RANA DUBU

By JameelarhSadiq

124 10 0

KINGDOM STORY More

002
003
04
05
06
07
08
09
010
011
012
013
014
015
016
017
018
019
020

01

27 3 0
By JameelarhSadiq

*🌺RANA DUBU...🌺*   
*~A KINGDOM AND ROMANTIC LOVE STORY~*

_STORY AND WRITING BY_
*©️®️JAMEEY*

_M W A_

_WRITER OF_
*NIDA UWARMIJINA*
*BUƊARƊIYAR SOYAYYA*
*DA'IMAN ABADAN E. T. C*

_20/9/2023_

001

*MASARAUTAR MALI*

*2:30am*

Cikin kuka da zafin raɗadin haihuwa ta kamo hannun wata mata dake gefenta tana aikin hawaye,kallon ɗaya zakayi masu ka gane yanzun yanzun mai haihuwar tayi ta,dan ko uwa bata daɗe da fitowa ba,kuka take cin karfinta dan ko motsi daƙal take yin shi ga jaririn da yake ta kuka tun da ya fito duniya ta ɗauka tana mai kurama fuskarshi ido tausayinshi ne ya kamata ya shigo duniya mai cike da ƙalubale da kuma sarƙakiya iri iri..balle a inda a haifeshi gidan sarauta, gidane mai cike da qaddarori daban daban..ta tabbata idan har ta bar wannan yaron a wannan gidan mugayen mararsa imani ba zasu taɓa barin yaron yakai labari ba, saboda wani buri nasu marar taushe da kuma rashin imani da rashin tausayi da ya baibaye zukatansu..dan ba imani ne da su ba balle har zasuji tausayinshi,duba da durowarshi duniya kenan...Ba abinda suka sa a gabansu sai neman duniya da abinda ke cikin ta,dan sam basu tunawa da mutuwa balle kuma ranar tsiyuwa ranar kin dillacin amman tasan komai daren daɗewa gaskiya zatayi halinta dan ance *RANA DUBU* ta ɓarawo  *RANA ƊAYA* tak ta mai kaya,tana addu'ar Allah ya nuna mata *RANA ƊAYA* Ranar da gaskiya zatayi halinta,jona mashi nono tayi ya fara tsotsa ganin mudun tace zata barshi yasha nono to mutunen nan zasu iya dawowa su taddasu zare baƙin nonon tayi daga bakin yaron,kuka ya tsalla jin ta cire nonon waigawa tayi tana kallon matar da ke tsungune a gabanta kanta a ƙasa yake tana hawaye girgiza kai kawai tayi..a hankali ta buɗe bakinta sai kuma sauke ajiyar zuciya,murmushi ta sakar mata tana mai kamo hannunta ta ɗaura mata yaron samun hannunta tace.

"FATIMA"

Ɗago kanta wanda aka kira da FATIMA tayi tana mai kallon yaron da FAUZAJ RAHMA ta ɗaura mata a hannu, cikin rawar jiki da ƙarmar baki dan jikinta ba inda baya rawa tsabar tsorata da shiga firgici daƙyal ta iya haɗa yawau bakinta ta samu ta taitaro sauran natsuwarta tana cewa.."Na'am Allah ya ƙara maki girma da nisan kwana da lafiya yake ke uwar gajiyata  FAUZAJ RAHMA."Murmushi FAUZAJ RAHMA tayi tana sakar mata yaron tana cewa."na yarda dake Fatima kin wuce duk yanda kike tunani a wajena." Dan shuru tayi tana share hawaye masu zafi da suka zubo mata tana cigaba da cewa.."na tabbata duk kulawar da zan ba wanann yaron ke ma zaki ba shi,kuma duk soyayyar da zan nuna mashi kema zaki nuna mashi irinta koma fiye da ita,tarbiyar da nike mafarkin bashi kema zaki bashi ita har ma fiye da tawa..dan haka ga amana nan baki ki kula da shi ki mandashi ɗan da kika haifa da cikinki,kin san komai ba sai na tsaya gaya maki ba duk da kasancewar ki *HAKAZAUGA (BAIWA)* a gidan nan kuma ban san kowa naki ba, yarda dake da nayi da kuma tarbiyyarki zan baki amanar yaron nan karki maido shi masarautar nan har zai ya zama mutun ya mallaki hankalinshi kema ban ce ki sake dawowa Masarautar nan har sai ranar da *RANA DUBU* zata cika,ranar da gaskiya zata zama gaskiya ki gaya mashi baya da ƙurar da ya bari ki gaya mashi ƙalubalen da zai turƙara watan watarana."

