TA ƘI ZAMAN AURE...

By KhadeejaCandy

8.9K 367 24

"Ni ma ina da buri, ina da mafarkai irin na kowace mace, sai dai kuma kaddara ta shata min layi, yadda alƙala... More

Chapter 1
Chapter - 2
Chapter -3
Chapter -4
Chapter -5
Chapter -7
Chapter -8
chapter 9
Chapter -10
Chapter 11
CHAPTER 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Last Free Chapter

Chapter -6

418 27 5
By KhadeejaCandy

Duka sosai Mama tayi min tun tana dukana tana zagina har ta kai tana dukana tana kuka kamar yadda nake kuka. Hana ma kuka take saboda ta ga ina kuka daman haka take duk fitinarmu da ita idan wani abu ya bata min rai ko ya saka ni kuka ita tana shiga damuwa sosai, wani lokacin har ta kan fi ni ma saboda Mama tana cewa ni ban san ciwon kaina ba, sai dai wani ya sanin min. Na rarrafa na tashi zaune ina jin tsiyayar ruwan da na tabbatar na jini ne a kaina.

“Mama yanzu me ye amfanin haka? Gashi yanzu kin ji mata rauni a raunin da ta ji, yanzu kuma a koma jinya ana neman na magani Baba kuma ba badawa zai yi ba kin san tun da kudin nan suka kai hannunsa ba zai bada su ba, kuma halin nan ba dainawa zata yi miye amfanin dukan?”

Bana ganin fuskar kowa saboda kuka, sai dai zan iya shaidar muryar Yaya Nabil ne mai maganar cikin yanayin damuwa.

“Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un”

Shi ne abun da nake ta jin Mama na maimaita cikin kuka, na dai na samu na isa bakin kofar dakinmu da rarrafe, na shige ciki na kwanta. Daga lokacin da na kwanta sai kukan ya tsaya min daman can Allah be yi da son kuka ba, ba komai ke saka ni kuka na dade ba, sai dai na bar abu a cikin zuciyata idan na tuna ya kuna min rai, shi ma kuma da zarar na samu wani abu da zai dauke min hankali a take zan manta sai idan an bude sabon shafi kuma.

“Jinin ya tsaya?”

Na ji muryar Yaya Nabil sai na tashi zaune na kai hannu na taba gurin har lokacin zafi yake min sosai, kuma jinin yana zuba sai dai ba kamar dazun ba.

“Rashin jin magana ke ja miki shiga matsala Noor, ke babu ranar da zaki yi hankali? Kuma kin san idan kika aikata wani abu laifin a gurin Mama yake komawa, fitar nan da kika yi babu kalar fadan da Baba be yi ma Mama ba saboda ta barki kin fita, na dawo gida na tarar baki gidan sai wani sabon fada ya tashi”

“Ka ce Mama ta yi hakuri ba zan sake ba”

Shi ne akwai abun da na ji zan iya fada, domin ni na janyowa kaina matsala da kaina, kuma Mama ta yi gaskiya kwadayina ne sila. Yaya Nabil ya fita daga dakin be jimawa ya dawo rike da maganin ciwon kai ya mika min.

“Ki Sha biyu idan jinin be tsaya ba anjima sai mu tafi gurin Saminu ya sake gyara miki gurin, ni ma gashi kina son ki zama silar korata daga aiki, Allah kadai ya san me kika masa da yace na zauna gida na kwana biyu”

Na san fadar gaskiyar zai sake jefani a matsala ne, dan haka na zabi shiru daman hausawa sun ce shiru ya fi yawan magana alheri. Ina cikin dakin ban fito ba sai da aka yi sallah magariba, a lokacin jinin ya daina min zuba, dan haka na nemi tsumma na gyara gaban kaina na goge jinin na saka wani kyalle na daure gurin sannan na fito na nufi gurin da buta take na dauka na zuba ruwa na yi alwala. Ina ganin ledodin Kareem Restaurant a tsakar gidan na san Mama sun cinye komai, hakan kuma ba karamin koma min rai yayi ba, ashe wahalar banza na sha ba zan ci komai a ciki ba. Da hawaye na gama alwala na mike tsaye kenan Hana ta fito daga bandaki rike da buta, Mama kuma tana dakinta tana sallah.

