama da kuma Zafeer, tsammanin da nake Yaya Nabil yayi min fada ko duka ko ya min wata maganar babu ko daya, haka muka kwana cikin bakinciki da kuka. Baba be shigo ba sai da safe, a lokacin ragowar karfin jikin ma ya tafi ya bar ni, zazzabi kuma ya rufe ni har bana iya daga ido da kyau, ina jin lokacin da Baba ya shigo ya bawa Hana kudi wai ta siyo kunu, ta tashi ya fita bata jima ba ta dawo da kofin kokon ta aje a nan dakin ta nemi guri ta zauna ta yi tagumi, duk irin yadda take kaunar makaranta da rashin son wasa da karatun da take a yau ban ga tana shirin tafiya makarantar ba. Ina jin motsin fitowar Ya Nabil amman be cewa Baba uffan ba ya koma ciki, ba kamar yadda yake gaishe shi da safe idan ya ganshi ba, ni ma da na saba lekawa na gaishe shi a yau sai na ji bana bukatar ganin fuskarsa ko yi masa magana. Muna zaune dakin kamar wadanda aka yi ma mutuwa har wajen karfe goma sha daya, sannan Yaya ya sake fitowa yana wanke baki wato brush muka ji an buga kofar gidan, gabana ya fadi wata zuciyar na raya min cewar Zafeer ne ko wasani nasa. Sai da Yaya ya gama wanke bakin sannan leka waje, ya dan dauki lokaci sai dai ba sosai ba ya dawo cikin gidan ina hange lokacin da ya shiga dakin da Baba yake wato dakin Mama, sai na ga hango Baba ya fito da sauri ya fita. Wata zuciyar sai ta raya min cewar wani ne daga familyn Mama wata kila ya biyo sawu ya ji abun da ya faru. Sai dai yadda Baba ya dawo ya shigo dakinmu da kuzarinsa ya katse hanzarina.

“Ina... Nooriyya...”

Na tashi zaune jiki babu karfi.

“Taso ga Alhaji nan ya zo”

Na tashi tsaye ina jin kamar ba zan iya tsayi ba, ba kuma dan na san wane alhajin yake magana a kai ba.

“Saka Hijabinki mana”

Na juya na dauko hijabin na saka na bi bayansa, sai da muka fita waje sannan Baba ya tsayar da ni ya ce.

“Ke saurara kar kije ki yi hauka, kin ga dai mutumen nan mai mutumci ne, kuma yayi mana karamci yadda ya dace, zuwan da yayi yanzu yace min ya zo da magana ne, kuma na fahimci maganarsa ta neman aurenki ne, ban riga na bashi ba, amman dai na fada masa ke ma kina maraba da hakan, karki kunyata ni Noor, Allah ya ba mu wannan damar ya ba mu wannan ikon na zabawa yarinyar mijin da zai dace da ita, kuma ni ubanki ne ba zan zaba miki abin da zai cutar da ke ba, dan haka nake son na baki umarni ba shawara ba, duk abun da ya tambaye ki ki amsa da eh karki karyata mahaifinki karki saka kimata ta zube a idonsa, ki tafi a natse ku yi magana ta hankali idan kika dawo zamu yi magana ta fahimtar juna kin ji ko?”

Na daga masa kai ba dan na fahimci duka yaren da yake karanta min ba, ina mamakin  yadda ya kwantar da murya yana min magana kamar ba shi ba, abun da tun da na zo duniya be taba min ba, na bude ido ne da tsawarsa da duka ta tsana da fargabar fadan yau dabam gobe dabam. Na fara takawa ina ganin hanyar tana rabe min na isa gurin kofar na fita daga kan da zan yi na kalli dama da ni sai na hango Zafeer a tsaye nesa da kofar gidanmu ya rumgume hannayensa yana kallona. Na dauke kaina na nufi gurin da Abokin Kareem yake a zatona Kareem din yana cikin motar ne. Na karasa gurin na tsaya na rumgume hannuna ina jin hawaye na bin fuskata.

“Noor..”

Na ji ya kira sunana, na kasa amsawa kuma na kasa daga kai na kalleshi.

“Noor magana ce na zo da ita kuma na ga baki cikin yanayin da zamu yi maganar, amman zaki iya komawa ciki zan dawo anjima”

Na girgiza masa kai domin na san komawa ta ciki zai iya zama laifi.

“Noor akwai wata matsala ne?”

Na yi shiru, sai ya gyara tsayuwarsa.