Kuka sosai FATIMA ta fashe da shi tana zubewa ƙasa tana cewa.."Tuba nike yake uwargiyata tabbas wannan al'amari da ruɗu yake da kuma ɗaurewar kai,tabbas *KAZAUWAFA(YARIMA)* abun tausayi ne ace ranar da kazo duniya ko nonon mahaifiyarta baka tsotsa da kyau  ba a raba ka da ita,nayi maki alkwarin riƙe amanar da kika bani sai na saka maki hallaci da hallaci yake FAUZAJ(GIMBIYA)"..Haɗewa sukayi waje ɗaya suna kuka, cikin kukan FAUZAJ RAHMA take cewa.."Maza tashi ki tafi kafin su dawo nasan komai suke yanzun sun kusa isowa wajen nan jikina ya bani maza tashi ki tafi Allah ya tsareku da tsarewarshi." Rufe bakin FAUZAJ RAHMA keda wuya aka fara kwankwaso kofa, zabura FATIMA tayi tana yin hanyar baya da yake ba inda bata sani ba a cikin Masarautar Mali dan shekararta 20 tana aiki a cikin Masarautar a ƙarƙashin FAUZAJ RAHMA,tana shan wata kwana suna shigowa cikin ɗakin.

★★

Da gudu ta shigo cikin gida sai haki take ta boye bayan UMMATI tana boye fuskarta sai sauke numfashi take da sauri da saur,i ajiye tsintsiyar hannunta UMMATI tayi tana maido da yarinyar gabanta tana cewa."Wa kuma kika takulo mana faɗa yau *AMATULLAH*.?" Turo baki gaba wanda aka kira da Ammatullah tayi sai kuma ta faɗa cikin ɗakin tana banka kofar ta rufe sai kuma ta ruga cikin bedroom tana boyewa bayan mirror sai haki take tana cinno baki ita ɗaya a ɗaki...Da Sallama suka shigo cikin gida riƙe da hannun wani yaro yana kuka ga jini duk ya wanke mashi fuska,ansa sallamarsu Ummati tayi tana salati tana cewa."Inalillahi wa'innalaihirajiun ni UMMATI yau naga abun da ya isheni bai ishi Allah ba, daman tsiyar da yarinyar nan ta kulla kenan,shiyasa ta shigo gidan nan a bujajen kamar wanda tayi gudun ceton rai.?" Cikin ɓacin rai yarinyar da ta kawo yaron take cewa.."gaskiya UMMATI idan har bakuyi ma AMATULLAH faɗa ba a cikin unguwar nan to kuyi kuka da kanku dan duk abin da ya faru da ita itace ta jama kanta ba wani ba, dan haka tun wuri kuyi ma yarinyar nan faɗa ya yaro yana cikin wasan shi daga yar'gardama ta shiga tsakaninsu sai ta fasa mashi kai ai ba dadi."Ita UMMATI tun da Afra ta fara maganar take kallonta tana mamakin yanda yarinyar take ƙoƙarin zaginta akan ƙaninta..Amman ai ba laifin ta bane daman ance ɗan kuka shike ja ma uwarshi jefa, kuma tasan halin AMATULLAH ba jin magana take ba da ace tana jin magana da ko kofar gida aka ce ta fita ba zata fita ba, furzar da numfashi tayi tana cewa."Dan Allah Afra kuyi hakuri tabbas ba'a kyauta maku ba kuma daga yau hakan ba zata sake faruwa ba in shaa Allah." Murguɗa baki AFRA tayi tana cewa"Sau kuna cewa hakan ba zata sake faruwa ba idan har Yarinyar can ta bugu yaran mutane?nidai gaskiya wannan ƙaran ba hakuri zanyi ba sai dai ansan yanda za'ayi dan ko sisi nan bani da ita, kuma Mama bata nan balle har ta bada kudin da za'a kai shi chemist ayi mashi wani abu kuma dai kinga yanda jininshi ke zuba karda ya ƙara case ya koma babba." Cewar Afra sai wani harare harare take tana juya ido kirirs take jira ta fara aunama Ummati zagi dan a wuya take..ita dai Ummati bata da ko sisi dan tun da ta tashi yau bata yi ido hutu da kudi ba ko Naira biyar bata maganinta balle kuma tasan a ƙarance ta ba Afra Naira 500 da zasuje chemist din Iliya ayi mashi dressing din wajen.Girgiza kai Ummati tayi tana sauke ajiyar zuciya a jere dan rasa abu da zata ce ma Afra tayi ta rasa ta ina zata fara da wannan masifar, ita dai har ta fara gajiya da halin AMATULLAH bata san ya zatayi ma yarinyar ba,yarinyar ce ba mai hanata sai Yayanta shine idan har ya ajiye ƙara yace karda ta ƙeta rashi ba zata ƙeta rashi ba har sai idan yace ta wuce kuwa kuma baya nan yana makaranta da yake scholarship ya samu yana cairo yana karatun psychology,tun da ya ƙetare ya bar ƙasar ya tafi cairo AMATULLAH bata sake jin maganar kowa ba suma kan su hakuri suke da ita.