“Mama ta rantse ba zaki ci ba, shiyasa ban shiga da shi dakinmu na ci a dakin Mama”

Na kalleta cikin yanayi na rashin jindadi dake bayyana har a muryata na ce.

“Kun cinye duka kuma?”

Ta daga min kai.

“Mama ta miki haka ne saboda karki sake aikatawa gobe, dan Allah ki daina abun da kike Noor, dan Allah ki daina”

“Ba roka na yi ba, shi ya ba ni ku tambayi Yaya idan ba ku yarda ba, Hana har da yar tsutsar kun cinye?”

“Aa zubarwa aka yi, waye zai ci tsutsa idan ba ke da abinki ba Noor, abun kyama”

Ban sake ce mata komai ba na nufi dakinmu na shimfida dankwalina na saka hijab na fara sallah idan na yi sujuda sai na kai gefen goshina a kasa saboda rabin ciwon yake min. Ina gama sallah yaro ya shigo yana sallama, ina jin Mama ta amsa masa.

“Wai Zafeer yana sallama da Noor”

“Ka ce gata nan zuwa”

Yaron ya juya ya fita, shiru ban ji Mama tace na tashi na tafi ba, na san kuma Zafeer ba tafiya zai yi ba sai ya gan ni, ko kuma idan an fada masa ba zan samu fitowa ba. Dan haka na mike tsaye na fice daga dakin na isa bakin kofar dakin Mama na tsaya daga bakin kofa na fara da bata hakuri.

“Mama ki yi hakuri, ba zan sake ba”

Ta yi kamar bata ji ba.

“Na tafi gurin kiran da Zafeer yake min?”

Na tambaya a kokarin na zama yarinyar kirki.

“Idan kika tashin fitsararki umarnina kike nema? Yar iskar yarinya marar mutunci”

Daga jin wannan kalama na san Mama bata gama sauka daga fushin nan ba. Sululu na fice daga gidan kamar macijiya, ina fita waje na samu Zafeer tsaye yana danna wayarsa, kamin na karasa gurin da yake tsaye na fashe masa da kuka a take ya dago kai da sauri ya kalleni hankalinsa a tashe.

“Me ya faru Baby Noor waya taba ki?”

Ya kunna fitilar wayarsa ya haska fuskata.

“Subhanallahi me ya same ki waya fasa miki kai? Me kika yi Noor who did this to you? Who touch my Babeee”

Tambayata yake hankalinsa a tashe zuciyarsa na cika, ban yi mamaki ba domin ya saba fusata a duk lokacin da aka taba ni.

“Waya miki wannan duka Noor fada min mana...”

Cikin kuka na fada masa abun da ya faru tun daga irin karyar da Kareem yayi ma su Mama cewar mota ce ta buge ni, har zuwa dukan da Mama ta yi min.

“Kuma sun cinye duka naman ba su ba ni komai ba, ko yar tsutsar nan da na so na ci ba su ba ni sun zubar”

Juya baya yayi yanayin fuskarsa ya sauya kamar zai fashe da kuka, ya jingina da ginin gidanmu ya kife kansa. Kamin ya dago ya kalleni.

“Iyeyenki kadai suka kai su yi miki haka Noor, su kadai ne suka da ikon dukanki su fitar miki da jini haka kuma na kyale su, Allah ya daran talauci Noor, ba dan shi ba da yanzu na aureki da yanzu karkashina kike rayuwa, wani abu duk ba zai faru ba”

“Sun cinye komai har tsutsar nan irin wadda masu kudi suke ci, na so na ci na ji me ake ji”

“Ana zancen rauninki kina zancen tsutsa, idan kin ci me zaki ji?”

“Na ji abun da suke ci mana, har kai na dauko maka naka fa, ai kasan komai na samu sai na kawo maka”

Na fada cikin kuka.

“Ni dai dan Allah ki daina daukar komai kike gani ki saka a bakin nan Noor, wani abun da kike ganin masu kudi suna ci, masu kudin nan ba dukansu ne suka da hankali ba, komai kika samu ki ta kaiwa bakin nan na ki kuma idan mun yi aure....”

Na share hawayena na kalleshi.

