TA ƘI ZAMAN AURE...

By KhadeejaCandy

3.4K 292 20

"Ni ma ina da buri, ina da mafarkai irin na kowace mace, sai dai kuma kaddara ta shata min layi, yadda alƙala... More

Chapter 1
Chapter - 2
Chapter -4
Chapter -5
Chapter -6
Chapter -7
Chapter -8
chapter 9
Chapter -10
Chapter 11
CHAPTER 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Last Free Chapter

Chapter -3

203 20 4
By KhadeejaCandy

https://chat.whatsapp.com/ExyBEuiZZ0J1ivlVK5lIOx

Assalamu Alaikum...
Ina talata muku
KHADEEJA CANDY STORE 🥰🙌
Muna siyar da Atamfa, Laces, Mayafai, Talkami da Jaka, Akwaituna, Kayan Kitchen, Zanen Gado, da kuma kayan kawata gida ko falo.

✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧

𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆

𝐂𝐡𝐚𝐩𝐭𝐞𝐫  -3

Ina zaune a gurin wasu iyalai suka shigo, ba zan iya fadar cewar masu kudi ne sosai ko akasin haka ba. Sai dai alama ta nuna suna da rufin asiri. Teburin sake gabana suka kama yan mata hudu ne sai maza uku da kuma magidancin da zan iya shaidar cewar mahaifinsu saboda kama da tsufan da yayi. Wadda ta zauna a gefensa kuma bana bukatar a fada min cewar ita din uwace domin alamu ya nuna haka. Hannu biyu na saka na yi tagumi ina kallon yadda uban yake handling yayansa mazan suka koma a dayan teburin suka zauna matan kuma suka zauna tare shi.

Sai da suka fara daukar littafin dake teburin suka duba kalar abincin da suke so, tukuna daya daga cikin ma'aikatan gurin ya zo yayi taking orders. Ni kam sai kallonsu nake cike da burge, ba kudin ne abun burgewa ba, ba zuwa restaurants ko order abinci, soyayyar ce ta shiga zuciyata yadda uba yake nunawa yayansa soyayya da kauna yana ta hira da matan suna dariya mazan kuma suna jefo na su hirar daga can inda suke zaune. Wani abu ne da ni na rasa tun tashina, ban tana zama da mahaifina ya tambaye damuwata ko dadi ba, wata hirar farincikin bata taba hada ni da shi ba, ban taba aikata wani abu ya nuna jindadinsa.

“Noor....”

Na juyo dama da ni sai na yi arba da Yayana, hannayensa na ji a fuskata yana share min hawayen da ban san sun zubo ba.

“Kuka kike yi? Saboda na dade?”

Ya tambaya saboda ya san ni da kukan shagwaba kamar wata wadda ta tashi cikin gata. Sai na girgiza masa kai na juya na kalli mutanen

“Wani abu da na rasa nake kallon wasu da suke da shi, kalli yadda suke cin abinci tare da Babansu be burge ka ba Yaya?”

Ya daga kai ya kalli gurin kamin ya dube yana sauke ajiyar zuciya.

“Wata rana ina jin kamar hakan zai faru amman na san ba zai taba faruwa ba”

“Kin cika tunani da yawa, a kawo miki wani abu zaki ci?”

Na saka hannuna da kaina na share hawayen da suka sake zubo min na dubi Yaya dake sanye da uniform din gurin sai tausayinsa ya kama ni, na san yayana ba mutum ne mai son zaman banza ba, yana da kokarin nema, saboda dukanmu mun taso a rayuwar talauci mun san babu kuma mun saba da hakan. A aljihunsa ake samun kudin chefane gidanmu a kullum kuma da kudinshi Mama take zuba adashe tana mana tanadin kayan aure.

“Wa zai biya? Ni ba ruwana bana da ko shishi...”

Yayi dariya domin ya san kadan daga halina ne zan iya komai ko bana da ko sisi sai dai duk abun da zai faru ya faru.

“Za a cire salary”

“Toh a kawo, daman Yaya ban ci komai ba tun safe, kuma ban taba cin abinci a Restaurant ba”

“Me kika so?”

“Akawo naman kaza da na kayan ciki da shawarma da pizza da...”

Ban gama zanawa ba ya katsene.

“Ke fa baki da hankali, duk plate daya a nan 5k plate nawa zaki ci?”

Na bude baki na kalli mutanen gabana na kirga si na kirga kudin da za su kashe.