Kamo hannun yaron tayi tana cewa.."shikenan Afra gashi Malam baya nan yana gona bai kai da dawowa ba,bari na wanko mashi fuskar a sama wajen gishiri a samu jinin ya tsaya, kafin Malan ya dawo sai ya bada kudin da zaku je chemist din ni nan wallahi Afra ban maganin ko tasi ai da tuni na bada dan ayi mashi dressing din wajen kiyi hakuri." Ita dai Afra bata ce komai sai ɗaga kai take tana hurawa,tafiya da yaron Ummati tayi ta wanke mashi kan cikin ikon Allah jinin ya daina zuba dan gishirin ta sama wajen ta dawo dashi tana shiga wani ɗaki ta ɗako tabarma ta baja masu tana cewa.."Ga waje ki zauna Afra tsayuwar ba dadi karda ƙafafunki suyi sanyi kuma..nan da dan anjima Malan zai shigo sai a kai shi chemist din a bashi magani." Hararar gefen ido Afra tayi mata tana magana ƙasa ƙasa tana cewa.."ai ko kwana zai yi ba inda zani ina nan zai dawo ya taddani, dan wallahi bata rotsa banza ba sai kudinku sunyi kuka,wata ila idan kun ga ana maku haka kunyi mata faɗa ta daina duk iskancin da take a unguwar nan tun da kudinku sun fara kuka dan ba wani kudi ne da ku ba balle." Girgiza kai kawai Ummati tayi tana cewa.."Allah ya ƙara baki hakuri Afra ai laifi akayi maki komai zakiyi ita ta janyo mamu Allah ya shirya mana dai." Ƙara kwabe baki kawai Afra tayi tana mai dauke kan ta ta maida gefe ,itama Ummati ida haɗa gawayin tayi ta ɗaura tukunya dan yi masu abincin dare,Amman ita kaɗai tasan irin bugun da zatayi ma Amatullah a yau dan ta gaji da rigimar da take janyo mata ina dalili shekara 10 ace har yanzu bata bar wasan banza da wofi ba a unguwa, aikuwa anyi na karshe indai ita ce ta haife ta.

