AUREN WUCIN GADI 2

By zahraaliabdullahi5

446 9 2

Labarine da yaƙunshi soyayya cin amana dakuma zalunci More

2/1
2/3
2/4
2/5
2/6
2/7

2/2

51 1 0
By zahraaliabdullahi5

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITER'S FORUM* ✨

     ✨ *G.W.F* ✨

[ *GORGEOUS WRITER'S FORUM WE ARE THE BEST AMONG THE REST* ]

BOOK 2

CHAPTER 2

Saida tajita ajikin mutum koda bashi din bane ta tabbar Allah yatsiratar da ita daga zaluncin wannan mugun mutumin take wani irin kuka yazo mata tayi masa kyakkyawan ruguma tayi masa zobe da hannuwan ta ma'ana ta zagaye masa ƙugu da hannun ta duka,shima be cuci kansa ba ya rungumi abarsa shi kaɗai yasan halin da yashiga cikin ƴan awannin nan ƙiris ya rage zuciyan sa bugawa,a tare suka sauke ajiyar zuciya.

Abunda yafaru lokacin da suka fita daga gida a hanyan su ta zuwa asibiti  dubo Alhaji na Allah Mansur ne yakira shi a wayan yake sanar masa sunyi tracking lambar daya yake kiran mai gadi kuma shine yayi masa tranfer ɗin ƙuɗi ya faɗa masa inda yake,shine ya juya da akalan tafiyan nasa zuwa wajen suna waya da Mansur yana faɗa musu direction ɗin wajen harde suka isa koda suka isa basu wani sha wahala ba dan ba kowa a wajen sai ƙofofine birjik harma karasa wanda zaka nufa,suna cikin dube dube dan Mansur yake ce masa tsakanin ka da layin be wuce taku goma ba,kwatsam suka tsinkayi murya ana kuka hade da magiya shine suka faɗa ciki shine fa suka tadda wannan saƙandamin yana kokarin hakƙe mata,Ahmad beyi wata wata ba yayi tsalle yadaki kan wannan ƙaton take ya baje a ƙasa yakai masa wani mahaukacin harbi gaban sa,yariƙe gaban wando shine yake wani irin gurnani kaman mai shirin mutuwa.

"Ni bazan sake komawa wannan gidan ba ni kamai dani gun Anty hajia banason wannan auren wallahi ni nama fasa,murmushin gefen baki ya saki saida yasaka ta jikin shi sosai ya matsaeta kaman za'aƙwace masa ita ya laluɓi kunneta yakai bakin sa murya can ƙasan maƙoshi yaraɗa mata"ya haka da tsoro Amaryar wucin gadi ta kofa filin dagan bamu kaiga shiga ba,harkin fara karaya kode kinfasa daukarma Iyayen namu fansan ne?karfa ki haifamun baby matsoraci mai saurin kuka irin ki.

Kafin tayi magana ta hango Yah Faisal da wasu mutane tafe zuwa inda suke da alama jami'ai ne yana basu umurnin da ku tattare shege kukaimun shi ma'ajiya sannan a binciki lungu da tsako na nan ba za'a rasa wani abun ba.

"Yes sir suka amsa suna masu sara masa sannan suka tattare ƙatonnan kaman kayan wanki sukai gaba dashi,nufo inda suke tsaye rungume da juna Faisal din yayi cike da kunya Aisha tasoma ƙiciniyar kwace kanta amma Ahmad be bata wannan daman ba saima sake riketa da yayi tsab yana sake sakata jikin sa,ganin abun na Ahmad bana ƙarewa bane yasa Faisal din gyaran murya yana cewa"ƙanwata lafiyanki ko?"kanta kawai ta iya gyaɗa masa tanayin fuskan tausayi kaman zatayi kuka tace"Yaya ni gida zan tafi shiru yayi mata yana kallon Ahmad dayake ƙanƙame da ita yaƙi sakinta yace"Broo ai saika saketa mutafi ko bakaji me tace bane?

