KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TAS...

By missxoxo00

1.6K 80 3

KOWANNE DAN ADAM DA IRIN TASA KADDARAR💯IDAN KA YI HAKURI SAI KA CIMMA NASARA A GABA🤞...One really need not... More

free book🤸
1
2
3
4
5
6
7
8
9
11
12

10

78 4 2
By missxoxo00

_KADDARA!!!💔_*
     _KOWA DA IRIN TASA_
              👭👩‍❤️‍👨💍


©️®️ _NANA HAFSATU_
          _(MSS XOXO)_

    _SHAFI NA GOMA_

_Arewabooks:mssxoxo_
_Wattpad:missxoxo00_

_ADVERT👇_

_________

https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr

*_Assalamualaikum warahmatullah_*

*_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_*

*_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_*
____________________________.

  °°°°° *Kwanakin* Marwaa uku asibuti ana jinyar ta. Saboda ko bayan data farfado din bata gane wadanda ke kanta. Kuka take yi kawai tana salati. Tare da kamo sunan marigayiya Safaa ,

"Haba safaa ya zaki tafi ki bar ni? Banyi munyi alkawarin zamu yi rayuwa tare tunda kuruciya har tsufan mu. Kin manta muka ce idan mukayi kudi zamu bude asibiti kyauta na marasa karfi, zamu ginawa ummy gidah me gate ta koma... Safaa dan Allah idan wasa kike ki dai na ki dawo gare ni.. wayyo Allah na"

Wadannan surutai dama wasu barkatai sune Marwaa ke faman maimaitawa tana bubbuga hannuwan ta ajikin gadon asibitin. Tiburan kamar zatayi hauka. Hakan yasanya likitan duty ya sankama mata allurori tayi bacci..

A rana ta ukun ne aka samu ta farka babu surutan... Malama zuwaira na daga gefen ta a zaune akan kujera hannun ta rike da carbi tana ja.

Ya yinda Aisha ke tsaye ta goya baby Safaa a bayanta. Shesshekar kukan Marwan ne yasa malama zuwaira daga kanta tana dubanta. Haka ma Aysha dake jijjigar Safaa data goya ta.

"Kibar kukan nan haka Marwaa dan Allah ki dai na. Safaa addua take bukata .. ki dai na zubar mata da hawaye...."

Marwaa tashare hawayen ta da bayan hannun ta. Cikin murya mai sarkakewa dauke da damuwa tache,

"Ummy.... Yanzu shikenan Safaa ta ta rasu? Shikenan jda Safaa har abada ummy? "

Ummyda hawaye ke son taho mats itama tayi saurin tare shi ta dubi Marwaa tace,

"Allah daya halicceta ya kuma fi mu kaunar ta ya karbu abar sa. Haka zalika dukkanin mu nan daya bayan daya da haka da haka duk zamu tafi. Addua Zaki cigaba da yi mata kinji? Safaa ta tafi....Safaa ta dawo Marwaa" ummy ta karasa tana nuni da baby Safaa dake bayan Aisha..

Marwa ta sake goge hawayen ta ta na kallon baby Safaa. Aysha ta dorata akan cinyar Marwaa.

An sinkifeta cikin kayan babies pink color da ratsin white. An lullubeta cikin shawul white color shima. Sai tsotsar hannun ta take yi. Idanuwanta a bude saitin fuskar Marwaa.

Marwaa tayi murmushi ta kankame baby Safaa ajikin ta. Ta Kai kanta jikin baby Safaa .. Ta kumshe idanu ta bude su akanta ta dubi ummy tace,

"Kamshin Safaa take yi.... Idanunta ma irin na Safaa ne... Da bakin..." Kuka ta shjga yi marar sauti. Ta cigaba da cewa,

"Allah ya raya min ke Safaa. Allah ya tsare kuruciyar ki har girman ki safaa. Allah yasa ki gado mahaifiyar ki. Allah ya bani ikon cika alkwarin amanar ki da Safaa ta ba ni... Ummy kinsan Safaa fa tabani amana... Ko ince wasiyya kenan ko?"

