TA ƘI ZAMAN AURE...

بواسطة KhadeejaCandy

3.4K 292 20

"Ni ma ina da buri, ina da mafarkai irin na kowace mace, sai dai kuma kaddara ta shata min layi, yadda alƙala... المزيد

Chapter 1
Chapter - 2
Chapter -3
Chapter -5
Chapter -6
Chapter -7
Chapter -8
chapter 9
Chapter -10
Chapter 11
CHAPTER 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Last Free Chapter

Chapter -4

143 15 0
بواسطة KhadeejaCandy

KAREEM POV.

After fitarsu, Yusura ta fito daga kitchen rike da cup din ruwa.

“Me za a girka anjima?”

Daf da zata wuce shi tambaya. Ba tare da ya kalleta ba ya amsa.

“Ba a gida zan ci abincin dare ba”

Ta daga kadunta alamar ko a jikinta sannan ya wuce ta haye sama.

Mike tsaye ya saka hannunsa daya a aljihu dayan kuma rike da wayarsa a hannu ya sake cewa daga falon ya nufi gurin da ya saba zama. Sai da ya isa gurin sannan ya amsa kira na biyu dake shigowa wayarsa.

“Hello”

“Darling na yi missing dinka badly”

“Toh ya muka iya, tun da mijinki ya ki barin gari? Sai hakuri”

“Zamu iya haduwa ko yana gari...”

Yayi murmushi ya shafa sajensa.

“aa kar dai mu shiga hakkinsa da yawa, kar zunubin ya mana yawa, kara idan baya gari wannan kina da Hujja”

“Wata kila baka yi marmarina yadda na yi marmarinka ba ko?”

“Na yi mana, amman dai kar mu wuce gona da iri, kin san ai yadda nake kaunarki”

“Ko kirana baka yi Kareem”

“Be kamata na kira ki idan mijinki yana gari ba, akwai abubuwan da na iyakancewa kaina aikatasu, Safeena dole muna hakuri da wani abun fa”

“Kawai dai baka so na kamar yadda nake son ka shiyasa”

Ya shafa kansa yayi murmushi.

“You're the love of my life, ke kadai kika na aikata wani aiki da zai ba ni zunubi mai yawa Safeena, ke kin sani idan bana sonki ba zan yarda wata mu'alama ta hada mu ba haka ne?”

“Eh amman...”

Sai kuma ta yi shiru kamar wadda ta rasa abin cewa.

“Yau na ga wata yarinya mai yanayi da ke, har ta fiki wauta da sakarci ma”

Yana maganar yana murmushi.

“A ina ka ganta?”

Ta tambaya daga dayan bangaren.

“Wani yarona na gurin aiki ne ya zo duba ni sai ta biyo shi, ina kallonta ke nake ta tunawa”

Shiru ne ya biyo baya har na tsawon lokaci.

“Safeena...”

Ya kira sunanta sai ta amsa masa da muryar dake nuna ta damu.

“No wait ba abun da kike tunani ba ne, ke kin cika kishi fa, ba yadda kike zato ba ne, babu wannan a zuciyata har abada ke kadai ce kwallin kwal...”

Ta sauke ajiyar zuciyata.

“Duk ranar da ka so wata Kareem zan iya mutuwa”

“Ba zaki mutu ba, saboda ba zan so ba, na san yadda kike da tsananin kishi ai, zan kiyaye”

“Ina fatan haka”

“Ina mijikinki yake?”

“Yana daki, ni kuma ina harabar gida ne”

“Ni ma ina harabar gidan, amman yanxu zan fita, je ki samu mijinki zamu yi magana anjima”

“Okay i love you”

“I love you too”

Ya sauke wayar yana murmushi. Kana ya busar da iskar bakinsa ya sake shafa kansa ya sauko zuwa sajensa. Sannan ya juyo ya fito daga garden din ya nufo cikin gidan. Ganin kofar falon bude ya fahimtar da shi bako ya shigo gidan, domin daga shi har matarshi da yaransa biyu basa barin kofa a bude. Be karasa ba ya ji sautin kuka da kara mai razanarwa da muryar da be tantance ba. Hakan ya kasa shi cira kafa ya shiga falon da sauri. Yarinyar da ta fita dazun ya gani tsaye kusa da kofar rike da kai tana ihu, Yusura na tsaye gabanta rike da glass cup.