“Me? Kawai ba ina son na ji yadda ake ji ba ne, yanzu ai ba zan sake samu ba”

“Yanzu dai shiga cikin gida ki fadawa Mama zan kaiki a duba raunin nan”

Na juya sai ya kira ni na dawo. Ya haska fuskata ya saka rigarsa ya goge min hawayen da kyau.

“Kar ki shiga kuma tace kin min kuka ta miki fada”

Na dauke kai na koma cikin gidan na tsaya daga jikin kofar dakinta na sanar mata.

“A dawo lafiya”

Ita ce amsar da ta ba ni, sai na juyo ya dawo na fada masa muka kama hanyar titi ni da shi. Muna tafiya yana kallona har muka isa na zauna a kujera mai shagon ya bude ciwon ya sake wanke min ya sake rufewa ina kuka saboda zafi, Zafeer kuma yana rarrashina kamar wata jaririya.

“Ya isa ya isa shikenan an gama daga wannan, ka yi mata a hankali, da zafi fa”

Bayan ya gama ya bani maganin ciwon kai da na rage radadi. Sannan Zafeer ya biya shi muka taso muka kamo hanyar gida.

“Me kike son na siya miki?”

“Kana da kudi?”

“Ina da dubu uku fada min abun da kike so na siya miki, kin ce Mama bata baki komai ba ko?”

Na daga kai.

“Eh amman ka aje kudin ba kudin aure muke tarawa ba?”

“Idan ana tara kudin aure sai aki cin dadi? Jira ni a nan zan je na dawo”

“Toh”

Duk maganar da nake masa cikin shagwaba nake masa, daman can haka al'adarta take magana cikin shagwaba kamar wata wadda ta tashi a cikin gata, balle kuma na kai ga wadda ke shagwaba ni. Ta inda ya bar ni akwai hudu kasancewar unguwar babu wuta yau, babu wadda zai shaidi ni ce har ya je yayi siyayyar da zai yi ya dawo. Nama ya siyo min saboda ya san halina da son nama kamar kura, sai kayan marmari a dayar ledar dayar wadanda suka hada da Apple biyu sai ayaba da lemu da kankana, dayar ledar kuma cake ne irin kananan da ake saidawa 150 guda daya, ya siyo min guda hudu da kunun aya.

“Na gode sosai Zafeer”

Na fada ina jindadi sosai gaba daya ya wanke min kwadayi da bacin ran dake tare da ni.

“Anything for my Baby Noor, idan Mama tace fada min kika yi abun da ya faru, ki ce aa daman na zo da siyayyar tun kamin mu tafi”

“Toh”

Na amsa sannan na jera da shi muka kama hanya, muna tafe muna hira har muka iso gida.

“Ni zan tafi, yau babu hira saboda baki da lafiya, sai dai gobe idan na dawo, amman Noor ki daina bijirewa maganar iyayenki, duk abin da kika san zai saka Mama ta dukeki ko Baba ki daina kin ci? Kuma ki yi ta mana Addu'A Allah ya bude mana kofofi na samu karasa gidan da nake na hada komai a bani ke ki huta nima na huta”

“Okay, toh... Zafeer ina sonka sosai sosai sosai”

Yayi murmushi yana kallona cikin hasken farin wata.

“Ina sonki ninki yadda kike so na Noor, ke tawa ce har abada, we mean to be akwai wani bend a tsakaninmu da babu wadda zai iya karya shi i love you so much”

Magana yake min a hankali cikin sanyin murya da kwantar da kai kamar mai son na fahimta ko na haddace. Kamin ya juya ya duba ya ga babu mai ganinmu ya sumbanci goshina sannan yayi baya da sauri ya daga min hannu yana min bye bye. Ni ma na mayar masa sannan na shiga gida raina fess har na manta da komai, dakin Mama na fara shiga da murna ta sai kuwa na yi sa'a ina taka kafata wutar nepa na kawowa. Ba zube ledodin a gabanta da far'ata.

“Mama gashi Zafeer ya siyo min”

Wani banzan kallo da Mama ta watsa min ya saka annurin dake fuskata gushewa.

“Fada masa kike yi abun da ya faru yaje yayi miki siyayya?”