“Tab toh Yaya a kawo kaza”

“Kaza 10k ne ke kuma abun da zaki ci ba zai wuce 2k”

“Toh ai ka ce 5k ne plate”

“Rabi zan kawo miki”

Be jira abun da zan ce ba ya juya ya bar ni a gurin zaune. Babu jimawa ya dawo rike da plate wata yar shimkafa ce kamar na roka sai wani kofin lemu da gorar ruwa mai yawa.

“Yaya wannan ba zai ce min komai ba, iya halshe zai tsaya”

“Masu kudi kadan suke ci ki yi cin masu kudi, ko baki ga yadda Restaurant din yake ba?”

Ya zare min ido sannan ya tafi ya bar ni a gurin. Ba dan kar nutane su kalle ni da ba zan ci wannan abinci ba, wannan ai rowa Yaya yake min a gurin aikinsa. Na daure na kai zuciyata nesa na cinye abincin nan tass ko shimkafa daya ban bari a gurin ba, lemun ma duka na shanye sannan na dauki ruwan na sha. Kamin na mike tsaye sai ga Yaya ya zo yana kokarin dauke kayan har da ruwan aiko na saka hannu na dauke ruwana, gudun siyar da hali yasa be ce min komai ba ya shiga ciki da kayan, babu jimawa ya fito sanye da kayansa na gida ya rika hannuna muka kama hanyar fita.

“Mi zaki yi da gorar ruwa wane irin kauyanci ne wannan Noor dan Allah ki aje”

“Wallahi ba zan jefar ba, ai ba kyau wulakanta ruwa, kuma ai siya muka yi ba sata ba”

Ina jinsa yana jan tsaki amman ban jefar da ruwana ba, ko ba komai kowa ya gani zai san na ci abinci a gurin, masu kudi ma haka nake ganin suna yi ai, suna rike gorar ruwa a hannu idan suna yawa. Sai da muka fita gate din gurin gaba daya sannan yake tambaya me ya kawo ni ma.

“Yaya kudina zaka ba ni, bikin salwa zan je, dari bakwai daka ara zaka ba ni abuna”

Ya daka min tsawa.

“Ba salwa ba kwai, yanxu saboda bikin wata Salwa kika kwaso kafa kika zo har gurin da nake aiki har da aron na Napep, kuma sau nawa zan biyaki bashinki ne Noor shekarab jiya kin karbi dari biyu last week na baki dari uku dari biyu kawai kika biyo ni, kuma yanzu kin hau Napep da ita, gashi nan kin saka ni siyen plate daya 5k sakaryar yarinya kawai”

Ban san lokacin da na tsayar da tafiyar da nake na dube shi.

“Yaya wannan abincin da naman kahirar ne 5k? Kam bala'i Wallahi a ana zalimci duniya, kuma ni kudina 700 ne”

“Da yardar Allah ba zan sake rantar kudinki ba, ke idan an ari kudinki babu zaman lafiya, kuma sai ki rika kari saboda baki tsoron Allah”

Yana masifar yana tare mai adaidaita, yadda fuskarsa ta hade sai ka rantse da Allah ba shi ne yake tarairayata a cikin restaurant din ba.

“Kuma wannan abincin da kika ci bashi ne sai kin biya. Malam Wurno Road”

Ya karasa yana magana da mai adaidaita sahun.

“Yaya ba gida zamu je ba?”

“Ban sani ba, kuma Allah yasa mu je kin zubar min da mutunci mu koma gida ki ga yadda zan miki wulakanci”

“Toh wai ni nace ka kawo min abinci? Ba kai ka ba ni ba dan kanka to miye na masifa kuma”

“Saboda dari bakwai kika zo har gurin aikina, kuma idan ban kawo miki wani abu abokan aikina ai za su min gulma, kuma kin ba ni tausayi da farko”

Ban yarda na sake cewa komai ba, domin abu ne mai sauke ya sauke ni a hanyar ya tafi ya bar ni, na lura ba karamin hawa yayi wannan masifar da yake ta min kamar na ce ya ba ni abinci a dole. Tun da muka shigo unguwar mai adaidaita be tsaya ko'ina ba har sai da Yaya ya bukaci haka. Gaban wani katon gida ya faka Yaya ya fito ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudi ya bawa mai adaidainta.

“Zai wuce da ke gida”

Ina jin haka na yi saurin fita cikin Napep din na fara yi masa magiya ina kuka. Har ga Allah ba zan yarda ya shiga wannan katon gidan ba tare da ni ba, ko ba komai ai zan bawa idanuwana abinci.