“Me ke faruwa a nan?”

Yarinyar ta juyo ta kalleshi da sauri sai ta kara rushewa da kuka.

“Wai daga na shigo ina nemanka sai ta buga min cup din ruwa akai kalla har yayi jini”

Ta nuna masa jinin hannunsa. Sai ya juya ya kalli Yusura.

“Why?”

“Rashin kunya ta yi min”

Ta ba shi amsa babu alamar wasa a fuskarka. Yarinyar ta girgiza kai da sauri.

“Wallahi karya take komai ban ce mata ba, kawai na shigo nace dan Allah ina mai gidan nan, mijinta shi ne kawai ta buga min cup a kai”

Kareem ya juya ya kalli Yusura dake tsaye rike da cup din.

“Kishi kike?”

“Kishi?”

Ta maimaita tana ja baya tare da yin dariyar rainin wayo.

“Kishi dai kishi? Na rasa waye zan yi kishi sai kai? Allah ya tsare gatarina da saran shuka mtscheeeeeeee”

Taja dogon tsaki ta juya ya bar musu gurin. Kareem ya kalli yarinyar da jini ke fita a goshinta yace

“Me yasa kika dawo?”

“Yaya ya tafi abun shi, wai ba zai koma restaurant din ba, kuma zai buga waya ya fada musu karya nake kar a bani, yana ta min fada a hanya, kuma yace ba zan bishi gida ba sai dai kowa yayi tafiyarsa, shi ne ya saka a Napep yace ya kai ni gida, ni kuma sai da muka yi nisa sai na cewa mai napep din ya dawo da ni nan gidan amman ya biyo wata hanya da Yaya ba zai gani ba, kuma yana waje ban bashi kudi ba”

“All this long story ban gane me kike nufi ba”

“Ina nufin Yaya so yake na tafi gida ba tare da na karba kyautar da ka ba ni ba, kuma yace ba zai tafi da ni can din ba”

Ya rike kunkurunsa yana murmushin da ya kusa zame masa dariya.

“Ammm ya ma sunanki?”

“Noor sau uku kenan ina fada maka”

“Yanzu ba zan sake mantawa ba, I'm sorry yanzu muje a duba kanki...”

Ta juya tana rike da goshin ta fita daga falon, sai ya bi bayanta har sun saka entrance din sun isa gurin motarsa ya tuna keys dinsa basa aljihunsa.

“Noor jira ni a nan zan dauko keys dina”

“Toh amman ka yi sauri kar ta fito”

Yayi murmushi.

“Ba zata sake fitowa ba”

Ya juya ya koma cikin falon, kai tsaye sama ya nufa ya shiga dakinsa ya dauko keys din, ya nufo curtains dinsa dake dage zai sauke kasa sai ya hango Noor tsaye a inda ya barta sai daga hannu take bakinta na motsi da alama masifa take, hakan ya saka shi saurin saukowa domin yayi tunanin ko Yusura ce tsaye jikin kofar falon, saboda ya hango kofar take kallo. Ga mamakin sai ga ita kadai ce take fadan tana kallon kofar falon. Sai da yaja kofar sannan ya nufi Motar ya bude sai da ya fara shiga sannan Noor ta shiga, yayi reverse ya fice gidan, tuki yake a hankali yana kallon yadda Noor ta natsu sam ba zaka ce tana da yawan magana ko kiriniya ba, babu wannan alamar a fuskarta da jikinta natsassiya ce sosai idan bata bude baki ba.

NOOR POV.

Shiga motar alfarma irin wadda ban taba shiga ba, ga wani sanyi ac mai dadi da laushi yana ratsa fatata ya saka natsu sosai ina jin yadda duniyar masu arziki take da dadi, sam na manta da ciwon da mahaukaciyar matar ogan su Yaya ta ji min a goshi har sai da muka isa wata babbar Asibiti, ni da nake zaton chemist zai kai ni domin ciwon ba wani babba ne ba. Fakawa yayi a gaban kofar emergency baya tsoron ma su masa fada.

