DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUN...

JameelarhSadiq által

6.2K 234 122

labarin soyayya mai ciki da darussa iri iri mai masu tsayawa a zuci..masoyane suke nuna ma juna tsana marar a... Több

ZAZZAFAR KAUNA 01-10
ZAZZAFAR KAUNA 11_20
ZAZZAFAR KAUNA 21-30
ZAZZAFAR KAUNA 31-40
ZAZZAFAR KAUNA 41-50
ZAZZAFAR KAUNA 51-60
ZAZZAFAR KAUNA 61-70
ZAZZAFAR KAUNA 71-80
ZAZZAFAR KAUNA 81-90
ZAZZAFAR KAUNA 91-100
ZAZZAFAR KAUNA 101-110
ZAZZAFAR KAUNA 111-120
ZAZZAFAR KAUNA 121-130
ZAZZAFAR KAUNA 131-140
ZAZZAFAR KAUNA 141-150
ZAZZAFAR KAUNA 151-160
ZAZZAFAR KAUNA 161-180
ZAZZAFAR KAUNA 171-180
ZAZZAFAR KAUNA 181-190
ZAZZAFAR KAUNA
ZAZZAFAR KAUNA 201-210
ZAZZAFAR KAUNA 211-220
ZAZZAFAR KAUNA 231-240
ZAZZAFAR KAUNA 241-250

ZAZZAFAR KAUNA 221-230

219 8 3
JameelarhSadiq által

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://whatsapp.com/channel/0029Va9zjzE84OmE1ogwXn2I

*221-230*

A hankali ya daura bakinshi saman wuyanta yana kissing din ta da kuma sinsinata yana shakar kamshinta.. lumshe ido yayi yana budewa a hankali ya waigo da ita suna kallon juna ido cikin Ido,kallon zan mutu idan bake suke ma juna kwayar idonsu kawai zaka kalla ka gane sunyi nisa a kogin son juna..sun dade suna aika ma juna sakonni ta cikin idanu sannan ya k'ara hug dinta tight very tight yana cewa a hankali.."gaya man sunan turarukan nan naki Kalbi? please ki gaya man Ina kika samosu Kai ni wajen da kika saya na ba wanda ya sayar maki dashi kyauta..ki yarda dani ina bala'in son wannan kamshin naki yeah I love it so much Kalbi."

Kwantar da kanta tayi tana cewa cikin saukin sonshi da kaunarshi tace.."Hubby Kai ne sirrin komai nawa,ki sani komai nike yi dan kai nike yi shi domin kuwa ka gama zama bango a rayuwata Kaine jigon rayuwar Zulaihat sai da kai Zulaihat take gane komai sai da kai Zulaihat take sanin dadin duniya..kamar yanda kamshinka yake saka ni natsuwa da wani sauke marar musaltuwa Hubby Ina kaunarka."

Kallon juna suka dan yi suna sakar ma juna murmushi can kuma suka fara kissing mouth to mouth kamar zasu cinye junansu haka suka koma..daga tsaye suke tsotsar bakin juna suna shafa ko wani sako na jikinshi sun dad'e a haka sanann ya shureta bai direta ko Ina ba sai saman gado..dakyal ya lalubo switch ya kashe hasken dakin suna lulu duniyar da idan suka shigeta mantawa suke da a Ina suke..dan dukansu zakewa suke suna nuna ma juna babu wani bayan kai,suna mallaka ma juna zuciya da kuma rayuwa ma baki d'aya suna jinsu a wata duniya sun lula sun tafe haka suke ji.

Washe gari bayan sun tashi tare sukayi wanka suka shirya suka samu abunda suka saka ma cikinsu duka k'ara yin shirin tafiya school Kuma yau Zulaihat zata fara exams din ta final year..ba karamin kyau sukayi ba kallo d'aya zaka yi masu ka gane suna cikin kwanciyar hankali da kuma natsuwa,kallo d'aya zaka yi masu kace wa'annan masoyane kuma sun dace da junansu.

Yanda suke nuna ma juna taitali da kulawa a gaban kowa zai Kara burgeka ya baka sha'awa..zama da masoyi yafi komai dadi amman idan akayi dace da masoyi nagartaice na gari wanda zai dauki damuwar matarshi tashi ce haka itama matar,wanda zasu zauna zaman amana ba cuta ba cin mutunci to tabbas su Najeeb sun Kai duk inda kake tunani har ma sun wuce a fagen so da kaunar da suke ma junansu.