“Aa ban fada masa ba, na fada masa dai na ji ciwo ne saboda mota ta buge ni, daman ya zo da siyayyar kamin mu tafi na aje a zaure ne”

“Je ki ci ni wadda na ci dazun ya wadatar da ni”

Ta fada tana cigaba da jan carbinta, fadar hakan kuma sai ya saka na ji wani iri na ji komai ya fita a raina.

“Mama dan Allah ki ci”

Ta juyo ta kalleni sannan ta kai hannu ta bude ledodin ta bude ayaba ta dauki daya ta bude ta ci.

“Allah ya shirya ki, Allah ya yaye min wannan bakinciki na ki”

Ta fada idonta na cika da hawaye, ban san me zance dan haka na dauke ledodin na fice daga dakin. Hana ma kadan ta dauka saboda ta ci na dazu, na cire leda daya na ajewa Yaya nashi, daman shi Baba be cika maida hankali a irin wannan ba ko ba shi aka yi zai iya cewa baya ci ma.
Na ci komai sannan na dauki na yaya na kai masa dakinsa na dawo na yi sallah Isha'i na kwanta. Ban farka ba sai washe gari ana kiran sallah Asuba.

Kamar kullum Hana ta hada abun karyawa sannan ta wuce makaranta, ni kuma na fita na fara dibar ruwa daga fanfo ina kawowa cikin gida, Yaya ne yake yi sai dai a duk ranar da yake da makaranta baya diban ruwan ni nake yi saboda ni ce mai zaman banza. Bayan na gama na dauki tsintsiya na share ko'ina na shiga na yi wanka na dauki tufafin Hana na saka, ina fitowa Mama ta rufe ni da fada.

“A haka zaki kare saboda baki san ciwon kanki ba, wuce ki cire mata kaya”

“Nawa sun yi datti Mama”

“Ki saka haka, ko kuma ki daura zane ki dauko tufafin ki wanke, har na islamiyarku ki wanke dan yau sai kin je makaranta”

Na juya na koma cikin rashin jindadi na cire tufafi na dauki zane na daura na ciro uniform din da kala biyu na fito waje na wanke na shanya. Na koma daki na zauna, ina jin lokacin da yaro ya shigo yace Zafeer yana sallama da ni. Katon Hijab na nema na saka saboda zane ne a jikina nan ma ban tsira ba ina fitowa Mama ta fara halbina da kalamai marasa dadi.

“Ai dole ki zuba katon hijab saboda baki da tufafi, ke kan kin ji haushin rayuwa, wannan Zafeer din zai daukarwa kansa aiki, Allah yasa ma zai iya zama da ke, domin dai babu namijin da zai iya zama da mace irinki, matukar baki sauya hali ba zaman aure sai ya miki wuya Nooriyya”

Ni dai ban ce komai ba na fice daga gidan, sai na same shi a waje tsaye yana jiran fitowa.

“Baby Noor ya jikin?”

Na masa dariya a yayinda yake min murmushi.

“Na ji sauki, har na yi wanki na yi diban ruwa”

Ya kalleni kamar zai ce wani abu sai kuma yayi shiru.

“Mama ta miki fada jiya?”

“Aa ban fada mata gaskiya ba, yadda ka fada haka na ce mata”

“Shikenan ki shiga ciki ni zan wuce makaranta yanzu, yau zamu zana jarabarmu ta karshe ki min addu'a Allah ya ba ni sa'a”

“Allah ya baka sa'a Allah yasa ka fito da results mai kyau”

“Ameen i love you”

“I love you too”

Yayi min bye bye Ni ma na masa sannan ya wuce, ni kuma na koma cikin gidan. Kamar yadda Mama ta fada sai na tafi makaranta lokaci na yi na shirya cikin uniform dina kuka ne kawai ban yi ba amman bana son zuwa makaranta ko kadan, ina saka uniform Hana na tsokanata wai yau ni nice zan tafi makaranta za'ayi ruwa bla bla ne dai ban kulata ba, Mama ta zuba mana kwadon kanzo muka ci, Hana ya raga na hade da nata na cinye sannan na sha ruwa muka kama hanya.