“Za su maka fada basa bari a faka a nan ”

Daf da zai fita na fada masa haka sai ya juyo ya kalleni yayi min murmushi, da alama dai murmushi al'adarsa ce, ko ba komai ai yana masa kyau. Wani abun da ya ba ni mamaki shi ne har muka shiga cikin asibitin gaishe shi ake kuma babu wanda yace masa komai a yanayin yadda ya faka motarsa. Wani karamin daki da zan iya kira da office ya shiga da ni, yaja min kujera.

“Zauna”

Ya fada, sai na zauna kamar yadda ya bukata ina rabbata masa yadda komai ya faru.

“Ina yin sallama fa na ga ta sauko sai na ce mata ina wuni tace lafiya kalau, sai na ce dan Allah mai gidanki yana nan, sai tace me kike nemansa, na ce mata ni ce yarinyar da yace na je restaurant na karbi abu ina son magana da shi, kawai sai ta matso kusa da ni ta buga min cup, bata ma tsaya ta ji ko miye ba, ni ai ba soyayya muke ba balle ta yi kishi ko?”

Ya dauke idonsa daga kallon waya da yake ya kalleni.

“Ba kishi take ba, kawai dai kaddara ta hau kanki ne, wata kila ranta ne a bace, kin san daman irinku kaddara ta fi hawa kanku”

“Kishi take mana, ta ga budurwar kyakkyawa ta yi tunanin na zo gurin mijinta ne, ni kam lalacewa ai bata kai na bi saurayana har gidansu ba”

Wannan karon murmushin da ke bayyana hakoransa yayi.

“Ba kishi take ba, bata taba kishina ba, kuma ba zata fara yanzu ba?”

“Ba matarka ba ce?”

“Matata ce”

“Dole ai zata yi kishinka, iskanci kawai yayi mata yawa, ni daman tun zuwana na fahimci baku zaman lafiya, Wallahi da zaka bi shawara kawai ka yi mata kishiya”

Kamin na fadi kalmar karshe sai da na rage muryata gudun kar wani ya ji, ganin nake kamar tana kusa zata iya sake rusa min wani abun akai ne. Gira biyu ya daga yana kallona kamar mai mamaki.

“Wallahi ka kara aure, duk zata daina wannan halin”

“Wani be taba ba ni shawarar nan ba, amman kin kawo shawara mai kyau, sai dai ni bana sha'awar auren mace sama da daya, saboda haka na zabi na mutu a haka”

Na yatsina fuska zan yi magana aka turo kofar office din, wata likita ce ta shigo tana sanye da atamfa ta dora rigar likitoci a sama.

“Doctor gashi, ni kam na ce lafiya ka shigo yanzu”

Murmushi yayi mata ya karbi keken da ta turo masa.

“kin kare kenan thank you”

“Ur Welcome”

Sai da ta fice sannan na kalleshi jin an kira shi da Doctor.

“Kai likita ne ko?”

Ya daga min kai yana saka safar hannu sannan ya rika goshina ya fara gyara min gurin, sai da ya saka min wasu ruwan azaba na gane ashe na ji ciwo sosai kawai dauriya ce da jarumta irin tawa ta saka ban yi hawaye ba sai ihu. Idona ya kai gurin katon hotonsa dake office din yana sanye da suit a kasan hoton an rubuta masa Dr Kareem. Mamaki ya cika ni sai a lokacin hankali ya karkata akan abun da ya kamata na gane tuntuni.

“Kai ne Dr Kareem? Ana yawan fadarka har a redio ana hira da kai laaa ashe kai ne”

“Kina jin labarina kenan?”

Ya saki kaina bayan ya gama rufe min raunin.

“Sosai... Laaa amman Yaya be taba fada min kai ne Dr Kareem ba, kuma be taba fada min kai ne mai Kareem Restaurant ba...”

“Toh ai baki san ni ba, shiyasa be fada miki ba”

“Haka ne”

Na fada ina kallonsa cike da burgewa domin likita ne da yayi kaurin suna a garin nan, sai dai ban taba zaton zan ganshi bagas a arha haka ba.

