KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TAS...

By missxoxo00

1.5K 72 3

KOWANNE DAN ADAM DA IRIN TASA KADDARAR💯IDAN KA YI HAKURI SAI KA CIMMA NASARA A GABA🤞...One really need not... More

free book🤸
1
2
3
4
5
6
7
9
10
11
12

8

83 5 0
By missxoxo00

*_KADDARA!!!💔_*
     _KOWA DA IRIN TASA_
              👭👩‍❤️‍👨💍


©️®️ _NANA HAFSATU_
          _(MSS XOXO)_

    _SHAFI NA TAKWAS_

_Arewabooks:mssxoxo_
_Wattpad:missxoxo00_

_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

___________

      °°°°°Akwatuna ne saiti kala kala... Designers da na gidah masu dauke da kaloli gwanin ban sha'awa..

"Habibty pick your favorites..... Ki zaba mana masu kyau. Saboda zan dinga anfani da wasu idan ni kadai zanyi tafiya. Idan mu biyu me Kuma sai muyi twinning .."

Safaa tayi murmushi kawai kunya duk ta dibibiyeta. Ahsan ya dan matsa kusa da ita yana rage sautin muryar sa kasa kasa kamar rada yace,

"Babes.... Ki zaba mana... Kinji?"

Safaa ta kamo hannun Marwaa dake danna yar wayar ta mai Torchlight tache da ita,

"Twinny dauka mun kalar da kike so... Please"

Marwaa ta zare idanu cike da dinbim mamaki tace,

"Haba twinny... Ai wadanda kikeso zaki zaba. Idan kika biye tani zance duk wadannan kalolin basu mun ba"

Ahsan yayi dariya yana nunata da yatsa yace,

"Kiji tsoran Allah... Kai bari na Kira Faysal yazo ya tafi da ke ma"

"Ai ba Kai na biyo ba twin dina na rako"

"Yo daman idan ba dan itan ba kin Isa ki shiga motata?" Ya karashe fada yana dariya sosai don yasan tabbas ya shaka mata

Marwa ta mayar masa da hararar ta karasa gaban akwatunan tana dubawa bata tankawa Ahsan ba.

Safaa dai tana gefe sai dariya take musu. Marwa ta nuna wani set kalar purple tana murmushi tana mai duban tagwanta tace,

"Wannan yayi kyau"

"Yayi sosai ma shaa Allah. Habibi na dauke su?" Safaa tace da Ahsan

"Sunyi kyau kam. Amma a hadamana da wancen set din blue din yayi unisex ko?"

"Eh.. sosai ma "

"Yauwa habibty.."

Maaikatan suka daddauka sets din akwatunan biyu. Ahsan ya Isa wajen biya ya biya kudaden su. Yasa suyi delivering to gidan sister dinsa inda ake hada lefen..

Daga nan suka wuce sashen kayan sawa na atamfofi, shaddodi, materials,  dogayen riguna, kananun Kaya, rigunan bacci da sauran su..

Duka kowanne Kaya sai Safaa tace Marwaa ta zabar mata. Tun marwa na nokewa har dai ta hakura duk inda Sika nufa tastes dinta take dauka. Kowane sashe Suka je Kuma sai sunyi yar cacar baki da Ahsan.

Suka tsaya wajen underwearss... Ahsan yana daga dan nesa da su ya dubi Safaa wai meye size dinta...

"Marwa..." Safaa ta dan tabo Marwaa

"Ba size din dinmu daya ba.kin manta?" Marwa tayi saurin katse Safaa. Domin ta Fi Safaa kirji ita Kuma Safaa tafi Marwaa mazaunai kadan.

"Kunya nake ji"

"Malama je ki dakko mata Mana.. komai ai ke kike zabawa"

"Ko kana black stomach ne?"

Ya sake yin dariya harda kyakyatawa yace,

"What? no... Yar tayi ce ke kawai... Babbar Yaya ta kame tana bawa karama order shine fa ba wani big deal ba. Wuce ki dakko komai"

Harara marwa ta sake zuba masa. Wannan karon ji take inama ta zunduma Masa zagi kawai ko taji sassauci a ranta.