“Ni da zaki taimaka min ma ba zan tafi ba, sai na tafi bikin Salwa yau ne za'ayi na karshe fa, kuma jiya ban tafi ba, na san idan na yi ma mama magana zata min fada shiyasa ban yi ba”

“Da rauni a kai zaki tafi biki kamar Bikin dole? Yanzu duk fadan da aka miki jiya be shige ki ba, sai wani zancen bikin kike Noor kin shiga uku”

“Ni ban shiga uku ba, ke kika shiga uku”

Na rama, sannan muka cigaba da tafiyar, cikin rashin jidadi na isa Islamiyar, kowa mamakin ganina yake kusan tun da na yi sauka sai dai na leko makarantar na koma bana wani zuwa. Har Malaminsu sai da tsokani ne wai ya ga ana hada hadari a gari ashe ni ce zan shigo makarantar. Ni dai ban kula su ba, na bude littafaina aka fara zuba min karatu kamar ba gobe, shiyasa malamaina suke yawan yabani suna cewa da zan natsu na yi karatu ba karamin amfanina za aci ba, kuma ni ma zan ci amfamin ilimina domin ina da fahimta sosai ina da basirar haddace abu, kuma komai aka fada min bana mantawa, natsuwa ce kawai da jin magana suke ganin kamar bani da ita, nikam ina ganin natsuwata suke dai suke ganin haka. Kowa ya tambaya me ya same ni a kai cewa nake mota ta kade ni.
Misalin karfe biyar aka fara haramar tafiya duba Malam Sule mai bin babban malaminsu kusan komai da ya shafi makaranta shi yake yi, ashe ba shi da lafiya wai kariya ya samu sati biyu, ni ban sani ba sai yanzu, saboda bana zuwa karanta duk wani abu da ya shafi makaranta bani da labarinsa.

Malam Babba ne ya dauki nauyin duka Napep din da muka hau, mu biyar muka matse a Napep daya zuwa unguwar da Malamin yake, muna isa muka shiga cikin gidan muka gaishe shi, muna waje wata Hajiya ta shigo da manyan ledodi Kareem Restaurant ta aje sannan ta rage tsawo ta gaisa da Malamin. Ni kuma na kira Hana dake can gefe na nuna mata Ledodin.

Ta kalla sai ta yi dariya ni ma na yi dariya, sai dai kamar hakan be yi ma Matar dadi ba, ko kuma dai tana cikin fushi ne take son hausakewa a kanmu oho a take ta hau fada.

“Ledodin Kareem kun san abun da ke ciki? Ko kuma kun raina abun da na kawo ne? Wane irin abu ne wannan?”

Malam Babba ya kalleta.

“Hajiya Lafiya?”

“Ga yarinyar da ta kira dayar can ta nuna mata ledodin da ba kawo, ban san manufarta na yin haka ba”

Malam Babba ya juyo ya kalleni.

“Nooriyya me ya faru”

“Jiya ne mai Restaurant din ya zo da kanshi ba aike ba, har gida ya kawo mana kayan dadi, shi ne na kira Hana na nuna mata ledar ina nufin ta kalli wannan daga can ya fito shi ne wai ta fara bala'i ita masifaffiya, Wallahi na fiki bala'i ni har na siyarwa ina da, daga magana zaki fara fada kamar an miki wani laifi”

Na mayar amsa ina murguda mata baki, kuma na fada mata shi ya zo da kansa saboda ta san muna da matsayi muma.

“Oh ai ban dauka haka ne ba, na dauka wata maganar ce ya dabam, yi hakuri”

Na yi zaton haushi zata ji sai na ga ta maida abun na dariya ta saki fuska ta sauko wata ta fahimci ni ma muna da matsayi, ba dan ma muna cikin yan makarantar mu kuma kowa ya san Zafeer zan aura da sai na yi mata karya na ce saurayina ne. Sai dai wani abun da ban gane kansa ba shi ne kallona take har ta gama gaisawa da Malam Sule ta mike tsaye idonta a kaina yake. Gabatar da ita da Malam Sule yayi a gurin Malam Babba ne muka ji cewar ita ce silar ciwonsa saboda kade shi da ta yi da mota.

