GENERAL NASEER ZAKI (Book 1)

By Azizat_Hamza

3.8K 216 8

When a wounded soldier falls in love... Naseer Zaki Soja ne sa mazaje gudu. Aikin Soja a jininsa ya ke. Bashi... More

coming soon!
chapter one
chapter three
chapter four
chapter five
chapter six
chapter seven
eight
nine
ten
eleven
twelve
thirteen
fourteen
fifteen
sixteen
seventeen
eighteen
nineteen
Twenty
Twenty one
audio book available

chapter two

223 11 0
By Azizat_Hamza

*GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)

Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat

                           Page 002



                           *1995, AZARE*

Iya Abu ke zaune a ƙofar ɗakinta, tana ƙoƙarin saita rediyo dan ta kamo labaran yammaci. Rediyon sai shiiii shiiii shiiii yake alamar dai ba a kamo setin tasha ba.
Ta sa hannu ta fara bubbuga rediyon dan ta ɗan fara jin alamar magana amma ƙaran ya hana maganar fitowa.

Ta buɗe bayan rediyon batiran ciki sun kumbura har sun fara baƙi-baƙi. Ta ciro su ta ɗan bubbugasu ta sa harshe ta ɗanɗani saman batiran, ɗan garɗin sinadatin acid da ta ji ya tabbatar mata batiran da sauran ƙarfinsu. Gashi rana ta yi sanyi balle ta saka su a rana.  Ta dai sake bubbuga batiran sannan ta maida su cikin rediyon ta kunna. Wani murmushi ya suɓuto mata lokacin da ta ji ta fara jin magana da kyau ba kamar ɗazu ba.

Ta miƙar da ƙafanta kan tabarma tana riƙe da rediyon dai-dai kunnenta. An riga an gama karanto kanun labarai dan haka dole ta nitsu ta ji ko za a ambaci maganar hutun 'yan makaranta.
Ai kuwa cikin labaran da ake ta ji ana maganar gobe za a kammala jarrabawar 'yan Sakandare ta WAEC inda kwamishinan ilimi ke jinjinawa waɗanda suka samu damar rubuta jarrabawar sannan ya musu fatan samun nasara.

Alhamdulillahi ta faɗa, zuciyarta wasai. Nasirunta ya kusa dawowa.

"Salama Alekum" wata yarinya da ba zata fi shekara takwas zuwa tara ba ta shigo cikin gidan.

Iya Abu ta amsa sallamar tana ajiye Rediyonta a gefe

"Iya Abu wai inji Mamana a bani Omo da gishiri"
Yarinyar ta miƙawa Iya Abu sabuwar naira biyar, ta karɓi kuɗin ta shige cikin ɗaki ta ɗauko wata fanteka da ke ɗauke da hoton General Sani Abatcha.

"Ungo" ta miƙa mata ƙullin gishiri da ƙullin omo.
"Ki cewa Mamanki babu canji, ki dawo anjima ki karɓa"

Yarinyar ta karɓi saƙonta ta fice da gudu.

Iya Abu ta gyara zamanta ta shiga lissafta sauran kayan nata. Gobe dole ta aiki Malam ya siyo mata kwanon gishiri a kasuwa saboda ƙulli ɗaya ya rage.
Ta duba  daddawa da kuka ta ga da sauransu. Gishiri ne da sugar suka ƙare.

Bayan ta gama lissafi ta maida fantekarta cikin ɗaki ta shiga madafarsu wanda ke can gefe ta wajen rijiya. Ruwan miyanta ya tafasa ƙwarai yadda take so. Ta zauna a wata ƙaramar kujera ta fara kaɗa miya. Babu nama ko kifi a cikin miyar amma yadda miyar ta ji daddawa da citta da wake gaba ɗaya sai ƙanshi take.

Iya Abu na cikin rarraba abinci yaran gidan suka fara shigowa da sallama sun dawo daga makarantan Allo.
Hauwa'u da Hussaina suka shigo suka gaisheta kafin suka wuce ɗaki. Sauran kam sai da suka shiga ɗaki suka cire gyalensu tukunna suka fito suna yi mata sannu.

Da dare bayan Isha'i suna zaune a ƙofar ɗaki akan tabarma, yaran na cin abinci yayinda Iya Abu ke ta fama da bubbuga Rediyonta. Dole dai ta faɗawa Malam ya siya mata sabon batir.

