DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUN...

By JameelarhSadiq

6.2K 234 122

labarin soyayya mai ciki da darussa iri iri mai masu tsayawa a zuci..masoyane suke nuna ma juna tsana marar a... More

ZAZZAFAR KAUNA 01-10
ZAZZAFAR KAUNA 11_20
ZAZZAFAR KAUNA 21-30
ZAZZAFAR KAUNA 31-40
ZAZZAFAR KAUNA 41-50
ZAZZAFAR KAUNA 51-60
ZAZZAFAR KAUNA 61-70
ZAZZAFAR KAUNA 71-80
ZAZZAFAR KAUNA 81-90
ZAZZAFAR KAUNA 91-100
ZAZZAFAR KAUNA 101-110
ZAZZAFAR KAUNA 111-120
ZAZZAFAR KAUNA 121-130
ZAZZAFAR KAUNA 131-140
ZAZZAFAR KAUNA 141-150
ZAZZAFAR KAUNA 151-160
ZAZZAFAR KAUNA 161-180
ZAZZAFAR KAUNA 171-180
ZAZZAFAR KAUNA 181-190
ZAZZAFAR KAUNA
ZAZZAFAR KAUNA 201-210
ZAZZAFAR KAUNA 211-220
ZAZZAFAR KAUNA 221-230
ZAZZAFAR KAUNA 241-250

ZAZZAFAR KAUNA 231-240

187 6 0
By JameelarhSadiq

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*231-240*

"Kai ni dallah can matsa ka ban waje,ni banga amfaninka a wajen nan ba Najibu." tsaki tayi tana nad'e carpet din sallah tana cigaba da cewa.."Ina dalili yaran yanzun baku da kunya da kawaici wallahi,sai kace ce maka akayi mutuwa tayi zaka wani kama yi mana wannan rurudu..maza ka dauki matarka ku bar man waje ba zan iya wanann rashin ta idon ba nikam..daukarta ka maidata can shashen uwarka sai kaje ku karata a can amman na anan ba karma aja man sheri ina zamana cikin rufin asirin Allah."

Rasa abun ce mata ma yayi sai kama hannun Zulaihat da yayi tana kureta da ido tausayinta ya kama shi maike damunta tambayar da yake ma kan shi kenan,yasan lafiya lau ta bar gida tazo gidansu da cewa yayi ta tsaya yayi dropping dinta tace aa da motarta zata tafi tun da ta iya driving din nan itama dai ta hutar da shi ya tafi wajen aikinshi.

Har abinci sai da ta bashi yaci ya koshi da kanta ta shiryashi ta raka shi har bakin mota ta bishi da kiss and hunging sannan ya tafi ya za'ayi ya dawo kuma ya tadda bata lafiya dan ya tambaya ya zama laifi,tsaki Hajja tayi tana nuna mashi kofa tace.

"Ka dauketa nace ku barman gida,ni bansan jan sheri da neman bala'i daman Ina zaman zamana suka shigo man kuma ko ruwan gidana yau bata sha ba balle ace wani abu tasha a ci ahtoh ni ban son jan sheri da neman masifa dan haka a fice man daga gida kuma karda a sake a kama sunana."

Hawaye ta kama matsewa tana cewa.."Allah sai ya sakaman nikam Ladi duk wanda ya kama sunana a ciwon matar wanann marar mutuncin,sai nayi shara'a da duk wanda ya kama sunana dan hukuma ce zata rabamu da shi dan ba ruwana nidai akan hak'ina sai inda karfina ya kare,dan haka tun wuri kusan inda zaku ce ta fara cutarta amman ba dai nan ba."

Cikin kuka ta cigaba da cewa.."kuma wallahi kunji dai na rintse duk wanda yace a gida wannan matar tayi amai ban yafe ba kuma sai Hamisu ya shiga tsakani na daku ko kuma ba bar maku gidanku na koma wudil..na koma inda aka san mutuncina da kuma martaba ta ba zan zauna nan ba wanann marar mutuncin ya tisani gaba da tambayoyi akan matarshi bayan ni ko ruwan gida bata sha ba balle ace."