Safaa tada fa habarta tana mai rau rau da idanun ta tace,

"Twinny kuyi hakuri please..."

"Babe akan wani dalilin kike bata hakuri? Ki cigaba da bata order kawai"

Marwa har tayi taku biyu zata bar wajen ta juya ta dube shi tace,

"Dukkanin abunda nake dauka according to my taste yake. My likes and desires. Sannan Safaa yar uwata ce ta jini wadda aka haife mu tare aka rene mu tare muka girma kuma tare. So duk abunda nayi mata ban fadi ba... Kana ji na?"

Ahsan yayi murmushi shi dama akwai shi da yin murmushi ya dafa kafafadara ajikin wani sashen mayafai yace,

"Hakane kam dik abubuwan da Kika fada. Sai dai dana auri Safaa shikenan Kun rabu. Ta zama tawa ni daya..."

Tsaki marwa taja tabar wajen . Ahsan ya fashe da dariyar da sai da marwa ta jiyo ta ta sake kufulewa. Safaa ta girgiza kai zatabar wajen ya bi bayanta da sauri Yana Kiran ta,

"Baby meye hakan?"

"Ahsan nace maka ka Dena tsokanar marwa haka. Haba dan Allah."

"Teasing ne fa kawai... Dagaske "

"Ka bata hakuri kaji? Kalaman ka sunyi tsauri.. Marwaa rabin rai na ce... Gangar jiki na ce.... Ni ce Marwaa marwa ce ni... Duk duniya idan ka cire kaunar fiyayyen halitta data iyaye na to banda na biyu fyace ita... Ka ji? Kuyi hakuri dukan ku"

Ahsan ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ya Kada kai cikin tabbatarwa yace

"Na sani... Kinfi son ta akai na."

Dai dai lokacin da marwa ta dawo tana turo underwears acikin basket babba na turawa..

"Ai akace dan uwa jijiyar nan ta wuya dan uwa yafi kusanci da ita. Domin zaka iya canza miji amman ba zaka sauya yan uwantaka ba.... Kin dawo?"

Ta karasa fada tana duban Marwaa data ja ta tsaya..

"Eh...ga su. Sunyi ko a sauya wasu?"

"Sunyi sosai... Nagode kwarai rabin rai ta"

"Anytime... Darling pie"

Safaaa ta juya ta dubi Ahsan Kan gaa Marwaa ya Bata hakuri Ahsan ya kauda Kai gefe ya ki hada idanu da ita don Yana kallon ta Dole yaaikata abunda takeso.

Don haka ya dinga avoiding kallon ta har Sika karasa siyayyar ranar. Abunda basu saya ba yace Yan uwan sa zasu karasa sayowa idan aka kammala komai zaa kawo lefen.

Suka nufi mota suka shigaa. Nan ma dai Ahsan yanata kallon gefen sa idan zaiyi magana baya so su hada idanu. Ai kuwa Safaa ta Kira sunan sa da karfi ya juya Suka hada idanu ta yi Masa nuni da yatsa.

Ba yaddazeyi haka ya hakura ya kada mata kai.ya zura mukullin ya tashi motar Yana reverse yace,

"Kanwar mu.....?"

Marwaa tayi shiru batace masa komai ba. Tana Danna yar wayar ta.

Ya dubi Safaa ta sake gyada Masa Kai Kan ya sake magana. Ya danne ya cigaba da cewa,

"Marwaa"

Sai asannan ta Dan daga Kai. Suka hada idanu ta cikin mirror yazabga mata harara itama ta mayar masa..

"Ina miki magana"

"Kunne keji Ina sauraron ka ai"..

Ya dartse kasan leben sa yana Dan jansa. Ransa a kufule ya dubi Safaa ta kauda kanta gefe.

"Akan maganganun dazu ne"

"What about it?" Ta yamutsa fuska tana duba yatsun hannun ta na hagu data daga hannun tana dubawa..

"Safaa ce tace na baki hakuri Wai" ya fada in I don't care tune.

