2/6

70 0 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITER'S  FORUM* ✨

     ✨ *G.W.F* ✨

BOOK 2
CHAPTER 6

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.

  Yana fitowa daga toilet din ya miƙama Mansur dake sanye da kayan irin ta ma'aikatan wajen yana shara Jakar shikuma yayi waje ta wata hayan,shikuma Mansur saka jakan yayi cikin irin ƙatuwar dustbin ɗin nan mai taya yayi ya gurgura yafita da ita waje yana fita can baya inda ake tajiye dusbin din yanufa da ita yana zuwa ya bude ya ciro jakar yasa abayan a both din motar sa ya cire rigar jikin sa tamasu aikin yashiga motan sa yamata key yafita daga farfajiyar hotel din yana cilla hancin motan sa saman titi.

Ahmad ma yana fita yasamu Aisha tsaye har tasaka hijabinta,besan sanda yasauki ƙatuwar ajiyar zuciya daya sakata ɗagowa tana zuba masa idonta na maikama da maijin bacci ba.

Kallo kallo suka shiga yi a tsakanin su kowanne da abunda yake ayyanawa a ransa game da ɗan uwansa ita tafara janye idon ta dan bazata iya cigaba da kallon sa ba,wani irin ƙwarjini yake mata mugun girmansa da nauyinsa take tun daga ranan da ya maidata mace"zaki rakani wata ƴar nguwa,bazata ta tsinkayi muryansa batare data kalle shi ba tace"ina da abunyi a gida,da mamaki ya ɗago ya kalle ta dan beyi tsammanin zata gujema bukatan sa ba,shiru yayi yana kallon ta,sai kuma ya juya yashiga mota ba tare daya ƙara kallon inda take ɗin ba,sai kuma taji ba daɗi ganin kaman yana fushi da ita dik da haka ta daure ta share shi dan tana ganin wannan itace hanya ɗaya dazata bi dan ganin ta tsiratar da mutuncinta bazata sake yardan masa ba,har sai ya gane kurensa ya gyara ya karɓeta matsayin matarsa wanda ze rayu da ita harƙashen rayuwar sa,iidan ko yace ze cigaba da daukanta matsayin matar sa ta wucin gadi ita kuma ta gwammace tayi nesa da shi tafita daga rayuwan sa ko Allah zesa tasamu abokin rayuwa daidai ita.

Hon din motar shiya ƙatse mata tunani firgigit ta dago tana kallon sa,ya sauke glass ta inda yake shi kansa baya jin daɗin yanda yake kallon ta cikin damuwan nan to yazeyi hausawa sun magana zaran bunu,maganace yariga ya faɗeta a bisa kurkure zece ko kuma gangancin sa dan gani yake kaman tayi masa ƙanƙanta ta iya daukan larurarsa na shekara da shekaru.

Ajiyar zuciya ta sauke ba tare da ta kalli inda yake din ba tace"ku tafi kawai zan hau taxi dan komawa gida kuma naga kaman kana da wajen zuwa dan haka bani da matsala da hakan kana iya tafiya.

Maganar tata taso fusata shi dan yakasa ɓoye fushin sa akan hakan danko a muryansa saida fushin nasa ya fito"you're very stupid Aishaaaa yawani ja shaa din cikin wani irin salo dukda cikin fushi ya kira sunan ta haka be hana tasirinsa a gareta ba.

Idon ta suka shiko da ƙwalla duk yanda tayi kokarin hanasu zubowa kasa riƙesu tayi,wai ita ya yakeso tayine,shiga motan taje tayi ta daya ɓangaren tana jawo murfin motan da karfi yabada sautin bammm ritsa idon sa yayi dan har tsakar kansa yaji.

Ba wanda yayi magana a cikin su tafiyan kurame sukayi ganin shirun yayi yawa yasaka Mustapha dayake aikin tuƙi sakin sauti hakan sai yabama Aisha daman sakin kukan ta,laluɓo hannun ta yayi yasaka cikin nasa yashiga murzawa a hankali hankali.

Zame hannunta tayi daga rikon dayayi mata ta shiga girgiza masa kanta cikin kuka tashiga ce masa"dan kayi auren wucin gadi dani haka bayana nufin kana da cikekken ƴanci a kaina zaka fita wayo dani a duk sanda ranka yakeso ko kayi sha'awar yin haka ba.

Nasan kana gujema aikata zina ne amma bakayi la'akari ko tunanin shiga hakkina ta ɗiya mace da kayi ba,kasan zaka iya rabuwa dani ako wani lokaci meyasa kakeson muriƙa samun kusanci da junamu mesaya kakeson sainayi sabo dakai ahalin hakan cutuwace a gareni,kaga Oga dukda basan hukuncin hakan a addinance ba tunda ilimina bekai can ba,kafini shekaru da hangen nesa kaime hangen ka ya hango maka ka hanga ka hango shin wace fa'ida ke tare da Auren wucin gadi,tunda kashiga rayuwata na rabu da kwanciyar hankali wai meyasa saini meyasa karasa wacce zaka zaɓa matsayin matar ka ta wucin gadi sai ni?