Dan kuwa sun sauke duk wani girman kai da son girman tsiya duk babu su yanzun a tare da su kuma babu yar'ramuwa sun bude sabon shafin rayuwa dan rayuwa suke gudanarwa mai cike da salo mai tsayawa a zuci da kuma bargewa...kuma tana bashi girman shi tana respected din shi sosai bama kamar inda suna makaranta baka tab'a cewa sun san juna idan har suna class.

Daman ba kowa yasan suna da alaqa ba sai Zubaida da Baby shiyasa ba ruwansu da wani sa idon students..yanda yake tambaya ya tada wanda ya gadama haka yake tadata mudun Allah ya qaddara sai an tadata..kuma zata tashi ta bada ansa cikin natsuwa da kamun kai daman ba da kowa take harka ba a school din daga Zubaida sai Baby.

Su ukku suke komai nasu daman Baby tayi aurenta ta auri saurayinta Kamal suna shan soyayyarsu suma kamar ba gobe..idan suna son su sha dariya sai su tuno baya suna jan Zulaihat irin rayuwar da sukayi a baya ita da Najeeb kamar ba su ba sai dai tayi dariya.

Cikin sati biyu suka gama exams Allah yayi ya yarda Zulaihat ta gama degree kamar wasa shi Najeeb har mamaki ma yake gani yake kamar a mafarki duka duka yaushe taje hundred level gashi har ta gama..bayan sun dawo gida sai tsale take tana rawa gabanshi duk murnar gamawarce yana zaune sai kallonta yake yana murmushi dan ba karamin kyau rawar take mata ba.

Turo baki tayi tana kamo hannunshi suka cigaba da rawar tare,biye mata yayi yana rawa yanda yasan shi dai ya iya tun da bai tab'a rawa ba bama iyata yayi ba shi ko waka baji yake ba daga India har hausa zuwa ta turanci basu gabanshi bai ma da lokacin da zai wani zauna ya kalli Waka..barshi dai da yayi kallo kuma abunda yasa yake kallo yana son series sosai bama kamar wanda ake buga soyayya yana natsuwa sosai ya kalla dan yana daukar course sosai a cikin kallon dan idan ya gwada a wajen Sahibarshi yana ganin cigaba sosai a fannin soyayya sosai.

Rawa suke sai dariya suke ita Zulaihat dariyar yanda yake rawar take duk da ba iyawa yayi ha amman so Masha Allah ba karamin kyau rawar tayi mashi ba..bayan sun gama suka zube Saman kujera sai sauke numfashi suke daura kanta saman kirjinshi tayi tana shafawa a hankali sai  tace.

"Mijina."

Wani yarrrr yaji yanda ta kira sunan nashi cikin sexy voice haka ta k'ara sunan nashi bai san lokacin da ya lumshe ido ba yana budewa ya sauke a kanta sai da yayi kissing din hannunta sannan ya ansa, murmushi tayi tana cigaba da cewa.

"Yau Ina cikin farinciki marar musaltuwa Hubby wai yau ni Zulaihat Aminu na gama karatun degree..Allah dai yayi ma Umma albarka da kuma Kai Mijina Allah kuma ya jikan iyayenmu."

Murmushi ya sakar mata yana cewa.

"Tabbas Kalbi Umma jarumar mace ce na dad'e banga mace mai hazaka da zuciyar nema ba irin Umma..kiji fa tun kuna kananu take kula da cinku da shanku da kuma suturarku harda karatunku..ta dauki dawainiyar da maza suke yi ta daura ma kanta tana yi..wani hidimar da tayi ba kowane namiji yake iyawa ba..wani namijin haihuwa kawai yake son yaga ana mashi amman bai iya tsayawa ya fita hak'in yaran nashi harda matanshi ma,kawai dai yayi aure ya haihu ya tara yara kamar mai ya kasa cinyar dasu balle kuma azo ga tarbiya."

"Shi kiga b'arayi sun yi yawa a unguwa ga kuma almajirai suma sai addu'a kawai..idan kuma yara mata Allah ya azurta shi dasu sai su fara bin maza suna samun abunda zasu ci..shiyasa sai kiga karuwar sunyi yawa a gari rabin karuwan da kwata din su hali ne yake saka su a harkar wasu idan suka ga yunwa zata kashe su sai su fara bada kansu ga wasu mazan mararsa Imani suna basu kudi.. komai dai gashi nan ba dadi amman kam Umma jaruma ce dan mace ce mai kamar maza fari ne babu."

Lafewa kawai tayi dan ta rasa mai ma zata ce mashi tabbas komai ya fad'a gaskiya ne abunda zasu ce Allah dai ya shirya baki..
D'aya dan sha'anin duniya yanzun ya zama abunda ya zama sai dai Addu'a.

Bayan sun gama labarin soyayyarsu yace ta dan bashi 30mn haka zai je wani waje ya dawo sai da ta rakashi har bakin motarshi sannan ta dawo cikin gida ta fara..gyarawa dan Zulaihat ba daga baya ba wajen tsafta da kuma kwaliya ko ta nan wajen ta tsaya zata mamaye ko wani lungu da sako na zuciyar Najeeb ga kuma iya girki bata mashi wasa da cikinshi tana bakin kokarinta wajen ganin ta faranta mashi.

Bayan ta tabbatar da ta gyara ko Ina ta kuma baza kamshi dan harda cotton sai da ta chanza dan kuwa bedroom dinsu zagewa tayi ta gyarashi yanda ya dace ya chanza sabon bedsheet..daman duk bayan one week take sake masu sabon bedsheet bata wasa da wajen baccinsu ko kadan.

★★

*BIRNIN KEBBI 🥀*

Rayuwa ta juya komai ya sauya a gidan Haidar dan soyayya suke shi da Saddiqa kamar ba gobe..yanda suke son juna suke kula da junansu suna nunama juna *ZAZZAFAR KAUNA* ba zaka tab'a cewa auren hadi bane aka yi masu yanda suke rayuwarsu gwanin burgewa da sha'awa... Yanda suke rayuwarsu suke nuna ma juna so da kauna sai kaji Inama Kaine a inuwar auren.

Family ya k'ara haduwa zuminci suke kamar ba gobe haka.dan alaqarshi shida Yaya Muhd gaba tayi sosai dan ta wuce yanda take a baya dan sun had'e kansu su ukku shi da Yaya Muhd sai Yaya Auwal su ukku suke yin komai nasu gwanin burgewa.

★★

*JIGAWA 🥀*

Tare suka fito daga cikin pool rungume da juna dan sun dade sosai a cikin suna wasa a cikin ruwan dan su duka ba daga baya ba wajen son wasa da ruwa.

Bayan sun fito suka shiga gida suka chanza kaya sannan suka fito parlo ta fara fama da shi akan cin abinci sai da yaga tana shirin yi mashi kuka sanann ya bude baki ta fara bashi abincin yaci ba laifi sai da yaga tana niyar fasa mashi ciki da abinci ya rike hannunta ya daukota ya zaunar saman cinyarshi ya fara bata abincin shima.

Murmushi ta sakar mashi tana shafa gemunshi  tana cin abinci sai murmushi suke sakarma juna bayan sun gama cin abincin sanann kuma suka koma parlo suna kallo suna labari sai dariya suke bayan sun gama.suka tafi gidan Ammie anan sukayi firar dare sanann suka dawo gida bayan sunyi wanka suka kwanta rungume da juna cikin so da kauna.

Washe suka tashi da Jidda ba lafiya duk da ba wani ciwo take ba na azo a gani amman duk AK ya rude ya gigice ya fita haiyacinshi..ganin yanda ya wani hirgice mata ya fita a haiyacinshi sai ta dan fara nuna jikin da sauki..duk da haka kin yarda yayi da pretending din ta visa ma yayo masu akan next two days zasu tafi Rassia dan duba lafiyar jikinta.

Da fari ta nuna rashin amincewarta amman ganin ko saurararta bai yi sai ta saka mashi Ido ta bishi da Allah ya kaimu jibin..spoon hanata dauka yayi a ranar duk da ba komai ya iya ba dai dai da indomie bai iyawa girkawa ba haka a ranar ya shiga kitchen wai zai daura masu abinci.

Yanda yake kokowa da kunna gas ya bata dariya ta kama yi mashi kuwa..Sai da tayi dariyarta mai isarta sanann ta shiga ta samu ya barta ta nuna mashi yanda zai masu girkin..duk da ba wani ci tayi mai yawa ba baki d'aya ma bata son kamshin indomie din toshe hancinta tayi tana girgiza mashi Kai tace.

"Beb please matsar man da wannan noodles din ban son kamshinta."

Kallonta yake yana son yin magana ta fara k'ak'arin amai da gudu ta nufi toilet din parlo... bin bayanta yayi cikin damuwa yana mata sannu ji yake kamar yayi kuka da ace da yanda zaiyi da ya maido da ciwon jikinshi haka yake har cikin zuciyarshi haka yake jin aman da take yi.

Taimaka mata yayi bayan ta gama ya gyara wajen yayi mata wanka yana daukota ya fito da ita a toilet din room dinsu ya nufa da ita direct ya samu kayan sanyi ya saka mata bayan ya gama shafeta da lotion kwantar da ita yayi yana ja mata bargo.

Zaune yayi gefenta yana mata sannu duk motsin da zatayi sai yace mata sannu mai take bukata..itama narke mashi tayi tana zuba mashi madara shagwabar ta yanda ranta ke so.

Da lokacin Sallah yayi zaije yayi sallah sai ya dawo yake tadata tayo alkwallah tayi sallah kuma zai maidata kan gado haka.suka kare  ranar ba inda yake zuwa daga sallah sai sallah sai kuma ya dawo yaita lailashi yana sannu.

Ba wayar da bai kira ba akan yaji ko zasu samu flight din zuwa Rassia a Abuja amman babu suma sai nan da two days flight din zai tashi..dole ya hakura ya kira wani family Dr dinsu ya duba mashi ita ..bayan ya gama yi mata duk question din da zai mata ya gane kamar tana da shigar ciki dan wata biyu.

Test yayi mata ya tabbatar yayi ma AK wanann albishir harda kuka sai da yayi dan murna..bayan ya gama godema Allah ya ba Dr kyautar gida da mota yace yaje A-Kaɗir Motors ya dauki duk motar tayi mashi.

Shi Dr har tsoro kyautar da AK yayi mashi yake.. godiya yayi yana fita cikin farinciki dan baiyi tunanin samun wannan kyautar ba daga wajen AK kyautar gida da mota daga albishir din ciki,gidan ma a babbar unguwa yake unguwar masu kudi gaskiya kam ya taki sa'a.

Bayan tafiyar Dr AK ya kira su Dad waya yana kuka ya gaya masu Jidda tana dauke da cikinshi har na tsawon wata biyu..ba karamin dadi Dad yaji ba yace wani Dr ne ya duba Jidda din gaya mashi Dr din yayi yana kashe wayar ya koma ya cigaba da kula da Jidda.

Bayan Dad sun gama murna da Ammie suka kira Dr suka bashi kujerar makka da kuma daukar nauyin karatun babban d'anshi ko wace k'asa yake son zuwa kuwa ya zab'a zasu Kai shi har sai ya gayama.

Godiya sosai Dr yayi masu yana gode ma Allah da Allah ya zabe shi ya kasance shine ya duba matar har ya gano da ciki a jikinta..addu'ar Allah yayi ma abunda zata haifa albarka yayi da Allah ya raba lafiya.

Murmushi Dr yayi da ya tuna dole suyi abunda yafi hakama tun da suna da hali duba da d'ansu d'aya jal basu da wani d'a sai shi ga dukiya kamar ta kashe su amman babu zuri'a da yawa..dole suyi murna da karuwar da Allah ya basu yama daina mamaki sai dai yace Allah ya raba lafiya shi dai kam ai ya gama arziki.

Bayan kwana biyu suka shirya sai kasar Rassia(masko) dan a Kara duba mashi lafiyar matarshi da kuma abunda ke cikin cikinta...har airport su Dad suka raka su sannan suka dawo gida,dan Dad cewa yayi yayi zaman shi a Rassia ya kula da cikin matarshi karda ya dawo inda ma haihuwar ta kama tayi a Rassia din sunzo suna da duk mai bukatar zuwa dan ganin baby.

★★

*ABUJA 🥀*

Tafiya yake da ita a hankali ya kulle mata ido da wani white yadi yana cewa.."Zuciya sorry mun kusa isowa." Murmushi kawai take ta k'agara taga surprised din da masoyin nata yayi mata..dawowarshi kenan daga yar fitar da yayi yace ta bashi 30mn tana zaune yazo ya kulle mata ido yana tasowa da ita ya fito waje da ita.

Tafiyar two to three minutes sukayi suka iso inda yake bukatar,tsayawa yayi da ita yana kissing din kumatunta yana cewa a hankali cikin so.."bude idon tom Kalbi."

Bude idonta tayi tana saukewa a saman wata babbar mota mai numfashi kuwa anyi mata decoration ,waro ido tayi waje tana dafe kanta sai kuma ta waigo wajenshi tana rungume shi tana tsale sai ihun murna take.

Rungumeta yayi shima sai dariyar yake bata san lokacin da ta had'e bakinsu waje d'aya tana mashi wata irin tsotsa, hard and soft and also French kiss take mashi.

Sun dad'e a haka suna romance sanann ta ciro bakinta cikin bakinshi tana cewa a hankali.

"I love you I love you na yarda na kuma amince Kaine mahadin rayuwata..Hubby inajin a jikina ba zan tab'a iya rayuwa ba babu Kai a kusa dani I love you with all my heart Babe."

Hawayen da ke zubo mata yake share mata yana nuna mata gefensu..kallon gefen tayi tana had'a ido da Zubaida da itama sai murnar sayar mata mota da Moha yayi ga tsohon ciki jikinta dan cikin Zubaida zai Kai wata 6-7.

Murmushi tayi tana zuwa ta rungume Zubaida sai murna suke dan motarsu iri d'aya ce color ce kawai ta banbanta amman campany d'aya ne..bayan sun gama murnar mota suka kuma basu latest iphone wata sabuwar murnar ce ta balle.

A part din Zubaida sukayi dinner sannan suka sha firarsu gwanin burgewa sai da dare yayi wajen goma na dare sannan su Zubaida suka tafi gidansu.

Bayan tafiyar su Zubaida sanann suka shiga wanka.. bayan sun fito wanka suka shirya sanann suka zauna saman gado suna buga lido,ita Zulaihat ba iya lido tayi ba sosai rigima ce irin tata kawai tace zatayi amman daman tasan bata iya ba.

Game din suke sai turo baki take ganin ya kusa yi mata game over..shi kuwa sai dariya yake mata wai bata iya Lido ba ganin da gaske zai mata game over sai ta fashe da kukan karya tana rushewa da ihu sai birgima...take mashi a saman gado tana wani fadawa jiki sai kukan shagwaba take mashi.

Yanda take shigewa jikinshi tana wani shafashi tana wani makalkalewa a jikinshi ta fara chaji mashi zuciya..bai san lokacin da ya fara romance din ta ba yana nuna mata wata irin ZAZZAFAR KAUNA.. sosai ta bashi hadin Kai suka kwashi soyayyarsu sun nuna ma juna son da yake tsayawa a zuci bayan sun gama suka kwanta makale da juna sai murmushi suke na so da kaunar juna.

Washe gari tun da safe suka shirya suka tafi gidansu Najeeb da yake yau aka ake kawo kudin auren su Khadi da Salma sai kuma za'a Kai kudin Khalid Shima..aiki suke iya aiki dan abinci ake shirya masu kala kala na gani na fad'a ba karamin shiri aka yi ma wanda zasu kawo kudin ba.

Bayan an gama komai aka shirya a part din baki,suna dawowa part din Hajja Zulaihat ta kwanta kanta yana mata ciwo..sosai Hajja da ta damu da yanda Zulaihat take fama da ciwon kan,shinkafa da wake Hajja ta zubo mata ta kawo mata.

Tana kallon shinkafar ta fara yunkurin amai da gudu ta nufi toilet ta fara karara Amai..bayanta Yaya Seemarh ta bi tana mata sannu bayan sun fito da ita daga toilet din take mata sannu tana tambayarta daman bata lafiya ta kama aiki? Girgiza kai kawai take tana sauke ajiyar zuciya ta dan kwanta bata dade da kwnaciya ba bacci yayi awon gaba da ita.

Shigowa Najeeb yayi ya tadda tana bacci mamaki ya kama shi dan ya lura da yawan baccinta kwaba biyun nan..tambayar lafiya yayi aka gaya mashi amai tayi rudewa yayi yana cewa mai ke damunta mai akayi mata..harararshi Hajja tayi tana cewa.

*Akwai Data available masoya akwai ko wane network kuma cikin rahusa 270 1GB ko wane network,banda 9Mobile shi  300 1GB*

*Zaki biya kudin data idan kina bukata ta wannan account din 8160508316 Jamila Bello Abubakar Opay bank,08160508316 for call or whatsapp*

Share ✓

Olvasás folytatása

You'll Also Like

2.9K 299 67
labari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya m...
2.4K 224 27
Wannan ne littafi na na farko,Allah sa inyi abin arziki your comments and likes will be appreciated 😅 Life is full of ups and downs,when we think...
31.3K 1.4K 9
Story of a young blind Fulani girl👸🏻
1.6K 132 15
Labarin Innayi da 'ya'yanta.