DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUN...

Von JameelarhSadiq

6.1K 233 122

labarin soyayya mai ciki da darussa iri iri mai masu tsayawa a zuci..masoyane suke nuna ma juna tsana marar a... Mehr

ZAZZAFAR KAUNA 01-10
ZAZZAFAR KAUNA 11_20
ZAZZAFAR KAUNA 21-30
ZAZZAFAR KAUNA 31-40
ZAZZAFAR KAUNA 41-50
ZAZZAFAR KAUNA 51-60
ZAZZAFAR KAUNA 61-70
ZAZZAFAR KAUNA 71-80
ZAZZAFAR KAUNA 81-90
ZAZZAFAR KAUNA 91-100
ZAZZAFAR KAUNA 101-110
ZAZZAFAR KAUNA 111-120
ZAZZAFAR KAUNA 121-130
ZAZZAFAR KAUNA 131-140
ZAZZAFAR KAUNA 151-160
ZAZZAFAR KAUNA 161-180
ZAZZAFAR KAUNA 171-180
ZAZZAFAR KAUNA 181-190
ZAZZAFAR KAUNA
ZAZZAFAR KAUNA 201-210
ZAZZAFAR KAUNA 211-220
ZAZZAFAR KAUNA 221-230
ZAZZAFAR KAUNA 231-240
ZAZZAFAR KAUNA 241-250

ZAZZAFAR KAUNA 141-150

222 10 14
Von JameelarhSadiq

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*141-150*

Driving yake yana dan satar kallonta a kai a Kai,so yake yayi mata magana amman yana tsoro saboda ba ta bashi fuskar da har zai iya yi mata magana ba,har mamakin yanda yake tsoronta yake ganin idan har bai yi da gaske ba to ba zai tab'a iya yi mata maganar da yake son yi mata ba kuwa...daurewa yayi yana dan gyaran murya ya kira sunanta,bata ansa ba kuma bata kalle shi ba,sake kiranta yayi a karo na biyu nan ma shuru tayi mashi dan kallonta yayi yana cewa.
"Jidda."
D'agowa tayi tana mashi wani kallo tace.."lafiya dai ko.?" Murmushi yayi yana cewa.."lafiya ba lau ba Jidda." Dan shuru yayi sai ya cigaba da cewa."ki taimakeni dan Allah Jidda." Dan karamin tsaki tayi yanda ba zai ji ba,ita fa surutun da ta guda kenan shiyasa taki biyo shi bata son naci da kunata,shi kuma nacin tsiya gare shi sai kace wani maye turo baki kawai tayi tana k'ara maida kanta gefe bata ce mashi komai ba.

Furzar da iskan bakinshi yayi yana mai cigaba da cewa.."ya kamata ace kin gane irin son da nike maki Kulu,ya kamata ace kin tausayama kuma kin yantani,kin maida komai ba komai mun cigaba da soyayyarmu kamar da,dan nasan yanda nike sonki kema haka kike sona please Jidda wallahi na hukuntu iya hukuntuwa ki duba man I beg please SP."

Girgiza kai kawai tayi sai kawai tayi murmushi har yau har gobe tasan babu son shi ko digo a cikin zuciyarta,da dai kam tabbas ta so shi tayi mashi son da ashe shi ba irin shi yake mata ba,tayi mashi so iyakacin gaskiyar ta a da tana jin tabbas idan har babu shi ba zata iya rayuwa ba kamar yanda shima yake nuna mata ashe duk karya ce yaudara ce,ba sonta yake ba jikinta yake so yana wani depend da wai kishi.kishin bazan har da wofi mutun da yakita lokacin da take bukatar shi.

Wani irin kuka da hakuri ne ba ta bashi ba a lokacin,babu hakurin da ba bashi ba har cewa tayi ya aureta zata za mai mashi baiwa yar aiki ya auro wata,ita dai kawai aurenta take bukatar yayi dan kawai tana son ko ganinshi tayi taji dadi,amman yace shi bai son ganinta baya bukata sam and shi maganar gaskiya ba zai iya auren karuwa ba,abunda ya dunga ce mata kenan maganarsu ta karshe da shi wanda itace sanadin barin gidansu ce mata yayi.