“Please ki shiga ciki zan dawo anjima”

Kamar ina jira sai na juya da sauri na dawo cikin gidan ina jin kamar ana turani. Ban karasa dakinmu ba juri ya dibeni na fadi a tsakar gidan sai ga Baba da gudu ya zo ya kamani.

“Baki ji ciwo ba dai ko?”

Na dubeshi ina mamakin haka ko wane uba yake ko kuma dai nawa ne a haka? Na daga mishi kai sannan na mike tsaye shi ya rika ni ya saka ni a dakinmu sannan ya kalli Hama dake zaune ido a kumbure ya ce.

“Ke yau baki zuwa makaranta ne?”

“Ina zuwa”

Ta amsa sannan ya fice ita kuma ta tashi ta fara shirin tafiya makaranta a lokacin da na san kamin ta isa ta yi latti sosai. A tare suka fice da Yaya aka bar ni kadai a gidan sai damuwata da kunci.
Baba ne ya sake dawowa dakin ya same ni a kwance.

“Noor Allah yasa ba wata maganar kika fadawa Alhajin nan ba, na ga yayi saurin tafiya kuma kin dawo cikin gida”

Na daga kai na kalleshi.

“Ba mu yi magana ba Baba, yace zai dawo anjima ne”

“Tom tom tom shikenan”

Ya juya ya fita daga dakin be fita gidan ba sai bayan sallah azahar, a haukace na dauki Koko da Hana ta siyo na sha saboda wani yunkuri na amai da nake saboda yunwa har ina jin numfashina kamar zai dauke. Daker na iya tattalawa na fita na yi alwala na dawo na yi sallar a zaune saboda ciwon da cikina yake yi. A gurin na zube ban sake motsawa ba sai da aka yi sallah la'asar, ita ma dai haka na yi ta cikin karfin hali, ina jin kadaici da kewa domin ni kadai ce gidan, ba mamaki Hana ta wuce gurin Mama domin ya isa ace ta dawo daga makaranta tun karfe 2pm, Yaya ma be dawo ba balle kuma Baba da be fita ba sai azahar.

Yammancin La'asar na ji an buga kofar gidan har sau biyu, ban fita ba ban kuma tambaye waye ba domin babu kuzari ko muryar aikata hakan a gareni yanzu. Har sai da yaron makota ya shigo ya ce wai ana sallama da Noor inji Kareem da abokinsa, shi ma dai ban amsa masa ba amman na tashi sanye da Hijabin dake jikina ina dukuduku na fita dakin na saka talkamina na isa zaune gidan, sai na tsaya daga cikin zauren har sai da na dan huta sannan na rike gambun karfen na leka waje. Kareem da ya bawa kofar gidanmu baya ya juyo ya kalleni. Abokinsa kuma dake zaune a motar da gambunta yake bude ya fito daga motar,  sai na ja baya na koma cikin zaune na duka kana kallona ka san a wahale na ke.

“Noor...”

Cewar Kareem da ya fara shigowa zaure yana kallona, shi ma sai na duka daidai tsayina damuwar da tabbatar ta munafurci ce tana shimfide a fuskarsa.

“Noor...”

Ya sake kirana, muna hada ido sai na ji wani kuka mai karfi ya zo min a take na fasa kuka har ina sarkewa.

“Subhanallahi me ya faru Noor? Kin rame kuma kuka kike yi akwai wata matsala ne?”

Ni dai ban san ya aka yi mutumen da nake fushi da shi ya samu sa'ata ba har na bude baki ina fada masa damuwata.

“Baba ya saki Mama jiya, Hana tun da ta tafi makaranta bata dawo ba, Yaya be dawo ba, ni kadai aka bari a gidan, bana ina cin abinci jikina babu karfi kuma ina ganin jiri, Baba kuma yace ba zai aura min Zafeer ba, kuma Zafeer na san ba zai yafe min ba...”

Haka na jera masa komai tsab ina kuka sai ya matso kamar zai taba ni kuma ba taba din ba, sai ajiyar zuciya da ya sauke ya daga kai ya kalli abokinsa dake tsaye kamin ya sake dubana. 

“Saboda ke ne Baba ya samu matsala da Mama? Yanzu ina Mama take?”

Na watsa masa wani mugun kallo ina jin kamar na shake wuyansa.

“Ban san a ina Mama ta tafi ba, kila gidansu gurin Yayarta saboda saki uku Baba yayi mata, amman duk saboda kai ne komai ya faru, kai ka lalata komai Kareem, kai ne kasa Baba ya juya ma Zafeer baya, kuma saboda kai aka saki Mama jiya, kuma ka saka aka kama Zafeer...”