Ganin yanda take kuka bilhaki da gaskiya yasa Yaya Seemarh tashi ta koma hannunta ta zaunar da ita cikin kwantar da murya Yaya Teemarh tace.."haba Hajja kukan namaiye kike haka.?" K'ara rushewa da wani sabon kukan tayi  tana girgiza kai hadi da fashe majina tace.."bari Simatu barni nayi maganata ai gaskiya ce idan tazo dole a fadeta..ba yanda za'ayi a kama sunana a cikin wanann maganar ai dole na tashi tsaye sai inda karfina ya k'are dan ba zan duba Ido ba ina kallo ayi man sheri ba zan yarda ba."

Girgiza kai Yaya Seemarh tayi tana guntse dariyarta dan tana ma su Khadi warning da Ido da tuni sun fara dariyarsu sanin hali sanin wacece Hajja yasa suka kama hadiye dariyar tasu dan neman zaman lafiya...cikin kwantar da murya Yaya Seemarh tace.."haba Hajja ai ba wanda zai kama sunanki mai ma kikayi da har za'a kama sunanki?nidai ai bamu ga abunda kikayi ba,keda akayi ma laifi ma akayi maki amai a gida kuma kikayi hakuri ai godiya ma za'ayi maki amman ba wanda zai kama sunanki,Kinga ma bacci take idan ta tashi sai su tafi gida ko kuma ya kaita asibiti."

Share hawayenta Hajja ta kamayi tana cewa.."naji nidai ya tadata su bar man gida karda su sake dawo man Simatu,baki ga irin kallon da wanann marar mutuncin yake man ba shiyasa." Kuka ta cigaba da shi tana cewa.."haba abun da ciwo sosai da sosai kamarni Najibu yake ma kallon banza akan matarshi,duk wahalar da na sha dashi a banza ai nasan da Murjanatu ce ba zai mata kallon banza ba ko kuma Zainab da yake nice ya raina ma wayyo yake man kallon banza..to bari Kabir yazo sai yaji abunda akayi ma uwarshi yau a gidan nan bakin su tafi dai dole a zauna a bi man hak'ina ko kuma na Kai mutun a hukuma a anso man hak'ina dan akan hak'ina ba abunda ba zan yi ba."

Dariya Salma ta fashe da ita tana cewa.."Amman Hajja kina da abun dariya wallahi komai naki is so Funny wallahi."

Kowa na parlon sai da ya tsorota da maganar Salma ga dariya tayi mata ga kuma turanci Ina son ya kulle ruwan da take son ballowa ga kuma Salma ta ballo wani da kanta,bayan tasan an hana yin turanci gaban Hajja ko da kuwa yeah ne,tun da ba a dad'e da gama case din yeah din da Yaya Khalid yayi mata ba a gidan..har Police sai da tasa drive ya kaita ta dauko mashi tana kuka tana ce ma police bata yarda su anso mata hak'inta jikinta ne yayi mata zagin wulakanci zagin kare dangi,ba wanda ta manta bai zaga ba a danginta tun daga kan na wudil har na rano bai zaga ba.

Ba karamin tashin hankali suka ga ni ba a ranar da yake Abbu bai Kai da dawowa ba Dad ne aka iske kuma yace police din su tafi da shi shima yana kararshi akan zagar mashi uwa da yayi haka aka tafi da Khalid aka sashi bayan kanta..ana ta case sai da Abbu yazo ya samu dakyal ta hakuri akayi beli din shi aka dawo gida nan ma sai da su Abbu sukayi mashi tass sannan suka kwafa dokar daina yi mata turanci ko da kuwa ok ce balle wata yes ko no duk sun hana.

Kallon Salma Hajja tayi tana girgiza kai can ta nufa kofar fita tana cewa..."bari naje na tadda su Hamisun har wajen bakin nasu na gaya masu irin cin mutuncin da kikayi man,kuma naje sunyi bincike kuwa kafin su zo nema ma yaronsu auren marar kunya da tarbiya."

Sanin hali yasa Najeeb yayi saurin rike ta har ta tura kofa ta fita ya dawo da ita yana bata hakuri yana cewa..."Dan Allah Hajja kiyi hakuri karda kiyi haka mana,idan kika je Kinga zaki kunya ta su Dad ne." Fisge hannunta tayi daga rikon da yayi mata tana cewa.."sai mai Najibu?ai inace a gabanka ta gama zagina mai kayi mata? Dan zanje na kai kukana idan za'a kwato man hak'ina sai ya zama laifi? To sai naje sun dade basu ji kunya su Hamisu dai ko?sun dad'e basuji kunya ba yau."