“Yaya ka yi hakuri dan Allah karka ce ya wuce da ni gida, tare da kai zan tafi dan Allah Yaya ka yi hakuri, na yafe maka 700 din ka yi hakuri Yaya dan Allah”

“Ba biki zaki ba?”

“Na fasa”

Ya tsaya yana kallona kamar wadda ya rasa ya zai yi da ni. Ni ko sai rokonsa nake ina magiya kamar wadda za a saka a cikin wata ni'ima. Ganin haka ya saka ya sallami mai Napep din ya nufi gate din gidan dake rufe. Kwankwasa yayi aka bude masa farin gate din muka shiga ciki yana gaisawa da masu tsaron kofar.
Galala na yi ina tafiya ina kallon yadda gidan ya tsaru da abubuwa gidan sama har hawa biyu, gashi komai na gidan fari ne tun daga motoci har fentin gidan, wata babbar kofar ya nufa ya danna door bell sannan yaja ya tsaya, kallo daya yayi min na natsu sa kyau na sauke kaina kasa, ba sai ya tuna min ba, ni ma ai ina ganin yadda komai yake tsare na san gidan masu alfarma ne.

Wata yar lukutar yarinya ce ta bude mana kofar, fara ce sosai babu alamar kashi a jikinta tsokoki ne suke ta rawa kamar wata tufa.

“Tine babanki na nan?”

“Eh ku shigo”

Yaya ne ya fara wuce sannan na shiga ina maimaita sunan nata da yayi min kama da ba kafirai. Suuuuuu na fara jin sanyin ac na ratsani irin tsarin nan na musamman, wannan sanyin ya ci uban na wanda na ji a Restaurant. Da katon Tv na fara arba indiawa dake ciki suna magana kai kace fasa tv za su yi su fito, ga wani kamshin turare da ke tashi kamar dakin Amarya. Ban raina kaina ba sai da na zauna a kujerar da Yaya ya zauna, wani kalar laushi na ji da ban taba jin na zauna a makamancin abu na ji haka ba. Idanuwa suka ce me muka zo yi ba kallo ba, a nan na fara tantance komai na katon falon da ya kasance fari kamar yadda curtains din da labulaye suke, wata kalar wuta ce a rufin mai blue sai haskowa take.

A hankali na sauke idona gurin stairs da aka kawata kamar ba za a mutu ba, a nan na lura da kasan ba tile ba ne, ba kuma suminti ba, wani abu ne mai tsantsi da daukar ido aka malaya a gaba daya falon har zuwa inda muke zaune, ga wani zare zare da aka saka a ciki kamar maciji.

“Yaya Yaya Yaya”

Na kira sunansa na taba shi ya nuna masa wutar sama dake blinking na nuna masa tv na nuna masa tile din sannan na matse hannuna ina masa rada.

“Ac ac ac, sanyi dadi, kujera laushi, kamshi ko'ina ko Yaya?”

Da sauri ya kawar da fuskarsa yayi kamar be gan ni, can kuma ban san abun da zuciyarsa ta raya masa ba, sai ganin na yi ya mike tsaye ya kama hannuna na Mike tsaye muka nufi kofa ya bude kofar ya tura ni waje ya rufe. Ba dan ina da zuciya mai kyau ba Wallahi da na nuna masa tijara na koma ciki da karfi, daga zuwa gidan masu arziki sai wulakanci ta biyo baya, miye laifina dan na ga wani abu ya burge ni, ina ce ban taba gani ba sai yau. Kuma gidanmu ai ba ac nake ba fankar dakinmu ma ta lalace kullum a zafi muke bachi.

A raina na yi guntun tsaki, ina jin haushin yadda be bari na ga mutanen gidan ba, wata kila ma su kawo masa wani abu mai dadi ya ci shi kadai ko ma me ya zo yi a gidan oho, ta dayan bangaren kuma ina mamakin Ina Yaya ya san masu arziki haka. Entrance na nufa na tsaya a gurin na rumgume hannayena tare da gorar ruwan sa na yi guzuri, ina kallon kofar falon ko za a bude.

“Who's this?”

Wani mutun ne tsaye a gefena rike da laptop a hannuna yana kallona.

“Noor...”

Na amsa masa ina dauke kai irin dauke kan dake nuna fushi nake.

“Me kike yi a nan? Can i help you?”

“No ina tare da wani ne”

“Wani?”

“Nabil”

“Okay”

Har ya wuce sai kuma ya dawo baya kadan ya kalleni.

“Me sa kika tsaya a waje? Ke budurwarsa ce?”

Kallonsa nake jin yake yake kokarin kure hakurina da tambayoyi kamar wani dan jarida.