Shi ko ya aureta yana iya kashe ta saboda tsanar da yake jin yayi mata and yana nadamar saninta da yayi har yayi soyayya da ita karda ta sake kiranshi idan har kuwa ta kuskura ta k'ara Kiran shi sai ya kira Baba yace ya jama mata kunne ta bar Kiran shi idan kuma shi ke sata zai gaya mashi yama daina dan shi ba zai auri karuwa yar iska ba.
Wannan maganar da ya gasa mata yasa taji komai ya fice mata a rai bata son komai bata bukatar komai da kowa a rayuwarta zata je inda ba wanda ya santa tayi rayuwarta ba wanda yasanta balle har ya ce mata karuwa.

Sauke numfashi tayi tana cewa..."Yaya Haidar tun wuri kasan yanda zakayi ka fita daga rayuwata Ina ganin girmanka da mutuncinka ni da kake gani nan cikakkiyar karuwa ce mai lasisi kuwa kuma ba mutunci gare ni ba tsaf zan wankeka tas and ka manta da bakinka kace baka iya auren karuwa?to yanzun mai zakayi da karuwa yar'iska mai bin saurayi tana watan ni a wajen shi.?"

Har ya bude baki zai yi magana ta d'aga mashi hannu ta cigaba da cewa.."dakata man Haidar dan Allah bari kaji fa nifa nan wallahi ba zan tab'a aurenka ba da na aureka na gwanmace na Kara shiga duniya a karo na biyu kaji ma na gama maka,kuma wai ba kayi aure ba?to kaje kaji da matarka nima ka barni naje da wanda yasan mutuncina da martabata and ka barni na auri maisona tsakani ga Allah ba dan wani kyauna ba ko kuma surar jiki yana sona ne saboda da Allah dan haka kaji tun dare bai maka ba kasan nayi karda ka sake yi man maganar wani na soka har yanzun akwai sona zuciyarka."

Tsaki ta kuma ja tana cewa.."karyane wallahi Yaya Haidar baka sona kuma har abada ba zaka tab'a sona ba,okay na dawo kaga abunda matarka bata shi a jikinta shine ka dawo ka lalube ko?ko kuma ka tsotse ko?da kenan da ban da hankali ban san ciwon kaina ba shiyasa har na sakar maka jiki kana tsotsewa da lashewa Haidar idan ma karuwarcin ne ai kaine ka koyaman shi."

Kuka ta fashe da shi tana cewa.." wallahi kaci darajar iyayenmu da har abada ba zan tab'a yafe maka ba,ka cuceni ka yaudareni kaci amanata ka kuma nuna man maiye duniya ka koyaman darasin duniya in and out Haidar,tunda nike ban tab'a kissing din wani d'a namiji ba sai da ka shigo rayuwata ka daura ni a hanyar,ban tab'a romontic din kowa ba sai Kai nan da kayi amfani da kuriciyata ka koya man."

"Bayan ka gama samun abunda kake so sai akayi dai dai da qaddara ta fad'a man kace ba zaka aureni cikin mutane kace man karuwa bayan idan ma ni karuwarce to Kaine malamina a karuwancin duk ka manta ne wai Haidar?ka manta munanan kalaman da ka dun ga gaya man da har sai da suka yi *SANADIN* bari na gida?wallahi ba abunda Ahmad yayi man ba ya sani barin gida da shine da ba zan tsaya na haifi su Nana ba a gida,na rungumi qaddara ta na raini cikina har na haifo su lafiya,amman kai *SANADIN KA* na bar gidanmu saboda da kai Haidar na bar gidanmu dan haka wallahi da na aureka gwanma na mutu ba aure."

Shima kukan yake yana girgiza kai yace.."Kulu naji duk abunda kika fad'a tabbas ban kyauta ba kuma naga izina Kulu Allah ya saka maki tun anan duniya Kulu tabbas nayi aure kamar yanda kika ce Kulu,sai dai matar da na aura bata da kamun kai ban sani ba na aureta duk da kowa tsautsaran binciken da nayi kafin na aureta sai dai ashe duk a banza ne."

Dan shuru yayi ya cigaba da cewa..wallahi Jidda tun a haduwarmu ta farko naga ba yanda nayi tunani ba,amman nayi mata uzuri duk da Ina da bala'in kishi son da nike mata yasa nayi mata uzuri,daga baya kuma na gano ta bin mata ba karamin tashin hankali mukayi da ita ba har na korata gida,daga baya ta dawo bayan tace ta daina ashe ba anan ta tsaya ba har da maza take bi kuma bata fasa ba bin maza da mata ba wanda bata yi..daga karshe dai da wani na kamata a cikin gidana bisa gadon aurena daga ranar na yanke igiyar aurenmu yanzun banda mata Kulu kuma nasan hak'in kine ya kamani,kiyi man rai Jidda karda ki juya man baya karda ki duba kuskurena na baya Dan Allah."

