KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TAS...

By missxoxo00

2.5K 96 3

KOWANNE DAN ADAM DA IRIN TASA KADDARAR💯IDAN KA YI HAKURI SAI KA CIMMA NASARA A GABA🤞...One really need not... More

free book🤸
1
2
3
5
6
7
8
9
10
11
12

4

127 6 0
By missxoxo00

*_KADDARA!!!💔_*
     _KOWA DA IRIN TASA_
              👭👩‍❤️‍👨💍


©️®️ _NANA HAFSATU_
        

    _SHAFI NA HUDU_

_Arewabooks:mssxoxo_
_Wattpad:missxoxo00_

_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

___________

*Ya fito* yana ta sauri ya cinma su yana doka sallama....

Aisha ta daga kai ta dube shi alokacin da ya karasa kusa da su din. Don ita azaton ta ma ko dan sahun lefi ya masa yadda ya tuko motar gadan gadan ya tunkare su ya faka motar..

"Idan kun amince zaku biya hakan yadda na fada ku hau muje idan baku yarda ba gaskia ba zanje a dari hudu ba Allah ya sa ni"

"Haba yayana Allah a haka muke zuwa ko ina fa ana ragi" Marwa ta ce da dan sahun cikin muryar roko..

"Gaskia idan ba zaku biya hakan ba sai dai ku nemi wani"

"Aboki na jeka kawai, Zan karasar da su... Assalamu alaikum sannun ku." Cewar saurayin daya fito daga mota

Duk suka tsaya suna binsa da kallo... Musamman Marwaa dake binsa da kallon ka renawa kanka hankali, Ta kasa hakuri tace,

"Akan wane dalilin zaka karasar damu gidah? Munsan ka ne? Bawan Allah mu ba irin yammatan nan bane masu shiga motar maza suna rage musu hanya. Da mu hau motar ka gwara mun karasa gidah a kafa wallahi. Ku shiga muje dan Allah."

Ta chusa Saafa aciki, Ta sake janyo hannun Aisha ta shiga, daga karshe ita kuma bayan ta tsaya ta watsawa saurayin dankareriyar lafiyayyiyar harara ta shiga ciki mai adaidaita sahun yaja suka tafi...

"Gaskia wanan gayen anyi dan renin hankali, Ni fa at first na dauka mai adaidaita ne ya masa ba daidai ba yasin.." cewar Aisha

"Nima dai yaban mamaki audacity din nasa yayi yawa" saafa ta fada..

"Bar dan renin hankali ... Irin samarin nanne masu rawar kai. Irin shi ga mai kudi dinnan cikin izza yana magana, ya dauka muma irin matannan ne ballagazazzu marasa kaman kai, Bamu sanshi ba haka kawai sai mu shiga motar sa. Mtscew dan renin hankali kawai" Marwaa tafada cikin hasalewa... Ta karasashe zancen da jan tsaki...

Mai adaidaita sahun ya na jan babur yana jinsu ya kyalkyale da dariya yace,

"Nafu tunanin wata yake so acikin ku gaskia"

"Allah ya kiyashe mu ya kuma tsare mu da kula irin wancen..."

Dan adaidaita ya juya ya kallo marwa data gama magana taja tsaki yace,

"Kila ma ke yake so kanwata"

"Allah ya kiyaye ya rufa asiri ko maza sun kare a duniya bana fatan hulda da irin wancen"

Dan adaidaita sahun ya sake kecewa da dariya yana gyara zaman mudubin side mirror yace,

"Ai kwa wallahi binmu yake a baya. Gaskia ya mato da san wata acikin ku" Yana nuna musu motar saurayin dake biye dasu ta baya ta cikin mudubi,

"Amma wannan ko nacacce to meye dalilin bin namu?"Aisha ta fada

"So yake ya fadi maku zuciyar sa mana to ai ni ya hurgeni da zafi zafi kan daki karfe .  Haka ake son gwarzon namiji" cewar dan adaidaita

Ita dai Safaa dariya ta kyalkyale da ita tace,

"Ko Aisha ko Marwaa wata acikin ku inaga ya kamu da so.."

"Allah ya rufamin asiri da yardar Allah bani bace... In kinji ana hate at first sight to abudna ya faru da ni kenan akansa. Gaba daya bai kwantamun ba... Banà kaunar sa"

Aishaa ta tuntsire da dariya tace,

"Oho dai, Ni dai na tabbatar 'da ya daga cikin ku yake so... Ina cikin ku wa zaice Yana so na? Ke dai Allah ya samu adanshin ku kawai ya dandana mana irin farin jinin ku"

Marwa ta daga hannu ta dada mata dundu a baya. Safaa dai dariya tayi tace,

"Allah ya shirye ki Aisha.."

"Wahalalle ai kuwa bin namu yake... Iska na wahalar da mai kayan kara" Marwaa ta fada ganin motar saurayin tana biye dasu har cikin titin unguwar su..