Iya Abu akwai son jin Rediyo. Rediyon Malam ne amma saboda yadda take amfani da ita sai ya haƙura ya bar mata.  Safe, rana, dare ba zaka raba Iya Abu da Rediyo ba.
Sauraron Rediyo ya rabata da shiga sha'anin 'yan gidansu. Ba zaka taɓa ji wai tana balbalin wata ana gulma da ita ba. Idan Malam ya fita kasuwa, yaran suka je Makaranta Rediyon ke ɗebe mata kewa.

Haruna yaron maƙocinsu ya shigo wai ance ya karɓo tuwo.
Iya Abu ta miƙe ta shige ɗaki ta ɗauko abincin Malam ta bawa yaron. Abincin dare kam tunda ta auri Malam shi da maƙocinsa da ƙaninsa Basiru suke zama su ci.

"Iya Abu kin ga Hussaina tana ƙaton loma ko"

"Wallahi ban yi ba, ƙarya take" Hussaina ta faɗa tana sake kai ƙaton loman tuwo bakinta.

"Ban hana ku magana idan ana cin abinci ba"

"Iya Abu ita ta fara" Hussaina ta faɗa tana nuna Hassana.

"To ya isa"

Yaran suka cigaba da cin abinci suna magana ƙasa-ƙasa.

Lokacin da Iya Abu ta miƙe za ta shiga ɗaki  ɗan cikinta ya wani juya.
Ta ɗan tsaya kaɗan kafin ta shiga ɗakin. Ita kam kunyar cikin take ji.
Yo abun kunya ne ace ita da 'yarta Indo suna da ciki lokaci guda.
Tun lokacin da ta haifi 'yan biyunta ta sawa ranta ta gama haihuwa. Musamman da Maimuna ta haifa musu jikan fari shekara ɗaya bayan haihuwar 'yan biyunta.
Sai gashi shekara bakwai, bayan ta gama cire rai da sake haihuwa sai ga ciki da rana tsaka. Ita kanta sai da cikin ya shiga wata na uku ta tabbatar ciki gareta. Ko Malam ɓoye masa ta yi sai da cikin ya girma sosai ya lura da cikin.
Wani abu da idan ta tuna yake ɗan sanyaya mata rai shine yiwuwar sake haihuwar ɗa namiji. Har cikin sallolinta addu'ar da take kenan Allah yasa wannan abinda ke cikinta ya kasance namiji.

Haihuwa goma amma dukkansu mata sai guda ɗaya tal, shi kaɗai namiji cikin mata tara.
Tun tana haihuwa tana tunanin namiji har ta cire rai da sake haihuwar namiji. Ɗayan dai da Allah ya bata kenan Muhammadu Nasiru. Amma bayan shekaru  wannan cikin ya sake sa mata kwaɗayin haihuwar namiji.

Kusan ƙarfe goma saura na dare Malam ya shigo gida bayan ya gama hira da abokansa a ƙofar gida.

Kafin su kwanta Iya Abu ke labarta masa cewa ta ji a labarai ana cewa an kusa gama jarrabawar Sakandare dan haka Nasiru ya kusa dawowa gida. Haka dai suka ɗan taɓa hira kafin suka kwanta.

***

Malam Muhammad Zaki ɗan Asalin garin Zaki ne wanda kasuwanci ya dawo da shi cikin garin Azare da zama.

Mahaifinsa babban Malami ne a garinsu.  Su shida Babansu ya haifa, biyu mata, huɗu maza.
Tun yana yaro da yai karatu a hannun Mahaifinsa sai da ya kai shekara goma shauku aka tura shi gaban wani Malami wai shi Malam Yusufa a garin Chinade. A nan ya shekara bakwai yana karatu kafin ya dawo gida bayan Malaminsa Malam Yusufa ya bashi 'yarsa ta uku mai suna Zainabu da suke kira da Abu.

Malam Muhammad na da shekara ishirin da ɗaya yayinda Abu ke da shekara shahuɗu aka ɗaura musu aure.
Lokacin da suka dawo Zaki abubuwa babu sauƙi dan kuwa Mahaifinsa ke ciyar da su. Da wannan Muhammad ya shiga garin Azare ya fara zama wajen wani ɗalibin Babansa yana koyon kasuwanci.
Haka dai har ya tara jari shima ya zo ya zauna zaman kansa.
Daga haka da abubuwa suka fara kyau sai ya ɗauko ƙaninsa Basiru, suka fara kasuwancin tare.
Allah kuwa ya yiwa kasuwar Albarka dan kuwa har fili ya siya ya gina gida shima Basiru da yai aure ya gina gidansa a filin da yayansa ya bashi kyauta.