Naga dawaya suna binka har Office ka auresu koda na wucin gadin ne amma kaƙi kodan kana ganin ba wata gata gareni ba yasa ka amsheni saboda ka kassaramun rayuwa,haɗa hannunta tayi guɗaya alaman roƙo na haɗaka da Allah kafita daga rayuwata kaje kayi rayuwarka da manyan mata nima ka barni nayi rayuwata da daidaini mana.

Tunda tafara magana yake sauraronta harcikin zuciyan sa yakejin kalmanta suke shiga masa,anƴa yamata adalci kuwa?idan tafiyar ta cigaba da hakan akwai matsala anƴa yama kansa da soyayyar sa adalci kuwa idan ya cigaba da ɓuye soyayyar da yake mata saboda yana ganin tayi ƙanƙanta ya bayyana mata"hmmmm yasauke ajiyar zuciya yana ɗan bubbuga mata ƙafada cikin salon maganar sa da kamewarsa yace"maganan ki abun dubawane daidai sanda motar su tayi parkin a cikin harabar gida su dan mustapha gida ya maidota,buɗe motar tayi tafita da gudu tunma kafin mustapha ya daidaita parkin din motan.


Alhaji Sunusi besan sanda yamiƙe wayan sa kare a kunnen sa ba yashiga cewa"Kai Jazuli ka tabbata abunda kake faɗamun hakane"eh ranka yadade wanda akira da Jazulin ya amsa ya daura da fadin wallahi Oga tunda yabi Yarinyar nan yafita haryanzu bamu ganshi ba kuma har waje mun fita amma ko kwallin sa babu,saide labari mara dadi datafi waccen"kai dallah Jazuli banason jan rai idan zaka faɗamun abu kawai kafaɗi koma menene kanka tsaye idan baso kake garin jamun rai na yanki jiki nafaɗi ba.

"Sorry Oga dama cema zanyi magana ne akan wancan ɗayan lazawan ai shima ina ganin kaman asuwanƴa nan allura sukai masa"Allu mai Jazuli yakatse shi da tambaya dan tuni jikinsa ya dauki wani irin rawa tsoro da ruɗani suka shigeshi lokaci daya zufa ce ke karyomasa hajia Bilki dake zaune kusa dashi tana jin komai dayake yasaka wayan a handfree amma dukda haka be hanashi daurawa a kunnen sa ba.

"Jazuli ina jakar ita tayi karfin halin tambaya shikan Alhaji Sunusi bashima da wannan karsashin dama zaman jiran sa take yamata Alkawarin kudin 3million dan tace masa tanason haɓaka kasuwancin ta dan cemasa tayi Saudiyya takeson kai wasu kayan.

Shiko Jazuli cike da halin ko in kula da rudewan da suke ciki yace"Jaka ai tuni sun fece da ita,nifa Alhaji gaskiya tsorona Allah tsorona waƴan nan mutunen masu neman talauta mutane dan da alama da shirin su sukazo"kana ina?"wai wa ni hajiya kike tambaya to wallahi inde ni kike nema kima dena dan yanzu haka ina cikin mota hanyata ta tafi garin mu,yau naga waƴanda sukafini taurin kai yau naga waƴanda suka fini iya shege sata rana tsaƙa ƙuru ƙuru ido na ganin ido kai ina gwara nakoma can garin mu nayi rayuwata cikin salama dana zauna nan nima asaka sunana cikin masu lefi Hajia Alhaji karku sake kirana awaya ta ba abunda nasani kuma banga komai ba yakare maganan bawasa  acikin muryan sa.

"Dakata Jazuli Alhaji Sunusi yayi saurin katseshi bayan ni da hajiya wayasan da wannan magana cikin ƴan term ɗinmu"babu kowa Alhaji dama Alhaji naso kira"a rude yace fatan de baka kirashin ba Jazuli yanda yayi maganan haryaso ba shi tsoro amma ya matse yace"ina bande fada masa ba,amma muddin kabari ƴan Hotel dinnan suka kai report awajen kolawa to fa sunan ja Sorry ba alhaji Babba da kake tsoron haji ba duniya gaba ɗaya zatasan halin da kake ciki daga haka be jira cewan saba yakashe wayan sa.

Zagaye falon ya shigayi cike da tsoron abunda ze biyo baya idan Alhaji Surajo yaji wannan maganan yaze daukeshi duk rashi kirkinsa da rashin imanin sa Alhaji surajo baban sane yadame shi ya shanye.

Yana cikin wannan hali mai gadinsa da driver suka shigo cicciɓe da Basma wacce bata ko numfashi da gudu Hajiya balki tayi kansu ganin yanda suka shimfiɗe mata ƴa makar gawa saman kugera.....


ALLAH YASA MUDACE

AUREN WUCIN GADI 2Where stories live. Discover now