Sosai ranta yake b'ace akan is so Funny da Salma tace mata..nufar kofar kawai tayi tana cewa cikin kuka.."Nidai Najibu ka kyaleni ka rabu dani yau dai gidan nan ayi ta k'are idan ma zaman gidan ne basu san suga inayi sai na bar masu gidansu na dawo gidanka ko kuma gidan Moha zai fiye man zaman lafiya nasan matanku matan kwarai ne suna da tarbiya ba zasu tab'a zagina ba,amman na gaji da wannan cin kashin da ake yi man a gidan nan na gaji iya gajiya nidai hakuri na ya k'are ba zan zauna ba yara su saman hawan jini Ina zamana lafiya yarana basu sanya hawan jini ba har na rabu da su ba zan zauna wanda ban had'a komai da su ba su daura man,na mutu nayi ma su Hamisu asara."

Zaunar da ita Najeeb yayi yana cewa.."Naji ba sai kinje ba Hajja zanyi maganin komai yanzun nan ba sai anjima ba je hado kayanki yanzun mu tafi gida kiyi zamanki ba sai sun sake ganinki ba balle har su zageki."

Share hawayen tayi tana tashi tace.."hakan ma yayi Najibu shiyasa nafi sonka a cikinsu dan kafi ji dani..amman kafin dai mu tafi gidan naka sai ka anso man hak'ina ko Najeeb?Dan ba yafe zagin wulakancin da yarinyar nan Salma tayi ba."

D'aga mata kai yayi yana cewa.."kwarai kuwa fara zuwa dai ki had'a kayan dan yanzun zamu tafi mu fara biyawa asibiti sai mu wuce gida."

Gaba tayi tana cewa.." Yauwa Najibu yanzun naji magana dan ni ba yafe hak'ina nike ba dan akan hak'ina ba abunda ba zan yi ba..ni dama zaka biye man ai da mun fara sauka office din yansanda mun shigar da kararta kamar yanda nayi ma Khalid ko kwana biyu ne tayi wajensu sai su sakota."

Basu ce mata komai ba har ta shiga bedroom dinta sannan Najeeb ya dawo kan Salma sai da balla mata maruka har sau biyu sannan yayi masu tas baki d'ayansu sosai yake masu fad'a akan turancin da suke a gaban Hajja tun da tace bata so ba sai su daina ba?ita ba wanann bokon tayi balle tasan wani turanci tun da turanci ba gadon uwa bane balle na uba kar wanda ya kuskura ya sake yin shi a gaban Hajja idan kuma aka sake sai ya karya mutun.

Hajja taji dadi sosai yanda Najeeb yayi ma Salma tas harda kuka sai da Salma tayi dan ba karamin zafi Marin da yayi mata yake mata ba,daman unexpected haka taji saukar marin daman tasan halinshi ba sauki ne da shi ba akan Hajja sai dai inda Hajja bata ce anyi mata ya dunga rashin mutunci kenan akan tsohuwar.

Da kanshi ya dauki jikkar kayan Hajja suka fito ta kulle part dinta suka shiga mota suka nufi asibiti sai nan da nan yake da Hajja yana k'ara bata hakuri..har zuciyarshi bai jin dadin turancin da suke a gaban Hajja yana mamakin yanda ake ma mutun abu bayan kuma yace baya so..shi rabon da yayi turanci a gaban tsohuwar har ya manta tun da tace bata so bai sake yi ba.

Dan bai son tashin hankali sam ita kuma Hajja ba tsoron tashin hankali nemanshi ma take.. gwanma kawai ta maida ta gidan shi da zama zai fi tun da ba jin magana suke ba kuma bai son ana sa su Dad magana a asibitin da suke ganin Dr Yayi parking ya taimaka ma Zulaihat ta fito da taimakon Hajja suka shiga cikin hospital din.

Bayan angama duk wani test da ya dace ayi mata aka kawo result.. bayan Dr ya gama duba results yaga tana dauke da cikin wata d'aya da sati biyu ba karamin murna Najeeb yayi ba da aka gaya wanann albishir sujjada yayi yana gode ma Allah akan kyautar da ya bashi ita kuma Hajja tsabar murna harda rawa sai da ta taka a gaban likita tana cewa..

"Ahh Dector ake ce maka ko mai?nidai bari nace maka likita kamar yanda na taso kaka da kakanni suna ce maka,Allah yai maka albarka mun gode mungode wallahi har ka yayeman bakin cikin da b'acin ran da yarinyar nan Salma ta tusa man."