Ummy ta gyada kanta alamar a'ah. Tana cigaba da jan carbinn ta. Marwaa ta cigaba da cewa,

"Ga amanar Safaa nan... Dan Allah karki bari tayi rashin uwa..karki bari Safaa ta wulakanta. Marwa ki kula mun da Safaa. Ban amince kowa ya rike mun Safaa ba fache ke Marwaa. Karki bari safaa ta tozarta. Na roke ki da girman Allah karki bari rikon Safaa yaje hannun wasu daban..... Sai nake ce mata menene hakan cuta ai ba mutuwa bace da sauran su. Ta sake nanata mun da, Dan Allah Marwaa ga amanar Safaa nan na bar miki ita har gaban abadan...Tana karasa fada ta fara wani irin tari.. sai na fito na gayawa likitan nan. Wannan shine maganar karshe da mukayi da Safaa ummy.. ummy ba zan iya rayuwa ba safaa ba. Ummy duniya ta mun zafi. Ummy kirjina na mun zugi da wani irin rada'di kamar zai ballo ya fado kasa ummy.. innnalillahi wa Inna ilaihi raji'un"

"Ki dai na kuka Marwaa. Kiyi hakuri. Allah ya jikan Safaa. Inshaa Allahu aljanna ce makoma agare ta. Kamar yadda ummy ta gaya miki...Safaa ta tafi, Safaa tadawo. Ga Safaa nan atare da ke. Sai kiyi kokarin cika alkwarin amanar data baki. Domin duk duniya ke da ummy me kawai zaku iya rike amanar Safaa. Kuma marigayiya Safaa ce ta zaba da ki kula da yar ta. Ke ta haifawa Safaa. Safaa yar ki ce yanzu. Safaa mallakin ki ce yanzu. Kiyi hakuri kowanne dan adam yana da KADDARar sa. KOWA DA IRIN TASA ne kawai. Allah ya bamu ikon cika wannan nauyi da ke kan mu mu dika gaba daya. Safaa ta samu alkhairi na tarin yabo daga bakunan jamaa kowa Yana fadin kyawawan halayen ta. In shaa Allah tata tayi kyau... Ki dai na zubarmata da hawaye." Aysha ta karasa fada tana Mai duban Marwaa dake rike da baby Safaa tana sauraron maganganun Aysha.

"Amin Aysha. Kin gama magana Allah ya saka da alkahiri kinji?"

"Amin ummy... Amin... Safaa amaniyata ce. Wallahi ummy hakuri da dauriya ce kawai muke yi amman baki daya duniyar tayi zafi astagfirullah Allah ya iya Mana"

"Allahumma Aameen.."

Haka dai sukayita maganganun su na tu'ajjabi suna kuma yiwa marigayiya Safaa addu'ar cikawa lafiya  da samun tikitin shiga aljannatul firdaws...

Sai bayan ishai aka sallame su. Da tulin magunguna da allurai. Domin bayan da karin ruwan da aka yi mata na karshe ya gama shiga. Likitan ya sake dubata inda dik tambayar da yayi mata sai kuka tana wasu irin weird acting. Atakaice dai tasamu depression. Ya Kuma dorata akan anti depressants na wata biyu.

Kawu Adamu ya taho da dan sahu. Su uku a baya an rike Safaa. Sai shi kawu Adamun a gefen Dan adaidaitan a haka Sika karasa har gidah.

Duk ba yan zaman makoki an tashi. Daman malama zuwaira tun ranar farko tace dan Allah kada ayi zaman makoki nan don bidi'ah ce kawai kowa yayiwa mamaci addua shikenan. Don yanzun gidan zaman makoki an mayar dashi sansanin gulma, Hira, wasu ma kasuwancin su kawai sike yi. Wata tawuce a na nuni da kasan atanfar ta. Ko a kasafce kudin kayan da ke jikin ka. Don hakan ba kowa sai yan cikin gidan kawai. Sai makota dake shigowa tsilla tsilla, Wanda basa nan akayi rasuwar da sauran su.

Aysha ta taya su suka gyaggyara dakin sannan tayi musu sallama ta tafi gidah.

