KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TAS...

By missxoxo00

1.6K 80 3

KOWANNE DAN ADAM DA IRIN TASA KADDARAR💯IDAN KA YI HAKURI SAI KA CIMMA NASARA A GABA🤞...One really need not... More

free book🤸
1
2
3
4
6
7
8
9
10
11
12

5

85 4 0
By missxoxo00

   *_KADDARA!!!💔_*
     _KOWA DA IRIN TASA_
              👭👩‍❤️‍👨💍


©️®️ _NANA HAFSATU_
         

    _SHAFI NA BIYAR_

_Arewabooks:mssxoxo_
_Wattpad:missxoxo00_

_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

___________

   Adamu ya riga su fita, Sannan su kuma suka zura hijaban su iri daya suka bi bayan sa...

Ahsan na dora idanun sa akan su gaban sa ya tsananta bugawa... Duba da yadda tsananin kamar tasu tayi yawa...

Adamu ya yafuto su da hannu suka karasa inda suke a tsaye. Marwaa ji take kamar ta saka hannu ta mangare kan Saafa . Da Saafa ta fadi gaskiyar itace wadda Ahsan yake nufi da tuni ba ita zaa fito.

"Acikin ku wacece ta shiga gidah a karshe?" Cewar kawu Adamu.

Marwa ta daga hannu zata nuna Saafa itama ta daga sukayiwa junan su nuni a atare.

Kawu Adamu ya girgzia kai cike da takaici yace,

"Banason wannan wasan na ku... "

"Marwa cee" Saafa ta fada tana murmushi

Marwaa ta daga kai ta sauke mata lafiyayyiyar harara. Ta hada da Ahsan daya ke binsu da wani kallo duka shima ta galla mai harara tace,

"Wallahi Safaa ce kawu. Ni ce na shiga a farko... Idan karya nake ta rantse yadda na rantse"

Ahsan ya sauke nannauyar ajiyar zuciyar dake tattare da farin cikin da ya mamayeshi. Daman tun daga hararar da Marwaa ta daka masa ya gano ba itace mutuniyar da zuciyar sa ta kamu da kaunar ta ta ba.

"Safaa wai haka? Kinsan dai bakyau rantsuwa akan karya ko?"

Safaa badan ta so ba ta daga kai ta murgudawa marwa baki kasa kasa tace,

"Eh.. Ni ce na shiga a karshe"

"Alhamdulillah....." Ahsan ya furta a fili. Murmushin fuskar sa na dada faadaduwa.

"Kawu na tafi ?" Cewar Marwaa.

"Toh wannan itace Marwaa tagwan Safaa." Cewar kawu adamu yana mai yiwa Ahsan nuni da su.

"Mashaa Allahu... Safaa da Marwaa Allah ya raya su Amin"

Marwa ta juya ta shige ciki. Yayi nda kawu adamu ya basu waje. Ahsan ya dan sake matsawa wajen Safaa taja baya tana lankwasa yatsunta yayi murmushi sannan yace

"Ranki ya dade barka da yammaci"

"Ina wuni?"
Ta gayshe shi kanta a kasa.

"Lafiya Lau ranki ya dade... Ina fatan zaki hakuri abisa abunda ya faru dazu... Ki Kuma bawa Yan uwanki hakuri. Nima wallahi ba hali na bane. Banason ki kufce mun ne har ya zamto na kasa saita kai na nayi katobarar cewa Zan dakko ku na kawo gidah dan Allah Kada kuyi mun kallon irin mazan Nan masu wayayyun idanu... Kinji gimbiya?"