Ita dai bata ce mashi komai ba duk da bata ji dadin labarin da ya bata ba,amman ko kadan bai bata tausayi ba kuma ba kuka ba ko kukan jini Haidar zaiyi mata wallahi ba zata tab'a jin zata iya auren shi ba...Koda kuwa babu AK ba zata aure shi ba balle yanzun da take da AK mutumin da yake mata son da yake mata har tsoro yake bata,mai zata yi da wanda ba sonta yake dan Allah ba,ta tabbata da ace matarshi na nan bai sake ta ba,ba zai tab'a dawo mata ba da yake bai da mata shiyasa ya dawo mata ita kuma ga banza sai ta aure shi aikuwa yana ruwa indai tunanin shi kenan.

Daidai gidan Wasi ya tsaya da motar yana sauke ajiyar zuciya yace.."da kamar yaushe zan dawo na daukeki Sp.?" Bude motar tayi tana cewa.."A'a ka bar shi ba sai ka dawo ba Yaya Auwal zai maido ni tunda yana gari." Girgiza kai kawai yayi bai ce Komai ba,bude baya tayi tana tada Dejarh da take bacci a baya tace ta tashi sun iso,fitowa Dejarh tayi tana kallon Haidar cikin dariya tace.

"Thank you uncle."

Murmushi kawai yayi ma yarinyar yana tunanin da ace komai bai cab'eba da shi aka haifa ma wa'anan kyawawan yaran masu kama da uwarsu,da kuma ace baice ba zai aureta ba da ta haifo mashi nashi masu kama da su.. amman yana nan bai da tsuntsu baida tarko ba d'a kuma ba mata gwanma ita Jidda din ta nuna su tace ita ta haifesu yaranta ne,shi kuma bai da wanda zai nuna saboda Koda Sopy ta samu ciki zuwa take ta zubda shi dan sau uku tana 'bari ana mata wankin ciki sai tace karamar mahaifa gareta bata iya rike ciki,haka ake ce mashi daga ita har likitanta daga karshe da likitan ya kamata suna Zina a cikin gidan shi.

Shigewa sukayi suka bar shi nan dan ko ta kan shi bata sake bi ba,tun da dai tace mashi ya ya tafiyarshi ai shikenan ta gama magana ta fita hak'in shi bata da abunda zata ce mashi kuma.

Da sallama suka shiga cikin gidan,wani ihu Wasi tayi tana makalkale Jidda sai kuma suka fashe da kuka tare suna rungume junansu,Yaya Auwal ne ya fito shima fuskarshi kunshe da murmushi yana basu hakuri sai da yayi da gaske ya samu suka yi shuru sanann suka shiga cikin dakin.

Kallonta Wasi tayi tana cewa.."Hauwa." Murmushi tayi tana cewa.."Na'am Wasi." Hawaye kawai Wasi ta goge tana cewa.."Allah na gode maka da barni da rai na har naga wannan ranar da nike kwana Ina addu'a, Alhamdullahi Alhamdullahi Alhamdullahi Allah na gode maka." Kuka ta fashe da shi tana cewa.

"Ji nike kamar mafarki nike komai fatana nike ya kasance a mafarki na tashi na ganni a saman gadon Mami,Hauwa na shiga hali marar musaltuwa Hauwa ban san ya zan gaya maki irin tashin hankalin da na shiga ba samun labarin rashinki,amman Alhmdulh mun gode Allah."

Share mata hawayen Jiddah ta kama yi yana cewa.."Nima watarana sai nace Ina ma mafarki nike I wish naji anzo an tadani,sai na mintsili kaina naji zafi sai na gane ba mafarki bane komai ke faruwa dani gaskene ba mafarki ba."

"Amman kuma idan na tuno kowa da tashin qaddarar sai na gode Allah da ya qaddarar man haka nasan kowa da kalar tashi qaddarar kuma Koda yaushe kuna raina da ku nike kwana nike tashi Wasi hope ma samaiki lafiya.?"

"Lafiya lau muke ga kuma namesake dinki."

Daukar yarinyar Jidda tayi tana mata wasa ta kalli Wasi tace. ",Masha Allah ya kuke ce mata?kuma ita kadai ce yarku?naga ko shekara bata yi ba." Murmushi Wasi tayi tana sauke ajiyar zuciya tace.