Nanma marwa ta bude sabon shafin kuka hango kayan sawar safaadake kusada na ta ayar karamar drawer din su. Dakyar ummy ta lallasheta tadai na

Ummy tasake hadawa baby Safaa yar madarta a feeder tabata... Don madara aketa bawa babyn. Kuma Alhamdulillah an samu ta karba Tana sha. Don cikin Yan Kwanakin da aka haifetA ma tini har tayi yar kiba kadan. Gwanin ban sha'awa. Kamar su daya sak da marigayiya Safaa Kai kace kaki tayi ta tofar saboda tsabar kaman tayi yawa.

     °•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•

   Ahsan kuwa sai da ya shafe kwanaki Tara a asibuti yana jinya Kafin a sallame shi. Don da fari ma har an fata cure Rai akansa. Saboda suma ya dingayi yana kakkafewa jikin sa na wani irin kakkarwa.

Dakyar ya iya shan creamy tea din da Mahaifiyar da ta hada Masa ya Mike Yana tangadi.

"Ina zakaje Ahsan?"

"Mama wurin Safaa zani. Ko itama bazan ganta ba shikenan ba safaa ta wayyo Allah" ya fashe cikin wani matsananckn marayan kuka mai tsuma zuciyar duk Wanda ya saurara.

"Ka bari ka ka dan yi wasu mintinan magani da shayin daka Sha zubi jikin ka sai muje Ahsan.. ba inda baby Safaa zataje tana nan. Safan ka kuma da yardar Allah muna kyautata zaton tana aljanna inshaa Allah. Kaji ko?"

Ya gyada mata Kai kamar wani karamin yaro. Ya koma ya zauna akan wata kujera yadafe kansa da hannuwan sa.

Minti ashirin na cika ya mike. Mahaifiyar sa ma hajiya Laila ta bi bayan sa suka futa harabar asibiti. Direban su na ganin su ya ja motar zuwa inda sike Suka shigaa,

"Hajiya Ina muka nufa?"

"Gidan surukan Ahsan"

"Toh"

Gidan su Marwaa Suka nufa. Alokacin  Marwaa na tsakar gidah tana shanyar kayan baby Safaa. Sanye cikin wata dogiwar rigar A-shape ta atamfa. Kanta ba dankwali. Tayi fakin gashinta, Jelar har gadon bayanta.

Idanu hudu sukayi da Ahsan da yayi sallama. Ta amsa da sauri ta shige daki ta dakko hijabi ta zura.

Shi kuwa Ahsan kadan ya rage zuciyar sa ta ballo ta Fadi gani yai kamar Safaa ce . Badan bakinsa ya Masa nauyi bama da tuni ya Kira ta da safaan.

Suka zhjga dakin aka fara gaisawa. Ummy ta Mika musu baby Safaa dake baccinta cikin abun goyo. Ahsan ya kankameta kamar Zai mayar da ita cikin sa. Kallon ta yake  cikin tsananin so da kauna..

"Allah ya Miki albarka.... Allah ya Raya min ke Safaa" Ya fada da alama a zuci yake son yi baisan a fili ta futo ba.

Dukkanin su Sika amsa addu'ar da yayi. Marwa na gefe tana lankwasa hannuwa.

"Marwa kawo musu ruwa"

"Wallahi a koshe muke. Daga asibuti muke ai. Kinsan jiya da mukai waya nake ce miki maybe  suyi sallama. "

"Tabbas haka Kika fada kam gashi an sallame ku. Jiki yayi kyau Alhamdulillah Allah yakara afuwa"

"Allahumma Aameen."

Haka dai sukayi ta yar magana lokaci zuwa lokaci. Ahsan dai yayi shiru Yana duban baby Safaa . Ya yinda marwa ke Wasa da jelar zaren tabarmar.

Sun kai kaman awa daya haka sannan hajiya Laila tace bari su tafi. Dakyar Ahsan ya bada baby Safaa . Hajia Laila ta Kama hannun sa Sika tafi.

Bayan tafiyar su da awa biyu nanma Mai aikin su direba ya kawota da kayan abinci buhu buhu da kayan babies na Safaa da atamfofi da kudi bandir biyu yan dari biyar.

Ummy tai tagodiya ta Kira hajiya Laila awaya tana Kara mata godya.

     _______

   Haka rayuwar kowane sashin tasu ta kasance. Kullum sai sunyiwa Safaa addu'ar samun rahamar Allah. Gefe daya kuma baby Safaa na samun kulawa sosai. Don hajiya Laila ta roki alfarmar idan suna son ganin Safaa. Direban na zuwa ya dauki Marwaa da goyan Safaa suyi awanni biyu sai adawo dasu.