“Malam dan Allah ba ni aron dalibar ka zan yi magana da ita”

Ta nuna ni, ni kam abun nema ya samu daman so nake na nuna mata karyar arziki take da kurin banza na ga mai arzikin da be dauki kansa wata tsiya ba, ba kamar ita ba daga magana ta fara ruwan masifa. Malam ya juyo ya kalleni.

“Allah yasa dai ba wata matsala ba ce?”

“Babu wata matsala Wallahi tambayarta kawai zan yi”

Ta amsa fuska a sake. Malam yayi min izini da na tafi sai na mike tsaye na isa gurinta, sai ji na yi ta dafa kafadata muka fita tare bata min magana ba sai da muka isa waje, gaban motar da nake kyautata zaton ta, ta ce muka tsaya tana murmushi ta ce

“Ya sunanki?”

“Noor”

Na amsa a takaice.

“Shi Kareem din mai Kareem Restaurant Saurayinki ne? Ko dan'uwanki”

Jimmmm na dan yi ina tunanin na zaba sakanin saurayi da dan'uwa, idan na ce mata dan'uwa zata san ina da muhimmanci amman Saurayi zai fi karamin kwarjini a idonta dan haka na amsa da.

“Saurayina ne, me yasa kika tambaya?”

Ya sauke ajiyar zuciya da alama jin haka be mata dadi ba.

“Kawai na tambaya ne, saboda ina yawam siyen abinci a restaurant din, kuma a yadda na ji shi Kareem din kwararen likita ne mai duba mutane, na so na samu maganinshi tun da dadewa amman ban samu haka ba, saboda masu aikinsa basa bari na ganshi kuma asibitin idan naje bana samun na duba ni, shiyasa yanzu da na ji kin ce kin san shi na ji dadi kuma har na nemi magana dake private”

“To me zan yi miki?”

Gabana ya fara faduwa karta roki na yi mata alfarmar da ba ni da halin yinta.

“So nake ki hada ni da shi dan Allah”

“Aa gaskiya shi baya son haka”

“Taimaka min zaki yi ina cikin matsala ne, ina fama da wani ciwo ne na kansa a ciki, kuma ance idan har na samu ganinsa ya rubuta min magani zan samu lafiya, dan Allah ki taimaka min kinji kanwata, ni zan ma iya biyanki”

“Aa gaskiya, ni yanzu ganin Malaminmu muka zo, gidanmu idan aka ji za'ayi min fada”

“To karya kike yi ba saurayinki ba ne kenan?”

Na fara saurin kare kaina.

“Aa da gaske ne mana”

“To ki nuna min, indai har da gaske ne, ki kai ni gurinsa”

“Toh ai yanzu baya gida”

“Eh yana restaurant dinsa, daman ance idan Yamma ta yi restaurant dinsa yake zama, idan kin yarda ga mota nan mu tafi yanzu, ga mota nan sai mu shiga, ni zan ma biyaki zan baki ko nawa kike so, ni dai ke hada ni da shi kawai na yi magana ne burina”

Na yi shiru ina nazari na bita ko kuma dai na ki tafiyar, idan kuma na ki tafiyar zata karyata ni, idan kuma na tafi ba lallai ne nima su bar ni na ganshi ba.

“Mu tafi? Dan Allah ki taimaka min, sai magiya nake miki kamar ba musulma ba? Ke baki da tausayi ne a zuciyarki?”

Na kalleta, bata yi kama da mayaudara ba balle na ce karya take, kuma yadda ta marairaice murya nan sai na dan ji tausayinta.

“Ba zamu dade ba?”

“Ba zamu dade ba, kina hada mu zan baki kudin Napep ki dawo sai ki bar mu a can”

“Toh”

Ta bude min mota na shiga sannan ta shiga, ni dai zan taimaka mata ne saboda ta nuna tana cikin damuwa, ba wai dan kar na karyata kaina kawai ba. Har muka isa Restaurant din wata kalma bata shiga tsakanina da ita ba. Na bude motar na fita ita ma ta fito bayan ta saka mask kuma ta maida mayafin dake wuyanta zuwa saman kanta. Gabana na faduwa muka doshi reception din ina ta sake saken kar na ga Yaya duk da na san by this time ya wuce gida domin karfe shida ta yi. Me zan fadawa ma'aikatan su bar ni na shiga ciki shi ne abun da ya tsaya min a rai, idan ma sun bar ni ban san a ina Office dinsa yake ba.