“Wai mutane suke cewa wai idan mace ta yi cikin shege ko kuna unwanted ciki domin da ta zo gurin Dr Kareem zai zubar mata, haka suke fada wai gaskiya ne?”

Ba da wata manufa na yi tambayar ba, tambayar abun da nake son sani ne akansa a iyakar gaskiyata domin haka mutane suke yawan fada akansa shiyasa ake cewa yana da kudi sosai. Sai dai yanayin yadda na ga ya dago ya kalleni ya razanar da ni, ni ko a ganina tambaya ce kawai na yi domin hausawa sun ce waka a bakin mai ita tafi dadi. Matsowa yayi kusa da ni ya raba hannayensa biyu ya daga kujera da nake zaune yana kallon cikin idona.

“Noor shekararki nawa?”

Na yi saurin sauke idona kasa na kama jikina sosai zuciyata na bugawa.

“Ka ba ni tsoro”

Sai yayi murmushi ya dauke hannayensa ya matsa baya.

“Aa sheri suke min kin san mutane akwai hassada, hassada ce kawai”

Ni dai na yi shiru domin jikina na bani da farko kamar tambayar ta wa bata masa dadi ba, ko kuma ya fahimta a baibaiye ne.

“Kin san me yasa na tambaya shekarun ki?”

Yana tambayar yana kallona, na girgiza kai ina jin kamar duka na zai yi duk kuwa da kasancewar murmushi ne a fuskarsa.

“Saboda my ex kamar ke take, zata yi tambaya any how, zata fadi duk abun da ya zo mata a bakinta, bata tunani irin na mutane ita a komai nata tunanin dabam yake, yanayin surutunki mu'alamarki sakin jiki da kowa duk haka take, ina son ki zama kawata shiyasa na tambaya shekarunki”

Sai a lokacin hankalina ya kwanta, sai na yi dariya na mike tsaye.

“Idan na zama kawarka hakan yana nufin idan na zo asibitin nan, kyauta za a duba ni, kuma a duk lokacin da ba ga dama zan tafi restaurant dinka na ci abin da nake so ko na karba ba zaka ce komai ba”

“Huh?”

Ya furta yana kallona cike da burgewa, sai na daga masa kai.

“Eh shi ne abotai ai”

“Shikenan na yarda”

Ya furta cikin sanyi murya, yana kada kai a hankali. Farinciki ya cika ni har na kasa ce masa komai sai murmushin dake tattare da dariya nake.

“Mu tafi ko?”

“Toh”

Na bi bayansa domin tuni yayi gaba ya bude min kofar.

“Ni daman na san sheri suke maka ai da kana zubar da ciki ba zaka haifi wannan yarinyar ba, matarka zaka fara zubarwa...”

Ban karasa ba na ji hannunsa ya rufe min baki, dayan hannunsa kuma a wuyana ya saka ni gaba yana turani kamar wata akuya, aiko sai na duke na subuce na juyo na kalleshi rai a bace.

“Ya kana min haka sai aje ce an ga Noor wani Kato na taba ta”

Ya nuna kansa.

“Ni ne Katon? Beside neman mata ba halina ba ne, kowa zai iya shaidata da wannan bana neman mata, kuma na rufe bakinki ne saboda karki fadi wata maganar wasu su ji”

“Na gane”

Na amsa a hankali sannan na jera tare da shi muna tafiya, kana gani kasan ni kanwarsa domin ya fi ni tsayi sosai. Da kaina na Bude Motar na shiga shi ma ya shiga bangarensa a yanzu kam na gane dalilin da ya saka ba ayi masa fada ba a lokacin da ya faka mota a kofar emergency. Ban sake cewa komai ba domin na lura kamar surutuna ya fara effecting dinsa.

“Noor ya na ji ki shiru, ko maganar ta kare”

A lokacin da na juyo na kalleshi sai na ga kallona yake da da abun da ya zame masa wajibun wato murmushi a fuska.

“Na ga ai baka son surutu ne?”

