TA ƘI ZAMAN AURE...

By KhadeejaCandy

8.9K 367 24

"Ni ma ina da buri, ina da mafarkai irin na kowace mace, sai dai kuma kaddara ta shata min layi, yadda alƙala... More

Chapter 1
Chapter -3
Chapter -4
Chapter -5
Chapter -6
Chapter -7
Chapter -8
chapter 9
Chapter -10
Chapter 11
CHAPTER 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Last Free Chapter

Chapter - 2

593 30 0
By KhadeejaCandy

Daga bakin zaure na tsaya ina leka ciki sai na hango Hana tana daka a turmi Mama kuma tana zaune gaban murhu tana aikin hura wuta. Yaya Nabil kuma yana daga gafe yana wanke wandonsa da talkami.

“Ina kika je?”

Na kalli Yaya sai na jingina da kofar bana son amsa masa tambayar domin na san fada zai min ni kuma ban iya karya ba komai za ayi min sai na fadi gaskiya.

“Ba magana nake miki ba”

Ya daka min tsawa, na dan matsa baya na saka hannu a baki ina cin akaifata.

“Yaya Mama fa ta cinye abincin da ka kawo kuma tace zata min duka shi ne na bar gidan na tafi gidansu Zee mamanta ta ba ni abinci bayan na ci ta zuba min wani a kula na kaiwa Zafeer”

Yaya ya girgiza kai yana murmushi.

“Yanzu ke gidan ku ana kokuwar yadda za a cefane a girka masara amman kin samu abinci sai ki kaiwa saurayinki? Noor Allah ya shirya ki”

Mama ta tabe baki

“Ai wannan yarinyar abu ne mai wahala ta yi jinkaina, duk abun da ta samu a duniyar nan sai dai ta kai ma saurayi babu ruwanta da ni”

“Toh ni Mama me nake samu? Kullum fa babu ne a gidan, kuma ai kece kika ce dukana zaki yi shiyasa na kai masa”

“Kya ji da shi dai, wuce ki daki kasan gadona ki dauki kudin adashe ki kai ma Assabe ki ce ga zubi na biyar nan”

“Mama yanzu kina da kudin adashe kika hana ni na babur din da zan tafi bikinsu Salwa?”

“Kudin adashen zan baki ki tafi biki? Wa nake ma dashen ba ku ba? Kudin kayan aure nake tara muku ai”

Ina jin haka na san Mama ta sauko kenan dan haka na wuce cikin gidan na shiga dakinta na dauko kudin a gurin da ta saba ajewa na fito ina kallon Yaya Nabil da zai zubar da ruwan kumfa.

“Yaya na kawo kala ɗaya ka wanke min dan Allah?”

Wata uwar harara ya watso min sai na yi saurin barin jikin kofar dakin na nufi hanyar waje.

“Kawo kala daya amman”

Ban yi mamakin jin haka daga gareshi ba, daman Yaya Nabil mutum ne mai sauki kai a gareni. Na juyo cike da kuzari da jindadi na nufi dakinmu na dauko tufafina na sallah babba da mayafin sai kuma na tuna ba lallai ne Hana ta yarda ta min kwaliya ba dan haka na dauko abayata na mika masa ta.

“Gashi Yayana na gode”

Na mika masa cike da ladabi.

“Kuma na fada miki ki daina zuwa gurin aikin Zafeer ko? Ba yau na sha miki magana amman baki ji”

“Abinci kawai na kai mishi idan ba yace na kai mishi abinci ba ko kuma na zo na karbi abu Wallahi bana zuwa, Yaya ni ma fa ina da hankalina”

Be sake ce min komai ba ya jefa abayar a ruwa ya fara wankewa ni kuma na nufi kofar fita ina yi ma Hana gwalo. Domin na san idan ita ce ba zata wanke min ba ko da kuwa zan yi hauka.

“Dan Allah can mai kayan aro”

“Na ji dai na ji dai ba zan cire ba”

Na fice abuna ina tafiya a natse, daman can bana kama da marasa tarbiya ko natsuwa zakewar da nake abu ma idan na san mutum ne ne nake yi, idan ban sake jiki a guri ba ko uffan bana cewa. Cikin natsuwa na isa gidansu Talatu mai adashe na bata kudin kuma na fada mata zubi na shida ne kamar yadda Mama tace ma fada, sannan na juyo na fito, a kokarina na takaitawa kaina wahala na biyo ta kwararo kwararo domin ya fi sauki sama da mike hanya sambal.

