KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TAS...

By missxoxo00

1.5K 73 3

KOWANNE DAN ADAM DA IRIN TASA KADDARAR💯IDAN KA YI HAKURI SAI KA CIMMA NASARA A GABA🤞...One really need not... More

free book🤸
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11

12

146 6 0
By missxoxo00

_KADDARA!!!💔_*
     _KOWA DA IRIN TASA_
              👭👩‍❤️‍👨💍


©️®️ _NANA HAFSATU_
          _(MSS XOXO)_

    _SHAFI NA SHA BIYU_
     _(KARSHE/FINALE)_

_Arewabooks:mssxoxo_
_Wattpad:missxoxo00_

_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

___________

*WASHE-GARI*

      Bayan Marwaa tayi sallar asubahi gari ya fara haske. Ta bi lafiyar gado ta sake nannadewa bacci mai nauyi ya dauke ta..

Sai da ta dau lokaci sosai tana ramuwar baccin da batayi a baya ba saboda hayaniyar unguwar su ma kadai ya tasheta a baya... Nan kuwa shiru kake ji sai karar kanaru da hazbiya.

Da addua ta tashi tana mai yin miqa hadi da tayar da hannuwan ta sama.. Ta rufe bakin ta da hannun ta saboda hammar data taho maata.

Ta saka hannuwanta tana shafa lallausan zanin gadon da aka shimfide shi akan katuwar katitar 8by6..

Ta runtse idanu tana tuno yar katitar su dake gidah a baya... Ta tuno su lokacin da suna cin danwake itada Safaa a wata shekara a sallar bara. Suna cewa idan suka girma sukai kudi zasu sayawa ummy gidah katoto ko'ina zasu zuba mata gadaje da katifu luntsuma luntsuma da talabijin da firji da sauran kayan da suke gani a gidajen yan gayu...

Wasu zafafan siraren hawaye suka shigaa ziraro mata... Ta sanya hannun ta tana goge su. Cikin dakushasshiyar murya mai dauke da damuwa tace,

"Allah ya jikan ki da rahama Safaa... Nayi kewar ki sosai wallahi. Allahu ya gafarta Miki ya raya Safaa Amin. Allah kuma ya bamu ikon kula da ita Amin"

Mikewa tayi ta nufi kofar da ta gani take kuma tabbatar da bandaki ne. Da addua dauke a bakin ta ta shigaa..

Sabon brush ta gani da toothpaste ta matsa ta wanke bakin ta. Ta tara ruwa tayo wanka. Bayan ta futo ta tsane jikin ta ta shafa mai da deodarant a hammata. Ta shafa turaruka ta zura kayan ta. Riga ce doguwa ta lace kalar royal blue. Batayi kwalliya ba tadai shafa man baki na lipgloss data gani an jera akan dressing mirror.

Ta na zaune akan kujerar gaban mudubi.... Cikin ta sai qugin yunwa yake. Ta wawwaiga cikin dakin babu alamar akwai abun da Zata saka acikin ta. Don haka ta mike da sauri ta bude kofar ta fita..

A gyare ko'ina yake. Tsaf tsaf da alama an sake gyara wajen ne..  Domin har kamshin tiraren wuta ne ke tashi a parllorn na khajinguru din kamfanin tiraren yerwa incense and more.,

Wajen dinning ta nufa, Food flasks din abinci ne a jere akan dinning table din.. Gefe daya da kayan tea da kofuna da plates, komai dai a killace an ajiye dukkanin abunda zaa bukata.

Kujera taja ta zauna. Ta dau plate ta zuba komai dai dai cikin ta. Ta hada tea mai kauri tana ci tana korawa da shayin.

Ahsan ya fito daga cikin dakin sa shima sanye cikin wani yadi kalar zaiba.. Bai sa hula ba. Kanannadadden gashin sa na fulanin usuli ya kwanta luf.

Tana daga zaune akan dinning ta jiyo kamshin tiraren daya sata saurin waigawa suka hada idanu tayi azamar janye idanun ta da sauri..

Ahsan ya tabe baki ya nufi wajen fridge ya bude... Shi kansa bai masan me yake nema ba. Amman tabbas zuwan nasa wurin firjin na da nasaba da kyawun da Marwaa tayi masa.