Ta inda na yi sa'a na samu abokin Yaya da duty a gurin kuma ya san ni farin sani, hakan ya taimaka min gurin fada masa ya shiga ciki ya fadawa Dr Kareem Noor ce take son magana da shi.. Babu jimawa ya dawo sai ya ce Dr Kareem din ya ce a shigo da ni ciki, dadin dake cikin raina baya misaltuwa haka na wuce gaba matar da ban san sunanta ba tana bayana abokin Yaya kuma yana gaba har muka isa office din sannan ya nuna min kofar ya juya ya koma. Na juyo na kalli matar dake jan numfashi da karfi tana fitarta wata kila saboda ciwo ne oho dai, na yi murmushi na juya na kai hannu na murda kofar na bude na shiga ciki.

“Noor... Lafi...”

Be karasa ba yayi shiru yana kallon gefena, matar dake bayana tana shigowa wani mutum dake zaune tare da Kareem din da ban san waye ba ya kalleni yana murmushi ya ce.

“Noor Amaryarmu!!!”

Na kalleshi da sauri ina mamakin jin furucinsa kamar wadda ya san karyar da na shiryo. Kareem din ma kallonsa yayi tare dake bayana kuma na ji ta sauke numfashi da karfi ta juya. Ni kuwa na kai hannu na taba ta wai na fada mata ga Dr Kareem din nan, sai jin na yi ta kama hannun ta murde tana kokarin karyawa.

“Safeena...”

Na ji Dr Kareem ya kira sunan da karfi sannan ya nufo inda muke yana kokarin kwace ni a hannunta...



__________________________

Domin samun littafaina akan kari, ku yi following din Channel dina mai suna KHADEEJA CANDY za su samu TA KI ZAMAN AURE daga farko har zuwa inda ake, kuma a can zan rika posting duka littafaina In Sha Allah.

Amman kamin nan ku fada min wane Team kuke.

Team Kareem
Ko
Team Zafeer

Anya kuna ganin Kareem yayi ma kansa adalci kuwa? Mu'alama da matar aure mai yaya har uku?
Shin kuna ganin akwai Uba irin Baba kuwa? Babu dadi gurin matar gidan haka kuma babu gurin yayan gida?
Anya abun da Mama take yi ma Noor tana kyautawa kuwa?

Ku aje min ra'ayinku ni kuma na aje muku dogon shafi gobe idan Allah ya amince.

#KhadeejaCandy

Continue Reading

You'll Also Like

12.6K 377 20
ဒီကောင်မလေးကို ပြန်ပေးဆွဲထားတာဘာအတွက်လဲ ချစ်လို့လား ကြိုက်လို့လား လိင်ကိစ္စကြောင့်လား မဖြစ်နိုင်ဘူးလေ မင်းက Asexualတစ်ယောက်လေ.... possessive type, Re...
32.1K 710 38
Now you gotta ask yourself. What would it be like to find out that the people you love and would die for, turn out to be self centered assholes who w...
246K 16.9K 29
𝐓𝐇𝐄𝐘\'𝐑𝐄 𝐀 𝐌𝐀𝐅𝐈𝐀.🧠💸🛢️. عالم مُغطىٰ بالذهب الأسود وَ السوَآد . حياة اعيشُها حالكةُ الظُلمِ وَ الظلام . أرواحٌ مــأسـورةٌ في سـرآيا ا...
49.1K 2K 16
Book 2 of the 𝕱𝖎𝖌𝖍𝖙𝖈𝖑𝖚𝖇 series {Duology} 𖤓 𝕾𝖔𝖒𝖊 𝖒𝖊𝖒𝖔𝖗𝖎𝖊𝖘 𝖓𝖊𝖛𝖊𝖗 𝖑𝖊𝖆𝖛𝖊 𝖞𝖔𝖚𝖗 𝖇𝖔𝖓𝖊𝖘. 𝕿𝖍𝖊𝖞 𝖇𝖊𝖈𝖔𝖒𝖊 𝖕𝖆�...