“Inji waye? Ni ina son surutu sosai, shiyasa na sake da ke ba, ni mutum mai mai son wasa da dariya mai son nishadi, shiyasa kika burge yau din nan domin ina son mace da ko iska ya wuce sai ta bani labari yadda ya wuce, shiyasa nake son Ex dita amman na lura ke kamar ma kin fita”

“Ex din mutuwa ta yi?”

Ya girgiza kai ba tare da ya kalleni ba.

“Tana nan”

“To ka auro ta mana, ka aje ta a gidan ka, ka ga matarka ma ba zata sake fasawa baki kai ba saboda kishi”

“Ta yi aure ai, ina miki zancen baya ne”

Na yi kwafa.

“Wallahi ba dan haka ba da zai na zugaka ka kara aure, ni Wallahi da ni ce kai aure zan kara matar nan ta bata min rai daga tambaya? Kamar ta ji kowa kishi”

Wannan karon dariya yake min.

“Matata bata kishi, babu wani abu mai alaka da kishi a tsakanina da Matata, kawai dai kin zo a rashin sa'a ne, ko dai kin mata rashin kunyar kamar yadda ta fada, kawai an rubuto jininki zai zuba a yau ne”

Takaici ya hana ni cewa komai, wato bangaren matarsa zai dauka har yana yarda da zancenta ya watsar da nawa. Har muka isa restaurant din ban sake ce masa komai ba.

“Me za a kawo miki?”

Na dan kalleshi ina turo baki gaba.

“Ai da kunya ba komai zan iya fada a nan ba, ni dai zan shiga na karba ka fada musu”

Yayi shiru yana kallona kamar ba zai ce komai ba, sai kuma yayi murmushi ya daga min kai, sannan ya ciro wayarsa ya kira wadda ban san waye ba, ya fada masa wata zata shigo yanzu ya bata duk abun da take so.

“Zaki iya tafiya, amman ba sai kin fadawa kowa tare muke ba, ba a taba ganina da mace ba”

“Zaka iya tafiyarka ai, ni ma ba a ganina da maza, ni ma ba yar iska ba ce ba wai kai ne kadai na kwarai ba”

Ina fada ina yatsina fuska domin na lura so yake ya nuna shi na kwarai ne, ni ce yar iska.

“Ban ce ke yar iska ba ce, kawai ina son na kai ki gida ne cikin mutunci saboda na yi ma iyayenki bayanin yadda kika ji rauni, waya sani idan ban tafi ba za su iya dukanki”

Na kalleshi da sauri na tuni ma na manta da rauni.

“Eh Wallahi musamman ma Baba, bari na je na dawo to”

Na bude motar na fita ina jin kaina kamar wata yar shugaban kasa, ahh a rayuwata fa ban taba shiga mota mai kyau mai tsada irin wannan ba, kuma ina fitowa motar na shiga restaurant na karbo kayan dadi, wayyo Allah ina ma yan unguwar mu za su gan ni a yau. Sai da na kusa shiga reception din sai kuma na tuna da wani abu na dawo baya da sauri na kwankwasa gilashin motarsa sai ya sauke bakin gilashin yana kallona.

“Dan Allah ko zaka min alfarma idan na fito daga sai ka rufe idonka ko kuma ka fita motar har sai na saka abun da na karbo tukuna”

A bakin gaskiyata nake fada masa, domin kar na kwaso kaya da yawa ya ji babu dadi ai da kunya ko, daga kyauta na wuce gona da iri kuma yana gani.

“Ki ce karya min jari zaki yi ko?”

Yanayin yadda yayi maganar da kamar tsoro sai ya saka dariya ta subuce min, na yi bayabaya ina tafiya da baya baya ina dariya, shi ma murmushi yake yana kallona har na juya. Ni dai iyakar abun da na sani ba zan bar wannan banzar ta wuce ni ba, ba zan yarda na fito ba tare da na dauko abun da nake so ba, waya sani ma ko ba zan sake zuwa ba, ai Yaya ba zai bari na sake zuwa ba, kuma hausawa sun ce waman taraka bati sidda fa huwa wawa au sakare, wai duk wadda ya ga bati ya bar shi shi wawa ne ko sakare.