Wani abun da ban saka rai da tsammani ba ashe rabon ganin wani abun ne ya biyo da ni ta hanyar, Abbah na gani tsaye kofar gidansu Gambo mai furar yan gayu rike da yar ledarsa baka sai gyaran riga yake. Ban yo mamaki ba domin akwai zaurawa a gidan har biyu da kuma yan matan da ba a taba yi ma aure ba. Rage tafiya na yi saboda na samu damar ganin wadda Abbanmu yake so cikin ƴaƴan gidan, amman hakata bata cin ma ruwa ba, domin har na kawo kusa da Abbah yarinyar bata fito ba.

“Abbah ina wuni”

Na gaishe shi, sai yayi saurin dauke kai kamar be gan ni ya hade rai.

“Abbah gidan dawo (Fura) za a siyo maka kawo na karbo maka”

Na fada cikin ladabi sai dai hikimar ba dan na siyo masa ba ne kawai sai dan na dalilinsa na zuwa gurin.

“Me kike yi a nan?”

Ya daka min tsawa dai da na zabura zuciyata ta buga kamar zata fado.

“Mama ce ta aike ni na siyo mata fura”

Na fada ina kokarin kare kaina, rufe bakina ke da wuya sai ga Bilki ta fito daya daga cikin yan matan da suke gidan ta chaba ado kamar wanda zata je gurin biki. Ganina tsaye ina kallonta ya saka ta juya da sauri ta koma cikin gidan ba tare da ta fito ba.

“Zaki wuce ko sai na ci ubanki?”

Kalamin da Abbah yayi ya dawo da dubana gurinsa sai na matsa baya da sauri na kama hanyar gida ina tafe ina waigensa shi kuma be fasa cika yana min dakuwa ba (Zagin hannu kun san hausar mu da ta ku ba daya ba😁) har sai da na karya kwana a nan na boya cikin wani kwararo ina lekonsa, wayarsa na ga ya ciro yana dannawa sai dai kamin ya kai wayar a kunne wani kamin yaro ya fito yayi magana da shi, sai na ga Abbah ya mika masa ledar hannunsa sannan ya juya ta hanyar da na biyo ya wuce.

‘Wato Balki da Abbah na take soyayya kenan hmmm’

Na fada a raina a zahiri kuma sai na juya na nufi hanyar gida, kamin na isa zuciyata ta cika har ta kusa fashewa tsabar takaici da baki ciki. Ban tsaya sallama ba haka na shiga gidan na zauna kusa da Mama dake tuka tuwon masara na jera mata abun da ya faru sai hakki nake saboda bacin rai.

“Wata kila dai fura zai siya”

Yaya Nabil ya fada kamar wanda be yarda da maganar ta ba.

“Wallahi ba wata fura, ai ba leda aka kawo masa ba shi ya bada ledar aka shiga da ita gidan, kuma har ce masa na yi ya kawo kudi na karbo masa sai ma zagina da yayi”

Ina maganar ina yamutsa fuska.

“Wallahi sai na mata mugun duka”

Mama ta nuna ni da muciyar da take tuka tuwo da alamar dake nuna babu wasa maganarta.

“Wallahi ko yatsa na ji ance kin nunawa Balki sai na ci ubanki sai na miki dukan da zai daukeki lokaci kina jinya, kuma kin san halin Abbanku ko? Bara saboda Amaryarss ya karya miki hannu, idan baki cire idonki akan Balki ba sai zai iya kashe ki ma”

“Amman abun da yake be dace ba, irin wannan ke janyo raini s unguwa, kuma ko aure zai yi me zai yi da Balki Fisabilillahi”

Cewar Yaya Nabil cikin da bakinciki. Mama tace

“To ya zaku yi Mahaifinku ne sai Hakuri, idan ya tashi aikata abu kun san babu wanda ya isa ya hana hakan faruwa, saboda haka bana son na ji bakin kowa a cikinku, musamman ma ke Noor ke ce marar jin magana, duk dukan da za'a miki ba ki ji”

Na turo baki gaba, domin Allah kadai ya san irin rashin mutum da zan yi ma Balki idan ta yarda da auri ubanmu.