Ya matsa baya da sauri ya mike tsaye ya juya zai fice daga zaure.

“Kareem...”

Na kira sunansa cikin kuka sai juyo ya kalleni.

“Na tsane ka...! Da na san haduwa ta da kai haka zai zame min matsala da ban yarda na hadu da kai ba, kai ba mutumen kirki ba ne, yanzu na gane me yasa matarka bata sonka, kai mai son kai ne i hate you...”

Murmushi na gani a fuskarsa a madadin bacin rai, yana kallona yace.

“Kin jahilci waye ni Noor, na zo miki a baibai ne, kuma ni ban shiga tsakaninki da masoyinki ba, ni bana shiga tsakanin masoya na san yadda abun yake, a gurin ma ni da nake babba balle kuma ke, da wannan nake miki addu'a ina rokon Allah idan aurenki da Zafeer din alheri ne, Allah ya tabbatar kuma ki fada masa ya zo ya same ni zan masa duk wani taimako da ya dace har ya aureki kuma saboda ke zan yi, domin rayuwarki abar tausayi ce...”

Ya juya ya fice ya daga zauren sai ya rage daga ni sai abokinsa, sai da na ji karar rufe mota sannan abokinsa ya kalleni ya ce.

“Noor be kamata ki yi haka ba, kin ga na daya dai Kareem ya girme ki, ba tsararki ba ne, na biyu kuma shi babban mutum ne fiye da yadda kike tsammani, be kamata ki rika fada masa magana anyhow ba, kuma abokina mutumen kirki ne, shiyasa be so zuwa nan ba saboda kina dora masa laifi ni na takura masa da zuwa nan din kuma kin ga ya fita ba cikin dadin rai ba”

“Ba ruwana na da mukaminsa ba ruwana da shekarunsa kawai dai bana sonsa karka sake zuwa da shi”

“Tom”

Ya amsa sannan shi ma ya fice sai kuma na fashe da sabon kuka.

KAREEM POV.

Ya ciro wayarsa ya lalabo Number Nabil ya kirashi.

“Hello ranka ya dade”

“Kana lafiya?”

“Lafiya kalau oga”

“Naje aiki yau?”

Ya dan yi shiru for seconds sannan ya ce.

“Aa ranka ya dade shekaranjiya nan Noor ta dauki wayata ta kiraka ta yi maka rashin mutunci ban sani ba, sai da na dawo Mama take fada min abun da ya faru, na yi tunanin ko akwai wata matsala ne ko ka yi fushi”

Kareem ya shafa fuskarsa.

“Ina tunanin ko ku da kuke yan'uwanta ba ku fini sanin halin Noor ba a yanzu, ita ma ai ba laifi ta yi ba balle har ya shafe ka, ka cigaba da zuwa aiki, yanzu kana ina?”

“Ina gurin abokaina”

“Noor din tana lafiya?”

“Ban sani ba na fito tun safe ban koma ba”

“Toh ka koma ka dubata sai ka dawo gurin aiki”

“Toh ranka ya dade Allah ya saka da alheri”

“Ka rika mata wani abu kamin ka shiga gidan, ba mamaki ma kila bata ci komai ba”

“Toh ranka ya dade Allah ya kara sutura”

Kareem ya sauke wayar ba tare da ya amsa ba, kuma ba tare da ya kalli Hafiz ba ya ce.

“Yaron nan ma yana karatu wai? Ni na manta kamar ya taba fada min yana yi ne ko be yi na manta dai, amman ya kamata ace yana yi saboda rayuwar gidansu abar tausayi ce musamman mahaifiyar da kuma kanensa”

Hafiz ya rage gudun motar ya faka gefe ya kalli Kareem.

“Me yasa ka kira shi?”

Da mamaki Kareem din ma ya kalleshi.

“Baka ga halin da muka baro yar ficikar yarinyar nan ba kuma ita kadai cikin gida? Idan tana bukatar wani abu ai zata fada masa kuma zai dubata ko?”

Hafiz yayi murmushi.

“Ko yargwangwani ce ka damu da yarinyar nan Kareem, da na same ka a office na fada maka Noor tana cikin damuwa kuma tana bukatar ganinka office din ka bari ka shigo motata ka biyo ka dubata a yanzu, kuma Wallahi dazun na tambayi yarinyar akwai wani matsala ne bata min magana ba amman kai tana ganinka sai ta fashe da kuka ta bude maka cikinta”

Kareem yaja tsaki.