"KULU muke kiranta,eh kin san tun bayan tafiyarki lokacin ina da ciki wata hudu jin tafiyarki na yanke jiki na fad'i saboda tashin hankali dalilin faduwar na samu miscarriage daga nan ciki bai sake zama a mahaifata ba haka akaita fama itama Kulu ba anan kasar na haifeta ba,a India nayi rainon ciki da likitoci har Allah yasa cikin ya isa haihuwa,amman sunyi man wani aiki sun ce in shaa Allah zan k'ara haihuwa ba tare da ansamu wata matsala ba."

Share hawayenta Jidda tayi tana kallon Wasi tama rasa mai zata ce,wata irin soyayya ce Wasi take nuna mata ita da mijinta?duk tsawon shekarun da suka dauka basu haihu ba da suka haihu maimakon su sunan iyayensu sai suka saka sunanta,ita har bata san da bakin da zata auna soyayyar da suke mata ba.

Cigaba sukayi da labari har da Yaya Auwal zama yayi cikinsu suna labarin duniya bayan ta gaya masu rayuwar da tayi bayan ta bar gida da huduwarta da su AK har suka maidota gida...ta kuma gaya masu dawowar da Haidar yake kokarin yi a rayuwarta bayan ta gama gaya masu Yaya Auwal yace..bata da mijin da ya wuce AK dan maisonta ne da gaske dan haka karda ta tsaya b'ata mashi lokaci ta bashi dama kawai tun dai ba wasa zasu tsaya yi ba da wanann shawarar ta dawo gida.

★★

*ABUJA 🥀*

Koda ya tashi bai wani tsaya bata lokaci ba ya shirya ya shiga kitchen ya dama checkers custard ya zuba mashi madara sosai dan yana son yaga ya dama checkers ya zuba madara sosai da sosai ,plantain ya soya ya dawo parlo ya zauna ya fara ci yana dan kunna kallo dan yana son gaya maimaicin film din da bai kalla ba jiya.

Kuma yau sai ten zasu shiga school saboda shi ne zai yi masu lecture din,yana cikin sha ta fito cikin shirinta tasa wani lace ta fito ta nufi kitchen da kasan ido take kallon shi kamar yanda shima yake kallon nata ta kasan ido yana mamakin tashinta da wuri haka har da shiryawa ma.

Time ya duba taga 8:40 sauran 1hr 20mn ,girgiza kai kawai yayi ya cigaba da breakfast din shi yana kallonshi ,fitowa tayi hannunta rike da tea sai turiri yake ga kuma  sandwich dinta a saman plate guda hudu,maimakon ta wuce room dinta sai tayi breaches a parlo ta zauna kujerar da ke pasing din shi ta zauna ta fara cin abincin cikin yanga da yakuna.

Yanda take cin abincin ya dan dauki hankalinshi cikin yanga da class shi dai yana son yaga mace tana yanga a rayuwarshi ganin kamar zata gane yana kallonta ya dauke kanshi ya karasa breakfast din shi ya tashi ya bar parlon dan yana da Gotv a cikin wayar ya dunga kallon a ciki daga yau tun dai ya lura yanzun ta fara dawowa zaman parlo to shi kuma zai koma da zama room din shi.

Da kallo ta bishi sai kuma ta dauke kanta ta Karasa abunda take ta tashi ta maida kayan da tayi using da su ta samu foodflake ta zuba sandwich din ta ta kule tana dawowa parlo ta ajiye a center table ta shige room dinta tayi brush tana gyara fuskarta ta dauko veil dinta ta yafa.

Tana sane ta yafe veil din dan tasan tabbas sai yayi mata magana yace ta koma ta dauko hijab,haka nan taji tana son yayi mata magana bata jindadin shurun nan da yake mata...zama tayi tana jiran shi can ya fito cikin black shidda dinki babbar riga da ta sha aiki abunka da farar fata sai ta Kara fiddo mashi da kyaunshi da kuma kwarjinin shi.

Kallo d'aya tayi mashi taji wani b'acin rai ya mamaye mata zuciya har ta kasa dauke kanta a saman shi,yanda yayi kyaun nan tasan tabbas sai yanmata sun kawo mashi kansu take kuma Baby ta fad'o mata a rai hango irin son da Baby take mashi tayi sai kawai taji wani abu ya tokare mata makoshi dakyal ta hadiye shi tana kauda kanta k'asa tana tashi ta dauko basket din ta ta nufi kofa.