“Har da leda baka ya bata”

Na sake fada ina tuna dukan da yayi ma Mama dazun saboda tace ya bada garin masara babu kudin cefane.

“Daman ke kin iya karawa miya gishi ai, idan baki fadi komai ba to ba ke ba ce”

Na juya ba kalli Hana na watsa mata harara. Yaya Nabil ya shafa kansa damuws na bayyana a fuskarsa.

“Wani lokacin sai na ji kamar na tafi na bar garin nan Wallahi, abubuwan da Abbah yake sun yi yawa, muna neman abun da za mu ci amman shi ta aure yake, yaushe ya auro Baaba Maryam yanzu kuma ace har ya fara tunanin auro wata, watan ma karamar yarinya sa'ar yarsa”

“Kuma dazun saboda kudin cefa ne ya doke ki Mama wai bata godewa komai ya kawo Allah kadai ya san meye a ledar nan da zai bawa Balki”

Mama ta rufe tuwon tana fadar.

“Cigaba karki fasa, tun da kin zama yar iska gararariyar gidan nan, ke idan aka ce kar ayi abu sai kin yi, ki cigaba”

Ina jin haka na yi shiru da bakina ban sake cewa komai ba, daga haka maganar ta mutu sai dai kowa da abun da yake sakawa a ransa. Ana hada hadar kiran sallah magariba Abbah ya shigo gidan a lokacin duka hannayenmu suna cikin tuwon masarar da Mama ta girka. Ni da Yaya muna ci a kwano daya daman idan yana gida hade mana abinci nake saboda na bawa Hana haushi.

“Wa'alaikumussalam”

Mama ta amsa mu kuma muka masa sannu da zuwa, sama sama yake kallo kamar wanda yayi arba da abun kyama, more especially ma ni.

“A kawo abincin ko sai ka yi Sallah”

Abbah yayi kamar be ji abun da Mama take fada ba ya nufi wani dutse da ya saba zama yayi alwala ya zauna, ina ganin haka na cire hannuna a abinci na nufi butarsa na dauka na zubo ruwa kamin na karasa gurin da yake zaune sai fada ya biyo baya.

“Wai kamar ni a cikin gidan za a wurgar min da buta a waje, aje ta babu ruwa har sai na taba, saboda an rai min wayo kuma duk laifinki ne Hajara”

Ban yarda na karasa gurin da yake zaune ba, na aje butar daga nesa domin yanayinsa yana nuna alamar ransa a bace yake kuma zai iya kai min duka. A madadin ya dora laifin a gareni sai ya juya ya kalli Mama yana nuna ni da hannu.

“Kin gani ko? Raina nin da kike min yara sun dauka, gashi ta kawo ruwa ta aje nesa da ni wato na taso na dauka”

Mama ta kalleni kamar zata ce wani abu sai kuma ta yi shiru, domin yanayin tsayin da na yi ya nuna alamar tsoron karasa nake kusa da shi. Ko da kuwa ban aikata komai ba Abbah zai iya min duka balle kuma na gan shi a gidansu Balki kuma ya san sai na fada.

“Ba zaki dauki ruwan ki bashi ba sai na ci ubanki”

Yaya Nabil ya daka min tsawa kamar ba shi ba, wata kila laifin da Abbah ya dorawa Mama ne ya fusata shi. Na duka na dauki ruwa, ban kai ga mika ma Abbah ba ya juyo ya kalli Yaya Nabil.

“Tooooo ka ci ubanta, ni kake zagi ba ita ba, daman ai ni na san ba kaunata kake a gidan nan ba, to sai ka ta so gani zaune a nan ki cinye ni, zan baka mai da yaji, daman ai yanzu abun da yara suke yayi kenan su kashe iyayensu, sai a fara saka ka a gidan redio ana hira da kai ka ga ka ci riba...”

“Subhanallahi kar Allah ya kaddara mana wannan ranar ko bana raye, kar Allah ya nuna mana wannan ranar, bana fatan hakan”

Mama ta fada tana cire hannunta a kwanon tuwon da take ci.

“Kina fata kan ai duk tarbiyar da kika koya musu ita suke yi, daga matan har mazan ita dai wannan babu albarka a tare da ita tun da aka haife ta komai ya lalace, gashi nan kuma yanzu tana daukar tarbiyar da kike koya Musu”

Ya karasa yana nuna ni haka yake yawan fada, wai tun da aka haife ni komai ya lalace masa har yau be zama kowa ba.