★★

*MASARAUTA 🥀*

Masarautar Mali babbar masarautace a nahiyar Afirka tana ɗaya daga  cikin manyan Masarautar da ke faɗa a ji a faɗin Afrika,a cikin babban birnin Mali take.. Masarautar cike take da mutane iri-iri da tungu da kuma makirci iri iri,a masarautar ba'a dauki Bawa a bakin komai ba, sannan kuma ba'a dauki rai a bakin komai ba a ƙarnin(Zamani/period) ZAUFAJ LAMIDO NA II,a kasar Mali suna kiran Sarki da suna *ZAUFAJ* Sarauniya kuma ana kiranta *FAUZAJ* sannan ana kiran Yarima da suna *KAZAUWAFA*...ZAUFAJ LAMIDO NA II yana da mata Ukku da FAUZAJ BILKISU itace ta farko sai FAUZAJ SALAMATU itace ta biyu sai Amaryarsu FAUZAJ HAJARA itace ta ukku kuma daga ita bai sake aure ba... FAUZAJ BILKISU ɗiyar Wazirin Baban ZAUFAJ LAMIDO ne mai suna MUSA,kuma itace matar ZAUFAJ LAMIDO ta farko auren haɗi ne dan iyayensu suka haɗa ba tare da sun tambayi ra'ayin yaran nasu ba..duk da ita FAUZAJ BILKISU daman ta daɗe tana fama da son ZAUFAJ LAMIDO bata da yanda zatayi ne sai kwatsam taji an saka ranar bakinsu ba ƙaramar murna tayi ba...aurenta da ZAUFAJ LAMIDO da shekara ukku ya auro FAUZAJ SALAMATU yar Sarki Maina karamin hauka ne kawai FAUZAJ BILKISU batayi ba,dan a tunaninta auren soyayya ne akayi tsakanin ZAUFAJ da SALAMATU sai da Babanta yayi mata jan ido sannan ta dawo hankalinta ta natsu dan tasan a lokacin da angano rashin amincewarta akan auren to sai ya sake ta take,dan ƙa'idar masarautar kenan idan har za'ayi maka kishiya ka nuna kishinka a fili to sai a sake ki kuma aure ayi shi babu fashi...Tun da aka fara shirin bikin FAUZAJ SALAMATU da ZAUFAJ LAMIDO, FAUZAJ BILKISU bata sake zama ba ita da iyayenta dan a ganinsu anyi saurin ayi mata abokiyar zama da wuri duk da daman can ansa za'ayi mata kishiya amman ita ZAUFAJ yayi sauri cewa zai ƙara aure duba da duk duka duka yaushe akayi auren ai ko barinta ta haihu ai yayi sannan ya fara tarkatar auren..kuma ita haɗa su akayi saɓanin FAUZAJ SALAMATU da auren soyayya ce zasuyi...Sai suka bazama bin malamai da bokaye da matsafa akan kishiyar tata ko da ta shigo to a hanata daukar ciki har sai ta BILKISU ɗauka sannan dan ba wanda ya cancanci ya haifa ma ZAUFAJ LAMIDO magaji da ya wuce ita tun da ita ya fara sani a matsayin ƴa mace kuma ita ya dace ta haifa mashi *KAZAUWAFA*

Da wannan tunani suka cigaba da neman asirai iri iri sai dai tunaninsu ba gaskiya ya gaya masu ba,yanda aka yaɗata da ZAUFAJ LAMIDO haka itama FAUZAJ SALAMATU aka haɗa asili shi ZAUFAJ LAMIDO ko ganin FAUZAJ SALAMATU bai taɓa yi ba mahaifiyarshi FAUZAJ FA'IZA itace tayi hadin auren nasu...Kamar yanda su FAUZAJ BILKISU suke nema haka suma su FAUZAJ SALAMATU sun tashi tsaye dan sun ga yana da mata kuma auren soyayya sukayi ba zata shigo gidan  haka kawai ba tare da wani shiri ba,yaƙi sauraronta bayan kaunar da take mashi..bayan auren FAUZAJ SALAMATU aka fara buga kishi tsakaninta da FAUZAJ BILKISU kishi suke ba na wasa ba dan inuwa ɗaya basu zama ko wace tana nuna ta isa ita ce gwana tauraruwa a wajen mijinta...Duk wanann artaba da ake a tsakanin FAUZAJ SALAMATU da FAUZAJ BILKISU dukansu ba wanda ta taɓa koda ɓatan wata,kuma tsaye suke wajen ganin sun haihu kuma ko wace fatan ta ta haifo KAZAUWAFA..a inda suke zargin da sa hannun ɗaya a wajen rashin haihuwar dan duk halinsu ɗaya wajen bin bokaye...ana cikin wanann yanayin babu zato babu tsammani akaji ZAUFAJ LAMIDO zai ƙara aure zai auri wata yar cikin gari ba yar kowa bace a kasar Mali duk da gidansu suna da rufin asiri amman idan ana lissafa masu kudin ƙasa ba za'a sanya babanta ba,ba ƙaramin rigici akayi ba da tashin hankali a cikin Masarautar tun daga kan iyaye da kuma matanshi dan a lokacin take dokar hana rigima idan ZAUFAJ zai yi aure sukayi..Amman duk wannan rigimar da ake da tashin hankali ba abin da ZAUFAJ LAMIDO yace akan lamarin auren dan kuwa shi dai yasan ya samu zaɓin ran shi kuma yana sonta da kaunarta kuma shi bai ga aibun Hajara ba da zasu tada hankalinsu, suna yan maganganu sai kace wanda ya aikata zunubi,da yaka ido bai yi masu sai ya maganta akan lamarin wajen ZAUFAJ NURANDEEN wato mahaifinshi ya nuna mashi ya dace ayi maganar auren nan tun da yarinya tace tana son shi kuma yayi masu biyaiya akan zaɓinsu suma a duba mashi ba.