"Idan kika tafi kika barni bazaki sake ganina ba,idan nasake meki hannu daga riƙon da nayi miki bazan sake riƙe miki hannun ba,idan na fiddaki daga jikina bazan sake sakaki ajikina ba,bazaki sake jin ɗumina ba baza.....rufe masa baki tayi tayi rau rau da idon tana girgiza masa kanta fuskarta duka ya ɓaci da ruwan hawaye tace"bazan iya ba bazan iya ba.

"Bazaki iya me ba?ya rada mata a kunnen ta"nide kawai karka tambaye ni amma gaskiya na tsorata Allahne kawai ya ceceni daga hannun wannan ƙato daya turoku da bansan abunda ze faru ba kuka ƙara minti goma.

Ba abunda ze faru dake matukar ina tare dake bazan bari ko kuɗane ya taɓaki ba,balle wani ƙato bake ba nan gaba idan ance ya taɓa wata maa baze iya ba.

Daddy Ishaq ya kalli Alhaji badamasi dake zaune saman gadon majinyata dake asibiti yana zaman hutu yace"Badamasi ko zamu iya sanin wasu irin magani suke safaran su da sunan na kamfaninka ne sanin su ze taimaka mana kwarai.

Shiru Alhaji badamasi yayi sai kuma ya numfasa yace"da bazanyi magana da kowa akan wannan abun ba amma yanzu ya zame mun dole zanyi tunda takai duniya tanamun kallon maci amanan ƙasa da al'umma hatta da ɗana yana zargina da aikata ba daidai ba,har yasashi kasa zama a inda nake mutane suna bamu yardarsu saboda suna da yaƙinin idan wata cuta ta samesu zamu iya taimakawa da ɗan abunda Allah yabamu ikon sani na magani wajen warkar dasu,cin amanan kiwon lafiya idan mu masu magani da likitoci muka zama barazana ga majinyata,haƙiƙa nayi kuskuren wajen amincewa da Sunusi da Surajo saide bantaɓa goyon bayansu akan abunda sukeyi ɗin ba.

Suna safaran maganin pregabalin ta tablet dakuma capsule sai kuma ta syrup da allurai amma wallahi banda masaniya sai daga baya bayan nanne ɗaya daga cikin manager na yake faɗamun ashe suna amfani da mazuban maganin mu su zuba nasu,amma bisa yarjejeniyarmu sun saka hannu jarine akan zasuna kasuwanci damu muna basu wasu kason magani da kamfani tayi ashe su idan suka ansa suna sauya maganin suyi amfani da tambarin mu,batun jayewa danace musu shine sukemun barazana da rayuwata gani da sukai zan basu matsala shine sukai kisa suka kawo gawan Office dina da alama kuma sun siye dukkan masu gadin kamfanin da wasu gurɓatattu cikin ma'aikatan.

Numfasawa Daddy Ishaq yayi yace"idan ban manta ba wannan magani da kake magana akai wani Litita a america ya taɓa rubutamun na saya yana maganin damuwa,sannan ba'asaida wannan magani haka kurun sai da saka hannun ƙwararren Likita kafin a baka sannan ba ason mai shan sa ya haɗa da kayan maye irin su wiwi da barasa,dan yakan zamo illa ga lafiyan mai shanta.

Zanma Ahmad magana da bayanin komai akan maganin yarana suna bibiye dasu In sha Allah sai mun kawo karshen zaluncin su"In sha Allah shima Alhaji badamasi ya amsa jiki a sanyaye.

Ammi da shigowarta ɗakin kenan ta kalle su fuska a sake tace"yanzun nan Faisal ya kira yake sanar dani sun gano inda Aisha take harma sunyi nasarar kame wasu dake wajen tare da kubutar yara goma sha biyu da aka sace kafin akai ga fita dawusu"Alhamdulillahi duka suka hada baki wajen yima Allah godiya.

Wannan karon Daddy Ishaq beyi nauyin baki ba yace ma Ammi kice ya maido da Aisha nan dan zanmata a can yanxu kuma ze iya zamowa hatsari ga rayuwarta dan zasu maida hankalin su kacokan akan nemanta saboda gani zasuyi kaman iita tajawo musu matsalan nan.