“Dukan abun da zai samu bawa daga Allah ne Malam ka daina maida laifin a gurin Noor, kuma ni bana koya musu tarbiyar da zai saka su raina ka Allah yana gani ai”

Mama ta fada cikin yanayin dake nuna kukan na son fitowa a idanuwanta da bakinta. Sannan ta kalli Hana ta ce.

“Karbi ruwa ki ba shi wata kila tsoro take ji kar ka doketa kasan halin Noor Malam ba sai an fada maka ba”

Kana ta kalli Nabil

“Tashi ka tafi gurin Sallah”

Ya cire hannunsa a tuwon da tuni ya dakatar da cinsa ya mike tsaye ba tare da ya wanke hannun ba ya fice a haka kamar wanda baya son kara minti daya a gidan. Hana ta karbi ruwan hannuna ta karasa kusa da Abbah ta aje masa, sannan ta Abbah ya kalleni.

“Kuma bari na fada miki Noor, idan na ji yarinyar da fadi wani abu akanki sai na lahira ya fi ki jindadi, kin san sau uku ina neman aure kina lalatawa ko? Allah yasa ki aikata wani na ji”

Na yi shiru ina tsaye a gurin kamar hoto har sai da Mama ta yi min alama da na bar gurin da kai. Sannan na kauce na koma na dauke kayan da muka ci abinci na kai gurin da muka saba ajewa, juyowar da zan yi sai hawaye ya sauko a ido. A cikin kalaman da Abbah yake yawan yi min babu mai bata min rai kamar cewar ni din ba alheri ba ce a tare da shi, kusan ya fi tsanata fiye da Hana da Ya Nabil. Hannuna na saka na share hawayena na nufi wata butar na dauka na zuba ruwa na nufi bandaki, ina fitsari ina hawaye, ban yarda na fito ba har sai da Abbah ya fice daga gidan, ba zan iya fadar cewar ni ce kadai ban san dadin mahaifi ba, kusan dukanmu haka muke tun da muka bude ido mun samu mahaifinmu mutum mai wuyar sha'ani da baya sakewa da iyalansa duka kuma babu kalar wanda be mana, musamman ma ni da na kasance marar jin magana. Abu ne mai wahala wani kalami mai dadi ya fito daga bakin mahaifinmu izuwa garemu, idan ma mun dada masa to zai bar abun a ransa ne ba zai yi magana ba, idan kuma muka bata masa a take zamu gani.
Mahaifina wani kalar mutum ne mai wuyar sha'ani mai wuyar mu'alama ga Iyalinsa, kuma mai son zuciya da zafin hannu abu kadan zai doke mu ko mahaifiyarmu a gaban idonmu. Rayuwar da muke yi a cikin gidan mu izuwa yanxu ya ci ace mun saba da ita amman ni na kasa sabawa da hakan, kullum ganin abun nake kamar sabo.

“Noor ba dai kuka kike ba?”

Na daga kai na kalli Hana dake rike da karamar buta tana dafe da kafadata.

“Hana Abbah yana yawan fadar bani da albarka ko ba ni da sa'a, yana yawan cewa sanadina ya rasa aikinsa sanadina ya fara talauci, idan mutum ya ce miki haka sai kin ji kamar ki kashe kanki, balle kuma mahaifi, kullum kalma sabuwa take zame min”

“Haba Noor ke da kike haske? Hake gidan nan hasken zuciyarmu, idan baki nan babu mai sakewa maganar Abbah ta daina damunki, Abbah ba shi da dadi a gurin kowa ke kin sani Mama ma be raga mata ba balle kuma mu, dan Allah karki bata ranki”

“Toh”

Na amsa ina share hawayena, sannan na cigaba da alwalar. Yaya Nabil be dawo gidan ba sai bayan Sallah Isha'i yana shigowa Mama ta hada mu gaba daya ta yi mana nasiha shi kuma ta ja masa kunne akan zagin da yayi min dazun a gaban Abbah.

