KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TAS...

By missxoxo00

2.5K 96 3

KOWANNE DAN ADAM DA IRIN TASA KADDARAR💯IDAN KA YI HAKURI SAI KA CIMMA NASARA A GABA🤞...One really need not... More

free book🤸
1
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12

2

161 9 0
By missxoxo00

*_KADDARA!!!💔_*
     _KOWA DA IRIN TASA_
              👭👩‍❤️‍👨💍


©️®️ _NANA HAFSATU_
          _(MSS XOXO)_

    _SHAFI NA BIYU_

_ADVERT👇_

_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

   :::::::::::::::

*** *Zulfa'u* ta shige daki zuruf... Adabiyya mahaifiyar ta ta bi bayanta da sauri ita da Hamdiyya.

Malama zuwaira kamar ko da yaushe ganin hakan yasa ta dan daga murya daga cikin daki da take tana kiran yaranta

"Safaa ku shigo da tabarmar nan dare yaja dama"

"Tohm Ummy.."

"Maman Safaa ba dai har kwanciya ba?"

"Dare yayi aunty amarya shi yasa"

"Toh shikenan Allah ya tashe mu lafiya nima bari na tafi"

Wadda malama zuwaira ta kira da aunty amaria itama ta nannade yar tabarmar ta tayi cikin dakin ta.

"Rage hasken fitilar nan Safaa"

"Tohm Ummy..."

Marwa ta sake makalewa a yar katitar su zatayi bacci. Malama zuwaira ta dubi saafa dake dauke da littafan su su biyu kamar ko da yaushe zata musu aikin gidan da aka basu a makarantar boko.

Ta daga hannu ta dada mata duka a dundu marwa ta mike da sauri tana shafa wajen,

"Wayyo Allah na ummy menayi?"

"Haba marwa ke kullum ba zaki wa kanki fada ba! Ki dinga tausayin yar uwar ki Mana, kullum itace ke muku duk ayyukanda ake baku a makarantar haba marwa."

"Ummy dan Allah kiyi hakuri.. itama tana tayani a makarantar a aji. " Saafa ta fada tana murmushi

Marwa sai kunkuni take tana cuno baki gaba,

"Zaki saki bakin ki ko sai na taso na hambare ki?"

"Yi hakuri ummy"

   Adabiyya ta fito daga daki tana ta tauna kashin kaza. Hannun ta rike da fika fiki biyu na gas meat tayi dakin su Saafa,

"Salamu alaikum ko kunyi bacci ne?"

"Waalykm Salam a muna shirin yi dai"

"Gashi ba yawa kamar ko yaushe saurayin zulfa'u ne ya kawo"

"Wlh da an barshi adabiya.. "

"Rike mana ai nama hakki ne dashi, ko ba zaki ci ba ai kya dan rabawa yaran nan"

"Toh shikenan angode. Rike ki raba muku marwa"

Adabiya ta fita daga dakin tayi wajen rijiya tana waka,

"Kujerar tsakar gidah......"

Amarya na jiyo ta tana dariya kawai ta fito daga daki ta dasa kujerar ta a kofar daki ta zauna..

Adabiya ta dubeta tayi yatsina ta koma dakin ta. Cikin haka sai ga dawowar Malam mai gidan. Ya doka sallama yana haskawa da yar cocilan din sa. Ya tura kofar ya rufe gidan.

"Malam ka dawo....?" Amarya ta karasa wajen sa tana riko hannun sa.

Adabiya dake leken su ta window ta gatsina fuska tana hararo ta

Amaria ta kwantar da kanta akan kafadar malam hannun ta daya kan gemun sa tace,

"Malam nayi kewar ka..... Tun dazu nake jiran ka"

Malam ya dashare baki kamar gonar auduga yana riko hannun nata yace,

"Nima hakan take awaje na..."

Wuff sai ga adabiya a tsakiyar su tana harzuka tamkar zata fashe

"Banason salon bariki... Da daren nan a bainar jamaa. Malam gotai gotai da Kai iyalin ka najiyo ku fisabilillahi meye hakan?"

Aunty amarya ta watsa mata harara taja hannun malam sukayi daki sika bar adabiya a tsaye tanata surfa masifa ita kadai..

Ta nufi kofar dakin malama zuwaira ta dage asaberin dakin cike da tsatsar bacin rai tace,

"Ke wallahi zuwaira Kamar sallamammiya. Kullum idan ana abu sai ki dinga yin shiru"

"To antun su mai zance meya faru?"

"Bangane meye faru ba? Kullum kina ganin wannan kalatacciyar rayuwar itace  ke cigaba da faruwa agidan nan. Matar nan tunda tazo ta sake sukurkurta malam dama can daya shima baisan hakkin iyalin sa da ke kansa ba. Kinga barikin da ta tsaya a saitin daki na tanayi"

"Dan allah addabiya ki bar zancen nan haka nan kije ki kwanta kema. Allah ya shiga lamarin"

"Hmm zuwaira kenan.. kishiyar nan dai ke akayiwa ba ni ba, Domin ni ke aka karowa, Ke kuma ita, meyakwan ma ace ke da jin haushi da kishi a'a sai ni ko da yaushe. Ke Kika sani"

"Allah ya baki hakuri..."

Adabiyya ta saki tsaki ta juya ta shige dakin ta... Safaa da marwa dai sukayi shiru basu ce komai ba kansu akan littafan su suna yin aikin gidah (homework/assignment) da aka ba su

Bayan sun gama suka ci abinci suka karanta alqur'ani sukayi alwala sika kwanta.