Da kallo ya bita sam shigarta bata yi mashi ba,da dai ace ba fita wani waje zatayi ba zama zata yi a gida bai da case da haka,amman ba yanda za'ayi tana matar aure ta fita haka da dan veil a kafad'a shi ba zai hanata saka gyale ba... amman tasan irin veils din da zata dunga yafawa, amman ba zai mata magana ba karda yayi mata magana ta zama zunubi kuma ita da take neman saki bata son shi amfanin mai ya dunga b'ata ma kan shi lokaci a kanta.

Fitowa yayi yana bude mota ya shiga itama ta shiga ya dauki hanya,shuru motar tayi ba kajin motsin komai sai karatun al'quri'ani mai girma gefen titi ta maida kanta tana mamakin irin tsanar da Najeeb yayi mata.

Wato bai kishinta?bai sonta kenan tun da dai baya kishinta,da ta san ba zai ce taje ta chanza veil din ta ba da ba ta sanya shi ba,daman ta sanya shi dan yayi mata magana har hijab ta ajiye saman gado da yace taje ta chanzo sai ta saka ta...amman gashi ya fito da ita haka da dan gyale babu ko kishinta babu kishi ko kadan tun da har ya fito da ita haka.

A bangaren Najeeb kuma mamakinta yake da karfin halinta ya yarda bata dauki auren shi bakin komai na tunda har ta iya fitowa da dan veil din nan,Ina son yake a haka Moha yake cewa yarinyar tana son shi idan har tana son shi ba zata fito haka ba kuwa amman ai komai ya kusa zuwa karshe in shaa Allah...dai dai inda yake parking din motar shi yayi parking fitowa tayi tana kama gabanta da kallo ya bita sai kuma yayi murmushi kawai ya kwashe kayanshi ya kai abunda zai Kai office sannan ya nufo lecture hall.

Koda ta shigo bata je wajen su Zubaida ba da taga sun wani had'e Kai da Baby suna magana k'asa k'asa,dan tsaki tayi tana hararar Zubaida ta samu waje ta zauna murmushi Zubaida tayi tana d'aga mata hannu, itama murmushin tayi mata kawai bata d'aga mata hannu ba kauda kanta tayi da sauri ganin Baby tana kokarin d'aga mata hannu.

Dan bata bukatar wani d'aga hannunta sam, murmushi Baby tayi tana kallon Zubaida tace.."Sis kinga abunda fa tayi man kina ganin ba matsala kuwa idan har na cigaba da pretending din nan gaban ta?ni ban san mu samu matsala ne kuma naga tana son mijinta tun da har ta kasa boye kishinta."

Murmushi Zubaida tayi tana cewa.."rabu da ita ba abunda zai faru nidai ai na gaya maki zaki rakani wani waje idan muka fita daga wannan lecture din ko.?" D'aga mata Baby tayi tana cewa.."okay ai shikenan ba damuwa Allah ya taimaka." Da Amin Zubaida ta ansa suna cikin magana Najeeb ya shigo can kowa ya kama kan shi ya shiga taitayinshi.

Cikin natsuwarshi da kamaiwarshi ya kowa masu ya kuma ansa tambaya ya kuma yi tambaya bayan ya gama ya kama gabanshi, daman shi baya k'ara time a cikin class da lokaci na cika yana ficewarshi bai wani tsayawa.

Bayan ya fita ne suka zo wajenta Baby tana cewa.."Sister barka da yau,an tashi lafiya.?" Murmushi tayi tana cewa.."barka dai Baby ya gida ya Momy.?" "Lafiya lau suke,ya naga baki tashi ba ko yau baki zuwa eatry ne.?" D'aga mata kai tayi tana cewa."gaskiya kam da yake ma yana zo da sandwich zuwa anjima zan ci but now am not felling angry."

Murmushi Baby tayi tana cewa.."Okay normal ne bari muje mu ci Koda shawarma ne ni banyi breakfast ba gsky only tea kawai na sha that why."

"Okay ku dawo lafiya." Cewar Zulaihat ta cigaba da karatunta tana rakasu da harara daga ita har Zubaida din wani irin haushin su take ji bama kamar Zubaida da ta ga tana wani rawar Kai a kan Baby..bayan gabanta take cewa tana son mijinta amman da ace ita ce ai ba zata tsaya bayan wata Baby ba,amman da yake ita bata son kishin yar'uwarta ba take bayan makiyarta.

