TA ƘI ZAMAN AURE...

By KhadeejaCandy

8.9K 367 24

"Ni ma ina da buri, ina da mafarkai irin na kowace mace, sai dai kuma kaddara ta shata min layi, yadda alƙala... More

Chapter 1
Chapter - 2
Chapter -3
Chapter -4
Chapter -5
Chapter -6
Chapter -7
Chapter -8
chapter 9
Chapter -10
CHAPTER 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Last Free Chapter

Chapter 11

372 26 2
By KhadeejaCandy

Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*

✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧

𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆

*Talla👇👇👇*

https://chat.whatsapp.com/GY1W0qJiFbJD5A5J6F0fqA
*INA MATAN DA SUKASAN DARAJAR GYARA❓DAKU NAKE MACE MAI GYARAN BATA ZAMA BORA❌*

*KUZO GA INGANTATTUN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI💪BA MUNA KAYABA❌ HAJIYA KIZO KISAI KAYAN MATA WURIN DA BAZAKIYI ASARAR KUDIN KI BA*

*INA MASU CEWA NI KO NASHA KAYAN MATA BASAMIN AIKI HMMM HAJIYA BAKIDAI SIYA KAYA MASU INGANCI BANE, KAYANMU SUNA KARA NI'IMA, TAYARDA SHA'AWA, DADI, TIGHTENING (MATSI), CIKO DA GABAN MACE (DUK BUDEWAR SA), DUMIN GABA GA, KAMSHIN GABA GA KUMA NA KARA DANDANO OVER 💃💃💃💃💃👉 GA KUMA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI DAGARGAZA SANYI KODA YA SHEKARA 10 A JIKINKI* 09038090328

*A DAYA BANGAREN KUMA MUNADA SABAYA MAI GYARAN NONO DUK LALACEWAR SA KO KIN HAIHU GOMA SABAYAR MU ZATA CIKO MAKI DA BREAST SUYI GIRMA SOSAI MADAME*

*GA KUMA TA HIPS (MAZAUNAI)SU CIKO SUYI BULBUL NONO YA CIKO SOSAI HJY KIYI KIBA YAR DAIDAI SKIN DINKI YAYI KYAU KI KOMA TAMKAR TARWADA*

AKWAI KUMA NA GYARAN NONO WANDA BAYA SAKA KIBA💃💃💃

GASKIYA NA YARDA DA INGANCIN KAYANTA👆👆👆


*Chapter - 11*

Ban bude ledar da na isa da ita gida ba, kudin ma sai na boye ban bari Mama ko Hana sun gani ba. Bayan na yi sallah La'asar Mama ta kira ni na fito ta ba ni danta malelen da aka girka, ko karba ban yi ba na ce na koshi daman wadda ya ci kayan dadi me zai yi da wani malele.

“Me kika ci?”

“Na ci abinci a can”

“Yanzu gaban maza kika zauna kika ci abinci saboda ki nuna ba ki da tarbiya? Kuma rokonsa kika yi? Ai na ga kin dawo da ledodi kin boye baki nunawa kowa ba. Yanzu duk abubuwan nan da suka faru kwana biyu ba su isa su zame miki darasi ba? Wai Noor idan baki yi hankali yanzu ba yaushe zaki yi hankali? Matukar baki canja rayuwa ba zaki sha wahala nan gaba, ki ce yayar Hannatu amman ke ce shashasha”

Na sauke kaina kasa ina jin kalamin na Mama yana min yawo a zuciya ta bangaren rashin dadi.

“Ba a gaban maza na ci ba, ni kadai ce lokacin da na ci, ya bar ni a dakin ne sai da na koshi sannan ya dawo”

Bata sake ce min komai ba, kuma daman bana wani abun fada dan haka na juya na koma dakin. Ban sake fitowa ba sai da aka yi sallah magariba ina gama sallah na kwanta ina jiran Yaya ya shigo na ari wayarsa na kira Zafeer domin na san Mama ba zata bar ni na fita na je gidansu Zainab na ari wayar Mamanta.
Bayan Sallah Isha'i Baba ya shigo gidan, ina jinsa na yi saurin dauko leda daya da na shigo da ita na dauko kudin da na boye na fito na tare shi.