"Barka da safiya...." Ta fada kasan makoshi. Tunowa da hudubar da su anty kulu suka mata.

Ahsan yayi murmushi a sunkuyen dama yake.daya daga Kuma ya hade rai Yana sake tamke fuska.

"Lafiya" ya amsa a hasale..

Itama tabe bakin tayi ta mike tashige cikin daki. Tana barin wajen, Ahsan ya nufi dinning din. ya samu kansa da zama akan kujerar data tashi. Ni'imantaccen kamshin tiraren khumran dufra na kamfanin tiraren wutan yerwa incense and more ya gauraue ilahirin wajen da gewaye

Ahsan ya sake baje kofifin hancin sa yana shakar kamshin. Ya janyo plates ya debi komi . Kasa cin komai yayi. Kujerar dake duban tasa ce ke masa gizon Safaa.

Allah sarki da tana raye yanzun da ta kujerar ta matsar da ita daf da tasa. Zata zuba komai a plate ta dinga bashi har ya koshi tana wani ririta shi tamkar dan karamin yaro..

Hawayen da yake ta matsesu ne Suka bijere Masa suka zubo... Yayi saurin saka hannun sa ya gogesu,

"Allah ya Miki rahama Safaa. Allah yasa aljanna ce makoma agare ki... Ina kewar ki sosai." Ya shigaa fada cikin rauni.

Dakyar ya caccakuni abincin ya mike ya hada kayan daya bata ya Kai kitchen..

Har yayi hanyar fita sai Kuma ya koma ya kwankwasa dakin da Marwaa take .

Alokacin Kuma tana zaune akan gado. ta mikeda sauri dankwalin Taya zume ya Fadi batama lura ba tayi hanyar kofar ta bude.

Tsayawa yayi Yana duban ta. Musamman gashin kanta daya Sha Kananun kitso sai kyallin Mai yake. Ga jelar gashin hargadon baya.

Binta yay da kallo tundaga sama har kasa. Tayi Masa kyau ba kadan ba.

"Ina sauraron ka..." Ta fada tana juyar dakai. Anan ta hango dankwalin ta a gaban gado. Da sauri tadakko ta daura. Tazabga Masa harara kuma kamar shi ya cire mata dan kwalin

Tsiwar ta dariya take bashi ma. Dik da ya lura Kamar tayi laushi bayan rasuwar Safaa. Sanda take kawo baby Safaa wajen hajian su da idan suma sunje gidan su...

Da sauri ya kauda kansa.. hannun sa na shafo keyar sa yace,

"Akwai abunda kike bukata? Zan fita"

"Babu komai"

"Alright then" Ya fada Yana daga kafadar sa.

Ficewa yayi daga cikin gidan. Ta sauke ajiyar zuciya tana gyara zaman dankwakin ta. Ya kalle mata gashi. Sam bataji Dadi ba.

Da Rana ma haka aka shako food flask dauke da abinci. Marwaa ta zuba taci. Ta mike ta sake kakkauda abubuwa ta koma tazauna tayi jingum...

Yar wayarta ta zaro ta danno lambar ummy. Bugu biyu ummyn ta dauka Sika gaysa,

"Ya baby Safaa?"

"Tana Nan kalau gata tanata bacci"..

"Yauwa alhamdulillah"

"Ya kowa da komai?"

"Alhamdulillah ummy"

"Mashaa Allahu to Allah ya baku zaman lafiya kinji? Allah ya kade fitnah"

"Aamin ummy"

Sukayi sallama ta ajiye wayar a gefen ta. Idanunta sai zafi suke. Bacci take ji sosai. Don haka tana yin sallar laasar ta kishingida akan doguwar kujera Nan bacci ya dauke ta...

Ahsan Yana dawowa ya saka key ya bude ya shigaa.. kwance ya sameta akan kujera 3 sitter ta takwaiwaye kanta.

Ya samu kansa da tsugunnawa Yana duba fuskar ta sosai. Numfashin ta Mai dumi na sauka ahankali...

