KOWA YA GA ZABUWA...

Von Gureenjo6763

13.9K 1K 46

Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko... Mehr

Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20
Page 21
Part 22
Part 23
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29
Page 31
Page 32
Page 33
Page 34
Page 35
Page 36
Page 37
Page 38
Page 39
Page 40
Page 41
Page 42
Page 43
Page 44
Page 45
Page 46
Page 47

Page 30

287 29 10
Von Gureenjo6763

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 30*

*FREE BOOK*

*Fav sis🥰❤️ wannan page ɗin naki ne I love you ok😘**

**Allah in ga Ruwan comment in ba haka ba tohm ni de Zaku jini a salansa🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️**

Garin yayi lublub kaman hadari Dukda ba hadarin bane sede tarin ni'ima da garin yake dashi shine ya ɓoye ranan a irin wannan lokacin, tana ta kallon hanya Dukda ba tafiya me nisa suka yi ba suka iso wani gaɓar ruwa me cike da tarin boats Parke a bakin gaɓar daga nan kana iya kallon effile tower Tarr sbd ginin da ya riƙe shin a kan ruwan yake.

Buɗe mata kofan da Paul yayi shi ya yanke mata Tunanin abunda ta zo yi anan ɗin, bayan ta sauko ya nuna mata wata mata baturiya yace
"she will guide u ma!"

Tace
"wait! Are you leaving?"

Yace
"yes ma! My work here is to just drop u and go back home"

Kai ta gyaɗa ya shiga motan ya fice kan ta kalli matar dake gaisheta ta amsa, jagora ta mata zuwa wani tamfatsetsen jirgin ruwa me tsananin kyau fari Kal, wani keɓantaccen wuri daga nan sama da yake kawace da tables farare ta ajiye ta tace
"enjoy the view of seine river ma"

Sossai kyaun wurin ya tafi da ita, ko don girman jirgin ne ko kuma don kyaun shi ne yasa bata ji wani alaman tashin inji ba kan ta ankara dae taga jirgin yayi nisa da bakin gaɓar, mikewa tsaye tayi ta taka a hankali ta karasa wurin karafunan jirgin ta rike tana kallo, masha Allah..

Bata taɓa ganin kayatuwar wuri haka ba, waennan karafun na Paris da ake kira effile tower an kawata shi da wuta blue da ja se walwali yake yi, se ta jita a cikin wani ni'ima na musamman wurin yayi shiru hakan ya saka mata peace of mind, zuciyarta blank ba Tunanin komai se kyau da ni'imar kogin.

Bata san iya adadin lokutan da ta dauka a haka ba wata mata daban da na farko ta zo tace
"weldone ma! Oga said it's time for prayer and dressing"

Kallon kayan jikinta tayi me ya faru zata chanza? Bata yi musu ba tabi bayan matar suka dan sauka cikin jirgin kan ta buɗe wani wuri suka shiga, wow ashe akwai wuri haka a jirgi bata taɓa sani ba se yau, parlor ne me ɗauke da ɗaki da kitchen da toilet, kuma komai akwai, tana ta aikin mamaki har ta nuna mata yadda zata yi anfani da bayin ta fice.

Da tayi alwala se ta tsaya kallon madubin bayin tana kallon kanta, lokuta da dama ta kan bace a tunani in zata ɓata lokaci a gaban madubi se ta shiga kokonton itace wannan ko wata me kama da ita, gabaɗaya ta tashi daga wanchan hidayat ramamma me idanu kaman na Mayu ta koma wata classic chic, ita kanta tana son yadda take tafiyar da rayuwar ta da kuma tsarin dressing ɗinta a natse ba hayaniyar kaya se na tsantsar kyau.

Fitowa tayi ta gabatar da sallahn la'asar ɗinta don ta samu sallaya a shimfiɗe da katuwar ƙimar jalbib a cikin ledan shi ta ɓare.

Bayan ta idar matar ta dawo rike da wasu akwatuna guda biyu tace
"permit me to dress you ma!"

Kai ta gyaɗa mata tana kallon ikon Allah, ita fa duk bata san me wannan ɗin yake nufi ba kuma, haka dae ta daure ta yi yadda matar tace a take ta fara rangada mata light nude makeup da yayi mugu mugun blending da skin color ɗinta ya bata wani astonishing color me fusgan hankali.