“Baba sannu da zuwa”

“Yauwa”

Ya amsa min kamar yadda ya saba da daure fuska, na dan tsawon wuya na leka dakin Mama na ga bana hangota sannan na mika masa ledar hannuna.

“Gashi Zafeer yace a baka”

Na hada masa da kudin da na karbo gurin adashen Mama. Baba ya karba yana dubawa.

“Me ye ne”

“Ban sani ba ni ma cewa dai yayi a kawo maka”

Ya bude abincin da ya fara expire saboda yana cikin leda kuma gashi na masa mugun boyo. Sannan ya kirga kudin na yi zaton dadi Baba zai ji saboda ya min gori jiya cewar Zafeer be taba ba shi ko dubu goma ba, a tunanina hakan da na yi zai haifar da faeinciki da jindadi a zuciyar Baba sai na yi arba da tsabanin haka.

“Fada masa kika yi? Ni fa bance ya kwashe kudin aikinsa ya kawo min ba, kar ya zo yana kuka da ni, kuma ban ce yayi sata ya ba ni ba, duk abun da zai biyo baya kar ya saka sunana a ciki”

Na yi shiru na rasa me zan ce, ban san taya zan kare Zafeer ba, haka kuma ban zan iya fitowa na fadi gasjiyar cewar kudin adashen Mama ne ba, kamar yadda kalaman Baba basa min dadi a yanzu.

“Wai ance ana kiran in ji Zafeerrr”

Almajirin da aka aiko ya fada bayan yayi sallama. Na kalli kofar Baba ma ya kalli kofar a daidai lokacin da Mama ta fito daga dakinta tana kallon ledar dake gaban Baba

“Je ka ce tana zuwa”

Mama ta fada, sai Baba ya mike tsaye.

“Bari na fara magana da shi daman ina nemansa”

Kan kace kwabo Baba ya mike tsaye ya fice daga gidan, ban ji komai a raina ba domin na san duk tsanani Zafeer ba zai tona min asiri ba ko da kuwa be san me na shirya ba ba zai taba fadar abun da zai haifar min da matsala ba. Bayan fitar Baba Mama ta dube ni ta ce.

“Fada masa kika yi Baban ki yace be bashi komai ba?”

Na sauke kaina kasa kamar ba ni ba, cikin na tsananin ladabi da ban san ta ina yake fito min ba na ce.

“Aa Wallahi ban fada masa ba, kawai dai kila anyi dace da yayi niyar aikata hakan ne”

“Amman wannan ledar tun dazun kika shigo da ita”

“Eh shi ya bani, acan ya siya komai sai ya ba ni tare da kudin”

“Allah yasa gaskiya kika fada, domin idan na gano rokon bawan Allah nan kika yi kudi saboda ki bawa Babanki sai na miki mugun duka a gidan nan”

A take cikina yayi kuka ba irin kukan yunwa ko wahala ba, kukan tsoron shan duka da na san idan Mama ta gane a gurin adashenta na karbo kudin nan sai ta fi cin ubana ma fiye da roko”

Ta dauke ledodin ta shige ciki ni kuma na juya na koma dakinmu ina ta tunanin matafitar da ban yi tunaninta ba tun farko. Bayan kamar minti talatin Baba ya dawo cikin gidan ya yana kwala min kira.

“Noor”

“Na'am”

Na amsa da sauri sannan na mike tsaye na fito.

“Tafi yana jiranki”

Na juya na koma cikin gidan ina jin faduwar gaban da ban saba ji ba, kuma ban san na Miye ba. Hijab dina na dauko na saka zuciyata bata raya min ransa zai bace idan na ba shi abun da na zo masa da shi daga gurin Kareem ba, kwalkwalwa ta mantar da ni gargadi da yayi min har sai da na fita rike da leda na tsaya a gabansa ina kallon yadda yanayinsa ya canja ba kamar yadda na saba ganinsa ba.

“Zafeer”

Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya kalleni.