Bayan ta gama rawarta suka ji dokokin da likita ya daura akan cikin suka sayi magani suka wuto gida..ita dai Zulaihat sai dai Murmushi take dan irin kallon da masoyin nata yake mata ita kadai tasan fassararshi da inda kallon ya dosa.

★★

*RASSIA 🥀*

Tun da suka sauka a kasar Rassia Jidda take samun kulawa ta mussaman a wajen AK ba irin kulawar da baya bata ta ko wani bangare..da tace wash yake tasowa yana tambayarta mai take so mai take bukata haka zai ta jero mata tambayoyi.

Idan kuwa tace tana son cin abu kaza ko kuma sha sai yaje duk inda abun yake ya nemo mata ya kawo mata..itama a nata bangaren sosai take kula da shi tana bashi hak'inshi kuma tana lura da duk abunda ta san yana so...bangaren abinci ma yanzun ansamu cigaba yana cin abinci sosai dan idan ma yace baya ci itama sai tace ta koshi dole yake bude ciki yaci abinci yanda take bukata.

Rayuwa suke gudanarwa mai cike da soyayya zallar da kuma zazzafar kauna..wata irin kauna suke nuna ma junansu basu son suga wani abu ya tab'a d'ayansu duk da kasar Rassia akwata da tarin sanyi kamar kasar Ukraine duk da daman makwafane..amman Rassia tafi Ukraine sanyi sosai shiyasa yake tsaye kanta yana kula da ita yanda ya kamata.

Cikinta Alhmdulh ya girma dan har ya kai wata shidda zuwa na bakwai..sayaiyyar kayan haihuwa babu ce kawai ba sayar masu ba dan kuwa ya kashe kudi iya kudi kamar ba gobe tun tana mashi fad'an ya daina saye ya daina kashe kudin haka yak'i ya daina sai ta saka mashi Ido kawai tana addu'ar Allah dai ya sauketa lami lafiya.

★★

*GUSAU 🥀*

Rayuwa ta juya ma Ahmad komai yayi mashi tsaye ya tsaya mashi cak ba abunda yake mashi dadi a rayuwa..dan komai ya juya mashi baya tun da aka kawo shi a prison tsawan shekara biyu kenan ba wanda ya tab'a kawo mashi ziyara a cikin yan'uwanshi.

Hatta matarshi da take sonshi da kaunarshi bata zo ba,babba abunda ke saka shi kuka juya mashi baya da sukayi ya tabbata sun yafe shi sun cire shi daga cikin yaransu sanann ita kuma Zainatuna yasan yanzun bata son shi bata ko San ganinshi yasan yanda take da kishin shi kuma yayi disappointed dinta sosai da sosai .

Dan bata tab'a tunanin zai iya aikata Zina ko ya take balle har azo da ciki kuma dauke yarinyar da yayi ma cikin yayi har na tsawon watan ni bai da sauran hope a rayuwarshi mutuwa ce yake fata tazo ta dauke shi.

Babu ranar da baya kuka Kuma babu ranar da baya cikin nadama mai tarin yawa yana tunanin yaran shi yasan yanzun bai da wani hope bayan nasu sune kawai ba zasu daina yi mashi addu'a ba komin lalacewarshi kuwa nan gaba kadan idan suka k'ara girma suka ji labarinshi da irin qaddarar da ta samaishi ya tabbata Koda sunyi fushi watan watarana zasu zo su ganshi.

Yanzun ya samu mai mashi k'arin karatun alquri'ani mai girma har litaitafan addini yana koya mashi kuma yana karuwa sosai ya yarda jallici mugun ciwo ne yafi hauka wuyar magani..Dan rabin abunda yayi ma Jidda harda Jallici da kuma gangar sheddar suka taka rawa wajen aikata komai yayi.

★★

*BIRNIN KEBBI 🥀*

Cikin Saddiqa ya shiga wata biyar babu irin taitali da so da kauna da Haidar baya nuna mata..wata irin soyayya suke nuna ma juna kamar sun cinye juna haka suke a gaban kowa suke nuna su din masoyane kuma suna son junansu sun yarda da junansu babu zargi ko kadan a zaman aurensu.

Dan har mota ya saya mata sabuwa mai kyau ta zamani ba irin kulawa da baya bata kamar yanda itama take tsaye akan mijin nata bata son taga ta gaza ta ko wani fanni tsaye take tsayin daka wajen ganin ta zama chief babba a wajen mijinta.