“Raina ne ya bace Mama Noor ce ta yi laifin Amman gurinki yake maida laifi, kuma ita ja hakan ya faru, ba wai na zage ta dan yana tsaye a gurin ba ne, Wallahi zuciyata ce ta rufe na yi mata zagin”

“Toh ka rika danne zuciyarka dan Allah ka rika kawar da ido akan komai, ka samu ku rabu lafiya da mahaifinku”

Yaya amsa da In Shaa Allahu sannan ya tashi ya dauko kayan da ya wanke ya shimfida tabarma a waje ya fara gogewa da dutsen karfe na wuta. Sai da ya gama goge na shi sannan na dauko Abayata ya goge min ya nade min ya kawo min har inda nake zaune ya mika min.

“Na gode Yayana”

Murmushi kawai yayi min ya juya ya shige dakinsa na kalli Hana dake sauraren littafi a wayar Mama na ce.

“Kin gani ba irinki ba, ke baki da nasiha ko tufafinki aka taba sai kin fara fada”

Uffan bata ce min ba gaba daya hankalinta ya tattara ya koma gurin wayar dake makale a kunnenta. Sai dai sallamar da Abbah yayi ya saka ta yi saurin cire wayar ta tashi zaune ni kuma na amsa sallamar na masa sannu da zuwa na  shige dakinmu, shigata da mintuna kadan Hana ta shigo. Daga ni har ita babu wanda ya sake fita dakin gar garin Allah ya waye.
 
Kamar yadda muka saba Hana ce take hada mana abun karyawa saboda ita ce mai zuwa makaranta, saboda haka da wuri take tashi ta dumama mana idan an raga abinci idan kuma koko za a siyo ko a dama duk ita ce take yi. Sai dai yau ni dai bana sha'awar cin dumame dan haka ban fito na karbi nawa ba sai da na ji motsin Yaya Nabil yana magana da Mama a tsakar gida. Fitowa na yi na zauna bakin kofar dakinmu a lokacin Hana ta dade da wuce makarantar boko.

“Yaya ina kwana”

“Lafiya Kalau sai yanzu kika tashi”

“Tun dazun ta tashi, wai ita yau bata son dumame shi ne taki fitowa ta karba”

Mama ta fada tana juyowa ta kalleni. Yaya Yayi murmushi ya girgiza kai.

“Ni dai yau ba ni da ko sisi idan zaki ci dumame ki ci, idan ba zaki ci ba cikinki ne”

“Yaya dan Allah ka siya min indomie Wallahi bana son dumeme kullum shi muke ci”

Mama ta saka dariya.

“Wuya bata ci ba yarinya, idan kika ji yunwa da kanki zaki nemi tuwon ma”

Mama ta tashi ta shige dakinta, Yaya kuma yayi fitarsa aka bar ni a gurin zaune, sai da na ga babu sarki sai Allah na dauki kwano na gutsira tuwon kadan na ci na aje sauran, tsintsiya na dauka na share ko'ina na gyara daman wanki da wanke wanke ko girki ba nawa ba ne, a cikin aikin gidan babu abun da na tsana kamar wanke wanke da wanki, girki kuma Mama ta fi sha'awa ta girka da kanta, ba kasafai take bari muna mata girki ba.

Misalin karfe biyu da mintun Hana ta dawo daga makaranta, ita kam bata tsaya neman wani abincin ba ta saka dumamen da na ce ba zan ci ba ta cinye abunta ta bar ni da yunwa a ciki. Ina tsaka da miyar ta cinye min tuwo kawata Zee ta shigo gidan cikin shirinta na ankon kamu, ba karamin burge ni ta yi ba domin ta yi kyau sosai ankon ya karbe ta gashi ni ban yi ba, sai yabon kyauta nake.

“Mama kin gani sai da na ce Yaya yayi min ankon nan ya ki”

“Komai dai Yayanki, ki rika tausaya masa mana Noor abun ai sai ya masa yawa, komai dai shi ne, me yasa baki ce Zafeer yayi miki ba?”

Na kalli Mama dake kare danta.

“Shi ai be da kudi”

“Shi kuma yayanki banki ne ko?”

Na turo baki gabana ina son yi mata kukan shagwaba.

“Yanzu kuma ko sisi ba ni da na tafiya bikin nan fa”

“Daina kallona Wallahi ni ma ba ni da ko naira”

Zee ta saka mana dariya.