Marwaa da Aysha suka koma makaranta. Amma dai rayuwa gaba daya ta sauya ba kaman ta baya ba. Marwaa batada walwala kwata kwara.tadawo shiru shiru batasan hayaniya.

Küllü yaumin Kuma baby Safaa na tare da ita wani lokacin har makaranta  take goye tata tafi da ita ummy tun tana fadan har ta dena.

Lokaci nata ja, Sa ranar da akayi na marwa da Faysal nata matsowa kusa. Gashi sunata shirye shiryen jarabawar su ma.

Ahsan ma yanata tunanin yadda zai samu iyayen sa da maagnar.domin ya gama yankewa kansa shawarar barin kasar na Yan wasu shekaru kadan. Idan ya dawo yasan Safaa ta dan girma sai ya karbeta kawai. Domin yanzu ya cire v aure agaban sa Sam baya ma son kalmar don Bai warke daga radadin rashin Safaa ba.

Gashi sai ramewa yake yi a tsaye. Alhaji Jamil Gwanzamu da hajiya Laila Sika zauna su biyu suka yi shawara. Suna Kuma fatan cikar burin su. Suka shirya ba da sanin ahsan ba Sika nufi gidan su Safaa. Suka nemi ganin mahaifan Safaa.

Alhaji Jamil ya roki alfarma da su dubi kokon barar da yazo da shi. Malam muhammd ya ce sai yayi magana da manyan sa.

Ya kirawo su dake basu da nisa Sika zo. Nan aka nemi bangaren faysal don jin ta bakin su don ba a neman aure akan aure . Wannan ma lalura ce saboda yar dake tsakani wato 'baby safaa'

Nan aka nemi Faysal dan jin ta bakin sa.. Da fari yayi jugum Saboda yana kaunar rayuwar aure da son kasancewar marwaa zama halaliyar sa. Amman dayaji Ance wasiyyar Safaa na akan Dan Allah Marwaa ta rike mata  yarta. Kuma dai mahaifin Safaa din shine zaifi cancanta marwa ta aura don gudun Rana Mai wuyar baci wadda baa fata. Sai ya amince yace ya barwa Ahsan ya auri Marwaa ..

Baa wani jjra jjn ta bakin Marwaa ba ko Ahsan, don sunsan duka ba yadda zasu yiba. Don basa jituwa kwata kwata kowa ya shaida.

Malama zuwaira ta tuntub’i Faysal da maganar Aisha ko zai iya aurenta? Bai musa ba yace ya amince da Aysha da su marwa duk daya ne sunada kyawawan halaye. Kuma Aisha itama ba baya bawajen  kyau da nutsuwa.

Hakan kuwa akayi sati nazagayowa. Batare da sanin marwa ba. Aka daura auren,

Ahsan Jamil Gwanzamu da amaryar sa Marwaa Muhammad Alhassan. Alan sadaki bisa daraja. Wanda yan uwa na kusa da abokan arzki da kuma shedu suka halarta. Kowa ya bisu da adduar zaman lafiya da fatan alkhairai!

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_

  _ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA  ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

         _1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

           _2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

              _3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

        _4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:600_
_UKU:800_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

®️MX

Continue Reading

You'll Also Like

869 65 13
Labarin soyayyar Aaliyah Badamasi Bulama da Sa'eed Aliyu Modibbo a shekarun 80's...
29.1K 1.8K 22
Tayaya ummi da salman zasuyi rayuwar aure wanda da abaya basu son junan su an hada su AUREN HAĎI ku biyoni muji yadda zata kaya
26.1K 674 13
THIS ISNT MY FANFIC IT IS OWNED AND MADE BY "starsthatlinethesky" ON AO3 I WANTED TO PUT IT ON WATTPAD INCASE OTHERS LIKED THE BLACK PHONE (2022) SCE...
54.1K 3.1K 50
Na kasa fahimta da gasgata abinda zuciyata ke ayyana mini a kansa, SO ne ko BIRGEWA?. Komai nasa birgeni yake, ban taɓa ji ko ganin wanda ya haɗa abu...