Kanar su daya da Safaa.. banbacin kadanne kawai. Ya sake rankwafawa. Idanunsa suka sauka akan labbanta dake shekin lipgloss.

Ya mikar da hannun sa zai taba labban nata. Shi kansa bai san dalilin dayasa ya samu kansa da son taba lips nata ba.

Marwaa ta bude idanu da sauri... Zumbur ya mike Yana shafa keyar sa. Itama mikewar tayi tana Masa kallon hadarin kaji.

"Meye hakan?"

"Aina?"

"Bangane ba... Gaka Nan azaune ka zubamin idanu. Da ka Miko hannun naka me kake shirin yi eh?"

"Na miko hannu a Ina? Malama Ni zobena nake nema agefen ki"

Murmushi tayi irin na renin hankalin naka yayi yawa ma. Ta grigiza masa kai kawai ta shige daki..

Ahsan kunya duk ta dabaibaye shi. Haka ya zuba abinci yaci ya sake futa zuwa masallacin dake cikin gidan su...

  Toh hakaa rayuwar tayi ta garawa... Kowanne bangare ana samun ups and downs Alhamdulillah .Zulfa'u an dauramata aure itada abbas. Sannan anyi auren Aisha da Faysal..  Ba taron biki akayi ba.. bayan daurin aure dai acikin gidah an zazzauna anyi karamin yini anci Kuma an Sha.. Ahsan ne yakai Marwaa gidah ranar da ake bikin. Tace zata kwana ya ce bai amince ba. Gashi dai wata mu'amala ta auratayya Bata taba shiga tsakanin su ba. Amman haka yake lailaya mata dokoki idan Yan rashin m dinsa Sika tashi...

A Kuma watanne aka kawo mata baby Safaa tadawo hannun su gaba daya. Tsabar farin ciki Marwaa har kuka tayi. Tayi sujjada tana mai godewa Allah abisa ni'iimar da yayi musu..

Marwaa ta dauka anan gidan su Ahsan din zasu zauna dindin din. Ashe komawa zasuyi can asalin gidan Ahsan dake wata area ta daban.. Sam bataso ba. Tafi kaunar ta zauna anan wurin su hajiya Laila. Uwa uba can din zai dinga tuno mata da Safaa..

Suka je sashen mahaifan Ahsan donyi musu sallama. Bayan sun gaysa anata zaune Ahsan yace zasu tafi. Alhaji Jamil Gwanzamu mahaifin sa yace su dakata.. ya shiga yi musu nasiha Mai ratsa jiki ya karkare da,

" Dukkanin wani ibtilain rayuwar da Zata ko ta afku a kanka, ko wata mummunar KADDARA ko jarabawar rayuwar da zasu faru da kai a rayuwa, to hakika masu sauki ne idan ka auna da na lahira. Saboda haka, kuyi hakuri ku jure kubi Allah da biyayya cikin duk abinda ya KADDARA shi a kanku., Babu wanda Allah yayi shawara dashi cewa zai zama wani abu a rayuwa. Kawai hukuncin Allah ne ke KADDARA hakan.Yaa Allah ka KADDARA mana da kyau..."

Suka hada baki wajen amsa shi da'

"Aaameen"

Ya cigaba da cewa,

"Ku bar yin damuwa, lallai babu wanda ya isa ya kange ka daga abinda Allah ya baka, sannan kuma babu wanda ya isa ya baka abinda Allah ya kange ka daga gareshi, wallahi mutane wasu da wani iko ko karfin cutar dakai ko amfanar dakai face sai abinda Allah ya rubuta maka, ko su kashe ka ko kuma su baka rayuwa face duk saidai abinda Allah  buwayi ya KADDARA maka... Kuna jina ko?"

"Muna ji..." Marwaa ta fada kanta a kasa..

Ahsan ma ya amsa da suna saurara, Alhaji Jamil Gwanzamu ya dubi hajiya Laila matar sa yace,

"Ko Zaki Kara musu da wani abun?"