Haka wajen kwaliya da gyran jiki gami da tsafta ba'a barta a baya ba..iya tafiya da magana kuma da kisisina da kuma rangwada ba wanda bata iya ba indai tana a gaban Oga Haidar...yanda take kashe shi da salonta ta ko wane bangaren yake sa idan ya fita bai yarda yayi Koda 30mn ne bai dawo gida ba.

Idan kuma ya wuce 1hr to yana wajen aiki..amman ko zaman majalissa baya yi kuma charting duk baya yi..dan yana iya yin sati bai leko online ba haka itama Saddiqa dan kullun suna manne da juna ba dare ba rana.

Tare suke rainon cikinsu idan wash tace to tare zasu ce wash din..yanda ya sangarta ya shagwabar da ita duk wanda ya kalla sai sun burgeka sun baka sha'awa.. family baki d'aya kan ya Kara haduwa zuminci ake kamar ba gobe..baka cewa a tab'a samun wata matsala a cikin family din dan an maida komai ba komai ba ana ruyuwa ta burgewa da sha'awa.

★★

*ABUJA 🥀*

Bayan sun koma gida hawa sukayi sama su kayi wanka suka shirya sannan suka fito parlo zaune suka tadda Hajja tana kallo da jikkar kayanta a gabanta kallonta Zulaihat tayi tana murmushi tace.

"Hajja ga daki can ki shiga mana."

Tashi Hajja tayi tana girgiza kai tace.."A'a Zulaihatu ni ba zan zauna a sama ba haka ake na matsa maku na hanaku rayuwarku cikin jindadi ni k'asa zan koma can zan dunga zamana ina kallona dan haka ni Kinga tafiya ta dan karda ku fito kuga ban nan ai da baku taddani nan..ni daman jinina bai hadu da wanann bainan ba ko a gidana ai kasa nike rayuwata har mantawa nike da wani bene kin dai ji."

Murmushi Zulaihat tayi tana girgiza kai tace.."Ai Hajja zaman kasan ba zai maki dadi ba...kin ga zakiji shuru amman tun da dakuna ukku ne anan sama ba sai ki zauna d'aya ba daman ba'a tab'a zaman shi ba."

Tashi Hajja tayi tana nufar kasa tana cewa. "Ai Inaga Hausa nayi maki Zulaihatu ba wani yaren na daban ba balle har kice baki gane abunda na gaya maki ba..nace maki ni jinina bai hadu da wanann benen ba kuma sai ace dole sai na zauna a saman..yanzun dan hawan da nayi baki ji yanda kafafun suke man zafi da zinga ba sai na sama aboniki kafin ma na kwanta."

Ansar Jikkar Hannun Hajja Zulaihat tayi tana bin bayanta tana murmushi kawai dan ita tsoron darun Hajja take har cikin zuciyarta shiyasa take bin ta sannu sannu Koda kuwa gidansu taje.

Dan bata tab'a manta fad'anta akwai wani fad'a da suka tab'a yi da Najeeb akan cinye nata salad da yayi daga shiga su gaisheta suka tadda bata parlo ya bude wani bowl yaga salad din Irish ya zauna ya cinye.

Tana fitowa ta tadda aika aikar da yayi mata ta zauna ta fara bala'i tana kuka tana cewa sai ya biyata salad dinta bata tab'a ganin wanda ya raina mata wayau irin Najibu ba..daga ajiye salad taje ta kuskuro bakinta ta tadda ya cinye sai kace ajiya ya kawo mata ko kuma bashi yake bin ta ko dandanawa bata yi.

Tana tunanin Wanda ta had'a mata salad din itama bata ci ba ya had'a hak'in mutun biyu ya danna a cikin cikinshi dole sai ya biyata ko kuma ta Kai shi a hukuma ta anso mata hak'inta dan akan hak'inta ba abunda ba zata yi ba.

Ranar Zulaihat taga tashin hankali dan dakyal ta samu Hajja ta hakura sai da ta had'a da majiya da ban baki sanann ta samu tayi hakuri..Dan shi Najeeb ko kallonta baiyi ba tana bala'in yana danna waya ma ita dai ta samu taita bata hakuri ta hakura ta fasa Kai shi wajen police.

Har daki ta kaima Hajja jikkarta zata fara taya ta gyaran dakin ta hanata tana cewa.

"Mai zakiyi Zulaihatu.?"

Murmushi Zulaihat tayi tana cewa.

"Dan gyara maki dakin zan yi Hajja Kinga ta dan yi kura saboda ba shiga ciki ake ba kuma ba yan aiki balle a gyara."

Kama baki Hajja tayi tana kallonta can kuma ta fara tab'a hannu tana cewa.."Na shiga aljana ni Ladi Zulaihatu sheri kike son jaman ko kwana ban Kai da yi a gidan naku ba?kija wanann marar mutuncin mijin naki ya koreni inda ya dauko ni cikin daren nan ko.?"

Rasa abun ce mata Zulaihat tayi daga taimako mata na son ja mata jall dan tasan yanda Najeeb yake ji da kakarshi bai had'ata da kowa ba zatayi magana Najeeb ya shigo dakin yana kallon Hajja yace.

"Mai kuma kuke nan wajen Hajja.?"

Kama baki tayi tana cewa.."dole ai ka tambaya yaron kirki Najibu nida Zulaihatu mana Ina zaman zamana zata jaman bala'i taja a daure ni a bar su Hamisu da biyan kudin beli..duk da dai ance beli din kyauta ne ai suna ansar kudi dan kwanaki gabana Kabir ya bada dubu ashirin aka fiddo Khalid da na Kai shi wajen hukuma."

Murmushi yayi ganin yanda Zulaihat take zaro ido duk ta rude kuka take son fashewa da shi...kama hannun Hajja yayi yana cewa.." Naji gaya man mai tayi maki har haka take son ja maki dauri a wajen hukuma kuma.?"

"Wai zata gyara man daki..bayan gabanta gabana kuma gabanka Likita yace a kula da ita sosai banda barinta tana aiki mai wahala,amman ta kulle ido ta toshe kunne take cewa wai ni Ladi na barta ta gyara wannan dakin duk girman shi salon wani abu ya samaita ace nice ta ja man bala'i to ba zan yarda ba gaskiya."

Fito da ita parlo yayi ya zaunar da ita saman kujera sanann itama Zulaihat din ya fiddo mata yana mata magana a hankali yanda Hajja ba zata ji ba yana cewa.

"Kin cika Rigima Babe ai Hajja ta fiki gaskiya tun da Dr ya hanaki aiki mai wahala mai zaije kice zakiyi ai dole Hajja tace zaki ja mata bala'i sai kinyi hakuri da Hajja."

Murmushi kawai tayi tana zama kusa da Hajja da kanshi ya gyara ma Hajja dakin harda shimfida mata sabon bedsheet ya had'a mata ruwan wanka yana cewa taje tayi wanka kaya ya fiddo mata ya jera mata sauran a wardrobe.

Kama matarshi yayi suka haye sama dan yana bukatar gaisawa da Babynshi sosai ya nuna mashi irin so da kaunar da yake mashi..tare suka sulala indomie da taji sardine shima ya girka indomie din da kan shi da tace tana so..itama kuma ta soya masu egg ta had'a tea dan tace tafi shi iya had'a black tea mai dadi..bayan sun gama ya dauki na Hajja ya Kai mata sai da yaga ta fara ci yayi mata sai da safe ya kulle gidan ya hawo sama.

*Akwai Data available masoya akwai ko wane network kuma cikin rahusa 270 1GB ko wane network,banda 9Mobile shi  300 1GB*

*Zaki biya kudin data idan kina bukata ta wannan account din 8160508316 Jamila Bello Abubakar Opay bank,08160508316 for call or whatsapp*

Share✓

Continue Reading

You'll Also Like

3K 213 22
Tunaninta da duk wata nutsuwarta sun ta'allaƙa ne akan abinda takewa kallo a matsayin MURADIN RANTA, Sedai saɓanin zuciyar ABOU HATEEM wadda take a...
2.4K 224 27
Wannan ne littafi na na farko,Allah sa inyi abin arziki your comments and likes will be appreciated 😅 Life is full of ups and downs,when we think...
1.6M 97.9K 39
"You all must have heard that a ray of light is definitely visible in the darkness which takes us towards light. But what if instead of light the dev...
7.2K 254 12
_Duniya makaranta a lokacin da wasu suke shiganta a lokacin ne wasu ke barinta,wasu na zuwa Duniya wasu kuma na barin Duniya, Rayuwa kamar shafin lit...