“Kai dai baka da zuciya Wallahi, ni ban yi zaton zaka sake min maganar yarinyar nan ba, yanzu gashi kasa na zo na ji bakar magana kawai kuma a gabanka ta nanata wadda take so”

Hafiz ya sauke numfashi.

“Ni ma kaina ban yi zaton zan sake maka maganar ba, amman zuwana dazun da niyar na fadawa mahaifinta gaskiyar cewar ba sonta kake ba sai ya tare ni da wani labari na dabam wai Noor ta fada masa tana so na”

Kareem ya kalleshi ya sake kallonsa ya kasa cewa komai.

“Abun da ban gama gamsuwa a yanzu shi ne, ita Noor din da gaske ta fadi hakan ko kuma dai mahaifinta ne ya fada saboda wani tunani nasa na dabam?”

Kareem ya dantse hakwaransa yana magana da karfi

“Ko dai minene kai ka janyo Hafiz... Mahaifinta be yi tunanin rabata da wadda take so sai da ka shiga rayuwar yarinyar nan, kuma yanzu kana jin yadda iyayenta suka rabo duk saboda kai ne”

“You're just blaming me Kareem, ni fa duk abun da nake yi saboda kai nake yi, bana jindadin yadda kake mu'alama da Safeena, kuma bana jindadin irin zamantakewar auren da kake yi, ina kokarin ganin ka samu farinciki ne ka koma kamar yadda kake a da, ina hango maka farinciki a auren yarinyar nan ita ma kuma ina hango nata farincikin a tare da kai, ubanta be tantance waye mai sonta ba kawai ya fada min tana so na kuma ni na san abu ne mai wahala Noor ta amsa haka, idan mu mutanen banza ne haka zai dauki yarinyar ya ba mu fa, baka kula da yanayinsa ba? Yarinyar nan abar tausayi ce matuka”

“Ni rayuwata ba abar tausayi ba ce? Na auri wadda bata so na yanzu kuma na sake auren wadda bata so na? Mahaukacin ina ne kai?”

“Akwai banbanci, Yusura baka sonta bata sonka, amman ita Noor kana sonta kuma ita zaka iya koya mata sonka cikin sauki, shi wadda take ikirarin tana sonsa hauka kawai take, wannan yaron ba zai iya rike ta ba, baka ga yadda yake mana hauka ba? Sabo ne kawai yake wahalar da ita kai ma tana sabowa da kai zata manta da shi, kuma ni a abun na lura halin da ake ciki a yanzu idan baka aureta ba mahaifinta ba zai bari ta auri yaron ba, kuma ba zai barta ta samu salama ba, saboda kwadayaye ne”

Kareem ya daga masa hannu.

“Hafiz ba zan auri yarinyar nan ba, idan kana tausayinta ko kana tunanin rayuwarta kai ka aureta mana sai ka koya mata sonka ba kace abu ne mai sauki ba, to ka gwada mana, kai ma ai kana bukatar kara aure matarka daya kuma kullum aiki take zuwa bata zama gida, kana bukatar mai kula maka da yara”

Hafiz ya nuna kansa.

“Ni kake fadawa haka Kareem?”

“Akwai illa a fada maka haka ne?”

Hafiz yayi murmushi.

“Tunanin kake kamar cutar da zan yi saboda ina kokarin ganin abubuwanka sun saitu? Zan baka mamaki kuma sai ka yi nadamar wannan maganar da ka fada min, and I'm sure you Wallahi Tsumma Tallahi sai na AURI NOOR, daman ka ce ni na bata komai to zan gyara”

Hafiz ya danna burgi ya ja motar da karfi ya fara tuki, Kareem be sake ce masa komai ba shi ma kuma be sake cewa Kareem din komai ba har ya isa gidansa ya faka a harabar gidan, Kareem ya bude motar ya fita Hafiz kuma yayi reverse ya juya ya fice daga gidan.

Kareem be samu Yusura a gidan ba amman ya samu note a center table rubuce cewar ta tafi dubiya tare da yara. A gurin ya zauna ya rike kansa yana jin kamar kan yana ciwo kuma kamar ba ciwon ba, ya rasa me ke masa dadi. Kamin ya mike tsaye ya nufi upstairs. Yana shiga dakinsa ya ciro wayarsa ya kira mahaifiyarsa da liyinta na waje, ya kuma yi sa'a wayar tana hannunta domin ba ko da yaushe take daukar waya ba.

“Sallamu Alaikum”

“Wa'alaikusalam Momma na kina lafiya?”