"Ai abban su ka gama fadar duk abubuwan da ke zuciyata. Ina musu fatan alkhairi Kuma Allah ya basu zaman lafiya ya Raya baby Safaa.... Sai dan tsokaci Nima Akan KADDARA Domin KOWA DA IRIN TAASA..Wallahi duk wani kunci da damuwa da kuma rashin walwalar da kake ciki, idan ka tuna cewa kai musulmi ne, kuma mai yin imani da KADDARA  mai kyau ko mara kyau, sai kaji abin yazo maka da sauki acikin rayuwarka, Ya Allah ka kara sanyaya zukatan mu da ni'imar imanin mu dakai...Kaddara (na akasin Alkhairi) abu ne mai wuyar jurewa, amma idan kayi hakuri don ALLAH zai zo ya wuce tamkar dai yar marigayiya Safaa.. Da mukayi hakuri muna addua ga sakamakon daya bamu nan.... kuma ka samu sakamako na lada mai yawa da kuma ruwan alkhairai daga UBANGIJIN ka, sa annan kuma kaje lahira kana mai cikakken imani domin na daga cikar imani, yadda da KADDARA !! Wata tata KADDARar kenan tazo duniya tayi sure ta haihu sai ta rasu sai wani ko wata daban yaci moriyar Dan data Bari. Wata tayi aure da wuri kuma bata haihu ba. Wata Kuma zata Kai shekaru ta tsufa ba aure Amman da tayi Kuma sai ta haihu. Wani zai gama karatu da shekaru bai samu aiki ba. Wani Kuma zai yi karatu a kure  Kuma ya samu aiki da sauri..Kanwa ta auri mijin yaya da sauran su dai gashi nan.. KADDARA ce KOWA DA IRIN TAASA.. Allah yasa ku koma a sa'a. Allah ya baku zaman lafiya da zuriah me albarka.Allah Kuma yaraya baby Safaa yasa mahaddaciyar alqur'ani ce Kuma mai amfani da shi. "

"Aamin Aaameen..."

Sukayi musu sallama. Ahsan ya karbi baby safaaa hannun hajia Laila mahaifiyar sa. Suka nufi mota suka shiga Ahsan ya tasheta suka tafi..

Lokaci zuwa lokaci yakan juya ya kallo marwaa da baby Safaa. Sai Wasa take mata tana magana kaman tanayi da babban mace. Gwanin ban sha'awa yanata murmushi. Ba karamin burgeshi sukayi ba..

Suna karasawa gidan Mai gadi ya bude suka shigaa. Gaban Marwaa ya yanke ya fadi ji take tamkar zata ga Safaa .. Ta runtse idanu kawai tana istigfhari. A haka tabi bayan Ahsan suka shig ciki..

Tasha mamaki ganin an canza furnitures din gidan baki daya tamkar ba shi ba idan aka shiga cikuy. Komai a tsare. Kallo daya zakai wa gidan kasan na masu hali ne...

Ta haye sama kanta tsaye. Tana tafe da baby safaaa a kafadarta. Ahsan ya dube su Yana murmushi. Ya giriza kai ya shiga dakin kasa don yin wanka a gajiye yake tikis..

  
       °°°°°°

Haka zaman nasu ya kasance... Alhamdulillah su kan zauna atare a parlor shima darajar Safaa yaci Marwaa ke fitowa su zauna. Yana mata Wasa idan suka gama ta dauketa su koma daki ta datse da mukulli sai Kuma washegari. Dake sanyi ake ma a garin nan da nan suke bacci da wuri.

Ranar wata laraba bayan marwaa ta dawo daga makaranta. Gidan su Ahsan ta biya taci abinci. Hajia Laila tace  tabar mata Safaa ta kwana biyu hakan kuwa akayi ana laasar Marwaa ta koma gidah cike da kadaicin baby Safaa.

Ko data koma Ahsan ya dawo daga aiki yake tambayar Safaa tace tana wajen hajian su tache dan Allah zata mata kwana biyu,

"baki bigo kin gayamun ba nazo na duake ki daga can?"

"Ai ban wani dade ba"

"To meyasa baki Kira waya ba?."

"Banda number ka."

"Ina wayar ki?"