Ba dan ZAUFAJ NURANDEEN yaso ba yasa aka fara nema mashi auren duba da shine ya fara ƙafa tarihi auro masu bare ba jinin sarauta ba,amman tun da yace yana so ba yanda akayi da shi sai dai ido, haka dai akayi auren ba mai so sai shi wanda ya jajubo auren..tun da aka kawo FAUZAJ HAJARA ta kauda idonta akan duk wani cikin kashi da cin mutunci da ake mata a masarautar...dan kuwa kishiyoyinta haɗe mata kai sukayi suka dunkulle waje ɗaya suna ɗana mata tungu iri iri sai dai tayi kuka ta ba kanta hakuri, dan bata taɓa gaya ma wani wahalar da take sha a cikin Masarautar tun daga wajen surukanta da kuma kishiyoyinta ba inda take jin dadi sai a wajen mijinta da yake nuna mata so da kauna kamar zai maidata a ciki haka yake ji dan so...Daman shi ZAUFAJ NURANDEEN ba ruwan shi ba ta su yake ba ga kuma jikin tsufa koƙari yake yaga yayi murabus ya ɗaura ZAUFAJ LAMIDO a saman kujerar mulki ya cigaba daga inda ya tsaya dan yana bukatar hutu iya hutu...Ranar da aka naɗa ZAUFAJ LAMIDO bisa karagar mulki a ranar FAUZAJ HAJARA ta haifo santaleliyar ƴarta a inda haihuwar ta ruɗar da mutane da yawa a cikin Masarautar dan ba wanda ya taɓa sanin tana da ciki sai dai akaji haihuwar ta.

A daren su FAUZAJ BILKISU da FAUZAJ SALAMATU suka ba zama wajen bokayensu dan jin ba'asi ya akayi sukayi masu haka?bayan ko wace bokonta ya gaya mata ita ce zata fara haihuwa ta kuma haifo KAZAUWAFA, amman yarinya daga zuwanta har ta haihu kuma basu gaya masu da cikin ba...suma bokayen lamarin ya basu mamaki dan a iya saninsu FAUZAJ HAJARA bata da ciki dan bokon FAUZAJ SALAMATU gaya mata yayi mata wani babban asiri wanda ma ko kusantarta mijinta bai taɓa iya yi ba balle har ta haihu,haihuwa kuma mamakin da sukayi kenan sai aka sake wani aikin, haka dai suka gama surkullensu akan tayi ta farko gami da ta karshe daga wannan ba zata sake haihuwa ba sai dai taga wasu sunayi ba dai ita ba...haihuwar da FAUZAJ HAJARA tayi ta samu uwar mijinta wato FAUZAJ FA'IZA ta fara yi mata magana dan tsawon shekara guda da yin aurenta da ZAUFAJ LAMIDO mahaifiyarshi bata taɓa yi mata magana ba,duk da kullum sai taje har gida ta gaida ta banda aikata mata da abinci da take duk juma'a amman bata taɓa yi mata magana ba..randa FAUZAJ FA'IZA ta fara yi ma FAUZAJ HAJARA magana sai da ta zubba hawaye dan abun yazo mata a bazata, dan har ta fidda rai da zata yi mata magana ma a duniya.

Tun da ta haifi yarinyarta FA'IZA wato DARMAMA FA'IZA dan a kasar Mali gimbiya yar Sarki da DARMAMA ake kiranta,ita dai FAUZAJ HAJARA bata damu da duk irin bakin kishin da kishiyoyinta suke a kanta,bai damaita ba duk da tana sane da duk wani motsinsu duba da idan har zakayi rayuwa a gidan sarauta sai ka samu amintaitu cikin bayin gidanka..to tana nan ake gaya mata duk wani motsi na kishiyoyinta sai dai ita tasan ta kama Allah dan dashi ta dogara tasan ba wanda ya isa yayi mata abun da Allah ba bai mata ba daga ita har ƴarta..dan kuwa DARMAMA HAJARA tsaye take tsayin daka  wajen yin addu'a da neman tsari a wajen Allah,shiyasa komai suke ita dariya suke bata da kuma tausayi dan su din ababen tausayi ne dan duk wanda ya manta da Allah Allah ne ya dauki shirka ya manta da mutuwa tabbas dole ya zama abun tausayi...Haka aka cigaba da buga kishi a masarautar Mali ta kone bangare ko wace tsaye take tsayin daka wajen ganin ta zama tauraruwa wajen mijinta..ga kuma su FAUZAJ BILKISU suna ta koƙarin ganin bayan FAUZAJ HAJARA ta ko ina sai dai komai suke suna yin shi a banza har da wofi ma dan DARMAMA FA'IZA tana da shekara ukku da haihuwa FAUZAJ HAJARA ta ƙara haihuwar ɗa na miji..a wannan ƙaran sai da FAUZAJ BILKISU ta yanke jiki ta fadi sai da tayi sati a asibitin masarautar,duk da tana kwance amman amintaitunta basu zauna ba tsaye suke wajen bin bokaye da matsafa wajen ganin sun ga bayan abun da FAUZAJ HAJARA ta haifa dan har da jirirai sai da aka yanka wajen ganin an kashe abun da aka haifa,amman yaro sai lafiya yake sunan da aka raɗa ma yaron shine NURANDEEN.