“Noor Baby Noor”

Yanayin yadda ya kira ni ma muryarsa ta sauya, ina karantar damuwar dake tattare da shi tun kamin ya fada min.

“Baba ya maka wata magana marar dadi?”

“Mai dadi ce amman dacin mai daci ne a gareni yanzu”

“Me yace maka?”

Ya kalleni.

“Baku yi magana da shi ba?”

“Magana daya ce kawai? Ni dai ka fada min”

Na masa magana a shagwabe kamar zan masa kuka.

“Baba ya min godiya, me kika bashi?”

“Kyauta da kudi dubu goma na ce masa kai ne ka ce bashi”

Ya sake dubana da mamaki.

“Kyautar me? Ina kika samu kudin?”

A nan fa ido ya raina fata domin ba zan iya fadar yadda na samu kudin ba, kara ma kyautar zan iya fada tun da gashi har na riko masa wata.

“Gashi dai yanzu ni dai na riko maka kayan dadi”

Na mika masa, sai ya kai hannu ya karba ya duba a take ya hade rai.

“Ban miki magana akan mutumen nan ba?”

“Shi ne yace a kawo ni zai duba min hannu ba ni ce na je ba”

“A gurinsa kika karbo kudi kika bawa Baba? Noor me ke damunki...!”

Ya daka min tsawa sai da na zabura, ba zan iya cewa ba a gurinsa na karbo ba saboda ba zan iya fada masa gaskiyar inda kudin ya samo asali ba.

“Mutumen nan kokarin juyar da hankalinki yake, yana son ya siya Baba, yanzu Baba ya gama fada min yana son ya aurar da ke karshen shekarar nan idan na shirya na fito, karshen shekara nan sauran wata uku, ba ni da gurin aje ki Noor, ba ni da wata kafkarfar sana'a da zan iya rike ki, a yanzu ne zan tafi service, ba ni da wasu kudi da na aje domin yin hidima, ina ganin kamar mutumen yana kokarin rabamu ne, kuma ya fara yin nasara tun da gashi har na miki magana amman baki ji ba”

Fada yake min sosai har jikina yana rawa domin be saba min fada ba, ban saba ganin bacin rai a fuskarsa irin haka ba. Na kai hannu na karbi ledar na aje a kasa jikina yayi sanyi, sam bana son na ji wani abu mai alaka da rabuwa tsakanin ni da Zafeer. 

“Ba zan sake ba, daga yau ba zan sake rashin ji ba, ba zan sake kin jin maganarka ba, ko ya zo ba zan sake kula shi ba, kuma zan yi magana da Baba zan fada masa ya bari har sai ka shirya tukuna”

Ya matso kusa da ni yana kallona.

“Ba ke zaki yi magana da shi ba, zan turo iyayena su roka min Baba ya daga har zuwa next year ko ma shekara biyu, inda muka fito be kai inda zamu nisa ba, kuma ba ki yi girman da Baba zai matsu ya aurar da ke ba, sai dai wata kila saboda wannan rashin jin maganar da kike ne, dan Allah ki natsu Noor, ni dai har ga Allah ina sonki a haka, kuma na so ki tun kamin natsuwarki ta kawo haka, kuma ina fata ina tunani nan gaba zaki daina, idan ma baki daina ba ni dai Allah ya saka min sonki a haka ina matukar kaunarki”

“Ni ma idan ba kai ba zan ma auri kowa ba”

Na samu kaina da fadar haka, sai na ji murmushinsa.

“Bana fatan ki auri kowa sai ni, domin ni kadai zan iya dake, babu namijin da zai iya zama dake Noor ya rike ki sai ni, duk wani mai ganin yana iya zama dake gani kawai yake, amman babu wadda zai iya zaman aure da ke, sai ni ke tawa ce har abada”

“Ba sai ka yi wata hidima mai yawa ba Zafeer, ni na ma yafe maka sadakin, kuma ba sai ka yi min tufafi ba, can gaba idan ka samu sai ka yi min”

Na fada a iyakar gaskiyata domin bana son masoyin nawa ya wahala. Sai na ji hannayensa a kumatuna ya kama fuskata ya rike yana kallon cikin idona ba tare da tunanin wani zai fito ya ganmu ko ya wuce ba.