Red dress ta ciro mata, doguwar riga ce kaman me zuwa promp night haka dress ɗin ya amshe ta Dukda ba ta inda jikinta ya bayyana banda tsagu dake bariyin kafan ta na dama shima se idan ta buɗe kafar sossai ne ake iya kallon skin ɗinta daga cikin net ɗin rigar shima be kai rabin sharaɓarta ba.

coler neck ne kaɗan ne kawai a buɗe se ta saka mata sarkar ta da ta zo dashi da wasu designers ɗan kunne da kyaun su kaɗai ya ishi bayyana tsadarsu suna dauke da back stones daga tsakiya, kanta se ta saka mata cikin wani silk black ɗan kwali da ya zauna sossai a kan nata se black shoes masu Tsai, harda wani black purse, duk wadda ze kalli hidayat a lokacin ze ɗauka irin international celebrity ɗin nan ce saboda kyaun da tayi.

Ita kanta se kallon kanta take a lokacin da aka gama shirin, matar ta feshe ta da turaruka masu sanyin kamshi.

Ta lura matar se duba time take, bata dae ce mata komai ba ta samu wuri ta zauna, se dab karfe biyar da rabi kan tace mata zasu iya fita.

Mikewa tayi da bismillah sbd takalman kafan ta, ji take kaman zasu yarda ita sbd tsinin su hakan ya sauya mata salon tafiya kaman me tafiyar tarwaɗa, sake idanunta tayi tana kwasar kallo sbd yadda saman ya juya mata daga yadda ta shiga ta bari, wow masha Allah, abunda ta furta kenan tana kallon jajayen furrani masu fitanannun kamshi da aka kawata jirgin dashi an yi organizing table da ɗazu ta zauna babu komai kai da wasu varieties na abinci harda cupcakes masu candle iska na ɗan kadawa kaman ze mutu kaman kuma baze mutu ba.

Abunda yafi ɗauke mata hankali kuma shine rana da yake ta kokarin faɗuwa yayi wani haske me kyaun gani bata taɓa sanin haka sunset yake ba, ta shagala da kallon sunset ɗin taji wani ƙara kaman na flying boat yana zuwa daga nesa, a hankali ta sauke idanunta saitin inda take jin ƙaran zuciyarta ne yayi wani kalar tsalle.

The view of him a tsaye ba riga se wata three quarter black yana riding flying boat ɗin cike da tsantsar kwarewa gashi ya fito ta ɓangaren da hasken ranar ke shirin faɗuwa se ya bada wani kalar kyau da ɗaukar hankali, lumshe idanu tayi ta sake buɗewa tabbas shine builded body ɗinshi se wani haske yake, bata san ta ɗan yi gasping ba ta kuma kasa ɗauke idanunta a kanshi har ya iso jikin jirgin da take yayi tsalle ya haye tare da Juyawa ya ja flying boat ɗin ya sa a mazauninshi na cikin babban jirgin.

Se ya juyo suka Haɗa idanu daga inda take tsaye, lumshe nashi yayi ya sake buɗewa she looks so breathtaking to him, kaman kawatacciyar flower dake samun ban ruwa ta fitar da Fure me tsananin kyau da ɗaukar hankali haka ta zama, ji yake kaman ya hadiye ta ko ze huta da bugawar da jijiyoyinshi suke da sunanta.

Cikin tafiyarshi ta xaratan maza yake tunakaro ta hakan yasa tayi kokarin fusgan idanunta daga cikin kwayar nashi se kuma ta saukar a inda ya kusa sumar da ita, don sun sauka ne bisa shafaffen cikinshi wandon shi ya ɗan sauka har kana iya hango v line ɗinshi cikin azama ta sake daukewa se ta rasa takamammen mazaunin da idanunta suke sha'awar kallo bayan shi ɗin.