Safaa ta juya dasauri ta dubeshi ya duake kansa yaki bari su hada idanu.

Marwa tayi dariya tace

"Hakuri ai ita azaa bawa da zata zauna , da zaman aure da Kai. Don kwa sai ta kai zuciya nesa. Zama inuwa daya da Kai amatsayn miji ai tsab matar zata samu lalura Yasin"

Ahsan ya kyalkyale da dariya yace,

"Wannan zancen karairakine  kawai. To bari kiji ai idan aka aura wa namiji ke a matsayin matar sa ta sunna. Allah mutuwa zeyi straight"

"Dan Allah ya ishe ku haka.... Idan Allah Kuma ya KADDARA kudin zaku zauna inuwa daya a matsayin matar da miji ya zakuyi kenan? Kashe kawunan ku zaku yi ko kuwa bijerewa Allah zakuyi da ya kadarta muku taku KADDARar a haka?" Safaa ta fada tana share hawayen ta.

"Kukaa twinny? Kuka innnalillahi wa Inna ilaihir rajiun. Dan Allah ki bar kuka twinny Wasa Mike fa... Dan Allah ki dena irin wannan maganganun. Inshaa Allah Mai kama da shi ma Allah ba zai KADDARA mun samu a matsayin miji ba. Haka zakila shima... Raha ce kawai akeyi"

Ahsan yayi saurin faka motar a wani kwalbato ya juya ya dubeta cikin rawar jiki da murya yace,

"Baby kuka Kuma? Wasan mu ne fa da muke ko da yaushe ..Dan Allah ki dena fadin haka. Sai kace yau muka saba musayar baki da Marwaa? Haba habibty na share hawayen ki please. Wasa ne fa....duk duniya banda kamar ki safaa don Allah ki dai na fadin wadannan maganganun...."

"To menene aciki? KADDARA ce fa KOWA DA IRIN TASA....Kuma Allah ya Kan jarabci bawan sa akan abunda yake wa tsananin kiyayya.. Ni dai ku dai na wannan maganganun banaso ku shriya ku zama yayada kanwa sai nafi farin ciki akan wannan yada maganar da kukewa juna.."

"Inshaa Allah zamu dai na..Inshaa Allah.. kinji?"

"Naji..."

Marwa ma hawayen ta farayi sai juyo shesshekar kukanta suka juyo. Dama hakan suke tun suna kanana. Idan daya ta fara kuka an bata mata Rai to sai dayar itama ta fara ko da kuwa batasan meyasanya tagwan tata kuka ba.

Safaa ta bude motar ta futa ta bude kofar inda Marwaa take ta tsugunna ta kamo hannuwa ta duka biyu.

"Twinny na Dan Allah ki dena kukan.kalle Ni fa na Dena Ni.dan Allah share hawayen ki kinji ko? Bakiji Rai na ba yadda yake susan wannan kukan da kikeyi"

Marwa tadaga tadube ta.. suka rungume juna.

"Na Dena kuka Safaa na dena.kiyo hakuri kinji?"

"Na hakura kema kiyi hakuri"

Sai da suka lallashi junan su. Tukun sannan Safaa ta koma wajen zamanta ta zauna. Ahsan ya tashi motar suka dauki hanyar gidah. Ya tsaya ya saya musu nama da su drinks da cakes ya sauke su agidaah.

Yanata mamakin darun su. Sai da ya tabbatar sun shrya da sahibar tasasannan ya tafi gidah ransa fari kal.. Domin Yana kaunar Safaa Kasancewar ta first love dinsa... Kuma wadda inshaa Allahu zata zama mata agare shi..

     ©©©©©©©©©©©©©©©©

     Ranar lahadi maza Yan uwan Ahsan suka kawo tulin kayan lefen Safaa gidan su.

Kayane Wanda gaba daya yawan su da kyawun sa ya tunzura mutanen yankin cike da mamaki da Kuma tu'ajjabin ganin su Safaa din ba yayan kowa bane yayan  malam ne talakan talak na soro Mai dattin hula marar farcen Susa.