Ina shiga gurin na fada musu abubuwan da nake so, snack kala kala da naman kaza da farfesun kifi da na kayan ciki, har da wata yar tsutsa da na taba ganin turawa suna ci a tv sai da na saka aka hado min da ita yau dai ni ma zan dandana kayan masu kudi na ji me ake ji. Haka na riko leda biyar na fito ina boye ledodin a bayana dan kar ya gani, yace ba ni da hankali na kwashe masa kayan shago. A lokacin da na iso gurin motar sai ya bude min bayan motar na saka komai a ciki na rufe sannan na bude gidan gaba na shiga. Cingan na tarar yana ci yana kokarin juya motar

“Ka ga me na zo da shi?”

“Ba kin ce kar na kalla ba? I respect that”

Ya amsa ba tare da ya kalleni ba. Hakan ba karamin dadi yayi min ba. Sai na saki jiki ina fada masa inda zai bi har muka isa unguwarmu.

“Kwanar gidan mu mota bata shiga, ka aje motarka a nan ka raka ni a kafa”

“Ko dai na kira Yayanki ya zo ya tafi da kai?”

“Aa ko da shi ya yarda Babanmu ba zai yarda ba, kara dai kaje idan aka kira Babana ka masa bayani shi ne zan tsira, dan Allah ka min wannan alfarmar ba zan sake damunka ba daga yau na maka alkawari ba zaka sake ganina ba”

Ya daga min kai, sannan ya kashe motar. Har na bude na fita sai kuma na dawo ya leka shi.

“Amman ka zauna a motar sai na yi nisa sai ka biyo ni”

“Saboda me?”

“Saboda Saurayina idan ya gani zai ji haushi ransa zai bace yana da kishi sosai zai iya maka duka ma”

Yayi murmushin kasaita.

“Ni mai dukana ai sai ya shirya, zai dai yi kishi amman ba zai ina nuna min yatsa ba ma”

“Yana da karfi”

Na fada masa dan ya san Zafeer dina ba rago ba ne.

“Yana da kudi?”

“Aa”

“Toh ba shi da karfi”

“Ba zaka gane ba ai”

“Ke ce dai ba zaki gane ba, saboda ke yarinyar ce baki san yanayin kasar nan ba”

“What ever ni dai karka jera da ni, kuma zan bar maka ledodin a mota sai ka dauko min idan mun isa ka bawa Yayana ya shiga da su?”

“Na dauko kuma?”

“Eh ai ni mutanen unguwa za su iya fadawa Zafeer sun gan ni da ledodi manya, amman kai babu wadda ya san ka ai, ko kuma idan mun tafi ka kira Yaya ka ce ya zo ya dauki ledodin”

“Toh sai dai haka”

“Da nine kai ma cewa Yaya zan yi ya tafi gida yayi kwana biyu”

Ya kalleni.

“Saboda ya wulakanta kanwarsa, ai idan ni yarka ce ba zaka so ayi min haka ba right? Kuma ya bijirewa umarninka be kamata yayi haka ba”

“Haka ne”

Na fita na rufe motar na kama hanya ina fakar idon mutane, sai da na yi nisa sannan na juyo na kalleshi, bawan Allah ashe yana bayana daga can nesa yana bin sawuna. Sai da na isa bakin kofar gidanmu sannan na ja na tsaya har ya iso.

“Ka aika yaro kace kana Sallama da Babanmu”

“Okay”

Tsakanin amsawarsa da okay da yayi da kuma fitowar Baba da ban yi zaton yana gidan a wannan lokacin ba ban san wadda ya riga wani ba. Na ja baya da sauri na koma kusa da ogan kamar zan shige jikinsa.

“Toh Yar iska marar mutunci ina kika dauko wannan kuma?”

Kamar yadda nayi tsammani kalma marar dadi ce ta fito daga bakin mahaifina a izuwa gareni a gaban mutumen da mahaifina be san waye ba.

“Ayi hakuri ranka ya dade, dan akasi aka samu ta bugu a kai shi ne na ce bari na zo na yi muku bayani”

“Ai dama mutuwa ta yi, wannan yarinyar bata da amfani a garemu, wawuyar banza yar iska, ta maka hauka ko?”