Wani ash cotton shirt da ya sa aka ajiye mishi a linke a wurin ya ɗauka ya sa kan ya karaso gabanta ya tsaya ya sakar mata shanyayyun idanunshin nan yana yaba kyaun halittar Allah a wurin, ganin ta kasa Kallonshi se kafafunshi da suke kyalli sanadiyar ruwan da ya taɓa su gasu bearfooted take ta kallo yasa yayi anfani da wata kalar murya yace

"diehard!"
Wani irin amsawa kirjinta yayi, tsikar jikinta suka bada wani yaammmmm she started to get confuse bata ɗago ba seda taji ya sake maimaita

"die hard!"
Did he mean da ita yake?

Cikin tsoro ta ɗaga manyan Fararen idanunta da suka ji liner ta zube bisa kanshi seda ya so yayi loosing balance ɗinshi, ya lumshe idanu ya sake budesu a kanta ze yi magana se wani cool music ya fara tashi a cikin jirgin inda ya haɗu da yadda suke ɗin ya tafi da bugun zuciyarsu ya bada wani romantic scene.

A hankali yace
"I know u have so many questions to ask but please do me a favor of keeping mute nd just follow my lead..!"

Yadda yake maganan da sanyi da wani kulawa yasa bata san ta ɗaga kai ba, yayi mata leading to kujerun wurin table ɗin da aka musu ado da jan kyalle, da kanshi ya janyo mata ta zauna kan ya tsaya daga gefenta kaman bawan ta ya shiga serving ɗinta a natse.

Se lumshe idanu take tana sauraren lyrics na wakan dake tashi a hankali zuciyarta ke skipping..
"It's you!
Ur eyes
Ur smile
The way you walk!
The way you talk!
The way you laugh!
I could stare at you forever
I love everything about you!
It's everything..."

Har wani rawa rawa hannunta yake yi tsabar yadda zuciyarta ya matse ya shiga cikin wani wahalalliyar yanayi da ya so mantar da ita komai da kowa a duniya se wannan moment ɗin da shi shi kaɗai.

"Eat die hard"
Da hannunta da yayi sanyi ƙalau tayi anfani ta ɗauki spoon ɗin ta fara cin brown rice da daga yadda yayi serving ma dole ya baka sha'awa, da coconut milkshake.

Tana sa abincin a bakinta ta lumshe idanu daaɗin shi ya haɗu da wakar da ya sauya bugu zuwa wani waka na daban wadda ya fi wanchan zama romantic nd cool inda ya fara daga kalmomi kamar haka

"I don't know how you do what you do...I'm so in love with you..! It just keeps getting better..
I wanna spend the rest of my life with you by my sideee! Forver and ever! Every little thing that you do baby am amazed by you...!"
A hankali take cin abincin kaman me tsoron taunawa.

A natse a kuma tsorace ta ɗago idanunta dake fallasa asirin zuciyarta se suka Haɗa idanu yayi relaxing just watching at her giving him goosebumps from the sunlight reflection, how he wish she's already married to him! Har wani lumshewa idanunshi suke suna buɗewa da kansu.

Da kyar ta iya mishi alaman shifa? Idanu ya ɗan kaɗa mata alamun nah he just want to keep staring at her amusingly..

Ba sakon kaɗai ya isar ba harda jinin jikinta Seda ya kaɗa, ɗauke idanun tayi ta maida kan abincin kaɗan ta kara feeling restless da irin kallon da yake aika mata, tissue ta ɗauka ta share bakinta daidai lokacin wakar ya sake chanzawa zuwa...

For my hand na Burnaboy ft ed sheeran

A hankali ya mike ya dawo ya ɗauke plate ɗin ya matsar se ya ɗauko na cupcakes da aka musu heart-shapes kowanne da candile a kanshi yana kadawa daidai inda ake cewa..

"When ever am broken' u make me feel whole.. When ever am lonely' you're there for my soul...! Where ever you are girl that's where I call my home!...

When ever you doubt it, I'll be letting you know whoaaa... Girl I want to be dancin' with you forever..! U see through the storm and take me as I am.. Baby it's magic anytime that we're together! I make I just love you and hold you for my hand! Hold you for my hand.. My hand!!!"