'ga ta"

Ya karbi wayar me Torchlight Yana dubata duk numbers dinma sun koke ya gita daga gidan itadai tana ta kallon ikon Allah. Ya dan jima ya dawo da sabuwar waya gadagau ya Mika mataa. Ta karba tana duddubata. Yace siya mata yayi

Taji Dadi Sosai tayi Masa gofia. Abunma ya bawa Ahsan dariya daman Marwaa na faraa da sakin baki haka cike da girmamawa?

Ya nufi dakinsa farin ciki ya mamayeshi ya rasa meyasa. Zuciyar sa sai wani bugu takeyi. Ya daga hannu ya dora a saitin zuciyar sa Yana sauraron bugun.

Da sauri ya mike ya shige bandaki bakinsa dauke da addua..

Koda dare yayi Marwaa har ta kwanta kwanciyar bacci tsoro duk yaksla mata ta tukwikwiye a gado. Ko Dan tasaba kwana da baby Safaa ne don yau ba ita take ta firgita?

Mikewa tayi tadauki pillow tinkis tinkis ta nufi daya dakin dake fuskantar nata Wanda take da tabbacin anan Ahsan yake don tanan taga yana fitowa.

Ta kwankwasa. Alokacin Kuma ya gama addu'ar bacci kenan zai kwanta. Yaji tana knocking ya kallo agogo daya saura..yamike da sauri tunanin Kila emergency ne.. Yana budewa ya ganta rungume da pillow

"Ya akai?"

Batama amsa shi ba ta raba ta gefen sa ta wuce cikin dakin. Yabi bayanta da kallo.

"Menene uhm?"

"Tsoro nake ji"Ta haye gadon tana jan bargo.

"To Ni bari na koma dakin ki"

"Aa Dan Allah ...kaji,?" Yadda tayu maganar tana turo baki gaba ba karamin kyau tayiwa Ahsan ba kaman tana shagwaba

Komawa yayi gefen ta daga can karshe ya kwanta. Tanannade ajikin bargo. Ya kashe fitilar... Sanyi duk ya takura Masa tadauke Masa bargo. Sai juyi Yake Yana rawar dari ga wani yanayi da ke dabaibaye shi.. ya samu kansa da Dan daga bargon Yana lekawa

"Marwaa"

"Na'am..."

Hannu yssa Kan hular ta zai cure tayi saurin rike hannun nasa ta zare. Idanunta suka fara kawo ruwa. Ta tuno Safaa. Gani take kaman taci amanarta ne..

"Marwa please..." Ya sake fada Yana kokarin jawo ta jikin sa

Kuka take sosai tana janye hannuwan sa daga kanta... Shima kukan ya fara muryar sa tana rawa yace,

"Marwaa ba lefi na bane ba Kuma naki bane... Haka Allah ya kadarta mana... Ba yadda zamuyi. Marwaa I want you.. Dan Allah kiyi hakuri ki ban hadin kai Dan Allah..."kuka yaci karfin sa sosai. Gashi yanata rokon ta. Saboda a yanayin da yake ciki ko ta halin karfi ne zai iya .

Don haka duk tirjewar ta haka ya kashe ta da kalamai ga kukan da Mai ratsa zuciya

"Babu wani dadi da yake dauwama a gidan duniyar nan, to kayi godiya abisa duk abinda Allah ya azurta ka dashi, Kamar haka ne babu wani tsanani da yake dauwama shima a wannan duniyar, to kayi hakuri abisa abinda Allah ya KADDARA maka na kuncin rayuwa da Zaka fuskanta ko akasin haka.,... Kinaji?"

Ya tallabeta sosai ya mannata ajikin sa.. ahankali yake balle botoran rigar baccin ta.. Yana kuma sakar mata sumba a duk rassan jikin ta. Sai daya tabbatar ya kashe mata jiki tukun sannan yayi nasarar hade bakunan su waje daya. Sunbatarta yake cikin wani salo Mai wuyar fassarawa. Duk zillon Marwaa haka ta hakura. Sassan jikin ta na marabada sabon darasin da Ahsan yake aika mata.

Ya samu kansa da karanto adduoi da dinbin fatan nasara. Ya shiga auratayya da Marwaa. Ahankali cikin kwarewa da jefa wasu zafafan darussa ga Wanda ake koyarwa..