“Me yasa kake ta tambaya haka? Kai ne mai gidan nan ne ko kuma me?”

Ya daga kasansa ya Kalli gidan, da alama dai shi ma bako ne domin yanayin kallon da yake ya nuna haka.

“Aa ni yaron mai gidan nan”

“Daman ai baka yi kama da mai gidan ba”

Ya dan bude ido ya daga gira kadan yana kallona.

“Haka ne, ke budurwar Nabil ce?”

“Ni kanwarsa ce, mun fito daga wata Stupid Restaurant ne yace na rakoshi nan”

“Stupid Restaurant?”

Tambayata yake kamar mai mamaki shi ma dai da alama bakauye ne kamar ni.

“Eh mana idan ba Stupid Restaurant ba, ina za a siyar da abinci haka haka ba wai 5k”

Na nuna masa kam akaifata, sai yayi murmushi ya kara juyowa da kyau kamar mai jindadin zancen.

“Abinci akwai tsada ne?”

“Sosai ni zan iya cinye plate goma ma ban koshi ba, sai wani munafukin lemu da ake zubawa a cup, da ruwa ka ga ragowar ruwan nan na zo da shi, wai Yaya na jefar na Jefar ni kuwa na ki, har da wani cewa wai masu kudi ai kadan suke ci su koshi, masu kudi dan ba su san darajar naira ba za su je wannan gurin su ci abinci har na 5k wai kazar ma 10k ji fa? Saboda yan raina yan Nigeria, Mtseee”

Na ja guntun tsaki.

“Amman da gaske ke za ki iya cinye abincin plate goma?”

“Tsab kuwa”

Ya kalleni daga kasa zuwa sama kamar mai auna idan zan iya ko ba zan iya ba.

“Haka nake ba kiba sai ci, hahaha”

Na yi dariyar kunya kamin ya fara kokarin kare kaina.

“Wasa nake na koshi”

Yayi murmushi mai sauti. Sannan ya miko min hannunsa daya.

“Nice to meet you....”

“Noor...”

Na fada masa, sannan na duba ko'ina na ga babu mai ganina na mika masa hannuna, daman can gaisawa da maza na daga cikin abun da yake matukar burgeni.

“Kai me ye sunanka?”

“Kareem, you can call me Kareem”

“Nice, nan gidan kake zama?”

“Ba sosai ba, mai gidan be cika son ina zama ba”

Ya amsa ni, ni kam ban yi mamakin amsar ba.

“Ai dole yayi wulakanci wadanda ba su kai shi kudi ba ma suna wulakanci balle mai wannan gidan, kana gani ka san mai kudi ne sosai”

Na fada, sai ya sake daga kamshi yana kallon gidan.

“Not really yana da rufin asiri dai”

“Ba wani rufin asiri yana da kudi sosai Wallahi, kai dan Allah wannan gidan be burge ka ba?”

Yayi murmushi, a madadin ya amsa ni sai ya jefo min wata tambayar.

“Me yasa kika tsaya a waje? Da kin shiga ciki kin ga yadda cikin yake ai”

“Na shiga fa, amman Yaya ya fito da ni kar na masa kauyanci”

Be sake ce min komai ba ya nufi kofar ya bude, sai ya juyo ya kalleni yayi alama da na zo na shiga da kai. Abun nema ya samu haka na taka na nufi kofar na shige cikin falon, sai dai wani abun da ya daure min kai kuma ya ba ni mamaki shi ne mikewar da Yaya Nabil na yi zaton ko zai sake korani waje ne sai na ga ya risina yana mikawa mutumen dake baya gaisuwa.

“Ranka ya dade barka da yamma”

“Nabil ya gida?”

“Lafiya Kalau Oga, ban samu zuwa tare da Coworkers dina na duba ka dazun saboda ina can ciki gurin girki, shi ne na yanke shawara sai na tashi aiki sai na zo na gaishe ka”

“Ka kyauta have a seat please”

Ya nuna masa kujera sannan shi ma ya zauna, ni dai tsabar mamaki sai na tafi zan zauna a kasa saboda kunya da daurewar kai.

“Karki zauna a kasa mana, ga kujera”

Ya nuna min kujerar da Yaya yake zaune. Sai Yaya ya bugu kafadata.

“Ki gaishe shi mana, oganmu ne, shi ne mai Restaurant din da muke aiki”

Kulololo na ji cikina yayi wani kuka kamar na yunwa, har sai da ya kalleni hakan kuma be hana ni zubewa kasa na sabunta gaisuwata ba.