“Dan Allah ki natsu Noor, ki daina kula wannan mutumen bana son wata alaka ta sake hada ku, da ace ina da hali maganar da Baba yayi min sai na fito kai tsaye ayi auren nan, amman bana son na yi aure ni a wahale ke a wahale rayuwa nake son mu yi ta jindadi bance sai na zama mai kudi ba, amman zan wadata ki da kwanciyar hankali da tufafi da abinci mai kyau daidai gwargwadon halina”

Kamar an kwance wasu notuka a cikin kaina an daure wasu, an sabunta shafin tunanina, an wanke kwakwalwata an haska basira, haka na ji a lokacin da Zafeer ya zuba kalamansa a cikin kaina. Sai aka sakaukar min da natsuwa da wani rauni a zuciya, aka share duk datti yake a cikin tunani na, aka daure wasu karafuna da suke rawa a kaina. Daga ranar ne Zafeer yayi nasarar sauyani daga wata yarinya da ake cewa bata jin magana zuwa mai tsananin ji, daga marar hankali da shashanci zuwa mai natsuwa da hankali da tunani. Daga ranar aka dauke nishadi na, aka nesantar da rashin tunanina, aka bude min wani sabon littafi mai sabon shafi da sabuwar rayuwa.

Tambaya ta yake wane kalar gida nafi sha'awa a rayuwata, ina fada masa yadda nake son tsarin gidanmu ya kasance a ban gaba idan zai gina mana gida. Sai goma na dare muka yi sallama ya tafi ba tare da ya karbi ledar ba, ni ma kuma ban sake kallon inda take ba tun bayan da na karba daga hannunsa na aje ta a kasa. A daren ranar ban yi bachi ba, ina ta jina kamar bani ba, abun da ban taba yi ba a rayuwa shi na raya daren da shi a ranar wato sallah dare, sai a lokacin da na daga hannu da niyar addu'a sai na rasa wacce zan yi, Allah ka bawa Zafeer abun aurena ko kuma Allah ya sa Baba ya daga masa kafa har zuwa lokacin da zai samu komai? Na kasa rokon ko daga sai kawai na roki Allah ya lullube mu da alheri ni da Zafeer da Iyayena.
Sai da na yi sallah Asuba sannan bachi ya buge ni, na fara bachi kamar ba gobe. Ko da na farka Rana ta yi sosai abincin karyawar da aka aje min har ya sha iska, a haka na dauki kokon na sha, na balle magani ba dan rai yana so ba na sha sannan na fito waje ina kallo ashe Mama har ta gama gyara gidan. Abakin balcony na zauna ina tunanin kudin da na karbo jiya, gashi tace a dawo mata da shi yau, kuma ban isa na tinkari Baba nace ya bada kudin ba, a take wata zuciyar ta raya min cewar na fadawa Mama gaskiya idan ma kashe ni zata yi to ta kashe ni na huta. Cikin karfi hali na tashi na nufi dakin shi kam tsoro daman na dade ina samun nasararsa domin ko ina jin tsoro ina aikata abu balle kuma yanzu da gaskiyarce nake nufi bayyanawa, a tare da canjin da yake jikina yanzu. Sallama na yi na shiga dakin na zauna kasa ina rike da hannuna na ce

“Mama daman wata magana ce ma zo mu yi gaskiya ce na zo na fada miki”

Tana jin haka ta kashe redio dake kunne ta kalleni.

“Gaskiyar me?”

Ban boye mata komai ba, na fada mata dalili na yin haka saboda Baba yayi gori ne, sannan na fada mata inda na karbo kudi. Wani irin wawan duka ta kai min a fuska

“Wannan yarinya baki da mutunci, yanzu kudin da nake tarawa na aure kika je kika karBo kika ba ubakii da baya tsinana muku komai? Ashe dai ke har abada ba zaki yi hankali ba? Har dubu goma Noor?”

Ta mike tsaye ta fice daga dakin a take hankalina ya tashi gabana ya tsananta faduwa, sai gata ta shigo dakin rike da katon kudi.

“Ce min karya kike ba gaskiya ba ne”

Cikin kuka na ce

“Da gaske ne Mama, amman na miki alkawari daga wannan ba zaki sake dukana akan rashin jin magana ba, Wallahi na daina Mama”

Ina maganar ina yin baya ina tara hannun nawa mai ciwo ina kare fuskata. Wata kila tausayi na bata sai ta jefar da itacen kasa ta fashe da kuka.

“Ai har abada ba zaki daina ba, ba zaki daina saka min bakinciki ba, ba zaki daina wannan haukar ba, ni dai ban yi ma iyayena haka ba, uwata bata zubar da hawaye akaina ba, amman ke ina ji miki tsoron gaba Noor bakinciki uwa bashi da kyau, ni ban san wace irin ya Allah ya ba ni ba, kara ma ayi miki auren na huta ni, yaje can shi idan zai iya ya rike ki, idan ba haka ba nan gaba gawata za'a gani, bakinciki yana cikin zuciyata yayi min yawa”

Ta zauna bakin gadonta ta rike kai tana kuka, ni ma kukan nake amman hakan be hana ni bata hakuri ba.

“Yi hakuri Mama, Wallahi ba zan sake ba daga yau, dan Allah ki yi hakuri”

“Tashi ki fita ki bar min daki”

Ya fada cikin kuka, sai na tashi na nufi kofar dakin na fita, hakan kuma yayi daidai da shigowar Ya Nabil yana rike da bakar leda, na nufi dakinmu na zauna ina sauraren zuwan Yaya domin na san zai zo matukar yayi arba da hawayen Mama, sai gashi kuwa ya shigo dakin ya doso inda nake zaune, wani mugun shuri ya kai min a ciki har sai da jini ya fito min ta baki kokon da na sha kuma ya fito min ta hanci, ya fisgeni ya jefar a dayan gefen ya saka kafarsa ya bugar min kai.

“Wai ke miye a cikin kwakwalwarki ne Baba ya saka ta kuka ke ki saka ta kuka? Me yake damunki?”

Kamar zai ruguza dakin haka yake tambaya yana shurina kamin ya cire talkamin kafarsa ya fara dukana da shi, can kuma ya fita sai gashi ya dawo rike da wayar wuta ya fara dukana da ita ta ko'ina har sai da ya fasa min jiki, ba kafai yake dukana ba, amman idan ya fara be iya ba sai ka rantse baya so na ko babu imani a tare da shi idan yana dukan. Sai yayi min zina zina ya hada min jini da majina sannan ya fita ya bar ni ina kwara amai, ko'ina an jikina yana zugi kamar an zuba min wuta.


KAREEM POV.

Noor na ficewa da yan mintuna Hafiz ya shigo office din daman nan suke zama idan yamma ta yi kowa ba shi da aiki sai su tare a nan suna tattauna ko warware wata matsalar, Kareem dake kallonsa yana Murmushi ya ce.

“Yanzu nan Noor ta fita”

Kamar wadda aka yi ma albishir haka Hafiz yayi murmushi.

“Me ta zo yi?”

“Hannu ta zo na duba mata, kuma ta ba ni sako na baka”

Kareem ya fada masa, Hafiz yayi fuskar mamaki.

“Sako? Ni?”

Kareem ya zayyana masa yadda suka yi da Noor yana kwasar dariya kamar wadda yayi a dazun bata wadace shi ba. Hafiz ma dariyar yake sosai

“Tun a nan zaka fahimci yarinyar nan she's very silly girl, idan ba ita ba wa zai tonawa Babansa asiri? Kuma tace wai a bawa saurayinta kudin? Da Baban ya san ta zo nan maybe sai ya yanke mata kafafuwa”

“I'm telling you, tace kar na fada masa ai nace amininsa ne ya fada min”

Kareem ya saka yatsansa ya cire kwalla data cika masa ido saboda dariyar da yayi, ya busar da iskar bakinsa.

“Na manta rabon da na yi dariya irin yau Wallahi”

Hafiz yayi murmushi yana kallonsa.