Idanunshi ya sarkafe cikin nata ya ɗan zube hannayenshi bisa table ɗin sun ɓata bat a kallon juna kaman masu kallon kuda, har zuwa karshen lyrics ɗin kan ya lumshe nashi ya nuna mata cake ɗin da idanu, itama da idanu ta tambayeshi what's for? Se yayi mata alamun iska da bakinshi wadda ya feso mata sassanyar kamshin lemon mouth wash ɗinshi da ya saka zuciyarta yin tsammmmm

A hankali ta juya ta hure juyowar da zata yi don ganin what's next se ta ga mutum bisa gwiwowinsa a durkushe a gabanta in a stylish way, hannunshi rike da wani gidan zobe me haske da kyau..

A daidai sadda ze yi magana yaji motsin ruwa ɗagowar da zasu yi se hasken camera click click click har guda uku a kansu, be motsa ba sanin spies ne.. Celebrity rayuwarshi be taɓa tafiya a sirri ba, he doesn't like anything da ze yi distracting wannan moment ɗin nasu hakan ya sa be motsa ba bare ya kira security ɗinshi..

Kamshin junansu dake ratsawa yake shiga kofofun hancinsu yana aika musu da wasu sakonnin na daban tare da ni'imar wurin ya haɗu ya bada wata sassanyar moment me natsuwa da amincin ruhi..

Cikin wata kalar murya ya fara magana..

"Hidayah! That first moment da na ɗaura idanuna bisa kanki daga sannan na san cewa ruhinmu are connected in one way or the other... Daga sadda kika bani labarin rayuwarki daga sannan kika kasa barin kwakwalwata, u r all over me, in my head! My thoughts! My dreams nd my eyes! I did my best to keep that feelings hidden but I can't any longer, believe me ban taɓa sanin menene so ba se a kanki, your tears make me restless, dariyarki me sanyaya zuciya, kalamanki masu kwantar da hankali... Everything about you is so charming and breathtaking...kin gyara rayuwarmu from bad path to good path u r Morethan an angel to me nd my children.."

Kirjinta ne yake bugawa fiye da misali se ta hau rawan jiki kaɗan kaɗan tana raba ido, ta ɗan sauke kanta se kuma ta ɗago jin yadda muryarshi ya fara rawa rawa se ta daure ta bashi glance ɗin dake nufin ya cigaba...

"Please hidayat help me and give me ur heart or share with me na miki alkawari I will never hurt nor leave you!"
Lumshe idanunta da suka cika tabbb da kwalla tayi zata fara kuka sbd abun ya fi karfin Tunaninta da hankalinta, ta kasa tuna komai bare kowa...

A hankali yace
"pls baby don't cry for me! Na jima ina so na fallasa miki sirrin zuciyata amma ina tsoro, by Allah ina ƙaunar ki fiye da Tunaninki I love you with all my heart and soul hidayah...
Ko bazaki so ni ba just know that the love I have for u is enough for both of us. Don Allah ki bani dama to be ur only husband...sirrin ki, farin cikin ki, ur man, ur true and last love I beg of you hidayah!"
Se hawayen idanunshi suka zubo..

Wani irin siririn kuka me nauyi ta fashe dashi.... Ze haukatata.. Raed is making her go out her mind, be san kwakwalwarta ƙarami bane? Be san zuciyarta bakuwar soyayya bace...!

#Vote
#share
#comment

                    🖤Gureenjo🖤

Weiterlesen

Das wird dir gefallen

430K 23.9K 17
𝐒𝐡𝐢𝐯𝐚𝐧𝐲𝐚 𝐑𝐚𝐣𝐩𝐮𝐭 𝐱 𝐑𝐮𝐝𝐫𝐚𝐤𝐬𝐡 𝐑𝐚𝐣𝐩𝐮𝐭 ~By 𝐊𝐚𝐣𝐮ꨄ︎...
1.6M 98.4K 39
"You all must have heard that a ray of light is definitely visible in the darkness which takes us towards light. But what if instead of light the dev...
67.4K 7.4K 58
Murmushi tayi mishi wanda ya tafi da imanin sa yayin da ta juya kallonta ga duɓɓin mutanen wajen. Dogayen yatsunta biyu wanda suka sha jan lalle ta b...
11.5K 1.5K 61
Kaddara! Mece ce ita? Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta cikin mummunar kaddara, irin kaddarar da b...