Mamaki ya kashe marwaa a lokacin da take jin hannuwan Ahsan a duk ilahirin jikin ta. Babu inda baya tabawa. Yayinda yake sanya harshen sa Yana lasar bayan kunnenta. Kadan ya rage Bata sume ba alokacin da Ahsan ya mayar da ita cikakkiyar mace. Ta saki razanannigar Kara ta na Kiran sunayen su Safaa da Aisha ciki harda malam harisu mai itace na unguwar su.

Shi dai Ahsan Dadi ne ya gama mamaye shi. Don haka sai daya samu nutsuwa sosai. Yana hawaye tanayi. Ya burgima ya kwanta akan pillow ya jata jikinsa suka shiga baccin gaskiya. Ana kiran sallah kuma Ahsan ya mike ya tanaadi komai a bandaki ya dauki marwaa tanata ihu ya shigar da ita. Da kansa ya gasa mata jiki yasa ta shigaa bath tub me ruwan zafi. Data futo ya bata magani Tasha.

Tanata binsa da kallo tana dankaraa masa harara hadi mita kasa kasa ..  haka suka kasance cikin satin nan ana abu daya.. duk yadda Marwaa zatabi ta gujewa Ahsan ta kasa. Shi kansa mamakin kansa yake tabbas ya kamu da kaunar Marwaa da bai taba zato ba. Har kaunar ma ta wuce yadda yake tunani. A haka ya cusa mata kaunar sa itama a zuciyar ta. Tun tana ki har dai ta bada Kai. Suke gudanar da soyayya cike da tarin cigaba sosai

   ::::::::::::;;;;;;;;;;;;;;;;;;

Ta kwantar da baby Safaa kenan akan gadon ta sai ga shigowar sa ya dawo daga office..

Tana tsaye gaban madubi ya Isa wajen ya sakala hannun sa ta kugunta. Kansa akan kafadarta ya dinga rada mata da,

"zai iya kasancewa, niba ajin ki bane, ba irin namijin da kike so bane, amma inaso ki saka a zuciyar ki cewa nayi alkawarin zama irin namijin da kike mafarkin samu a rayuwar ki, nidai dama nake bukata...Marwaaa ta kinsan meyasa nake kasancewa cikin farin ciki a koda yaushe, ko wanne dare, muryar ki ke samar da natsuwa a zuciya ta kafin na kwanta bacci. Duk safiya inna tashi daga bacci, muryar ki ke samar mun da farin ciki.   Nasamu babban rabo a wannan rayuwan kinsan meyasa? Nasami mata tamkar aminiya, mai kula dani, mai sani farin ciki, tana kaudar mun da bakin ciki. Hakimar dake tare da ke yafi mun komai a wannan duniyar...The world feels like a better place with you in it. My confession is that your love has transformed my world into a beautiful and magical reality. My love for you knows no limits, and my heart belongs to you entirely. It’s time to confess that you are my forever, my always, and my one true love... Sometimes, words are not enough to convey the depth of my feelings. My love for you is beyond words, but I’ll try anyway: I love you more than life itself."

Marwaa ta juyar da Kai tana duban sa. ta danyi dage ta sakar Masa sunba akan Karan hancin sa tace,

"Masoyi na, kasan meyasa nake son ka? Soboda babu abunda kafi so a zuciyar ka face sani farin ciki. Nazamo mace mai son namiji wanda zai damu dani, ya soni kamar yadda yake son kansa, kuma na sameka. Ina son ka. Tunda nake a rayuwa ta, ban taba zaton zan shiga irin farin cikin nake ciki yanzu ba. Soboda kai, na daina shiga damuwa, na daina jin duk abunda mutane suke fada duk ta dalilin ka.miji irin ka a wannan zamanin, kudi bai iya siyar su. Duk safiya inna tashi daga bacci banji muryar ka ba. Sai naji kamar an soke ni a cikin zuciya. Shiga cikin damuwa nakeyi. Duk dare inban saurari muryar ka ba, ban iya bacci dan babu natsuwa a tare da ni ko kadan.My love for you only comes naturally without a single doubt. When I say I love you with all my heart, believe me, darling that it is just the truth. The father of my child.. I wish you can open my heart to see how special you are kept in it. I will continue to love you till the end of time, my hero i found love when I found you. The way your eyes shine when you smile, the way your hand fits perfectly in mine. You are my most precious treasure. I am irrevocably in love with you.You are the best thing that happened to me. You are not just my partner, you are a thoughtful person who enriches my life in every way. I promise to love you until my last breath, creating our own true love story..."