Safaa tayi murmushin da hakoranta suka bayyana tace,

"Allah ya yafe Mana gaba daya... "

"Aamin ya rabbi.. batare da Bata lokaci ba kamar yadda na fadawa kawun ku... Alkhairi ne ya kawo ni wajen ki.... Allah ya dasamun kaunar ki a kallon danayi Miki na farko. love at first glance. Nan take zuciya ta sai ta kamu. Kuma son ki nake da aure.  Kuma batare da an dau wani lokaci Mai tsawo ba.. Domin ashiriye nake haka zalika magabata na ma dama jirana suke na kawo musu maganar inda nake neman aure..... Toh Amma kamar yadda kawun ki ya fada... Idan kinada wani tsayayye bazan tauye Miki hakki ba... Kinji Safaa? "

Shiru Safaa tayi, taki amsa cewa komai. Haka kawai daga haduwar farko sai maganar aure Kuma?

"Ki ce wani abun?" Ta sake juyo muryar sa ya katse mata tunani.

"Bawan Allah yau ne fa farkon haduwa ta dakai" ta samu kanta da bashi amsa haka nan

Ahsan yayi murmushi Mai sauti yace,

"Kuma alkhairi ne ya kawo Ni ba... Inata zuba banma gaya Miki suna na ba. Sunana Ahsan Jamil Gwanzamu. Na gama karatu na har ya zuwa matakin degree na biyu.. Ina aiki a federal inland revue service (firs)....  Ni da mahaifa na muna zaune a unguwar Dex crescent 2.. office dinmu Yana hanyar makarantar ku kwana ta biyu dayan titin.. Safaa Allah ne yayi hadiwata da ke lokaci daya na kamu da kaunar ki Mai wuyar fassarwa.. kinsan ba Dan Adam ne tsara wa kansa rayuwa ba.. bamusan me Allah ya rubuta Akan mu ba safaa.. ki bani chance indai ba wani a kasa da yake neman ki... I promised to be an excellent lover, lovable husband kuma caring family.. ba zakiyi Dana sanin Kasancewar da ni ba... Dan Allah ki dubani ki tallafamun"

Ita maganganun sa ma sai suka soma Bata tsoro. Daga haduwa da ita yau sai kace zai zauce. Babban mutim Mai cikar Kamala kana ganinsa kasan Dan gidan dattako ne yazo kamar zai mata sujjada saboda tsananin rokon ta karbi kokon barar soyayyar sa...

"Safaa kice wani abun...."

Ta dauke ajiyar zuciya ta juya ta dubi kofar gidan su tace,

"Ni ba yar kowan kowa bace... Gaba da baya mu ba masu hali bane muna dai da wadatar zuciyaa..."

"Sssssshhh... Safaa ya Isa hakan nan. Ke nake so ba Wai dukiyar ku ba, ke nake so ba Wai suna ko sanayya ba.. ke nake so ba auren kwarya tabi kwarya ba.. A kullum addua ta Allah ya hadani da matar kwarai, wadda zata so ni tsakani da Allah ba Dan wani Abu nawa ba. Wanda Nima Zan so ta tsakani da ALLAH badan dukiyar ta ba, ko dan surarta ba ko dai wani Abu da zai gushe ba. A kullum addua ta shine Allah ya hadani da matar tagari Mai tarin albarka, Mai nasaba, ilimin addini da boko, kunya, kawaici, biyayya, kyawu dai dai gwargwado da kyan halaye.."

Safaa tayi murmushi tace,

"Acikin lokaci kalilan kasanni. Ko ince kazo kofar gidan mu. Bakasan wacece ni ba. Ta iya yiwuwa dik suffofin nan daka lissafa bani da ko daya..Ta iya yiyuwa ma inada wasu halaye marasa kyau baka sani ba. Ko kyan Dan maciji ne waya sani?"

Ahsan ya girgzia kai yace,

"Addua bata faduwa kasa banza... Tun sanda na dasa idanu na akan ki na tabbatar banyi zabin tumun dare ba. Kuma na tabbatar wa Kai na Allah ne ya amsa adduoi na ya sa na biyo ta Nan muka hadu da ku... Ni kawai ki bani dama kinji?" Ya fada Yana sosa keyar sa.

Safaa tayi murmushi tana jan kasan lebenta tace,

"Mu cigaba da addua Allah yayi Mana zabi nagari. Idan alkhairi ne Allah ya tabbatar idan ba alkhairi bane Allah ya musanya Mana da mafi....