       Hannun sa daya akan sitiyari yana biye dasu a motar sa... Murmushin fuskar da ya fadada alokacin daya tuno bakinta data bude tana dariya ta shiga cikin adaidaita sahun..

Ya samu kansa da saka dayan hannun sa yashafo kasan keyar sa...  Ya kamu da kaunar yarinyar da yayiwa kallo daya bisa ka'ida...

Tsukukun layi ne, Dakyar motar sa ta shjga ciki Kasancewar tana da girma da Kuma Fadi ba lefi.

Ya hango Dan adaidata sahun daya faka a kofar wani gidah Marar bene dai dai haka na marasa karfi.. ganin sun fito daga cikin adaidaita hakan yasanya shima saurin fitowa daga cikin motar tasa har hular kansa na faduwa a kasa..

"Yanzu Wa zai cika mun kudin acikin ku?" Cewar Dan adaidaita sahun daya dakko tsunma Yana faman goge gogen cikin adaidaitan nasa.

"Ni ce Ina zuwa." Marwa ta shiga bubbude littafin ta ta zaro gudar nera dari data manne da jikin littafin ta tana Mika masa

"Angode Kawas" Aisha ta mata godiya

"Mungode sissy.... "

"Dalla kumin shiru, godiyar meye haka? Nima tun darin da kawu adamu yace na rike chanjin nance fa last week"

Dan adaidaita da shegen tsegumi ya leka ya hango saurayin Yana murmushi yace,

"Gaskia ba dan sauri nake ba dana tsaya naga ya wasan zai Kare.. mutumi na fa dagaske yake."

"Matsalar ku ce Kai da shi din." Marwa ta bashi amsa.

Ta shige cikin gidah da sauri. Aisha ma ta musu sallama ta tafi. Saafa ce ta shige daga karshe bayan dan adaidaita sahun yaja ya tafi.

Shi dai Yana tsaye Yana kallon su har suka shjgye cikin gidah. Ya jingina da motar sa na wasu mintina ya gama tabbatarwa da lalle gidan su ne..

Ya nufi wajen samarin daya ga suna zaune tun dazu a bakin kofar gidan Sina hira da butar shayin buzaye agaban su suna dafa shayi.

Hannu ya basu sukayi musabaha yace ,

"Dan Allah abokai na yar tambaya Zan muku idan Babu damuwa"

"To Allah yasa mun sani" Cewar daya daga cikin samarin.

"Yammatan da suka shiga cikin gidan nan Dan Allah yan gidan ne?"

"Masu uniform yan biyu da suka shiga ciki?"

"Eh eh su fa...." Ya amsa musu... Kasan zuciyar sa Yana dama yaga alaman Yan biyu ne saboda tsananin kamar su sai sai dai kamar daya tafi daya tsiwa

"Saafa da Marwaa ne yan gidan ne"

"Dalla malam Kai banza ne wawa. Kawai sama taka mutum yazo ya yana cewa abu bamusan shi ba gari ba tabbss mugaye sunyi yawa har kana gaya masa sunan yaran mutane. Malam meya kawo ka?" Wani acikin samarin ya fada bayan ya haskawa abokin sa harara. Ya mike yana kobara.

"Gaskia ne abunda ka fada. Amma wallahi wallahi wallahi kaji rantsuwa uku ta musulmai? Narantse da Allah ba cutarwa ce ta kawo ni wajen su ba. Hasalima a kofar makarantar su na gano su naso muyi magana tacan ma basu amince ba Kasancewar nayi wautar ce musu suzo na karaso dasu gidah ganin suna maganar kudin motaa da dan sahun Yana bazai kawo su ba... Wallahi Allah ne ya doramun kaunar daya daga cikin su wallahi na kasa samun nutsuwa har sai Dana bjyo bayan mai adaidaita nazo Naga unguwar da sike da gidan su. Domin su dinma yadda ku ka nuna rashin yardar haka suka min basu ma tsaya munyi magana ba daya daga ciki tace zata cika kudin suka hau adaidaita ya kawo su . Ni Kuma bazan iya hakura ba na biyo su nazo... Wannan shine gaskiyar lamarin. Wallahi ba da cutarwa nazo ba alkhairi ne ya kawo ni"

"To Mashaaa Allahu.... sunyi daidai da basu biyo ka dinba don kannenmu ba masu budadden idanu bane. Haka zalika Kai ma kayi kaifin tunani daka biyo su ka gano unguwar ta su."

"Nagode Allah ya saka da alkhairi"

Ya dan sosa keyar sa... Yana so ya sake cewa wani abun Amma sun masa kwarjini ya tsiri juyawa Yana kallon motar sa

Ganin hakan yasa daya daga cikin samarin da suke zaune yace wa na tsayen da sukai magana dashi,

"Kune Yan uwa da yaran Nan gwara ku koma gefe kayi magana da shi Naga kaman yanaso ya sake cewa wani abun Amma Yana jin kunya"

"Aboki na muje ko?" Ya fada Yana nuna masa can gefe suka tsaya.

"Nagode kamar kuwa kasan kwarjini kuka mun na kasa karasa zancen dana fara"

"Allah sarki Ina sauraron ka"

"Wato azahirin gaskia Allah ya dasamun kaunar daya daga cikin Yan biyin nan. Kuma ba da Wasa nazo ba aurenta kawai nake so nayi Domin ashiriye nake Ni dama agidaah ana ta cewa na kawo matar aure zaman jiran me nake yi..."

"Allah sarki Allah ya temaka"

"Aameen Yaa Allah.... Sunana Ahsan Jamil Gwanzamu. Kuma ni ma'aikaci ne a ma'aikatar federal inland revenue service... Gidan mu yana unguwar Dex crescent 2...."

"Masha Allahu... Sunan mahaifin ka ai ba boyayye bane ma a garin nan kowa yasan Alhaji Jamil Gwanzamu saboda temakon sa da alkhairai da yakewa talakawa Allah ya biya shi"

"Amin Aamin..."

"Wato wadannan yan biyu daka biyo da mahaifiyar su da ni uwar mu daya uban mu daya.. 'Yayan yayata ne 'yaya na ne nima... Saafa da Marwaa su kadai Allah ya azurta mahaifiyar su dasu. Yara ne ga malam Muhammad Alhassan . Kuma ba masu kudi bane domin duk tashi fadi ake gaba daya dai Allah Yana rufa asiri ne Alhamdulillah. Kuma ganin ka fito daga babban gidah irin wannan kaskanci ne awajen ku masu hannu da shuni kuke kula kananan masu karfi haka. Don zuri'ar mu ba muda karfi gaba da baya... Wadatar zuciyaa ce kawai"

"Assha ka dai na cewa haka. Da talaka da Mai kudi duk matsayi daya sike awajen Allah... Ta iya yiwuwa ma wani talakan yafi wani Mai kudin matsiyaci awajen Allah. Dukiya ai shirme ce watadar za itace komai. Iyaye na ma baza su hanamuu ba mu a zuri'ar mu baa haka.."

"Kasan wasu masu kudin auren kwarya tabi kwarya zuke. Idan an auro musu talaka ma sai kaga ana renata a dangi ana nuni da mata zunde. Irin wannan ne muke gudu gaskia gwara daidai ruwa daidai tsaki"

"Wallahi aboki na bada Wasa nake ba. Kuma bama wulakanta Dan Adam ko Yaya suke. Nima iyayen nawa ba tashi sukayi cikin kudi ba. Allah ne ya hore musu lokaci daya. Kabar fadar haka. I promised to be an excellent lover, husband and family ."

"To Mashaaa Allah. Sai dai wani hanzari ba guduu ba. Sai idan har wacce kake so din batada wani data zaba tana so. Don idan tanada saurayi sai dai kayi hakuri gaskia baa auren dole adangin namu"

"Ba matsala... Duk decision din da aka yanke.. na amsa da hannu biyu"

"Wacce ce daga ciki Saafa ko Marwaa?"

"Wadda dai ta shige cikin gidan ta karshe"

"Kaman marwa ce kaman kuma Saafa"

"Turkashi...."

Adamu yayi murmushi yace,

"Ina zuwa..."
Cikin gidah ya shige da sauri. Ahsan Yana tsaye Yana duban kofar gidan shi dai

Ko da ya shiga dakin malama zuwaira ya wuce. Su Saafa har sun sauya uniform din sun zura atanfa iri daya suna cin danwake...

Suka gayshe shi ya amsa. Ya gayshe da yayar tasa shima. Ya fada mata dukkanin abunda ya faru. Take sanar dashi dama yanzun suka gama gaya mata suma yadda komai ya kasance tun farkon biyo su dayayi a kofar school..

"Yanzu dai bari a gama dashi don yana tsaye a waje..Wacece ta shigo daga karshe acikin ku?"

Marwa tayi hanzarin nuna Saafa tace,

"Gata nan don ni na fara shigowa na bar su day Aisha"

"Ba wani itace nan kawu adamu... Marwaa ce tashigo a karshe"

Kawu adamu ya grigiza Kai kawai ya sake tambaya har sau biyu kowacce ta Musa ba ita bace. Yamike tsaya Yana nuna su yace,

"Zuro hijaban ku kuzo yan renin hankali....


#FREE BOOK
#NOVELLA (SHORT NOVEL) DAN GUNTU NE🤭

®️MX

Continue Reading

You'll Also Like

108K 9.6K 51
Boddo is a Fulani girl, who will be married at young age of 13yrs to the man who she never knew or saw in her life who is also educated.....how will...
148K 14.4K 42
Love story 💞 heart touching 😞 and very emotional 😟☺️ read to find out more.......... On 'YA MACE NOT EDITED ⚠️
1.1M 112K 56
He is the only son of the king Heir to the throne The most selfish and arrogant man you'll ever come across When he speaks everyone listens....... T...
1.5M 25.1K 20
Suxin followed the original plot and played the green-tea villainess role well. But why can't this duck just die in peace?! -- "Bai Suxin, why are yo...