“Alhamdullahi ya gidan ya yaran?”

“Kowa lafiya kalau Momy ban da danki”

“Subhanallahi me ya samu ďana nawa?”

“Momy baki kusa kuma kin san babu mai yi ma Kareem gata sai ke, na yi marmarinki Momy”

“Babban mai maka gata shi ne Allah wadda ko bana raye zai kula da kai, kuma yana nan kusa da kai, ni na zo a ta biyu ne idan kuma bana kusa matarka Yusura tana nan dan haka kana da gata ta ko'ina”

Ya sauke ajiyar zuciya.

“Momy yaushe zaki dawo? Ina tunanin daukar hutu na zo na dubaki ko na sati ne”

“Aa cikin satin nan zamu dawo da yardar Allah, jiki yayi sauki sosai matarka ma ta matsa na dawo zamu dawo babu jimawa”

Yayi shiru kamar ba zai ce komai ba.

“Amman jikin yayi sauki ko?”

“Sosai sai ka yi mamaki idan ka gani”

“Alhamdullahi haka nake so, zan kira ki video call anjima”

“Na turawa matarka video ai tana ta murna ta ga jikina yayi kyau, ta ji dadi bata nuna maka ba”

Samun kasa yayi da kasa amsawa har na dakika biyar.

“Ta fada min, amman ta manta bata nuna min video ba”

“Ta manta kam, Yusura yarinya ce mai kirki Kareem, ka rike ta amana dan Allah yarinyar nan bata da uwa bata da uba sai ni, sai kuma kai da kake matsayin mijinta a yanzu, tana so na tana girmamani kuma tana da hankali da natsuwa, abu ne mai wahala a samu mace kamarta a wannan zamani, ba zaka gane hakan sai ranar da ka kara aure ko ka rabu da ita bana fatan hakan amman duk ranar da ka rasa Yusura ka rasa mata ta gari”

“Haka ne, ai na fi kowa sanin halinta Momy”

“Na san kai ma kana da hakuri amman dai ta fika gashi tun da aka yi aurenku ba a taba jin kanku ba, hakan yana saka ni farinciki kuma yana kwantar min da hankali”

“Hankalinki zai cigaba da kwanciya har abada Momy indai aurena da Yusura ne ba zaki taba jin wata matsala ba har abada”

“Allah ya muku albarka ya raya abun da kuka samu”

“Ameen Momy Allah ya kara miki lafiya kuma ya dawo da ke lafiya”

“Ameen Ameen”

Yayi mata sallama ya sauke wayar, ya dade zaune a dakin sannan ya fito ya sauko kasa dinning ya nufa ya bude abincin dake gurin kamshin ya daki hancinsa sai dai hakan be be saka shi sha'awar ci ba domin ba kasafai yake son cin abun da Yusura ta girka ba, ba dan bata iya girkin ba sai dan babu shaukin yin duk wani abu da ya shafe ta. Kitchen ya nufa kamin ya shiga yaransa suka turo kofar falon suka shigo da gudunsu, ya juyo yana kallonsu da murmushi a fuskarsa.

“Kun dawo?”

“Yes Daddy yanzu ka dawo?”

Babbar ta tambaya sai ya daga mata kai ta cire hijab dinta ta aje ta nufi gun da yake tsaye.

“Zan sha ruwa Daddy yau na gaji da yawa na yi gudu a Islamiya”

Ya shiga kitchen din ya debo ruwan ya mika mata. Bayan ta sha ta kalleshi.

“Ina Momy?”

“ina momyn kuma? ba tare kuka je duniya ba?”

“Aa mu muna islamiya ai nan muka barta gida”

Yayi fuskar mamaki yana jin gabansa na faduwa.

“Ba tare kuka fita ba?”

“Aa”

Ta mika masa kofin sai ya karba ya aje ya fice kitchen din da sauri, gurin da ta aje masa takardar ya nufa ya dauka ya sake karanta abun da ya rubuta.

“Na tafi duniya tare da yara”

Ya nufi sama rike da takardar ya shiga dakinsa ya dauki wayarsa, sai da yayi ba searching sannan ya iya kama sunanta domin rabon da ya kirata a waya ma har ta manta, kiranta yayi tana dagawa ya ce

“Kina?”

“Wane irin tambaya ne hak...”

“Kina ina...?”

Ya daka mata tsawa.

“Ina gurin duniya”

“Umarni ne ko kuma?”