Bayan haihuwar KAZAUWAFA NURANDEEN da shekara biyu FAUZAJ SALAMATU ta haifo yan biyu maza suka ci suna KAZAUWAFA ALIYU sai kuma KAZAUWAFA ABDULLAHI duk da taji dadin haihuwar tata amman ba haka taso ba,amman ta kudurtama kanta sai tayi yanda zatayi taga ta kashe KAZAUWAFA NURANDEEN  domin cikar burinta na ganin KAZAUWAFA ALIYU ya zama ZAUFAJ a ƙasar Mali...Ita kuma FAUZAJ BILKISU har yanzun shuru haihuwa babu magani dai tayi har yanzun shuru kake ji..ba wajen bakoyen da bata je ba har yanzun dai babu magana ga kuma hankali da ta maida wajen ganin taga bayan KAZAUWAFA ALIYU da KAZAUWAFA NURANDEEN da kuma KAZAUWAFA ABDULLAHI dan har yanzun tana kan baƙarta ba wanda ta isa ta haifi ZAUFAJ idan ba ita ba,yanda ta zama matar FAUZAJ ta farko dole ita zata haifi ZAUFAJ kuwa ko ana ha maza ha mata ta ko wace hanya sai ta bi dan ganin itace zata haifi ZAUFAJ ba zata zauna ta zuba ido ba tana kallo yara da suka zo daga baya su haihu ita bata haihu ba dan haka ta shirya haihuwa ta ko wace shiga, kuma kashe yaran zatayi ita ce ke da masarautar Mali lokaci kawai take jira...

*Jama'a ana wata ga wata fah🤔 yanzun zamu fara shirin tafiyar dan ko tafiyar ba'a fara ba kuwa dan labarin RANA DUBU labarine mai cike da sarƙaƙiya da sururkule iri iri ga dai FAUZAJ SALAMATU da FAUZAJ BILKISU nan ko wace fatan ta taga bayan KAZAUWAFA NURANDEEN Ita kuwa  FAUZAJ BILKISU duka take koƙarin ganin ta kashe shin FAUZAJ BILKISU tana haihuwa?kuma tana kashe yaran da take ikirarin cewa zata kashe? Wannan Ansar sai kun biyoni cikin wannan labarin zakuji ya wanann cakwakiyar zata kaya🫣😂*

_It's 300 via 077512438 Jamila Abubakar Bello access Bank 08160508316 for evidence_

*Akwai Data available masoya akwai ko wane network kuma cikin rahusa 300 1GB ko wane network*

*Zaki biya kudin data idan kina bukata ta wannan account din 8160508316 Jamila Bello Abubakar Opay bank,08160508316 for call or whatsapp*

Share domin Allah✓

Continue Reading

You'll Also Like

312K 9.4K 78
(Fixed/Fan-TL) Top idol group Stardust, whose members disappear like dust. The group that used to have seven members ends with four members... "Is...
154K 6.5K 40
Amaira Romano , the princess of ITALY. A cute little inoccent girl who can make anyone heart flutter at her cuteness. Everything was going smoothly...
513K 36.2K 45
ပဲပြုတ်သည်ငပြူးနဲ့ ဆိုက်ကားဆရာငလူးတို့ရဲ့ story လေးတစ်ပုဒ်
546K 19.8K 166
The young lady from the Xue family was talented and beautiful, and married the dream husband at the age of 16. They had a loving and harmonious relat...