"Alkhairi nema... Kuma inshaa Allah Nan kusa zamuyi aure. Inaji ajiki na. Yaushe zanzo na samu abban ku?"

Safaa ta daga kai ta dube shi da sauri lalle mutumin Nan dagaske yake. Cikin zare idanu tace,

"Da wuri  haka? Aa dan Allah ka Bari dai tukun"

" Da zafi zafi kan daki karfe... Ai baa sanya yanzu... Kuma so nake Nan kusa muyi auren mu me zamu jira?"

Abunma ya so ya Bata dariya ta kanne kawai tace,

"Allah ya shiga lamarin."

"Aamin... Ki ban number ki..."

"Banda waya.."

"To yanzu ta Ina zamu dinga magana har my fuskanci juna? Zan dawo gobe to inshaa Allahu"

"Shikenan ba damuwa"

"Godiya nake... Allah ya saka Miki da alkhairai Safaa Allah ya amince ya sa ki zama mallaki na..Ni  kuma Zan nuna Miki Dan halas ne Ni Kuma ba zaki zaben tumin dare ba."

"Sai anjima..... Zan yi aikin makaranta" Ta fada tana dan matsawa don tafiya gidah,

"Nagode da lokacin ki. Allah ya saka Miki da mafificin alkhairin sa. "

"Amin " shigewa gidah tayi da sauri.

Har sai data shige sannan ya dena kallon ta. Ya bawa su adamu hannu sukayi sallama. Adamu ya bishi a baya har wajen motaa. Ahsan yace dashi,

"Nagode kawun mu.. Kuma da alama Safaa tabani dama.. Domin yadda mukayi dai ba maganar wani a kasa. Naso ma tabani number wayar ta tace batada waya."

"To alhamdulillah! Allah ya zaba abunda yafi alkhairi tunda kaji daga bakinta ai shikenan..Eh ba waya a hannun su yanzu gaskia saboda kaga ba wani jimawa sukai da fara karatun ba. Danma dai sunada girman jiki ne Kuma sun Kare makaranta da wuri. "

"Allah sarki hakan yayi ai... Inshaa Allah Zan dawo gidah ma naso ma Naga abban nata na gayshe dashi Domin yabani dama Amma tace nabi a sannu tukun"

Adamu yayi murmushi yace,

"Kasan nagaya maka ai Yara ne.. Kuma gaskia basa wani fitowa tadi.. "

"Mutunci ne ai hakan. To Allah ya kara tsarewa Amin"

"Amin Amin.. "

"Nagode Allah ya saka da alkhairi.. sai ka sake jina ko zaka ban taka number idan ba matsala?"

Kawu adamu ya karanto masa number sa Ahsan ya saka a waya.. Ya sake bashi hannu sukai sallama ya shiga mota ya dauki hanyar gidah m

Yana tuki idanunsa na Yi Masa nuni da hotan fuskar  Safaa. Kunnuwan sa na tariyo Masa zazzakar muryar ta Mai dadin sauraro.. ya kumshe idanu yabude ahankali yace,

"Yaa Allah ka mallakamun Safaa..."

=====

       Kunsan wasu ghetto area din na gargajiya akwai gulma da soke soken aure..  Don tuni wani ya samu malam Muhammad Alhassan mahaifin su Safaa ya sanar Mai wani Mai babbar mota mai kudi yazo wajen su Safaa ya biyo su tun daga makaranta ya Kuma Dade a kofar gidan...

Ai kuwa malam Muhammad ya tafi gidan ya dinga surfawa malama zuwaira fadaa kan yaranta sun fara kawo Masa kattai kofar gidah... Kuma ina kudin da aka bayar yake? Ance mai kudi ne mutumin da yazo.?

"Ina abunda ya kawo ya bayar din iye? Ance shirgegiyar mota yazo shi da ita ya dade a kofar gidan nan.. "

Malama zuwaira da abun ya isheta ta fito daga cikin daki tace dashi,

"Maganar ka kenan kullum kai?  Malam ka gafar ceni bantaba mayar maka magana ba amman yau ka kai ni bango.. Wato malam ba zaka yiwa kanka fada ba? Shekaru sun ja meyakwan ace yanzu ma tallafi yaran ka ka nuna musu kauna amman kai tarbiyar su bata gaban ka? Cin su, shan su, lafiya da sutura da duk wasu hakkokin 'ya'yaye akan iyayen su Malam baka yiwa yaran da ka haifa... Ka zama kamar wani kaji sai da tsaba? Mutane suyita zugaka awaje kazo kana sauke bambamun fada akan iyalan ka.. To dai Safaa da Marwaa ba samari ne da su ba domin ko tadi akazo wajen su basa fita. Wannan ma biyo su yayi daga makaranta yana son Safaa. Kuma yace zai dawo yayi magana da kai. Naira biyar dinsa kuma bata shigo hannun su ba... Ka tsaurara bincike.. Haba ace kullum kana Kara shekaru amman abun naga gaba yake yi.. Hakkokin yaran nan wallahi mu iyayen su sai Allah ya tambaye mu..." Malama zuwaira na gama magana ta shige cikin daki tana tsaki saboda yadda ranta ya baci sosai akan mai gidan na su..

Duk yan tsakar gidan sukayi shiru kamar ruwa ya cinye su ciki harda malam Muhammad da shi kansa yayi matukar mamakin wai yau zuwaira ce ta fada Masa maganganu haka?!

Zulfa'u tafito daga daki taci ado cikin riga da skirt sun mammatseta tayi hanyar fita zata tafi malam muhammd ya daka mata tsawa,

"Ke kuma Ina zuwa?"

Addabiyya tana zaune tana taunar cingam tace,

"Malam yau dai bansan meya hau kan ka ba.... Tunda da dai ka bar mana ragamar mu matan mu kula da yaran mu kai ba zaka iya ba ai shikenan.... Inda zataje bai shafeka ba. Ba kuma matsalar ka bace. Zulfa'u je ki"

Zulfa'u ta saka kai tayi ficewar ta. Malam muhammd yaja tsaki ya dauki buta ya shige cikin bandaki yanata surfa masifa shi kadai...

      __

Bayan komawar Ahsan gidah. Kasa nutsuwa yayi. Duk wani bincike da zai fara akan Safaa ya fara. Tun daga makarantar school of nursing din da suke duk yaji halayenta masu kyau ne itada yar uwarta

Hakama daya saka ayi bincike a unguwar anyi musu shaida ta arziki su da mahaifiyar su idan ka cire gogan nasu wato mai gidan malama zuwaira.

  *GIDAN MALAM MUHAMMAD ALHASSAN*

   Malam Muhammad Alhassan shine asalin cikakken sunan sa... Matan sa uku, Adabiyya, zuwaira da kuma Asmau suna ce da ita aunty amarya...

Allah ya azurta malam Muhammad da yara guda....

#NOVELLA: SHORT NOVEL... 🤞

®️MX

Continue Reading

You'll Also Like

3.2K 236 18
AMJAD-Aikin da aka aiko ni zan iya yinshi kuwa? Tuntuɓen da nayi a hanya bazai kawo min matsala cikin aikina ba? Zan iya ceto rayuwan dubbanin mutane...
27K 364 58
A WOSO Oneshot book Oneshots of favourite Women's footballers Mainly the Lionesses, Arsenal Women's team,Chelsea Women's team, Man City Women's team...
15.8K 1.1K 47
Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko sede mu zubawa sarautar Allah idanu zuwa...
26.1K 674 13
THIS ISNT MY FANFIC IT IS OWNED AND MADE BY "starsthatlinethesky" ON AO3 I WANTED TO PUT IT ON WATTPAD INCASE OTHERS LIKED THE BLACK PHONE (2022) SCE...