KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TAS...

By missxoxo00

1.6K 85 3

KOWANNE DAN ADAM DA IRIN TASA KADDARAR💯IDAN KA YI HAKURI SAI KA CIMMA NASARA A GABA🤞...One really need not... More

free book🤸
1
2
4
5
6
7
8
9
10
11
12

3

89 8 0
By missxoxo00

       *_KADDARA!!!💔_*
     _KOWA DA IRIN TASA_
              👭👩‍❤️‍👨💍


©️®️ _NANA HAFSATU_
          _(MSS XOXO)_

    _SHAFI NA HUDU_

_Arewabooks:mssxoxo_
_Wattpad:missxoxo00_

_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

___________

  *Ranar* laraba Saafa da Marwaa suka zana jarabawar zangon karatun su na karshe na matakin babbar sakandire.. paper chemistry da ita suka karashe. Fuskokin daliban baki daya kumshe suke da farin ciki marar misaltuwa na yau suma burikan su sun cika sunyi candy..

Sukai ta ife ife bayan sun gama zana jarabawar. cike da maduakakin farin ciki kuma suka shiga musayar sunayen su suna rubutawa da marker ajikin hijaban su.. wato signout..

Su dai malaman sai bin su kawai sike da kallo, suna masu taya su murna.

Headmaster ta tsawatar musu ganin sun dauki tiyo suna jika jikin su da ruwa . Ta dauki lasifika ta shedawa kowannen su ya saurara...

Ta shiga yi musu nasihar ban kwana mai ratsa jiki da yadda kowannen su zai cigaba da rayuwa bayan makaranta. Kowanne ya karbi rayuwar da Allah ya dora masà ita ya yita cikin lumana bisa tafarkin tsira.

Bayan ta gama jawabi, daya bayan daya malaman kowanne ya shiga tofa albarkacin bakin sa. An kuma yaba sosai kan kwazo da hadin kai da yan ajin suke da shi.

Daga karshe aka kira headgirl tazo tayi bayanin sallama ta kuma bawa dalibai yan uwanta shawara.

Malama Batula, malamar physics dinsu itace ta sake Kiran sunan Saafa a Karo na biyu Kan tazo tayi jawabin bankwana a matsayin ta na headgirl din makarantar Kuma ta ajin karshe da suka kammala.

"Ina headgirl dinne? Saafa Muhammad  Alhassan.... "

"Malama! Ga Ni"

"Yauwa karaso ki karba"

Saafa ta sauke zuciya. Gabanta na tsananta bugawa. Marwaa ta daga mata Kai da mata jinjina da hannu alaman karfafa mata gwiwar zata iya..

Saafa ta karasa kan tudun da malaman sike a tsattsaye yayinda daliban ke tsaye daga kasa suna kallon su. Ta karbi lasufikar tana gyaran murya tace,

"Assalamu alaikum wa rahamatu Allah... Ya Yan uwana"

Suka amsa sallamar tata da karfi. Ta cigaba da cewa,

"Dukkan yabo ya tabbata ga Allah mamallakin kowa da komai. Kamar yau mika fara karatu gashi cikin ikon sa da kudirar sa mun kammala lafiya alhamdulillah. Muna rokon Allah yasa mun gama jarabawar nan a sa'a Allah Kuma ya bamu sakamako mekyau ya mana zabi nagari a rayuwar mu ta gaba. Malaman mu ubangiji Allah ya shi musu albarka ya biya musu dukkanin bukatun su . Bamuda bakin godiya agare su sai da mu roki Allah ya biya su da gidan aljanna madaukakiya. Allah Kuma ya sakawa da iyayen mu alkhairi da duk wasu da suka temakawa karatun mu da tarin alkhairi.... Allah yafee mana gaba daya. Dukkanin mu masu lefi ne bare mu perfects dole mun batawa wani Ina neman afuwar dukkanin ku na Kuma yafewa kowa nii. Allah yabamu sakamako meyau mu dora agaba. Ya mana zabi nagari"

"Amin" daliban da malaman suka amsa baki daya..

Saafa zata mika lasifika ta sauka headmster tace da ita,

"Headgirl yanzu wani matakin na gaba Zaki dauka.. aure ne ko karatu?"

Saafa tayi murmushi kanta akasa tace,

"Allah shine mafi sanin komai... Kana zabin ka ALLAH na nasa, na Allah Kuma shine dai dai, KADDARA.. KOWA DA IRIN TASA... Ina fatan Allah ya kadarta mana sauran rayuwar mu da inganci mai tattare da fatan alkhairi da albarka Amin"

"Amin Saafa kinyi magana mekyau...Dadi na dake damaa akwai hankali.. toh Allah ya muku zabi nagari dukkanin ku inda zamuyi alfahari aduk inda muka shiga mu bigi kirji muce eh wadannan yaran 'yayan mu ne kuma daliban mu ne.."

"Amin malama... Amin"

"Mu tafa mata dan Allah... Saafa sannun ku da kokari da dawainiyar da kuke dake da sauran prefects gaba daya da yan uwan ku daliban duka"

"Amin malama..." Sika hada baki wajen amsa ta"

"Indo halliru ke fa me kikeso ki zama likita ko lauya ko maaikaciyar banki?"

Indo halliru ta kece da dariya tana matse hanci tace,

"A/b/u mai labile dai malama"

Dalibai suka fashe da shewa suna tafa hannuwa. Jin indo tana nufin aure takeson tayi ita...

"To Allah ya sa hakan ne yafi alkhairi Allah Kuma ya aurar da ku dika Amin"

"Marwa ke fa?"

"Maaikaciyar lafiya..."

"To Allah ya tabbatar da alkhairi Amin"

"Zulaiha ke fa?"

"Banker nake so..."

Haka dai daya bayan daya headamaster ta shiga tambayar su suna amsawa. Wasun su suna son su cigaba da karatu ne a jami'u da kolejojin ilimi sauran Kuma aure suke so suyi. Duka aka hada aka musu fatan alkhairi. Malaman suka bisu da adduoi akayi hotuna a wayar malaman da wayoyin wasu daga cikin daliban sannan kowa ya watse ya kama hanyar gidah....

    Ko da suka koma gidah nanma ummy da sauran abokan arziki da yan gidan sun tattaya su murna.

Ummy dan karfin hali ma zakaran da take kiwatawa ma ta yanka tayi miya ta dafa shinkafa da salak. Sukaci sika koshi harda Karin tiara data hada yasha kankara itama. Ranar dai kamar sallah haka suke jin ta. Ummy ma farin ciki baki daya ya mamayeta yaran nata sun Kare karatun sakandire. Domin tanason suyi karatu shysa ta tsaya tsayin daka wajen basu gudunmuwa dikkuwa da makarantar gwamnati sukeyi kamar sauran yaran talakawa marasa shi..

Sannu a hankali haka rayuwar tacigaba da garawa. Makarantar tahfiz ma sunyi sauka data dare. Ummy ta sake yanko musu form din wata islamiyar ta saka su anan tsallaken unguwar tasu.

Sakamakon jarabawar tasu ya futo sun cinye duka fiye da yadda suke zato. Sosai sakamakon result din yayi kyau don kowane gurbi sike so zasu samu.

Sun samu gurbin matakin karatu a school of nursing and midwifery. Tuni har sun fara lectures ma gwanin ban shaawa

Uniform dinsu riga da wando da hijabi dik farare. Ummy ta saya musu takalmi kowa daya sau ciki baki sai jaka ta ratayawa itama guda daya daya.

Sun mayar da hankukan su sosai wajen yin karatun tukuri suna Kuma kokarin zuwa makarantar da wuri su uku sika samu gurbin karatun a layin su. Su biyu sai Aisha Mudi kawar su.

     ::::::::::::

 
Kamar ko da yaushe bayan sun kammala lectures dinsu suka tafi bakin titi don tarar abun hawa..

Aisha ce a tsakiyar su gefe da gefe Kuma Saafa da Marwaa ne. Suna tafe suna hirar karatun su na ranar..

"Gaskia naji dadin lectures din nursing fundamentals.. Ba karya malamar nan ta iya koyarwa" Marwaa ta fada tana duba yar jotter hannun ta

"Gaskia nima tamun dadi.." Cewar Aisha

"Ba lefi kam, Amma nafi son pharmacology.." Saafa ta fada itama

Haka dai suka yita hirarrakin su suna bitar karatun dake abun hawa na dan wahala, Kasancewar makarantar tayi cikin lungun titi kadan, masu adaidauta sahu na wahala.

Cikin haka sai ga Faysal dan ajin su Kuma classrep ya taho da sauri har Yana hadawa da gudu. Yana karasawa Aisha ta kyalkyale da daria tana tsokanar sa tace,

"Sister kenan...sister Faysal ... Nurse sister  Faysal..."

Faysal yà girgiza mata Kai Kawai yana murmushi ya dubi Marwaa yace,

"Habibty bami sallama ba zaki tafi?.... Babbar Yaya Ina gaisuwa"

Ya daga hannu yana sarawa Saafa tayi murmushi tace dashi,

"Na amsa da hannu dubu in-law...."

"Gaskia minti uku mika baku" Cewar Aisha ....Taja hannun Saafa suka San matsa gaba.

"Godiya mu ke sister Indo..." Cewar Faysal

Ya saka hannu ya sosa keyar sa yana bin marwa da kallo tamkar zai mayar da ita cikin sa saboda tsabar yadda yake jin kaunar ta cikin ran sa.. cikin wata iriyar murya ya karya ta yace,

"Ya kike... Uhm?" Ya fada yana dan rankwafawa wajen fuskar ta taja baya da sauri tana murmushi

"Meye haka?"

"Kaunar ki ce ta jawo hakan..... Shine Zaki tafi baki jira na muku rakiya titin ba yau?" Marwaa habibty.... Kinyi shiru?"

"Bangan ka ba shi yasa"

"Kunfa wuce ni ta gaban cafeteria kuma dai mun hada idanu ma..."

"Ayya..."

"Ina kaunar ki sosai Marwaa..."

"Nagode"

"Meye haka?"

"Me zance?"

"Ki ce, Nima Ina son ka mana"

Tayi murmushi tana kare bakinta da jotter hannun ta..

Wayar sa ce tayi Kara ya dauka ya kara a kunnen sa,

"Okay sir.. gani nan"

"Sai anjima"

"Kai daman so kike na tafi? Habibty ki dena haka. Malam yunus ne yake Kirana Zan bashi attendance sheet.. Soo Bari na je... Bye take care.. I love you"

"Bye...love you too"

"Yauwa yar garin, yau zan kwana Ina murmushi... Bye"

Ya dagawa su Saafa hannu ya koma makaranta da sauri. Ita Kuma ta nufi wajen su Aisha sunata tsokanar ta

Suna tsaye cikin ikon Allah sai ga empty adaidauta sahu ba kowa aciki da sauri suka tare shi suka fara ciniki.

     ***Tun daga nesa yake hango su, Tafiya yake ahankali cikin motar sa kalar sararin samaniya..... Ya kasa janye idanun sa daga kanta, Har adaidaita sahu ya tsaya a saitin su ya kare masa fuskar ta. Sai kokarin juyar da Kai yake dayan gefen yadda zai hango ta hanun sa daya akan sitiyari, saura kadan ya culla motar tasa a rami tsabar hankalin sa da kallon sa kacakom ya tattara ya dora akanta...

Dakyar ya saisaita kansa ya kara gudu ya cinma bayan adaidaita sahun ya faka motar da sauri ya fito yana.....











®️MX

Continue Reading

You'll Also Like

26.1K 674 13
THIS ISNT MY FANFIC IT IS OWNED AND MADE BY "starsthatlinethesky" ON AO3 I WANTED TO PUT IT ON WATTPAD INCASE OTHERS LIKED THE BLACK PHONE (2022) SCE...
54.2K 3.1K 50
Na kasa fahimta da gasgata abinda zuciyata ke ayyana mini a kansa, SO ne ko BIRGEWA?. Komai nasa birgeni yake, ban taɓa ji ko ganin wanda ya haɗa abu...
8.3K 152 13
Labari ne akan wani rich,young and handsome dr whose mother is igbo by tribe while his father a Fulani..duk dunia babu qabilan daya tsana kaman Hausa...
3.9K 188 11
Labarin wata ba fulatanar budurwa mai suna FANTA! Da matashin saurayin ta MAHBUB dan birni😉 Written by MISS XOXO and NAFEE ANKA😍 (2016...)