Malama zuwaira na zaune akan sallaya tana jan carbi kamar ko da yaushe sai data gama itama ta kwanta... Tsakiyar dare ta farka tayo  tsarki ta yi sallar dare har ya zuwa sanda aka Kira asubahi bata koma ba. Ta tashi yaran sukayi sallah sika koma bacci ita kuma tana zaune tanata addu'oin ta.

   Bayan gari ya waye.... Malama zuwaira ta sake tashin su Marwaa.

"Ummy Ina kwana?"

"Ummy Ina kwana?"

"Lafiya kalau yan albarka... Kun tashi lafiya?"

"Alhamdulillah ummy"

"Alhamdulillah"

"Toh mashaa Allah... Ga ragowar canji nan akan samira ku karbo koko da kosan gidan Lantana sai ku biya shagon hashiru ku sayo sikari kuyi sauri ku karya ku tafi makarantar"

"Tohm ummy"

Fita sukayi atare. kayan su iri daya nan da nan suka wuce gidan kokon suka sayo suka biya shagon  ma suka sayo sikari sanan suka koma gidah.

Wanka Safaa ta shiga tayo bayan ta gama marawa ma tayi... Sannan suka karya suka shirya zuwa kayan makarantar suna ta sauri .

"Kunje jun gayda malam ne?"

"Mun kusa makara fa ummy... Kuma ba ma lalle ya amsa ba. Ko mu bari adawowa mu tsaya majalisar su..."

"Kinga marwa kar ki bari na tashi na hanbare ki. Zaki wuce ku gayda shi ko sai na tashi"

"Allah yabaki hakuri ummy"

"Bari muje mu gayda shi.. sai mun dawo" saafa ta fada tana riko hannun marwa .

"Ungo ku rike kowa ashirin da biyar biyar kenan.."

"Mungode ummy"

"Mungode ummy"

"Kuyi sauri Allah yabada saar karatu yasa albarka Allah juma ya tsare ku Amin"

Zasu shiga dakin aunty amaria sai ga futowar malam mahafin na su da aswaki a bakinsa suka tsugunna har kasa kamar ko da yaushe cikin biyayya suka gayda shi,

Ya dube su ya dauke kansa... Dakyar kamar ba zai amsa ba yace,

"Lafiya Lau"

Mikewa sukai domin idan da sabo sun saba.. Tamkar ba yayan sa na cikin sa ba..

Suka sake lekawa dakin mahaifiyar su suka mata sallama sun tafi, ta amsa tana sake binsu da adduar Allah ya dawo da su lafiya..

Kan hanyar su ta tafiya makaranta kabiru ya hango su. Sanye yake shima cikin uniform dinsa ya musu karin guga. Ya rike yan littafan sa a hannu da biro . Kansa da hular sa ta prefect..

"Safaa." Ya fada yana daga musu hannu.

Marwa na hango shi ta saki tsaki tana jan hannun saafa,

"Yasin kina tsayawa makara zamuyi"

"Gaisawa fa kawai zamuyi"

"Sai ki gaisa ai... Ni na tafi.......

"Marwaa ya gidah?" Kabiru ya daga murya sosai yadda zata juyo shi..

"Lafiya Lau ta amsa shi tana yin gaba abun ta bata juya ba.."

Saafa tabu bayan ta da sauri tana jefawa kabiru murmushi bayan sun gaysa.

Haka suka karasa makarantar sunci sa'a basu makara ba. Amman Marwaa tasha dukan dorina awajen malamin science dinsu ya musu duka itada firdausi da sukayi fada ana koya musu practical...ko ajikin ta kuwa dukan data sha domin ta saba alakada mata na jaki a boko da islamiya saboda rashin jin ta... Tanada kokari sosai idan ta mayar da hankali amman wasa da tsokana sun mata yawa... Dan wani fadan ma ba da ita ake ba take sayen sa ya dawo kan ta..

Mahaifiyar su malama zuwaira ta tsaya tsayin daka akan su wajen ganin sun samu ingantacciyar rayuwar islama da kuma boko.

Kauyen su take zuwa ta saro kayan kauye da su mai da manja ta sayar. Tana kuma yin kitso na kudi..Ta haka take samu ta rufawa rayuwar ta da yaranta asiri. Tana zaune ne kawai agidan zaman yaranta. Domin ko kadan mai gidan nasu bai san hakkokin iyalan sa dake kansa ba... Babu ruwan sa da kowacce iriyar rayuwar da zasu jefa kansu aciki..

   Haka rayuwar Saafa da Marwaa taci gaba da garawa.. Har Allah ya kawo ranar larabar da suka zana jarabawar su ta karshe a makarantar government girls science college Danken.

Kyawun su ya kara fitowa da haskakawa.... Sun sake zama yammata sosai. Kamar su daya wato identical twins. Kana kallon su kasan yan biyu ne.. saboda tsananin kamar su. Wanda ba sanin su yayi sosai ba, Ba zai gane wacece Saafa ba ko Marwaa.....

©️MX

Continue Reading

You'll Also Like

1.9M 96.9K 35
[Historical Reincarnation Series : Book 1] ※THIS IS AN ORIGINAL STORY. #RAYV: About a gentle kindergarten employee that was reincarnated in a mysteri...
1.8M 114K 166
Choose me or Lose me ? I don't want to be your second CHOICE ! Start Date : 4th Feb 2022 End Date : 4th Nov 2022
804K 78.4K 78
[UNDER EDITING] BASED ON A HAUSA LIFESTYLE. --- "Too bad you're mine and you have no choice but to stick with me" --- Umar Kashim is rich, and from h...
1M 119K 68
{Completed} Jawahir Malik Zayyad, the last thing she expected to happen to her is getting married. Especially when she has just finished high school...