Bayan sun fita ba inda suka zarce sai office din Dr Moha,zaune suka tadda shi yana waya bayan sun samu waje sun zauna suna dan jiran ya gama wayar,bai wani dad'e ba ya kashe wayar yana murmushi ya ansa gaisuwar Baby ya kalli matar shi yana cewa.
"Sannu Madam,anshe lecture hope dai bai gajiyar man da ke da yawa ba da zafin questions din shi.?" Murmushi kawai Zubaida tayi mashi tana langwabar mashi da Kai,ita dai Baby mamakine fal ranta ya haka?su duka lecturers ne mazajensu ga su yan'uwa suna auren abokai kuma gwanin burgewa.
Kallon Baby yayi yana cewa.."Khadija ya karatu.?" Murmushi Baby tayi tana cewa.."Alhamdullahi Sir." "Masha Allah,Allah ya taimaka." Amin suka ce baki d'ayansu can kuma Moha ya kalli Baby ya fara cewa.

"Khadija taimako nike son kiyi man dan Allah,duk da taimakon yana da dan girma amman ba sosai ba gaskiya." Kallon Moha tayi sai kuma tace.."wani irin alfarma ne wanann Sir.?" Murmushi Moha yayi yana cewa.."so nike a gaban Zulaihat kina nuna kina soyayya da Najeeb ki nuna mata soyayyarku tayi karfi,har kuna waya da shi ma only abunda nike bukata kenan."

Zaro ido Baby tayi tana cewa.."Sir amman taya haka zata faru?ni nan karda ku jefa rayuwata a matsala duba da son da nike mashi na kuma fara cire ma kaina son shi ya kuma zan yarda da wannan aikin nazo na samu heart attack daga karshe."
Murmushi Moha yayi yana cewa.."hakane kin kawo naki uzurin nima sai da nayi wannan tunanin amman baki da saurayi wanda yake sonki da gasken gaske.?"

Dan shuru tayi sai kuma can tace" Ina da shi" murmushi Moha yayi yace ."Good kin ga ta nan zaki jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya,da shi zakiyi soyayya a zahiri Najeeb ne amman da shi zaki dunga wayar soyayyarki a gaban Zulaihat kin ga kema a haka son shi zai shiga a zuciyarki in har kin yarda da hankalin shi da kuma tarbiyarshi."
Tabbas gaskiya ya gaya mata idan ta fahimta zata dunga soyayya da saurayinta a gaban kawarta to amman wajen zuwa office fa?ai tunda har za'ayi soyayya dole ko yayane Zulaihat ta dunga ganin tana zuwa office din shi,kallon Moha tayi tace.

"Naji Sir kuma na fahimta and ya maganar zuwa office fa?kasan dai tun da ana soyayya ya dace ta dunga gani na a office din shi ko.?" D'aga mata kai Moha yayi yana cewa.."baki da matsala zaki dunga zuwa office din shi amman ba ko yaushe ba ,Kinga dan kuna soyayya ba zaki dunga zuwa office din shi ko da yaushe ba gudun zargin mutane."

Hakane Sir zanyi duk yanda kace, daman Kamal ya matsaman akan na so shi na kasa zan yi kokari ta wannan hanyar nima na tusa soyayyar Kamal a zuciyata in shaa Allah Sir." Godiya sosai Moha yayi mata sannan ya sallamai su shima ya wuce office din Najeeb.

*Akwai Data available masoya akwai ko wane network kuma cikin rahusa 270 1GB ko wane network,banda 9Mobile shi  300 1GB*

*Zaki biya kudin data idan kina bukata ta wannan account din 8160508316 Jamila Bello Abubakar Opay bank,08160508316 for call or whatsapp*

Share pls✓

Weiterlesen

Das wird dir gefallen

1.7M 94.9K 87
Daksh singh chauhan - the crowned prince and future king of Jodhpur is a multi billionaire and the CEO of Ratore group. He is highly honored and resp...
1.6M 96.8K 39
"You all must have heard that a ray of light is definitely visible in the darkness which takes us towards light. But what if instead of light the dev...
20.6K 1.5K 40
labari ne akan Najma, wacce hasada, kyashi da yayu nata ya sanya a suka mata auren dole , inda zata fuskanta k'alub'e iri-iri a rayuwa. ku biyoni don...
31.3K 1.4K 9
Story of a young blind Fulani girl👸🏻