Ammi tace"Ɗan jarida nima nayi wannan tunanin kuma na faɗama shi Faisal ɗin yau komai dare su hawo jirgi ya kawomun ƴa idan basu samu jirgin da ze zo Kano ba ko ta wata state ce su hau amma ban yarda kwannan su a can din ba.

Alhaji Na Allah

A firgice ya farka daga baccin yake da alama de haryanxu alluran da akai masa begama sakin sa ba,duba da yanda yafara sumbatu kaine ko kafaɗamun gaskiya da saka hannun ka ake neman ganin bayana,duk ya firgice yafita a hayyacin sa sai sumbatu yake yana neman cikumo Ahmad dake tsaye Mami da Sajid na rirriƙeshi dole de likita aka sake kira yaxo yama alluran bacci yace abarshi shi daya yana bukatan hutu daso samune Ahmad ya dakata da shigowa inda yake harsai ya koma normal dan ganin ka da Alhajin yakeyi yana sake firgita shi da abunda mukeso ya manta hakan kuma koma bayan aikin mune.

kai kawai Ahmad din yayi gyaɗawa dan dama yazo nan dinne saboda kawar musu da tunani idan wani abun yataso.

Faisal besha wani wahala ba wajen samar musu tiket na jirgi,saide besamu wanda zeje  Kano yau ba sai ta Lagos dan haka ba bata lokaci jirgin ya tashi dan ko sallama basu samuyi da Ahmad din lokacin da yakira wayan sa su kuma lokacin suke fama da Alhaji na Allah shiyasa be samu dauka ba,sai daga bayane bayan yafito daga cikin dakin Sajid da Mami na biye dashi suna bashi  baki akan abunda Alhajin yayi masa"bakomai Sajid karkaji komai ni kaina da nasan abunda yasaka Alhaji cikin wannan halin ni mai magance masane saide nima ɗan Adam ne zuciya gareni banajin dadin halin da yake nunamun wani ma idan yagani sai yayi tsammanin da saka hannuna kan halin da yashiga wallahi ni sai yanzuma nake danasanin barin Mahaifina cikin ciwo lokacin da yake bukatana kusa dashi sama dakomai na tsallake shi nazo nan"haba Ahmad karkace haka shima Alhajin nasan zafin ciwone razana akan abunda yafaru dashi koma menene amma da zaran yaji sauki komai ze dawo normal cewar Mami dan ita ma kanta tana da wani plan dinta akan Ahmad ɗin bataso yayi nesa dasu kafin ta cimma manufarta.

*****
Karfe sha biyun dare dot agogo yabuga jirgin su ya sauka a burnin Ikko Goga shi yaje taran su filin jirgi duk da nikaf da Aisha take sanye dashi hakan be hanashi ganesu ba saboda tare take da Faisal kai tsaye mota suka shiga sai gidan da suke ɗaki guda aka warema Aisha mai ɗauke d toilet aciki sai katafaren gado da mirrow sai sopa ƙwaya ɗaya tal dake ciki,wanka tashiga tayi kafin ta fito ta tadda an ajiye mata jallabi irin ta mata da sabuwar hajibi sakawa tayi tayi sallah tana nan zaune tana addu'a akayi knocking ƙofa izinin shiga ta bayar bata damu da sai tawani kintsa ba dan sanye take da hijabi a jikin ta wata dattijowa ce ta shigo hannun ta dauke da faranti ƙura mata ido Aisha tayi cikin rawar baki tamiƙe a azarane ta furta.....An..an...na cikin rarrabuwar murya.


ALLAH YASA MUDACE

Continue Reading

You'll Also Like

20.8K 1.7K 100
labarin wani matashi daya auri wata yarinya na wucin gadi saboda wani dalilin sa.
31.5K 2K 42
❝"I refuse!", was her deafening scream. The temple full of people stood in silence. He watched her, taken aback at the audacity, but not out of his i...
26.4K 1.4K 33
Labari akan wata uwar miji wacce ta takurawa matar dan ta tin kan suyi aure. Komai ta tashi ta turo mata but sai ya kare akan ta. Shin uwar mijin na...
3.2K 215 45
Ƙaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar...