TA ƘI ZAMAN AURE...

By KhadeejaCandy

3.4K 292 20

"Ni ma ina da buri, ina da mafarkai irin na kowace mace, sai dai kuma kaddara ta shata min layi, yadda alƙala... More

Chapter 1
Chapter - 2
Chapter -3
Chapter -4
Chapter -5
Chapter -6
Chapter -7
chapter 9
Chapter -10
Chapter 11
CHAPTER 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Last Free Chapter

Chapter -8

155 17 0
By KhadeejaCandy

Daga Yaya har Mama babu wanda ya ce da ni shigo ki zauna ko kuma juya ki koma. Ina tsaye a gurin na kasa kuka na kasa magana har Baba ya shigo.

“Shiga ciki ki zauna mana, ai duk abun da kike ba laifin ki ba ne uwarki ce ta ke goya miki baya, baki da matsala ke”

Cewar Baba sannan ya wuce ni ya shiga cikin gidan. Mama kamar tana jiransa ta ce.

“Daman ai kullum ni ce ice mai dadin hawa, nan gana Noor ko kisan kai ta yi ni zaka dorawa laifi, duk abun da kowa zai aikata kaina zai dawo, shin ni kadai nake da hakkin tarbiyantar da ita? Kai ba Uba ba ne?”

“Saboda ina uba sai aka ce na zauna gida na kula da yara? Tarbiya ai ta uwace no Cewa aka yi na fita na nemo, ke zaki kula da gida dan haka dole duk abun da yara suka yi na ce laifin ki ne”

Mama ta yi shiru na san kuma ba dan ta rasa abun cewa ba sai dan tana gudun fadan yayi nisa.

“Ni na gaji da halin yarinyar nan, tun da aka haife ta cikin wahala nake, kar taje nan gaba ta dauko min abun magana tun da har ta gane bibiyar maza a inda suke, daga bige hannu da kai ban san inda za'a tsaya ba, ko yanzu Allah kadai ya san gaskiyar abun da ya faru, kar taje ta dauko min abun kunya na kasa fita cikin jama'a, zan fadawa yaron idan ya shirya fito ayi auren daman ni dai ba wani abu na aje ba, balle na ce zan dauka na kai masa, ko zane daya Allah ya hore masa ya kawo a hada ya da tabarma ayi musu aure su je can su karata, ke dai ba iya tarbiyarta kike ba tun rana karama balle kuma yanzu da take kara girma”

A fusace Mama ta mike tsaye sai ganin na yi bulalar wayar wuta ta fado a jikinta.

“Wai Malam tunanin kake abun da Noor take dadi yake min? Ko kuma ganin kake ni nake zaunawa na tsara mata shirirtar da zata je ta yi a waje? Daga Islamiya fa ta bar yar'uwarta ta tafi gurin yawon shiririta, a can idan kasheta za'ayi an dade ba'ayi ba, kuma kamar Noor ace ta san ta tsame kafa ta bi wata su tafi restaurant, kanen ubanta ne a can ko na uwarta, babu sanarwa babu neman izinin kowa”

Baba ya rike gemu.

“Toh.... Ai ga irinta nan a gabansu kike fada min magana son ranki kina min tsawa saboda kin isa, ai tarbiyarce suke kallo suna dauka”

“Tarbiyar ce, idan baka Gamsu da ita ba Malam ka auro wata uwar ta zo ta ba su wata tarbiyar, daman ai ka saba aure aure”

Yau kai na ga dabam, Baba ce take fadawa Baba magana cikin bacin rai abun da bata taba ba a gaban idona. Baba kamar yana jira sai ya nufe ta yana nuna kansa.

“Ni kike cewa na saba aure aure...?”

Ya Nabil dake zaune yayi hanzarin mikewa tsaye ya tare Mama ya shiga tsakiyarmu.

“Toh ko dukana zaka yi? Nace dukana zaka yi?”

“Ba dukanka zan yi ba Baba amman ba zan zuba ido ina kallo ka daki Mama ba a gaban idonmu, Baba abun da kake babu dadi wani abun ba laifinta ba ne amman sai ka dora mata laifi komai aka yi a gidan nan cewa kake laifinta ne, ta ina yanzu laifin Noor ya shafe ta? Baba be kamata ace a gaban idonmu ka doke Mama ba wani abun ai ka daga mata kafa ko dan mu”

“Ayyy haka ne, lallai Nabil wuyanka yayi kwari, yanzu ni zaka zauna ka tsarawa magana haka son ranka? Ashe kai ma baka da mutunci toh sai ka doke ni na san ka girma marar mutunci, saboda ina talaka kake raina ni?”

Mama ta ja Nabil gefe ta tura shi.

“Fita can waje idan ya fita sai ka dawo...”

Tana rufe baki Baba ya dauke ta da mari.

“Ya fita sai na fita ya dawo wato ga mahaukaci ko? Ga mahaukaci na hauka”

“Baba...”

Ya Nabil ya zaburo da karfi yana hakki har sai da Mama ta rike shi.

“Kul kul kul ko yanka ni ubanka yayi ka kai hannu ka dake shi ban yafe maka ba Nabil, karka kuskura zuciya ta debeka ka aikata abu makamancin wannan”

Sai kuma ya fashe da kuka Mama ma ta saka kuka.

“Fice ka bar min gida, karka sake kwana min a gida daga yau, kuma kar a sake ba shi abincin gidana”

Baba ya fada yana nuna masa kofar waje. Ni kam na yi tsaye kamar hoto ina kallon drama da ake a cikin gidanmu, na san halin Baba na dukan Mama ko fada mata magana marar dadi, domin mahaifina irin mazajen nan ne da ba su girmama matansu sun maida matansu kamar ba yi, shiyasa duk auren da yayi babu mai dadewa suke fita su bar Mama. Sai dai abun da ban saba gani ba shi ne mayar da martani na magana da Mama ta yi a yau, da kuma yunkurin da Ya Nabil yayi, duk kuma saboda ni ne. Baba ne ya fara ficewa daga gidan sannan Yaya ya nufo kofar fita sai na jinin jikina na matsa jikin gini sosai gabana na faduwa hawaye na ta zirya a fuskata. Ashe dai ban tsira ba domin yana kawowa kusa da ni ya dauke ni da mari mai bala'in zafi da radadi har sai da na taune halshena. Kuma yaja ya tsaya a gabana, jira yake na yi kuka ko na kalleshi ko kuma na furta wani abun yayi min duka. Ban yarda na daga ido ba balle na kalleshi ban bar wata kalma ta fito daga bakina ba, kuma kuma ban yunkurin yin motsi ba har ya gaji da tsayin yayi ficewarsa.

Sannan na dago kai na kalli na kalli cikin gidanmu, Mama na jiyo tana fadin.

“Kin yi nasara an kuri dan'uwanki ga dakinsa can sai ki share ki zauna, ba ke kadai na haifa ba amman ke kika saka ni ciwon kai da ciwon zuciya kullum, girmanki ya kai ace kina da wayo da hankali amman yayi miki nisa, baki bar ni da bakincikin ubanki ba, ba ki bar ni da bakincikin neman abun da zan aurar dake da abun da zamu ci ba, wani kike lalabowa kina yafa min, kullum nuna miki ake amman sai ki rufe ido bako duban daidai na gaji da halinki Noor”

Na durkusa daga inda nake tsaye ina son na bata hakuri na kasa magana. Gurin da muke aje kayan wanke wanke ta nufa tana juyowa na ga wuka a hannunta, domin tabbatarwa sai ta nufi suminti ta koda wuyar sannan ta juyo ta kalleni.

“Kin ga wuka nan na koda, yau sai na kwantar da ke na yanka, na gaji da halinki yau din ba zaki kwana da rai ba...!”

Yanayin da na samu kaina a lokacin da Mama da nuna ni da wukar tana furucin da ya dursaso da tashin hankalina a kusa ya wuce misali. Ashe har na gundurar da Mama haka, rashin jin magana ta ya kai Mama tace zata yanka ni? Ashe uwa zata iya kashe yarta? Na mike tsaye ina jin kamar wata murya na fada min na juya na fice daga gidan, sai dai idan na fita ina zan je? Wa zan je na roka ya bawa Mama hakuri? Yau ta yi fushin da bata taba yi ba, yau ta furta min kalmar gajiya, ta furta sao ta yanka ni, na tabbatar babu wadda zai ceto ni a yau na kwana da rai.

Na fito na tsaya daga bakin kofar gidan na raba jikin ginin na rumgume hannuna ina tunanin inda zan je. Kamar ance dago kai ina dagowa na yi arba da Hana tana kuka ashe tana cikin gidan amman ban ganta ba duk abun nan da ake.

“Ki tafi gidansu Maman Zainab ki kwana, dan Allah karki gudu ki karawa kanki laifi, Baba yayi min duka saboda na ki fadar inda kika je lokacin da na dawo daga makaranta har sai da na fada sannan ya kyale ni, Noor miye amfanin abun da kike yi? Dubi yadda kika sakawa kowa bakinciki yau”

Ita ma dai bani da amsar da zan bata dan haka na duka na duka a gurin ina jin halshena yana zogi saboda marin da Yaya Nabil yayi min.

“Hannatu...”

Mama ta kira da karfi, sai ta juya da sauri ta koma cikin gidan ta bar ni a gurin duke ina tunanin makoma. Can kuma na mike tsaye na nufi gidansu Zafeer domin ban san wani abun da zan yi ba, sai dai tunawa da ba lallai ne Mama ta hakura ba ko da ya mata magana ya katse hanzarina, a madadin shiga cikin gidan sai na mike na kama hanyar gidansu Kareem. Tafiyar da zan biya 200 a kai ni gidan ita nake yi a kafa ba tare da gajiya ko kasawa ba. Zan iya shaidar kaina ina ba basira da gane abu ko da kuwa sau daya na gani, hakan ya saka na yi saurin gane gidan sai dai na shiga unguwar a lokacin da sawu ya fara daukewa ne, bana da agogo balle na iya fadar karfe nawa, amman tabbas dare yayi domin mai gadin gidan ma hanani shiga yayi bayan na kwankwasa.

“Toh dan Allah ka fada masa Noor ce tana waje”

Na bashi sako sannan na ja na tsaya ina jin tsoron wajen saboda babu kowa.

“Ki jira a nan ina zuwa”

Ya rufe gate din ya bar ni a gurin tsaye, bayan dan lokaci na sake jin an bude kofar.

“Shigo”

Na shiga cikin gidan, na doshi main door kamin na karasa Kareem ya fito sanye da pajamas ya nufo inda nake sai muka ci karo a tsakiyar gida.

“Noor lafiya?”

“Mama tace sai ya yanka ni, tace yau ba zan kwana da rai ba, ta nuna min wuka kashe ni zata yi, Yaya yayi fada da Baba har ya koreshi saboda ni, kanwata ma an mata duka saboda ni”

Ina maganar hawaye suna fadar yau ce ranar mu, jikina na karkarwa kamar mai jin sanyi. Shiru yayi yana kallona kamar mai tunani me zai fada ko ya aiwatar.

“Babana yana jin maganarka, Mama kuma tana jin maganar Baba, so nake ka tafi ka bawa Baba hakuri shi kuma ya bawa Mama hakuri ta yafe min, ka fada ma Baba ya fada mata daga yau ba zan sake ba, ka ce ina rokonta ta yafe min”

Na fada masa bukatata.

“Waya kawo ki nan?”

“A kafa na zo, ka yi hakuri ba zan sake takura maka ba daga yau ba zan sake batawa kowa rai ba”

Ni dai ban san ya aka yi ba na jini na jikinsa ya rumgume yana rarrashina.

“Ya isa haka Noor I'm sorry”

Ji na yi kamar na samu wata mafaka sai na fashe da kuka mai mugun karfi.

“Ya isa ya isa haka kar yarana su ji”

Ya sake ni da sauri.

“Shigo ciki na canja kaya sai mu tafi gurin mahaifin naki”

Na bi bayansa muka shiga cikin falon sai na tsaya daga bakin kofa ina kallon matarsa dake zaune tana cin abinci. Sama ya nufa be jima ba ya sauko sanye da jallabiya da hula hannunsa rike da keys.

“Wani taimako take son na yi mata, zan je na dawo yanzu”

Ya fadawa matarsa, sai ta dubeshi ta dauke kai.

“Kai ka ta shafa, idan ka aikata abun kunya yayanka ne a kunya ba ni ba, ni matsalarka bata gabana”

Amsar ta bata ba ni mamaki ba kamar yadda shi din ya ba ni mamaki ta hanyar dauke kai ba tare da ya ce mata komai ba ya kalleni ya ce

“Mu tafi”

Na juya na fara fita sannan ya fito, sai da ya janyo mota sannan na bude da hannun hagu na shiga domin na dama a daure yake. Tun da muka shiga motar be ce min komai ba, ni ma ban ce masa ba muka isa unguwar yanayin yadda na ga mutane sun rage ya tabbatar da dare yayi sosai.

“Ina zamu samu ganin Babanki a yanzu?”

“Yana zama a majalisa kamin ya shiga gida”

“Ina majalisar take?”

Na fada masa sai ya bude motar ya fita yana kara tambayar kwatancen domin be san kan unguwar ba.

“To jira ni a nan”

Na daga masa kai na bishi da kallo har na daina hangoshi. A kiyasina za'ayi minti talatin da fitarsa sannan na hango bullowarsa tare da Baba dake rike da fitila duk da kasancewar akwai wutar nepa. Na bude motar na fito ina kallon Baba.

“Ah ah Noor to ai da sauki ma tun da gurinka ta tafi, da ta fi duniya ai shikenan to zo mu tafi gida”

Na nufeshi ina jin tsoro, Kareem kuma ya koma cikin motar ya zauna har sai da muka yi nisa sannan ya biyo bayanmu. Baba ne ya fara sallama ya shiga cikin gidan sannan na bi bayansa.

“Ke Hajara fito ga Noor din gata nan ki yanka ta”

Da gudu na ga Mama ta fito har sai da na tsorata naja baya.

“Noor ina kika je?”

Ta tambaye ni tana kuka

“Ina kika tafi na aika nemanki ko'ina baki nan”

Ban samu amsa mata ba Kareem yayi sallama ya shigo sai Baba ya amsa masa sallamar. Kareem ya kalli Mama ya gaisheta

“Dan Allah ayi hakuri, abun da kika furta kin tsoratata ma bar gida ta tafi a kafa ta same ni har gida tace na zo na baki bakuri tare da Babanta, kuma tace na fada miki ba zata sake ba, dan Allah ki yi hakuri”

“Babu komai na yafe mata, ni ma na gane kuskuren fadar hakan da na yi bayan ta bar gidan, domin bayan gidan nan bata da wani masauki, kuma mace ce hankalin ya tashi sosai a lokacin da aka duba ko'ina ba ganta ba, wani lokacin rai ne yake baci ka aikata abun cikin bacin rai, Zafeer ma be dade da aikowa kiranta ba nace a fada masa bachi take, na mata haka ne saboda ta tsorata ta daina abun da take, ba dan ina da niyar aikatawa ba”

“Alhamdullahi, daman na san uwa dole zata nemi yarta duk runtsi, addu'a ya kamata ana yi ba sai tsoratarwa ba”

Kareem ya fada sai Mama ta mika hannu ta janyo ni ta rike.

“Ai Alhaji Noor din ce sai hamdala, ni ina ganin aurar da ita kawai zan yi na huta, shi yaron nan idan ya shirya ya fito idan kuma be shirya ba ko a Masallaci ne zan yi cigiya na bada ita sadaka, ita ta huta mu ma mu huta”

Baba ya fada, sai Kareem ya kalleshi ya ce.

“Noor din nawa take da za'ayi mata haka? A dai yi hakuri, ni zan koma ga dubu ashirin a siya wani abu”

Baba ya saki fitar hannunsa ya mika hannu ya karba.

“Ahhh Allah da iko yake, kai yaron nan gajiya da kyauta, dazun ma fa sai da ka ba ni wasu kudin, Allah dai ya saka da alheri ya rabaka da iyayenka lafiya Allah ya kara budi”

“Ameen Ameen”

Har ya juya sai kuma ya juyo ya kalli Baba dake kokarin yi masa rakiya.

“Am Baba dan Allah ina son na bada hakuri akan Nabil ka yafe masa shi ma dai ya dawo gida ya zauna, ku daina daukar zafi akan yaranku ayi hakuri dan Allah”

Baba ya amsa da sauri.

“In Shaa Allah, babu komai na yafe masa ya ci albakarcin ka ba komai”

“To na gode”

Ya juya ya fice Baba ya bishi yana addu'a, ni kuma na kalli Mama.

“Mama ki yo hakuri daga yau ba zan sake ba”

Sai ta kwantar da ni jikinta tana kuka.

“Na yafe miki Noor, bakincikin ne yana min yawa, amman dai idan bana duniya babu wadda zai fada miki gaskiya, Allah ya sauya miki rayuwa ya canja wannan hali na ki”

Ta nufi dakinta da ni tana rumgume da ni, wani dadi da natsuwa na ji marar misaltuwa saboda yafe min da Mama ta yi har ta rumgume ni.




KAREEM POV.

Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya faka motarsa a harabar gidan, sannan ya ciro wayarsa ya shiga WhatsApp dinsa da datarsa take always on ya shiga chatting dinsa da Safeena ya rubuta mata sako.

“Safeena wannan ya zama karo na karshe da zaki sake kai hannunki jikin yarinyar nan, babu wani abu tsakanina da ita, duk abun da ta fada ko Hafiz ya fada sun fada ne kawai saboda su fusata ki, ina sonki kin sani, kuma na san kina so na, amman hakan ba zai baki damar ki aikata sakarci a gaban kowa ba, ko kuma ki yi yunkurin cutar da wani ba zan lamunce miki wannan ba, kuma babu ruwanki da yarinyar nan daga yau”

Yana aje mata sakon ya bude motarsa ya fita ya rufe sannan ya kama hanyar falon gidan. Shiga falon ke da wuya sakonta ya shigo wayarsa sai ya bude arba yayi da hoton bari da kuma rubutun sakon dake bin bayan hoton.

“I lost my baby today saboda bakincikin jin cewar kana son wata Kareem, mijina ya kasa gane kaina yau saboda kai, na fitunu da kaunarka da Kareem, amman kokarin cire ni kake a rayuwarka bayan duk budulcin da ka yi min na kin aurena”

Ya karanta sakon kusan sau uku sannan ya sake duba hoton barin da ta turo masa, a madadin ya ji dadi abun da yake nema ya samu wato cikin ya zube, sai abun ya tsorata shi, har ya fadi zaune a kujera yana mamakin kansa.

‘Ta ya yayi zurfi a zuciyar matar wani haka? Har bakincikin jin cewar yana son wata zai saka cikinta ya zube, me yake aikatawa haka? Wane irin mutum ya zama? Wane kalar uba ya zama? Wane kalar miji? Wane kalar ďa? Ashe tasirin sabon da zuciya take kwadaituwa da aikawa ya kai haka?’

Ya mike tsaye zuciyarsa na bugawa da karfi, idan ya mutu a cikin daren nan yana da wata hujja da zai fada ya fanshi kansa a gurin Allah? Me ya aikata haka? Zina ba halinsa ba ne me yasa zuciya ta kai shi? Ta ya yake kokarin lalata rayuwarsa? Su ne tambayoyin da suke masa yawo a kai idonsa suka cika da hawaye. Ya nufi sama da sauri ya tura kofar dakin yaransa ya tsaya daga bakin kofar yana kallon Tine dake bachi ya karasa ya zauna kusa da ita ya kai hannu ya shafa kanta yana tuna maganar matarsa.

“Kai ka ta shafa, idan ka aikata abun kunya yayanka ne a kunya ba ni ba, ni matsalarka bata gabana”

Ya hade yawu ya mike tsaye ya gyara mata bargonta sannan ya fice dakin a hankali ya ja kofar. Dakin matarsa ya nufa nan ma a hankali ya tura kofar ya shiga sai same ta kwance tana bachi Areef na gafenta shi ma yana bachi. Karasa yayi ya kalli dansa ya kalleta ya mika hannu ya shafa dansa sannan ya juya ya fice.

Continue Reading

You'll Also Like

3.7K 85 15
Book #2 of my SpiderWitch series Placed during TASM2 " All I can say is it was, Enchanting to meet you.." " Please don't be in love with someone els...
5.2K 242 9
Jk : YES I WANT BREAK UP!!! He yelled and for him and for yn everything became still he look sideways and heard a thud sound he see his love of life...
157K 10K 40
WANNAN LABARI NE DA WASU BANGARE YA FARU A GASKE. BAN CANJA SHEKARUN YARINYAR BA KO ALAKA BA,AMMA NA CANJA SUNA, SANNAN BABU SUNAN GARI DA KUMA ANGU...
5.1K 234 48
Labarine akan soyayya,cin amana da tausayi,tunasar da iyaye da emmata da ilimintarwa.sakayya Read and find out d main lesson in it