Ahsan ya saka hannu ya rufe bakinta. Yana Mai zagaye labbanta da yatsantsa yace,

"Ina ma a ce na kasance da ke a duk bugun numfashina, kaunarki ce take kara tasiri a ruhina, babban burina na ga bayyanar fitar murmushinki a kan wannan kyakykyawar fuskarki, ya kuma zamana ni ne sanadin hakan. Bana son Allah ya kawo lokacin da za ki fushi da ni sosai kaina ba zai dauka ba, hakika Allah ya wadata ki da abin da mata da yawa suke nema sun rasa ke kanki kin san a cikin jinsinku, mata irinku kadan ne da a ce na iya rubuta labari da a kan fuskarki zan rubuta littafi mai suna kyauta daga Allah, Babybabe Dan Allah ki so ni Mana..." Ya fada Yana sakar mataa sunba a tsakanin wuyan ta. Yana Mai shakar kamshin dake tashi daga jikin ta.

Daukar ta yayi cham yanata nishin nauyi yayi dakin sa da ita,

."baby Safaa..."

"Ba yanzu zata tashi ba so... Please please.."

Marwaa tayi murmushi.. Ya Sanya kansa akan kirjinta. Yana gogawa ahankali. Cikin wata iriyar murya tace,

"Ahsan ina son ka, me ya sanya ka ke yin kokwanto a bisa kalmar so da na furta a gare ka? Tabbas kaine mutum na farko da haduwa da shi ya kore min bakin ciki, KADDARA ta..ya wanzar da farin ciki a zuciya ta ya yalwata murmushi a saman fuska ta hakane dalilin da ya sanya na ke kiran ka da SADAUKI. Ahsan, ka yi nasara ka yi nasarar jan ra’ayin soyayya ta a kan ka kaine na mallakawa linzamin zuciyata, kaine mutum na farko da na taba furtawa kalmar SO  kuma a yanzuma zan kara mai-maitawa a gare ka ina son ka.... Kaji?"

Ahsan ya sake rarumar ta kam. Kalaman ta sun sake tsuma shi. Ya shiga nuna mata wata iriyar kauna sosai. Ranar dai kamar itace first night dinsu saboda tsananin yadda su biyun sike nunawa junan su bajin ta...

  00000000000000

  Haka Kwanakin suka yita shudewa. Kowane bangare na labarin na samun cigaba da Kuma rashe rashen rayuka..

Malam Muhammad mahaifin su Marwaa ya rasu. An raba gado.. duk da dai kadanne gadon domin gidah da suke ciki ne kawai kadararsa sai gona a kauyan su.

Mahaifin Ahsan ya baiwa malama zuwaira gidah kyauta da fari taki karbar Amman daga baya ta amince da mutanebsuka saka baki.

Tacewa abokan zamanta su koma tare. Amarya Asmau taCe a'ah tana da wajen zama. Don haksla addabiyya da yaranta da basu da inda zasu sai Suka bi malama zuwaira. Sama da kasa ne gidan don haka ta tare a sama ta bar musu kasan suci arziki..

A kuma cikin shekarar ne Marwaa ta samu ciki. Dangi saj murna ake. Ahsan ya dau son duniys ya dorawa cikin nan ya hanata aikata komai. masu aiki har hudu ya dakko don dinga taimaka mata..

Har Allah ya amince ta suaka lafiya. Ta haifi mace kanar su daya da ita da baby Safaa. Taci sunan hajiya Laila ana ce da ita Marwaa.

Hajiya Laila tace marwa  awajenta zatai goyo. Ahsan Sam bai so ba. Gashi ta hanashi kwana agidan sai nashi gidan.