“Umarni ni”

Ya kashe wayar, ya sauka falon yana tunani kala kala gaba daya sai ya ji ya kasa natsuwa har sai da ta turo kofar falon ta shigo a lokacin yaransa suna bayan gidan gurin da lilinsu yake suna wasa.

“Ina kika je?”

Ta cire mayafinta ba tare da ta kalleshi ba ta amsa.

“Duniya”

“Kin ce kin tafi da yara ga yara sun dawo ba tare da ke ba, waye ba lafiya? Duniyar wa kika je?”

“Kawata ce Zeenatu”

Ya mike tsaye ya fuska a daure.

“Karki sake fita ba tare da yaran nan ba, kuma karki sake fita ba tare da na baki izini ba”

Ya wuce zai haura stairs sai ta bishi da kallo.

“Na saba idan zan fita rubutu nake na aje maka, idan zaka fita kai ma haka kake min? Me yasa aka samu canji yau? Zargina kake yi?”

Ya tsaya cak sai dai be juyo ba.

“Wani abun kake aikatawa da kake ganin kai ma za'a iya aikatawa matarka? Duk yadda duniya ta lalace har gobe akwai na kwarai Wallahi, ni ba zan iya zina ba ko babu aure balle da aure da Yaya, idan ma kana tarayya da matar aure, budurwa ko bazawara wannan kai ya shafa, ni dai ba za'ayi da ni ba, ubana be yi da yar wani ba ba zan aikata ba Wallahi, amman kai ka kuka da yarka kuma Allah ya isa zargin da kake min...”

Ta wuce shi ta haura stairs din ta shige dakinta ta rufe kofar da karfi. Shi kuma ya juyo ya sauko yana jin babu dadi wani abu ne ya same shi a yau da be saba samunsa ba, be taba zargin matarsa ba ko sau daya amman yau ya ji rashin natsuwar a fitarta gashi har ta ja masa Allah ya isa. Falon ya koma ya zauna ya rufe ido, yana tunanin wata kila da ba baya aikatawa da duk hakan be faru ba. Wayarsa ya ciro ya kama number Safeena ya saka a blacklist sannan ya goge number yana kallon hoton yarsa dake lake a falon.

NOOR POV.

A zauren da suka tafi suka bar ni a nan Yaya ya shigo ya same ni, ina kuka sai ya rika ni ya shiga da ni cikin gidan ya tambaye ni lafiya.

“Ba komai”

“Ko dan an barki ke kadai?”

Na daga mishi kai, sai ya tashi ya fita be dade ba ya dawo da fura irin wadda ake siyarwa a titi damammiya ya zuba min a kofi na sha ya debo min ruwa na sha.

“Ina Hannatu?”

“Bata dawo ba”

Na amsa da muryar kuka.

“Kila ta wuce gurin Mama, Baba kuma be dawo ba?”

“Eh ni kadai aka bari”

“Shi ne kika yi ta kuka ko? Ni ma oga ne ya kira ni yace na zo aiki kuma na dubaki”

“Ina ka ganshi?”

Na yi shiru bance komai ba, mintuna da ya kara be wuce talatin ba ya ce min zai tafi aiki ya fita ya bar ni.
Ama daf da kiran Sallah magariba Zainab ta shigo gidanmu sanye da uniform dinta na islamiya, kamar da tsoro ta shigo dakinmu tana tambayar ina mama.

“Bata nan”

Ta saka Hannu a jakarta ta dauko takardar da miko min sannan ta tashi da sauri.

“Bari na tafi kamin ta dawo kar tace ni nake kawo miki sako”

Ni dai binta kawai na yi da ido har ta fice sannan na maida dubana gurin takardar gabana yana faduwa, na san mai aiken sakon ciki ne dai ban san me ya kunsa ba. Na dade ina kallon takardar cike da fargaba sannan na bude.