“Ashe kuwa ba za aje da ke ba, ni ma ba ni da kudin tafiya, na san dawowa ba zai yi wahala ba saboda samari”

“Bari na tafi gurin Yaya ina binsa kudi 700 ya bani ko 200 na samu na napep”

Na tashi na zuba ruwa a bokita na shiga bandaki na yi wanka na fito na shafa mai na dauki hodar Hana na shafa da jan bakinta na yi kwalliya na yi kyau sosai sannan na saka abayata na dora mayafin, na fito daga dakin na bar Zee tana kara gyara fuskarta sa kayan kwalliyar Hana dake ta yi mana masifa wai sai mun biyata ai kwaliyar kudi take ba kyauta ba.

“Daga nan zaki iya tafiya a kafa har gurin aikinsa? Kuma kika sani ko yana da kudin ko babu, wannan tafiyar kamar ta dole Noor?”

Mama ta fara kokarin hana ni, aiko take na bata fuska.

“Mama komai fa ban tafi ba na Salwa kuma wannan ne event na karshe ni dai ina son zuwa, kuma Yaya ba zai rasa kudin da zai ba ni”

“Allah ya kiyaye ga ki ga hanya, idan be ga dama ba ai ba zai baki ba, ko ma ya hana ki tafiya bikin”

Na saka talkamina na high hill na fice daga gidan, ba a kafa na taka ba titi na isa na tari mai adaidaita sahu na fada masa inda zai kai ni yace na bada 200 naira kasancewar babu wani tazara sosai.

“Kadai san Kareem Restaurant ko?”

“Hajiya tun da ke kin san guri ai babu wata matsala”

Na shiga Napep din ya ina ta rabon ido har muka isa Fancy Restaurant din na fito na shiga ciki domin ba wannan ne zuwana na farko ba, can ciki na wuce na yi magana da wani na fada masa ya kira min Yayana.

“Yana can ciki aiki suke lafiya?”

“Lafiya kalau mai Napep zan sallama kuma zan yi magana da shi”

“Bari na kira shi a waya amman idan suna girki ba a bari su fita”

Ina tsaye a gurin abokinsa yana ta kiransa a waya be amsa ba, hakan ya saka hankali ya dan tashi domin na san halin wasu masu Napep ba su da mutunci. Komawa na yi na leka waje na sake dawowa ganin hankalina ya tashi ya saka Yusuf tambayar nawa ne kudin napep din na fada masa sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro 200 ya ba ni na fita da saurina na kaiwa mai Napep din.
Sannan na dawo na tsaya reception din, ina ta kallon mutane da yadda ake ta sake sabunta gurin, a kullum idan ka zo sai ka ga ya sake zama sabo.

“Noor yayi picking yace ki zauna ki jira shi sai sun gama girkin zai fito”

Abokinsa ya fada, na kalli katon agogon dake gurin na ga uku da yan mintuna, na san ya kusan tashi aikin ma gaba daya, saboda haka na nemi guri a teburin da mutane suke zama na zauna ni kadai ina ta jin rashin sakewa saboda akwai mutane da yawa a gurin, duk kuwa da kasancewar kowa sha'anin gabansa yake. Ta dayan bangaren kuma ina jin dadin yadda sanyin Ac ke ratsa jikina, rabon da na ji sanyi ac har na manta. 

Continue Reading

You'll Also Like

His burning desire By charmi

Mystery / Thriller

49.7K 3.3K 29
"he was her dark fairytale,and she was his twisted fantasy" 〜⁠(⁠꒪⁠꒳⁠꒪⁠)⁠〜 This is psychopathic Romance novel which is mix of office rom-com+marriage...
31.9K 4.4K 65
🐾️ Caractors වෙන වෙනම introduce කරන්නෙ නම් නෑ.. 🔞 කොටස් සහිත නිසා කැමති අය විතරක් කියවන්න හොඳේ. Daily Updates නම් දෙන්න බැරි වේවි.. පුළුවන් ඉක්මනට...
5.1K 985 12
هەموو شت بە باشی دەڕۆیشت هەمووان دڵخۆش بوون بەڵام دووبارە ناخۆشی هات و پێویست بوو بە تاقیکردنەوەی ژیان تێپەڕن
246K 16.9K 29
𝐓𝐇𝐄𝐘\'𝐑𝐄 𝐀 𝐌𝐀𝐅𝐈𝐀.🧠💸🛢️. عالم مُغطىٰ بالذهب الأسود وَ السوَآد . حياة اعيشُها حالكةُ الظُلمِ وَ الظلام . أرواحٌ مــأسـورةٌ في سـرآيا ا...