Lokaci guda kuwa karayar arziƙi ta faɗa kan Malam Muhammadu. Daga nan kuma ya hau jinya. Mutane dayawa na faɗin wani abokinsa mai suna Malam Hamisu ne ya masa asiri, amma bai taɓa yarda da hakan ba duk da akwai alamu da suke nuna yiwuwar hakan. Dan kuwa tunda ya fara jinyar Malam Hamisu ya ɗage ƙafa daga gidansa. Wasu kuɗaɗensa da ya bashi aro duka babu su, kuma Malam Muhammadun ya kasa tambayarsa ina kuɗin.

Sai da Malam yai jinyar sama da shekara biyu kafin Allah ya tashi kafaɗarsa.

Bayan ya samu lafiya sai ya koma harkan noma gadan-gadan. Akwai rufin asiri kam, amma ba kamar da ba. Musamman ma da iyali suka fara yawa gashi mahaifinsa ya rasu shi ke kula da mahaifiyarsu da ƙannensa.

Wannan rufin asiri shi ya kawo su ga wannan lokaci, babu arziƙin amma akwai wadata da kwanciyar hankali.
Yanzu haka yana taɓa noma da kasuwanci kuma Alhamdulillahi ya fi ƙarfin roƙo.

Allah ya Azurta Malam Muhammadu da 'ya'ya goma. 'Ya'ya huɗu Abu ta haiho duka mata kafin aka samu namiji.
Sai da aka samu Maimuna, Aisha (Indo), Mariya, da Bintu kafin aka samu Muhammadu Naseer. Daga shi kuma aka sake haifo wasu biyar ɗin duka mata. Hadiza, Hauwa'u, Amina, da kuma 'yan biyu Hassana da Hussaina.

Yayyen Naseer duka an aurar da su. Maimuna aka fara yiwa aure tana gama makarantar Firamare. Daga baya aka haɗa Indo da Mariya aka musu aure, dama shekara ɗaya ne tazarar dake tsakaninsu.
Ita Bintu shekara biyu kenan da aka aurar da ita. Cikin 'ya'yan da aka aurar Bintu ce ba a aurar da ita da wuri ba, dan sai da ta kai shekara shashida kafin aka mata aure.
Ta gama Primary ta yi Form 1-3 kafin Malam yace bokon ya isa haka.

Hadiza da ke bin Naseer ma sai da aka shigo da maganar aurar da ita Naseer yace fau fau a barta ta kammala Sakandare tunda tana son karatu. Dama wani ɗan Baffansu ne ya fito wai yana sonta. Malam da Iya Abu kuwa dama basa iya yiwa Naseer musu saboda yadda suke son ɗan nasu. Har gara ma Malam ya kan ɗauke ido ya masa faɗa wani lokaci, amma Iya Abu sam duk abinda Nasirunta yayi dai-dai ne bata iya masa faɗa.
Kafin ta haifi Naseer, har gorin haihuwar 'ya'ya mata ake mata da aka ga ta haifi huɗu a jere duka mata. Bayan haihuwarsa kuma sauran ma matan ne dan haka shi take gani ta ji cewa yanzu babu mai mata gori. Bata haifi maza dayawa ba, amma Nasirunta ma NAMIJI ne kamar kowanne ɗa namiji...


***

Top-Notch season 3 wannan karan sun zo muku da daɗaɗan labarai guda uku.

NAZNEEN...exquisitely beautiful (Mai Dambu).
BINTUN BATUL (Shatuu).
GENERAL NASEER ZAKI (Azizat)

Za ku samu labarai ukun ta whatsapp a farashin 1300
Ɗaya #500
Biyu #900

Ku tuntuɓe ni ta whatsapp 08137311900.

*Account Details*

0008219237
Jaiz Bank
Azizat Hamza
08137311900

Ko kuma ku bibiyesu a manhajar Arewabooks.

@ Azizat
@Shatuuu095
@maidambu41




Continue Reading

You'll Also Like

10.8K 608 42
labari ne mai cike da cakwalkwalin cakwakiyoyi
416K 16.5K 48
Vikram, a senior officer, prioritizes his duty above all else, much like his father, ACP Rajendra. He has three siblings: one is an officer, and the...
304K 10.9K 53
Anhay Sharma:- Cold business tycoon who is only sweet for his family. He is handsome as hell but loves to stay away from love life. His female employ...
181K 17K 79
"Sickler gare ta, kuma ku kuka ja mata." Ta yi shiru daga nan, dafe da goshinta, tana jin yadda kanta ke sara mata. "A kullum dad'a wayar wa mutane k...