A Kuma ranar ne iyayen Ahsan suka roki alfarmar dangin Safaa da su temaka a daura auren a ranar idan yaso shagalin biki sai ayi agaba. Kasancewar zuriar tasu ba mazauna Nigeria bane zasu kokkoma kasashen su wasunsu Kuma zash tafi hutu ne

Hakan kuwa akayi.aka dunguma masallacin jumuah dake gefen gidan kadan ba nisa .. Yan uwa da abokan arzuka suka sheda saurin auren Ahsan Jamil Gwanzamu da amaryar sa Safaa muhammad Alhassan akan sadaki mafi daraja..

       Ko da labari yazowa Safaa Kan an daura aurenta a ranar sai dayayi kuka. Domin sun gama tsarawa a Rana daya zaa daura musu aure itada marwa. Allah Bai yarda ba.

Ummy da Marwaa da su kawu Adamu me Sika Bata hakuri Suka tausasheta Dakyar dai ta yarda ta dena kuka ta karbi tata KADDARar.

Aka Sanya ranar biki wata biyu. Anso a hada dana Marwaa shi Kuma Bai gama shiryawa ba. Dan gini ma yakeyi Kuma Bai Dade da farawa ba. Itama aka kawo kaya daidai misali aka saka Rana shekara daya cuf.

           Ranaku nata wucewa... Har Allah ya amince date din da aka saka bikin Safaa yazo..bawata hidima akayi ba kasancewar basason taro. Itada kawayen ta sukayi walima suka Yi saukar karatun alqur'ani . Ranar jumuah Kuma malama zuwaira tayi wunin ta anan cikin gidan akayi kidan kwarya. Amarya Safaa Kaya iri daya ta saka da marwa sai kace duka su biyun ne amaren. Gwanin ban shaawa Ahsan yazo aka daddauki hotuna. Marwa na gefe Ahsan a tsakiyar sai Safaa daga gefe itama hotunan sunyi matukar kyau.

Anci an Sha sosai dai dai karfin malama zuwaira da Yan kudaden ta dakuma Wanda Yan uwa daa abokan arzuka Sika Bata gudunmuwa.

A ranar ne da daddare Kuma aka Kai Safaa gidan ta dayaji komai da komai na rayuwa.dakuna biyu da parlor malama zuwaira ta sakawa Safaa komai daidai gwargwdon karfusu. Yayinda daya dakin da parlor Kuma gidan su Ahsan su gyara Masa nasa..

Gidan yayi kyau sosai bungalow ne gidan qasa dayaji komai da komai na rayuwa...

Safaa da marwa sai  da akayi dagaske suka rabu dominn tsabar kuka na rabuwa da kowanne su keyi duk wani Dan Adam dake wajen sai da ya zubar da hawayen tausayi.

Don zazzabin sosai ne yarufe marsa sai da aka dangana da asibuti Tasha allurai aka koma da ita gidah tayi bacci..

Haka rayuwar ta cigaba da garawa. Marwa da Aisha na zuwa makaranta adawowa Kuma Safaa ce da Ahsan ke dawo dasu gidah kullum ba gajiyyawa..

Bini bini Safaa na gidah idan ahsan za shi aiki idan ba makaranta zata saka yakawo ta gidah ko ta roki marwa taje itadaa Aysha

Har ta samy ciki Allah ya temaka  sai dai cikin yazo mata da laulayi sosai ta na shan wahala daga karshe sai gidah ta dawo ta dinga jinya da renon cikin.

Wata tara da kwanaki kuwa ranar wata sanyayyiyar alhamis Safaa ta tashi da matsanan ciwo aka wuce da ita asibuti Ahsan duk ya gigice... Akace haihuwa ce..Amma sai dai a mata cs..

Hakan kuwa akayi aka curo katuwar 'ya tubarkallah.. suka shiga yin sujjadar godia ga Allah.

Aka futo musu da jariiruar suna kalla. Ahsan ya dauketa yayi mata huduba.

"Ya sunanta?" Cewar kawu adamu yana murmushi..

Ahsan Yana duban yar kaman zai cinyeta saboda so yace,

"Safaa Ahsan Jamil..... Dr zanj iya ganin maman nata. Ko tana bed rest?"

Likitan daya fito daga dakin da aka kai Safaa bayan an mats operation din  ya zare facemask din bakinsa yana duban su cikin sauke nunfashi daya bayan daya Mai sauti yace,

"Wacace Marwaa.?"

" Ga ni Dr..."

"Kije tana neman ki karki dade please."

"Tohm Dr."

"Bama ni mjjin ba?"
Cewar Ahsan Yana turo baki gaba..

Likitan yayi murmushi kawai yace,

"Ita kadai tace dai for now.. "

"Ba matsala..."

Marwaa ta tura kofar dakin ta shiga. Safaa na kwance akan gadon.  Ta daga wa Marwan hannu tana kakaro murmushi..

Marwan ta karasa wajenta. Wata nurse ta shigar da yar ta dorata akan Safaa.

Safaa ta dan dubeta tana murmushi.

"Sannu twinny Allah ya Raya mana ita ya mata albarka. Ke Kuma Allah ya baki lafiya da lafiyar shayarwa Amin"

"Aamin... " Safaa ta amsa hawaye daya nabin daya..

Ta mikawa Marwan yar tana dartse bakin ta cikin ciwo tace,

"Ya sunanta?"

"Kaman Safaa itama"

Safaa ta gyada kai ta sake cewa,

"Marwaa..."

"Na'am..."

"Ga amanar Safaa nan... Dan Allah karki bari tayi rashin uwa..karki bari Safaa ta wulakanta. Marwa ki kula mun da Safaa. Ban amince kowa ya rike mun Safaa ba fache ke Marwaa. Karki bari safaa ta tozarta. Na roke ki da girman Allah karki bari rikon Safaa yaje hannun wasu daban..."

"Meye hakan Safaa? Cuta ai ba mutuwa bace. Zaki warke da yardar Allah...ke Zaki tarbiyyantar da baby Safaa ki bata kulawa irin wadda uwa ke bawa yar da ta haifa"

Safaa ta girgiza kai hawaye na zilalo mata tace,

"Dan Allah Marwaa ga amanar Safaa nan na bar miki ita har gaban abadan..." Tana karasa fada ta fara wanj irin tari..

Marwa ta futa dasauri jaririyar na hannun ta tace,

"Dr tana wani irin tari ta kasa magana."

Dr din ya shiga da sauri. Marwa ta mikawa ummy jaririyar ta shiga Kai kawo a harabar inda suke. Hakama Ahsan daya kasa tsayawa waje daya.

Likitan ya fito daga ciki bayan sun dan jima suna gwaje gwajen su akanta...

"Menene doctor...ana bukatar wani abun ne ko jinin vai isaba a Kara diba?"

"No ba haka bane....",

"Dr menene dan Allah? Wani ciwon ne daban? Marwa ta tambaye shi a gigice...

Likitan ya sake saka hannu ya shafo keyarsa ya dube su yace,

"Sai dai kuyi hakuri.... Ku dauki KADDARA.. Allahn daya fi mu kaunar ta ya karbi abar sa.... Time of date 3:00pm .. Thursday afternoon..."

    #NOVELLA!!
(SHORT NOVEL/GAJERAN LABARI....)


ZAFAFA PAID BOOKS
2024 INSHAA ALLAH

AMEENATUH:MAMUH GEE

KWANKWASON JIMINA (MAI WUYAR SHAFAWA): NANA HAFSATU

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE):BILYN ABDULL

GUDUN KADDARA:SAFIYYAH HUGUMA




®️MSS XOXO

Continue Reading

You'll Also Like

119K 2K 83
The titles say it all.
543K 35.5K 77
A story of a young Prince and his Mother with two sisters who have been deprived of their rights by a very heartless woman #MAGAJIYA#.......
79.8K 5.6K 60
Shubish oneshots because why not. Mainly fluff with a little angst on the side. Ps- I wanted to write like a long story but I lack a good main plot a...
262K 10.8K 37
Complete story of a young girl Ummy.