“Abu dai kamar wasa Noor ina shirin rasa ki, Wallahi ina sonki Allah ya sani, duk wadda yake son ki be kai ni ba, kuma zasu bata miki lokaci ne kawai su ci amanarki su gudu su barki, za su lalata rayuwarki ne kawai Noor karki aminta da su, babu wadda zan iya dake ya jure sai ni, ni kadai ne mutumen da zai iya zama da ke a kowane hali na rayuwa, amman duk wadda zaki aura Noor sai dai ki je ki yi ki dawo ba zaki taba zaman aure ba matukar ba ni kika aura ba, babu wadda zai iya zama da ke sai ni, kuma ke din tawa ce har abada ba zan daina kaunarki ba Noor har abada, kin manta yadda muka tsara rayuwa? Zaman tare duk kin manta Noor, Amana ta ba zata barki ba, ba zaki taba zaman aure ba,  ke je ki yi auren zan jira ki saki dawo, zaki gane kuskurenki Noor a lokacin da zaman auren zai gagareki, ba fata nake miki ba amman ni na san ba zaki taba iya zaman aure ba har abada...! Saboda na san wacece ke Noor, ba zan daina sonki ba, zan mutu da kaunarki Noor Ba zan taba son wata mace kamar ke ba, talauci yayi min illa, ke kuma zaman aure zai zame miki kaya kun ci amanata kuma amana ba zata barku ba, ban yi tunani zan baki umarni ki kauce ba, ban yi zaton zan miki magana ki juya min baya ba... Kin ba ni mamaki Noor... ”

Na dunkule takardar a hannuna ina jin tausayin kaina da, gashi ba ni da wata hanya ta wanke kaina daga zargin da Zafeer yake min. Na kwanta a gurin ina kuka. Ban sake ganin kowa ba sai bayan sallah Isha'i da Baba ya dawo da ledar nama. Duk yadda bakina ya saba da kwadayi sai na kasa cin wani abun kirki sai kadan ka ci na bar sauran na shige dakinmu cikin hudu na kwanta har lokacin Yaya da Hana ba su dawo ba, daman Yaya ya saba yin dare a waje shi da Baba Hana ce dai rashin dawowarta ya dame ni domin na koma ni kadai a gidan.

“Wato Hannatu ta zabi uwarta ko? Shi ne daga makarantar ta wuce gurin Hajara ko? To sai ta yi ta zama a can kar ma ta dawo gidan nan”

Fada Baba yake sosai inda yake shiga ba nan yake fita ba, tafiyar Hana gurin Mama ta yi masa ciwo sosai. Ni dai ban ce uffan ba sai da yaro ya shigo yace wai ana sallama da Noor inji Hafiz. Sanin Hafiz din yana tare da Kareem ne ya saka na ji bana bukatar zuwa amman ban isa na yi hakan ba saboda Baba yana cikin gidan.

“Je kace tana zuwa”

Baba ya amsa masa ni kuma na tashi na dauki hijabina na saka na fito daga dakin Baba na haska min talkamina na saka na fita waje. Nesa kadan da kofar gidan na hango shi ganina ya saka shi fitowa daga motar da already tana bude ya rufe yana kallona. Ni kuma na karasa ina jiran na ga fitowar Kareem.

“Sannu Noor”

Ya fada sai na daga mishi kai ina kallon kasa cike da natsuwa.

“Ba tare da Kareem na zo ba, kuma ba matsalar Kareem ce ta kawo ni ba, na zo ne mu yi wata maganar dake mai muhimmanci”

“Ina jinka”

Na fada a sanyaye. Sai da ya sauke ajiyar zuciya ya gyara tsayuwarsa sannan ya ce.

“Dazun na so mu yi magana amman na lura kamar baki cikin yanayin da ya kamata na yi maganar”

Sai kuma na ji shiru jikina ya bani kallona yake, ina daga kai sai na yi arba da idonsa a kaina.

“Noor Baba ya fada min wata magana a dazun, ba zan ce ba haka ba ne amman abun ya ba ni mamaki”

Gabana ya fadi.

“Me ya ce maka?”

Ya matsa kusa da ni kadan ya rage muryarsa.

“Ya fada min wai ya tambaye ki fitar da miji sai kika ce ni kike so haka ne? Ko kuma dai Baba be fahimce ki ba ne? Ko kuma dai Kareem kike nufi Baba be fahimta ba yace ni”

Kallonsa nake ina ta kokarin hada kalmonin da ban fahimci manufarsu ba, ta dayan bangaren kuma gargadin da Baba yayi min dazun da safe yana dawo min.

“Noor ko ba haka ba ne?”

Kiran sunana yake tare da tambayar da bam san taya zan amsa masa ita ba. Ba zan iya karyata Babana ba, bayan duk gargadin da yayi min, idan har na yi haka ban zan me zai biyo baya ni ma zai koreni kamar Mama ne ko kuma zai yi ta dukane ne yace babu ruwansa da ni.

“Ban sani ba tukuna”

Na fada da muryar kuka ina kai hannu na na taba zuciyata.

“Hakan yana nufin ba gaskiya ba ne kenan?”

Ya sake tambaya ta sai na amsa masa ina fashewa da kuka.

“Gaskiya ne....”