“Ka ga idan ka aje ta a gidanka ka huta bakinciki”

Kareem ya kai hannu ya dauki tissue ya goge hannunsa da idonsa.

“Kai ma dai ka kusan zama kamar ita, ni dai na fada maka sakonta next time kar ta zo tana min masifa”

Hafiz ya kwantar da kansa jikin kujerar.

“Ba zamu fasa ba, zan iya ma Babanta gidan, kuma zan nemi saurayin na ba shi jari, ko na taimaka masa ta wani bangare”

Da mamaki Kareem yake kallon abokinsa.

“Wasa kake?”

“Wallahi da gaske nake, za mu fada masa ai ta nemi a taimaka masa ne, kuma taimako ba laifi ba ne”

Kareem ya jidadin jin haka daga amininsa hakan na nufi ya janye kudinsa na son sai ya lalata alakar Noor da wadda take so.

“Da ka kyauta kuwa, dan dai tana son gayen nan, duk da yake ba lallai ne ya iya rike ta ba ma idan ya aureta domin na ga yana da zafin rai, ita kuma sai mai hakuri zai iya zama da ita”

“Ita ai bata san wa take so ba, har yanzu akwai kurciya a tare da ita, kuma yanayin girma kowa da yadda yake yinsa, wani sai yayi shekaru yake hankali ya natsu wata macen ma zaka ga sai ta haihu, da zaka gwada mata soyayya tsab zaka siye zuciyarta balle ma har ta saki jiki da kai nan da nan ne zaka shawo kanta”

“No ni ba zan iya ruguza soyayyar wani ba, kuma ba zan so kowa ya samu kansa a yadda na samu kaina ba, ba zan so ta auri wadda bata so ba”

“Amman kai kana sonta ai”

“Wannan yar mitsitsiyar yarinyar? Ni fa ba sonta nake yi ba, kawai dai tana burge ni ne”

“Rainonta zaka yi irinsu sun fi dadin aure, yadda duk ka bi da ita haka zata tafi, ni dai burina ka rabo da Safeena kuma ka samu farinciki ne ne manufata”

Hausawa suka ce dan halak kaki ambato, wai da an ambace shi sai ya bayyana haka kuwa ne ya faruwa a daidai lokacin da Hafiz  ya ambaci sunan Safeena sai ga kiranta ya shigo wayar Kareem. Abokinsa ba zai iya rejecting ba, ba kuma zai iya kin picking ba saboda Safeena ce, tsohuwar masoyiyarsa dan haka ya tashi a hikimance ya fice daga office din ya nufi wani bangare dabam ya hade rai sannan ya amsa wayar.




__________________

Hmmmmm yanzu ne zamu tsuduma a cikin labarin, ina fatan kun shirya. Kun ji dai Kareem yace shi ba sonta yake ba. To Team Kareem sai ku tattara kayanku a gurin Noor ku ware 😆

Team Zafeer kun ji na ku yana cikin damuwa, sai ku fara tara masa kudin aure ko kuma ku roki Baba ya daga masa 😁

Noor dai tace ta daina anya zata iya? Ga mu dai gani gurguwa da aure nesa 🤔

Continue Reading

You'll Also Like

49.3K 2K 16
Book 2 of the 𝕱𝖎𝖌𝖍𝖙𝖈𝖑𝖚𝖇 series {Duology} 𖤓 𝕾𝖔𝖒𝖊 𝖒𝖊𝖒𝖔𝖗𝖎𝖊𝖘 𝖓𝖊𝖛𝖊𝖗 𝖑𝖊𝖆𝖛𝖊 𝖞𝖔𝖚𝖗 𝖇𝖔𝖓𝖊𝖘. 𝕿𝖍𝖊𝖞 𝖇𝖊𝖈𝖔𝖒𝖊 𝖕𝖆�...
15.8K 531 51
رواية مُنقذي سبايا داعش للڪاتبة ورده الشيخ محمد ((منقووولـــــــة)) « فتاة عراقية تخطف وتسبي من قبل ايدٍ اتخذت الدين غطائاً لها تسمى " دا؏ـش" تروي...
19.9K 471 55
"Do I have to end up like this because of love?"