Ogan Yaya ya juyo ya kalleni kamar mai mamakin jin furucin mahaifina akaina, ni kuma kunya da bakincikin suka saka na sauke kaina kasa ina taba yatsuna.

“Aa kareta ta na yi ba da gangan ba, ina tare da mota ne bata lura ba ni kuma burkin be tsaya ba sai na ji mata rauni a kai kadan, shiyasa na ce zan so na yi bayani a gidansu kuma na bada kudin magani, amman ayi hakuri dan Allah ba laifinta ba ne”

Baba na jin zancen mota da kudin magani sai fuskarsa ta sauya ya dan saki fuskar kadan.

“Babu komai, ita ce ai bata jin magana”

“Sunana Kareem Ibrahim Kalil, ni ne mai gurin da yaronka Nabil yake aiki”

“Maa Shaa Allahu, ashe ma abun duk gida ne, sannu da zuwa, bari na kira shi shi ma be dade da shigowa gida ba ai”

Kamin mutumen ya sake cewa komai Baba ya juya ya shiga gida. A lokaci ne ya juyo ya kalleni.

“Ki yi hakuri da abun da mahaifinki ya fada, wata kila ransa ne ya bace”

Na kalleshi ina murmushi.

“Na saba ai, Babana yana yawan cewa ba ni da sa'a babu alheri a tare da ni”

Da dare na karasa maganar irin dariyar dake tattare da bakinciki, shi kam kallona kawai yake kamin ya juya daga ni har shi mu kalli Yaya da ya fito daga cikin gidan. Cikin rawar jiki da girmamawa Yaya ya gaishe shi sannan ya kalleni.

“Noor ina kika je? Na iso gida Mama tace baki zo ba, dole na koma nemanki”

Na yi shiru ina turo baki, babu zato balle tsammani na tsinkayi muryar Ogan nasa yana karanta masa cewar ya zauna gida yayi kwana biyu.

“Ranka ya dade laifi na yi? Ko... Ko.. Noor ta yi wani abu ne”

Yana tambaya jikinsa na rawa.

“Kai ne dai ka yi laifi a wane dalili zaka tafi kai dabam ita dabam? Yanzu idan wani abun ya same ta fa? Kuma na baka umarni cewar ka tafi da ita ta dauki abun da kake so baka yi haka ba? Ban isa da kai ba kenan?”

“Dan girman Allah ka yi hakuri oga... Dan Allah ka yi hakuri”

“Ba korarka na yi ba, amman dai ka zauna sai Monday zaka koma aiki”

Wallahi ji na yi kamar na daka tsalle na dire saboda muryar lallai wannan mutumen mai saukin kaine sosai mai jin maganar mata.

“Mu je mota ka karbo mata sako, Noor Allah ya tsare gaba”

Ya karasa yana kallona.

“Ameen”

Na amsa sannan na shige cikin gida ina jin kaina kamar wata sarauniya a yau.



واصل القراءة

ستعجبك أيضاً

53.6K 3.1K 50
Na kasa fahimta da gasgata abinda zuciyata ke ayyana mini a kansa, SO ne ko BIRGEWA?. Komai nasa birgeni yake, ban taɓa ji ko ganin wanda ya haɗa abu...
22.9K 3.3K 31
جۆنگ کوک:بە نەفرەت بیت وازم لێ بێنە چیت لە من دەوێت تایهیۆنگ:ششـ ئازیزم بۆچی هاوار دەکەی ئارام بە بۆ باروودۆخت خراپە ༄༄༄༄༄༄༄ جۆنگ کوک:تـ تۆ چیت کرد ت...
5.1K 234 48
Labarine akan soyayya,cin amana da tausayi,tunasar da iyaye da emmata da ilimintarwa.sakayya Read and find out d main lesson in it
Destiny بواسطة JJK1725

قصص الهواة

5.2K 242 9
Jk : YES I WANT BREAK UP!!! He yelled and for him and for yn everything became still he look sideways and heard a thud sound he see his love of life...