Ai kuwa tana arbain da safe yaje ya dakkota itada baby Safaa da baby Marwaa. 

Marwaa ta kalle shi jikin sa sai rawa yake Yana zuge zio din rigarta tayi murmushi tace,

"Oh ni ya su na hadu da KADDARA..."

Ahsan shima yayi murmushi Yana manne jikin su yace,

"KOWA DA IRIN TAASA...kedin farar KADDARA tace...Sararin samaniya na cike da taurari, teku na cike da ruwa, doran kasa na cike da ciyayi, amma ni zuciyata cike take da soyayyarki ba ta gushewa kamar yadda taurari ba sa gushewa a sararin samaniya, ba ta kafe wa kamar yadda teku ba ta kafe wa, haka zalika ba ta bushe wa kamar yadda ciyayi ba kamar sukan bushe, soyayyarki dauwamammiya ce a farfajiyar madinan zuciyata da akwai wanda zai tsaga jikina da ya ga jininki yana gudana, a kan kaunarki na manta kaina, kikan hau ingarman doki domin ki taho mafarkina, hakika na kasance mai bayyana a mafarkinki kin kasance a fatar lebena. Duk wani taku da na yi a doran duniya sai inji takun na iso ni zuwa gare ki. So marurun zuciya ya yi min saka tun asali so ya shige zuciyata yana min illsr so Marwaa.... Ina kaunar ki sosai.. "

Ta bude baki zatayi magana yayi nasarar cafkar labbanta Yana Bata wani sako. ya yinda hannunsa ke yawo ajikin ta kuma Kan abubuwa mafi daraja dayafu so... Cikin murya kasa kasa ya shiga rada mata da,

" You are the best thing that happened to me. You are not just my partner, you are a thoughtful person who enriches my life in every way. I promise to love you Untill my last breath, creating our own true love story..... Ina kaunar ki sosai Marwaa kanwar safaa, Kuma mahaifiyar baby Safaa da baby Marwaa.. matar Ahsan. Tuni kin sace zuciya ta sai yadda kikai da Ni....... Allahumma barik 💖 " Da wadannan kalaman suka sake lulawa duniyar soyayya ta ma'auratah..  Ranar kuwa Marwaa taji ajikin ta kwanaki arbain din da basa tare duk Ahsan ya fanshe su a daren ranar...

   ALHAMDULILLAH!!!

ALLAH BAYA DORAWA WATA RAI...

"Allah cikin ikonsa da tausayinsa, baya taba dorawa wata rai wani abu face sai abinda yasan zata iya dauka, duk wani abinda kaga ya faru dakai, to kasani cewa lallai jarrabawa ce daga Allah, kada kace da badon abu kaza ba, to da abu kaza bai faru dakai ba, kawai kace Alhamdulillahi haka Allah ya KADDARA, domin shi yana aikata duk abinda yaga dama ne...Domin KADDARA KOWA DA IRIN TAASA 🤞

ALLAH YA RABA MU DA MUMMUNAR KADDARA AMIN..

"
ANAN NA KAWO KARASHEN GAJERAN LITTAFI NA (KADDARAH!! KOWA DA IRIN TAASA) ..

ABUNDA NA RUBUTA DAIDAI ALLAH YA HADAMU A LADAN DUKA. INDA NAYI KUSKURE KUMA ALLAH YA YAFE MANA BAKI DAYA..

__
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_

  _ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA  ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

         _1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

           _2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

              _3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

        _4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

Continue Reading

You'll Also Like

80.9K 5.6K 60
Shubish oneshots because why not. Mainly fluff with a little angst on the side. Ps- I wanted to write like a long story but I lack a good main plot a...
53.4K 3.1K 50
Na kasa fahimta da gasgata abinda zuciyata ke ayyana mini a kansa, SO ne ko BIRGEWA?. Komai nasa birgeni yake, ban taɓa ji ko ganin wanda ya haɗa abu...
39.4K 189 4
Dee Dee 🐑 အပြာစာပေ
127K 5.2K 46
A fire incident at his(Kim Jae-soo) husband's home while he (Baek Ji-Hu )was away made Kim Jae-soo return to his third year of university (he was reb...