“Ina wuni”

“Mun gaisa a waje ai, kin tuna? Tashi ki zauna”

Na mike tsaye ina juyawa na kalli Yaya Nabil sai ya watsa min wani mugun kallo. Na yi saurin sauke idona kasa ina jin kamar na tsargi kaina.

“Toh ai Yaya baka fada min oganka ba ne, ao ya za'ayi na sani...”

Na yi zaton a zuciyata nake maganar ashe ta fito ban sani ba, har sai da ogan da ban gama yarda shi ne mai gidan ba ya amsa ni.

“Toh me kika yi? You're just friendly that's”

Da sauri na rufe bakina, wata sabuwar kunya na kara rufeni, kamin na daga kai ina kallon wata mata dake saukowa a stairs, babu wani walwala a tare da ita, shi ma kuma mai gidan na lura da yadda fuskarsa ya sauya daga murmushin da yake min zuwa hade fuska irin na mazan da basa son wasa.

“Nabil”

“Hajiya ina wuni?”

“Lafiya Kalau ya aiki?”

“Alhamdullahi”

Ni ma na gaishe ta sai ta amsa min fuska a sake, sai dai bata yarda ko gefen da mijinta yake ta kalla ba, shi ma kuma sai yayi kamar be san da wanzuwarta a cikin falon ba. Har ta nufi wata hanyar da nake kyautata zaton kitchen ne. Yaya Nabil ya mike tsaye ya kalleni ni ma sai na mike tsaye.

“Zamu wuce oga Allah kara lafiya yasa kaffara ne”

“Ameen na gode”

Ni dai ban ce komai ba, na bi bayan Yaya ina kallon kofar da matar ta shiga.

“Nabil”

Yaya ya juyo da sauri yana kallon ogan nasa da ya kirashi.

“Ranka ya dade”

“Ka koma da ita Restaurant ta zabi duk abun da take so, Noor sai an jima ko?”

Ya karasa yana kallona da Murmushi a fuskarsa kamar ba shi ba, wani kyakkyawan murmushi na aika masa mai kayatarwa sa jan hankali saboda jindadin yace a ba ni duk abun da nake so.

“Amman... Okay Sir mun gode sosai Allah ya kara rufa asiri”

“Thank You”

Na fada in a low voice gudun kar matarsa ta ji ta fito tace zata min duka, domin na lura matan auren yanzu ba su da hankali akan mazanjesu sai su yi ma mace duka. Hannu ya dago min alamar bye bye sannan na juya muka cire tare da Yaya. Rufe kofar falon ke da wuya Yaya ya fara tambayata me na yi.

“Ban yi komai ba, amman Yaya baka lura ba? Kamar baya zaman lafiya da matarsa ko?”

Yaya janyo hannuna da sauri muka sauko daga gurin.

“Wallahi ba dan wani abu ba, da sai na ce masa ina gyaran aure saboda na ci kudi, na ce masa ni mai bada shawarware ni akan aure.... Kuma yana da kyau ko Yaya? Wannan lukutar yarinyar yarsa ce? Matarsa ma kyakkyawa ce ko Yaya?”

Muna tafiya ina fadar abun da ke zuciyata a iyakar gaskiyata.

“Ban sani ba, Noor Ban taba sanin baki da hankali ba, sai yau gidansa fa ko'ina camara ne har da wani fadar kina gyaran auren saboda baki da hankali, shiyasa kika nace sai kin biyo saboda ki zubar min da mutunci”

Be sake hannuna ba sai da muka fito daga cikin gidan gaba daya. A raina ina ta ayyana irin takeaway da zan yi ma rabin raina Zafeer idan mun koma restaurant din...

Continue Reading

You'll Also Like

157K 10K 40
WANNAN LABARI NE DA WASU BANGARE YA FARU A GASKE. BAN CANJA SHEKARUN YARINYAR BA KO ALAKA BA,AMMA NA CANJA SUNA, SANNAN BABU SUNAN GARI DA KUMA ANGU...
22.7K 3.3K 31
جۆنگ کوک:بە نەفرەت بیت وازم لێ بێنە چیت لە من دەوێت تایهیۆنگ:ششـ ئازیزم بۆچی هاوار دەکەی ئارام بە بۆ باروودۆخت خراپە ༄༄༄༄༄༄༄ جۆنگ کوک:تـ تۆ چیت کرد ت...
302K 19.1K 40
-: Миний хайрлаж байгаа цор ганц зүйл бол чи
3.1K 215 45
Ƙaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar...