DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUN...

Від JameelarhSadiq

6.2K 234 122

labarin soyayya mai ciki da darussa iri iri mai masu tsayawa a zuci..masoyane suke nuna ma juna tsana marar a... Більше

ZAZZAFAR KAUNA 01-10
ZAZZAFAR KAUNA 11_20
ZAZZAFAR KAUNA 21-30
ZAZZAFAR KAUNA 31-40
ZAZZAFAR KAUNA 41-50
ZAZZAFAR KAUNA 51-60
ZAZZAFAR KAUNA 61-70
ZAZZAFAR KAUNA 71-80
ZAZZAFAR KAUNA 81-90
ZAZZAFAR KAUNA 91-100
ZAZZAFAR KAUNA 101-110
ZAZZAFAR KAUNA 111-120
ZAZZAFAR KAUNA 121-130
ZAZZAFAR KAUNA 131-140
ZAZZAFAR KAUNA 141-150
ZAZZAFAR KAUNA 151-160
ZAZZAFAR KAUNA 161-180
ZAZZAFAR KAUNA 181-190
ZAZZAFAR KAUNA
ZAZZAFAR KAUNA 201-210
ZAZZAFAR KAUNA 211-220
ZAZZAFAR KAUNA 221-230
ZAZZAFAR KAUNA 231-240
ZAZZAFAR KAUNA 241-250

ZAZZAFAR KAUNA 171-180

241 10 13
Від JameelarhSadiq

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*171-180*

Tana shiga room dinta ta fad'a saman gado tana rushewa da wani irin kuka mai cin rai..sosai take kuka ga wani irin yanayi da bata tab'a ji ba tana ji a jikinta,dan wani tafiya tafiya take jin wani abu yana mata a duka jikinta ga kuma k'aik'ayin da boobs dinta suke mata...rasa yanda zatayi da abun tayi sai ta makure waje d'aya tana had'e kanta saman gwuwowinta tana mai kuka tana tura hannunta cikin sumar kanta tana sosawa..ta dade tana kuka daga basani ta samu dakyal ta sauko saman gadon ta fad'a toilet ruwan zafi mai zafi sosai ta had'a ta shiga cikin tana sauke ajiyar zuciya...lumshe idonta tayi a cikin ruwan tana mai sauke ajiyar zuciya tana share hawayenta,sai yanzun taji tausayinshi ya kamata tana kuma nadamar abunda tayi mashi kwana kin baya da ya nemi ta bashi hak'in shi ta hana shi..Ashe haka yaji?Ashe abunda yaji kenan irin yanayin da ya shiga kenan da har ta hanashi abunda yake bukata a lokaci.

Ta dade a cikin ruwan sai da ya huce sanann ta sake wani tayi wanka ta fito tana tsane kanta ta sake riga ta fashe turare ta kwanta...Koda ta kwanta bacci ga garar idonta yayi dan yau ta hukuntu a wajen Najeeb da ya san a irin yanayin da take ciki da bai barta a cikin wannan hali ba..tunda da take bata tab'a shiga wannan condition din ba tama yi zaton mutuwa zatayi jin yanda take jin duka jikinta yana mata yarrrr...mamakin yanda ta kasa jin haushin shi take sai ma son shi da ya k'ara nunkuwa a zuciyarta sama da farko ma,dan ta yarda ita mai laifi ce a wajen shi akan abunda tayi mashi idon shi ta kalla fa tace ma shi bata bukatar had'a jiki da shi and sha'awarta yake ba sonta yake ba, lumshe idonta tayi kawai alkwarin da ya daukar mata na sai ta kawo mashi kanta ya dawo mata... girgiza kai tayi tana cewa a hankali.."idan ma na kawo maka kan nawa ai ba faduwa nayi ba,ni yanzun akan sonka bani da girman Kai Hubbyna." Rungume pillow tayi tana sakin wani murmushi can kuma ta dan makale kafafunta waje d'aya saboda reaction din dazun ne ya dawo mata.

Yanda yake romence din ta  cikin nuna tsantsar so da kuma kauna,ta tabbata kuwa yana sonta ko ana aka tsaya tasan tarkonta ya fara kama shi kuma yanzun ta fara d'ana mashi tarko sai anje inda take bukata,ba dai yace daman zata kawo mashi kanta ba taji ta yarda zata kawo mashi kanta kamar yanda yace amamn hanyar da zata bi wajen kawo kan nata ba zai tab'a gane ita ce silar faruwar lamarin ba,dan yanzun ta fara shigar kananun kaya tana kuma baza kamshinta yanda ta gadama and tafiya kuwa yanzun ta fara chanza different styles sai ta rushe duk wata alaqa da suke kokarin kullawa shi da Baby a haka bacci yayi gaba da ita.

Tunda ya koma room din shi yake zagaye room din shi yana ta safa da marwa yarinyar a kullun sake firgitashi take da wutar sonta maiyake Shirin aikatawa dazun?shafa bakin shi yayi yana sakin murmushi har wani gar'di yake jin bakinshi yana yi,dan har yanzun yanajin bakinta a cikin bakinshi.

Bai samu ya fara jin ya dawo dai dai ba sai da ya kora black tea wanda yaji lemun tsami sannan yaji zufa ta dan fara keto mashi toilet ya shiga yayi wanka yana fito yayi kwanciyarshi..karfe hudun dare ya tashi ya dauro alwallah ya fara sallah sai da ya gama nafilolinshi ya tashi ya wuce massalaci bai shigo gida ba sai karfe shidda da rabi na safe.

Bayan ya dawo kwanciya yayi dan yana bukatar hutuwa tun da daga shi har ita yau goma zasu fita bacci ne ya kwanshe shi...bai samu ya farka ba sai wajejen tara na safe yana tashi ya fad'a toilet yayi wanka ya zauna ya shirya cikin suits ba karamin kyau sukayi mashi ba.

Yana fitowa ya tadda ta zaune parlo tana yin breakfast, kauda kan shi yayi yana wucewa kitchen dan samun abunda zai ci dan shi Najeeb bai wasa da cikin shi yana cin abinci sosai ma dan sai yaci ya nak yake barin abinci idan ya samai shi... cous-cous yayi jalop yaji kayan lambu da sardine ya zuba a plate ya dauki ruwa ya fito ya zauna yana fara ci cikin natsuwa.

Miyau ta hadiye kuttt tun yana kitchen kamshin abincin yake kawo mata ziyara take ji taliyar da ta dafa ta fice mata a rai ba abunda take son ci saman da cous-cous din da ya girka.. kallon cous-cous din take tana tunanin yanda zata yi ta samu ko spoon d'aya ne tayi.

Tasan halin yan kayanta tasan shi in and out bai son wasa balle kuma raini ,kuma tasan wanann raini ne ita bata girka mashi ba a matsayin shi na mijinta ya kuma girka ma kanshi ace kuma wai zata ci,dama ace zaman soyayya suke wannan normal ne... Amman suna wannan zaman na doya da manja amman kuma tace zata ci mashi abinci tasan ta ballo august.

Ganin yanda yake cin abinci kamar ana mashi dole ko kuma ba dadi ohoo,ko dai harda cin abincin sai anyi mashi yanga dan ta lura yanzun ya maida komai nashi yanga sai kace wata mace,ajiye plate din hannunta tayi tana daukar spoon ta rike tana ta shi ta nufi wajen shi a hankali take tafiyar tana wani karkardawa kamar wata macijiya haka take juya jikin.

Sakin baki yayi yana kallon ikon Allah ganin direct wajenshi tajo ga kuma spoon a hannunta kamar wata mayunwaciya,tsaye tayi a gabanshi tana turo baki sai kuma can ta tsuguna k'asa tana langwabar da kanta gefe sai turo baki take...kwarewa ya kusa yi yanda take cinno mashi bakin tana wani shagwabe mashi ba karamin kyau hakan yayi mata ba har bai san sanda yace mata.

"Lafiya dai ko.?"

Kallar tausayi tayi mashi tana dan yarfa hannu cikin shagwabar ta tace mashi.."Dan Allah ka dan dan'man Koda one spoon ne nayi please." mamakin Karfin halinta kawai yake wai ya bata,ya bata fa tace?ita ta girka mashi da zata wani ce ya bata tsaki yayi ganin rainin wayau yana kokarin shigowa sai ya gama kanshi bai sake kallonta ba ya cigaba da cin cous cous din shi.

K'ara marairaice fuska tayi tana cewa.."haba Hubbyna dan Allah ka bani nifa ce taka fa." Kusan sakin plate din yayi sai da yayi hanzarin rike abinci wani irin sanyi yaji ya zirarci zuciyarshi Koda kuwa dan ya bata cous-cous tace mashi Hubby taji dadi sosai,amman bai nuna mata ba sai ma kauda kanshi gefe da yayi ya yana cigaba da abunda yake ganin yana niyar cinye couscous din tayi sauri anshe plate din tana yin baya tana cewa.

"Allah ba zaka cinye wannan delicious din Kai d'aya ba, haba Hubby Kai ko dan tayin nan na ido guba babu ai wannan ba zaman amana bane." Ta ida maganar tana d'age mashi gira  d'aya da kashe mashi Ido tana mai Kai spoon a baki ta fara ci, lumshe Ido tayi tana kallonshi tana jingina mashi tace.

"Wooow."

Harararta yayi yana nufo ta da gudu tayi hanyar room dinta bin ta yayi yana cewa.."Kee tsaya ki bani abinci na." Makale kafad'a tayi tana cewa.."Allah ba zan bada ba idan baka koshi na ga sauran taliya nan sai ka ci."kwafa yayi yana cewa.."ce maki nayi ki bani abinci na ko.?" Girgiza mashi kai kawai tayi tana Kara loma,har wani lumshe Ido take tana wani karkarda Kai,tsaye yayi ya kama kuhu yana kallon yanda take cin abincin har wani lumshe ido take hakan da take sai ya Kara mata kyau ma.

Girgiza kai yayi yana sakin tsaki ya nufi hanyar room din shi,dariya tayi tana cewa da karfi.."God bless you Babe,ka iya delicious fa." Murmushi kawai yayi yana shigewa room din shi ya wanko bakin shi ya fito yana nufar wayar shi ya dauka yana nufar hanya.

Fitowa tayi da size bag din ta tana bin bayan shi ta shiga motar sai wani boye dariyar mugunta take, ganin yanda ya wani hadiye rai sai wani cin magani yake a dole bai ji dadin cinye mashi couscous da tayi ba,wayarshi ce ta fara ringing sai kuma ya saki murmushi yana kallonta ta gefen ido.

Take mood dinta ya chanza b'acin rai ya mamaye farincikin da take ciki,da yake yana da Bluetooth a kunnenshi picking din wayar yayi yana wani lumshe yace.."Myluv." Sai kuma ya sake sakin wani murmushi yana cewa.."missing you too thank God ma na kusa zuwa naga wannan madarar kyaun taki mai mantar dani waye ni."

Dariya yayi a hankali sai kuma ya dan turo baki gaba yana cewa." Kin san dai yanda sonki da kaunarki kullun suke luguje a zuciyata dan haka kwantar da hankalinki ni naki ne fa,daman ai na gaya maki banda mata dan haka yau zanzo gida zan yi magana da Dad sai a fara maganar bikinmu."

Shan kwana yayi da motar yana daukar hanyar makaranta sai wani murmushi yake yana sakin zafafan kalaman kauna masu tsayawa a zuci sun dade suna wayarsu shida Baby(a wajen Madam Zulaihat kenan ba 🌚) amman dariyar da yake ba komai bace face shirmen da Moha yake mashi dan a bangaren Moha ba wani kalaman soyayya yake mashi ba.

Sai ma labarin duniya da yake bashi yana tambayar hope plan din su yana tafiya yanda ake so,dan kuwa a yanzun shi Moha kira kawai yayi amamn soyayyar shi ma yake da matarshi dan sune bayan su.. d'ayar dariyar da yake kuma yanda take wani kwabe baki idan yayi wata maganar tana nuna I don't care bayan ba haka bane ga fuskar ta nan murtuke kamar anyi accident a saman fuskar.

Bai fasa gaya kalaman soyayyar shi ba sai da yayi yanda ya gadama sannan ya kashe wayar tana kissing din wayar yana girgiza kai a hankali yace.."Inasonki sosai Kalbi." Kallon shi tayi tana wurga mashi harara bama tasan tayi ba,sai kuma ta maida kanta gefe tana share hawayen da suke son kwasa mata a gabanshi,bata yarda ya gansu ba dan sai da ta gogesu tas cikin dubara tana fara wakar nan gani na bari,ta zama dai takalmin kaza shi Najeeb show din nata dariya ya bashi wai ashe ta zama takalmin kaza Ina sakin da take jira yayi mata to.?

Hakuri ne kawai take tana nuna bata damu ba,amman ita kadai tasan zafin da rad'adin kishin da zuciyarta take mata,wai bai da mata?a gabanta yake cewa bai da mata okay bata da amfani a wajen shi kenan?bai daukarta a matsayin mata kuma bai mata kallon matarshi kenan.

Kwafa tayi tana cewa a zuciyarta.

"Zaka gane baka da mata,soon zaka shigo hannuna sai kayi man bayanin kana da mata ko kuwa baka da ita soon."

Sai kuma ta saki murmushi tana hango cigaba akan yanda ta fara plan din ta soon komai zai wuce kuma taga cigaba tun da har yau ya tanka mata sannu sannu dai..kallon yanda take murmushi yake sai kuma yaga kamar ma bata damu da abunda yayi mata yanzun ba...ba kamar jiya ba da ta kasa boye kishinta ta , amman yanzun ko a jikinta Kodai har yanzun tana son ya sake ta kamar yanda tace kwanakin baya? murmushi yayi Shima da ya tuna yanzun ta gama yi mashi habaicin ita ta zama takalmin kaza mutuwa ce zata raba.

Yana fatan hakan kuwa yana fatan suyi rayuwa ta soyayya tsintsa mai tsayawa a zuciya yana fatan yana addu'ar Allah ya nuna mashi ranar da zata nuna mashi *ZAZZAFAR KAUNA* yana fatan ranar shi kuma zai mallaka mata komai nashi ya zama nata and zan rayu da ita har *DA'IMAN ABADAN* ko mutuwa yana fatan ta fara daukarshi ta barta dan ba zai iya juriyar rashinta ba a kusa da shi.

Kowa da abunda yake sakawa a ranshi har suka iso makaranta. Yana gama parking ya fito yana mai kule motarshi ,dan kallon shi ta tsaya yi sai kuma ta turo baki tana yin gaba murmushi yayi yana girgiza kai yace.."I like ur shagwaba myKalbi." Tafiya kawai office yayi yana hango dramar da sukayi a gida sai yayi dariya dan karfin halinta burgeshi yake a yanzun kam.

Bayan ta shigo lecture hall samun waje tayi ta zauna tana d'aga ma Baby hannu tana mata murmushi, sai kuma ta dauke Kai tana mai duba karatunta dan nan da kwana biyu za'a fara yi masu test kuma ana gama test da one week za'a fara exams.

Bayan sun fito daga lecture suka tafu cateria duk da ita ba yunwa take ji ba,amman bata jin zata bar Baby ta tafi ita d'aya tana son ta bita ta ga ko zata je office din Najeeb ko kuwa,itama Zubaida ganin zasu barta ita d'aya sai ta tashi ta bisu tana cewa.

"Wai Baby maiyasa baki tashi da wuri kiyi breakfast a gida?ke dai kullun a school kike breakfast."

Murmushi Baby tayi tana cewa."bacci ne ke cutata wlh kuma Ina tashi sai nayi wanka ga kwaliya kafin na gama na karasa cinye time din kuma ban san nayi letting gaskiya balle yanzun da Dr ya gaya man yana son yaga mace ta na ba karatunta mahinmamci bai son ana wasa da karatu shiyasa nike son na chanza baki d'aya."

Dariya Zulaihat tayi tana cewa.."cabb kice kina da babban aiki a gabanki Zaki auri Dr Najeeb kuma kin saba da baccin safe anya kuwa kin shirya Baby.?"

Murmushi kawai Baby tayi tana girgiza kai can tace.

"Kwarai kuwa na shirya kin san soyayya tana chanza mutun,zan iya yin komai indai akan Habibi ne,to maiye dan na sadaurkar da baccin safe faranta mashi fa zanyi and na kuma samu lada fa Zulaihat miji fa ba wasa ba."

Dan tabe baki tayi tana gaba tace.

"Gaskiya kam miji ba wasa ba,Allah ya taimaka wai ni ana ta soyayya kamar wasu Laila da majunun yaushe zamu sha shagalin bakin.?"

Zama sukayi a cateria tana order din abinda take bukata tambayar su tayi ko suna bukatar wani abu suka ce A'a bayan an kawo mata ta fara ci sai da ta dan ci da yawa ta maido jinin jikinta sannan ta kalli Zulaihat tana cewa.

"Very soon I think da aure na zan dawo next semester."

Langwabar da Kai Zulaihat tayi tana daukar ruwa ta sha tace.

"Sure."

D'aga Kai Baby tayi tana cewa.

"Yeah."

Murmushi ta sakar ma Baby tana cewa .

"Can't wait."

Dariya Baby tayi tana cewa.

"Hope zaki attending din kowa ne program da zamu yi ko.?"

Juya Ido tayi tana cewa ."yeah of course,mai ma zai hanani zuwa bikinki?sai dai mutuwa ko kuma ciwo Baby."

Kad'a Kai Baby tayi tana cewa." Ya dace kam inason nazo gidanku na gaida su Mom but ba zan samu zuwa this week ba maybe sai next I'll surprising you."

Ajiye bottle din hannunta Zulaihat tayi tana cewa.."why not ba zaki zo this week ba.?"

Goge bakinta da tissue Baby tayi tana kallonta sai ta sakar mata wani murmushi tana cewa.."bcox I have a guest."

"Guest.?"

"Yeah that why ba zan shigo ba."

Dan tsaki tayi a zuciyarta tana kallon Baby tace.

"Kice Dr Najeeb yana da rival kenan?"

"Ko d'aya ai ban iya hada soyayyar shi da ta wani d'a namiji,shine farincikina and mafarkina and rayuwata why zan hada shi da wani.?"

Girgiza kai Zulaihat tayi tana hadiye wani abu a makoshin ta da yayi mata tsaye ya tokare ta, murmushin karfin hali ta sakar ma Baby tana cewa.

"Ai naji kice ai this week kina da guest ne shine yasa tayi tunanin ko rival din shi ne zai zo."

"Ko d'aya shine da kan shi zai zo kinga ai fita bata ganni ba daga nan sahad zan je nayi shopping ni kuma ban shawarar mai zan girka mashi ma."

"Ai nasan kin san favor dish din shi."

Kureta da Ido Baby tayi sai kuma can ta girgiza kai tana cewa.

"Ban Kai da sani ba, duk da nice ban so da na sani din ba amman wannan zuwan da zaiyi zan sani."

Tashi Zulaihat tayi tana cewa." Is better." Daga haka ta nufi kofa tana ce masu.."ku dan yi excuse dina zan je wani waje na dawo please, Zubaida ki bata shawarar wani recipe zata yi ma guest din ta."

Ficewa tayi ta barsu da kallon kofa dan da kallo suka bita sai kuma suka kalli juna suna rushewa da dariya sai da sukayi mai isarsu sannan Baby tace.

"Wallahi Sis Zulaihat tana bani dariya sosai harda mamaki ma."

Girgiza kai Zubaida tayi tana cewa.

"Good job Yan mata aikinki yana kyau sosai dan ana ta samun cigaba sosai a wanann plan din."

Sauke ajiyar zuciya Baby tayi tana cewa.."Alhamdullahi fatana kenan ta gane irin son da take mashi ki duba kiga yanda son shi yake yawo a kwayar idonta ga kishin shi da take kasa boyewa kwance a fuskarta amman duk ta kasa ganewa."

Dariya Zubaida tayi tana cewa.

"Ai yanzun duk ta gano abu d'aya ya rage mata ta sauke girman kan nan nata ta kula da mijinta shine kawai yayi mata saura."

"Soon komai zai zama kamar ba'ayi ba in shaa Allah."

"In shaa Allah,but naji kince kina da guest this weekend da gaske ko kin fad'a ne kawai.?"

D'aga Kai Baby tayi tana cewa.

"Serious ina da guest wanda zan aura zai zo and upper week za'ayi engagement in shaa Allah."

Farinciki fal a saman fuskar Zubaida tana cewa.

"Woow Masha Allah Sis Baby naji dadin wannan surprised new din Allah ya kaimu ya baku lafiya."

Dariya Baby tayi tana cewa ."Amin Amin Sis Zubaida thank you."

★★

Koda ta fito daga crateria ba inda tayi ma tsinke sai office din Najeeb,dan nocking tayi tana tura kanta ta shigo sauke idonta tayi a kan shi yana ta aikin shi.

D'agowa yayi yana mata kallo d'aya ya maida kan shi akan aikin da yake,amman mamakin abunda akayi mata yake dan kallo dayan da yayi mata ya hango damuwa mai tarin yawa a saman fuskarta.

Yana son ya tambaye ta amamn sai ya fasa gudun karda yayi laifi tun da ita laifi bai da wahala a wajenta..tana rufe kofar ta nufi rest room din office din shi ta shige tana kwantawa ta fara kuka a hankali a hankali.

Wato sun ma kusa yin aure? Tace next semester da aure zata dawo duka duka saura three week su gama wannan semester din kuma baki d'aya hutun one month ne zasuyi ba wani hutu mai tsawo ba...harda zance kenan zashi a wanann weekend din can kuma ta tuna da suna waya dazun a mota yace mata yana zuwa zaiga Dad din ta a fara maganar aure,amman bata ji ya gaya mata randa zaizo ba sai dai taji a bakin Baby din.

Ta dade tana kukanta sai da taji kanta ya fara yi mata ciwo ta tashi ta shiga toilet ta wanke fuskarta tana dauro alwallah tayi sallah sannan ta koma ta kwanta dan sam ji tayi bata bukatar shiga next lecture din da za'ayi masu dan ko kadan bata son ganin Baby .

Hakuri kawai take tana mata magana,amman ita tama kasa gane matsayin Baby a ranta bata dai jin tsanarta kuma yanzun bata jin sonta gata nan dai,amman wani lokacin har ganinta kwatata bata son yi balle har tayi mata magana ma.

Murmushi kawai yayi yana girgiza kai yana son rigimarta to the extent yasan dai maybe kawarta Baby ce ta kunnota idan ba ita ba to da wa take taraiya? Yasan dai bata fad'a da Zubaida balle yace da ita suka yi ko dai mai aka yi mata ohoo Allah ma sani.

Cigaba da abunda yake yayi yana duba time ganin lokacin lecture dinta yayi ya tashi ya nufi rest room din turawa yayi ya shiga yayi tsaye yana kallonta ya harde hannunshi saman chest din shi.

Idonta biyu zaune take tana kallon kofa,yana shigo ta sunburo baki gaba tana kauda kanta gefe, murmushi ya saki yana murza girarshi ta dama yana tambayar kan shi laifin mai yayi da za'a sunburo mashi baki?kallon dan karamin bakin yayi yana sauke ajiyar zuciya sai kuma ya dan shafa nashi bakin dan kallon nata bakin kawai yayi abunda ya faru jiya da dare ya dawo mashi har yana jin kamar bakin nata yana saman bakin shi.

Zama yayi gefen gadon yana kallonta can kuma ya tsuke fuskarshi yana kallonta yace mata.

"Tashi kije ki shiga lecture zaman mai kike man anan.?"

Turo baki tayi tana cewa.."nidai gaskiya." Sai kuma tayi shuru tana gunguni,kwafa yayi yana cewa .."kedai gaskiya mai? lecture din ne baki zuwa ko mai.?"

D'aga mashi kai tayi tana cewa.."ai ban lafiya fa." Tsaki yayi yana cewa.."yaushe kika fara ciwon?tun wuri ki tashi ki tafi kiyi attending din lecture ko kuma na baki mamaki a cikin room din nan."

Turo baki tayi tana cewa cikin shagwaba.."Ayya kaina ke ciwo fa,kuma ban san hayaniya zata k'ara man ciwon kan ne that why."

Zaman yayi yana kamota ya daura hannunshi a saman kan sai kuma ya kalleta ya tashi yana cewa.."ba ciwon da kanki yake karya kike tunda na tab'a babu wani zafi fine tun da baki zuwa daman ai kin rainani ban Isa nace kiyi kiyi ba."

Saukowa tayi saman gadon tana fisgar bag dinta ta fice ba ta ce mashi komai,tsaki yayi yana koma ya cigaba da abunda yake..bata dade da fita ba ko one hour bata yi ba ta dawo tana ce mashi ai malamin yayi covering ya sallamai su. Nuna mata wajen zama yayi ya Kara abunda yake sannan suka fito dan tafiya gida .

*Akwai Data available masoya akwai ko wane network kuma cikin rahusa 270 1GB ko wane network,banda 9Mobile shi  300 1GB*

*Zaki biya kudin data idan kina bukata ta wannan account din 8160508316 Jamila Bello Abubakar Opay bank,08160508316 for call or whatsapp*

Share✓

Продовжити читання

Вам також сподобається

MENENE MATSAYINA... Від Hafsat musa

Детективи / Трилер

45.1K 2.2K 51
"Don ubanki wanki dana barmiki kimin shine kika kiyimin Kika zauna kika rungume wannan shegiyar d'iyar taki wallahi koki aje ta ko kuma yanzu jikin k...
38.8K 2K 19
Labarin sanyayyar tacacciyar soyayyar ruhi biyu.. Wanda akai wa auren dole da juna, Amman basu san da hakan ba. Shin ya zaman nasu zai kaya idan suka...
3.1M 253K 96
RANKED #1 CUTE #1 COMEDY-ROMANCE #2 YOUNG ADULT #2 BOLLYWOOD #2 LOVE AT FIRST SIGHT #3 PASSION #7 COMEDY-DRAMA #9 LOVE P.S - Do let me know if you...
28.1K 1.7K 31
labari akan wata yarinya me rawar kai da rashin jin magana sam, labari akan taɓarɓarewar zumunci, tarbiyya da rayuwar 'ya mace idan ta rasa me jiɓant...