Na juyo na shigo cikin gidan da wani irin kuka mai karfi, a tsakar gidan na zube na rushe da kuka ina jin tsanar mahaifina fiye da kowa a duniyar nan. Taya zai yi min haka ta ina zan iya Zaman Aure da Hafiz wane irin abun kunya ne wannan? Baba babu ruwansa da damuwata babu ruwansa da wadda nake so, daman can Hafiz ne yake so na ba Kareem ba ko kuma dai dukansu wasa suke da hankalina ne? Ni kadai ce mai uba irin Baba ko ina da ta biyu..!

“Lafiya wani abu ya faru?”

Na daga kai na kalli Baba ina kuka.

“Baba bana son Hafiz kai kace masa ina son shi? Ni Zafeer kawai nake  so, ni idan ba Zafeer ba ko an min auren ba zan zauna ba, Baba bana son kowa sai Zafeer”

Tsawa ya daka min sai da na zabura.

“Rufe min baki, Wallahi sai kin auri wadda na zaba miki sai idan shi yace ya fasa, kuma idan kika yi sanadin da ya fasa aurenki sai na lahira ya fi jindadi”

Yana rufe baki ya hau dukana.

“Karki yi zaman auren idan an kaiki ki fito ki dawo gida ki zauna, daman ai haka uwarki take so haka kike so, ke kin fi son ki yi ta gantali a gari kin zama wawuya to mu zuba ni da ke, Wallahi ko zaki mutu sai kin auri Mutumen nan idan ba ki aure shi sai na tsine miki Noor, ki bi duniya ki lalace daman kin fi son lalatar kin sha'awar ki zama watsatsiya kowa yana miki kallon mahaukaci, ko da yake ba laifinki ba ne, laifin ne da ban zabo uwar da zata koyawa Yayana tarbiya ba, gashi ita Hannatu ta bar gidan ke kuma kina son saka min hawan jini ko? To ba ku isa ba, ai yara da dawo ana musu aure ko basa so amman basa musawa sai ke da babu albarka a tare ke...”

Azabar dukan da yake min da hannu bata saka na gane kuskuren yi masa musu ba har sai da ua dauko maburkin Mama na ice yana duka na da shi, a take fara rokon gafararsa ina sosa jikina ta ko'ina ina jin kamar wuta yake watsa min a jiki.

“Na bari Baba na bari, zan aure shi Wallahi zan aure shi Ina son shi ina kaunarsa Baba zan zauna dan Allah ka yi hakuri Baba na bari ba zan sake ba”

Rawa jikina yake kamar mazari majina da hawaye sun hade min guri daya, numfashina na fita da karfi...

__________________

A nan muka kawo karshen Book One na litfafin TA KI ZAMAN AURE, sai bayan Sallah idan mai kowa mai komai ya amince mana zamu dora a book two... A inda littafin zai amsa cikaken sunansa.

Akwai tambayoyi da yawa da kuke bukatar amsoshinsun a tare da Noor da kuma Zafeer da Kareem da ma wasu a gaba.

Anya fitar Mama a gidan Baba zai haifa da da mai ido kuwa?

Wai ina labarin Safeena ne? Ta hakura ko tana kan bakarta?

Kuna Ganin Yusura zata iya juyowa ta kalli Kareem da idon rahama?

Shin Kareem zai iya jurewa Abokinsa ya auri Noor kuwa?

Me. Zafeer yake nufi da cewar ba zata ta Zaman aure ba?

Me yake Hana Noor zaman auren ne? Rashin dace da miji ne ko bakin iyeye ko kuma rashin Hali na gari? Ko kuma daga mahaifin ne?

Akwai wani dunkullen sako a cikin Littafin da nake son isarwa idan Allah ya ara min lokaci kuma ya amince min. Allah yasa mu amfana.

#KhadeejaCandy
+2348036126660

Continue Reading

You'll Also Like

162K 6.7K 83
A girl whom I thought as my best friend standing before me with a knife to kill me. She stabbed the knife onto my chest and told me "He will not like...
32.4K 2.3K 21
Ta zaci gamo tayi da aljani ashe ba aljani bane mutum ne kamar ita , soyayya ce kawai tsakanin su
7.9K 591 37
GABA DA GABANTA (Aljani ya taka wuta)😂 don't miss it, akwai cakwakiya
1.5K 123 26
Makahon so, shine lokacin da sashe ɗaya ya makance akan soyayyar ɗaya sashen. Gurgun so, shine son da sashe ɗaya yake mutuwar son ɗaya sashen amma ba...