DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUN...

Af JameelarhSadiq

6.2K 234 122

labarin soyayya mai ciki da darussa iri iri mai masu tsayawa a zuci..masoyane suke nuna ma juna tsana marar a... Mere

ZAZZAFAR KAUNA 01-10
ZAZZAFAR KAUNA 11_20
ZAZZAFAR KAUNA 21-30
ZAZZAFAR KAUNA 31-40
ZAZZAFAR KAUNA 41-50
ZAZZAFAR KAUNA 51-60
ZAZZAFAR KAUNA 61-70
ZAZZAFAR KAUNA 71-80
ZAZZAFAR KAUNA 81-90
ZAZZAFAR KAUNA 91-100
ZAZZAFAR KAUNA 101-110
ZAZZAFAR KAUNA 111-120
ZAZZAFAR KAUNA 121-130
ZAZZAFAR KAUNA 141-150
ZAZZAFAR KAUNA 151-160
ZAZZAFAR KAUNA 161-180
ZAZZAFAR KAUNA 171-180
ZAZZAFAR KAUNA 181-190
ZAZZAFAR KAUNA
ZAZZAFAR KAUNA 201-210
ZAZZAFAR KAUNA 211-220
ZAZZAFAR KAUNA 221-230
ZAZZAFAR KAUNA 231-240
ZAZZAFAR KAUNA 241-250

ZAZZAFAR KAUNA 131-140

184 7 5
Af JameelarhSadiq

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*Comment section kuna chnza man ra'ay fa🧐,sharhinku yasa na gantale yi yin posting during weekends ko hutun ma bamuyi ba wai mai ya faru ne😱🫣*

*131-140*

"Baba Bishir." Sai kuma yayi shuru yana maida kan shi k'asa yana sosawa a hankali,hawaye ne kawai yaji suna zubo mashi ya zai yi da rayuwarshi?tabbas ba zai iya rayuwa babu Jidda ba kuma yana sane da irin kallon tsanar da take mashi..ya cancanci haka daga gareta amman yana son ta sake bashi dama a karo na biyu,yana son tayi mashi uzuri akan abunda yayi mata a baya,sonta da kishinta ne suka rufe mashi ido har ya aikata abunda ya aikata.
Baba Bishir ne yayi magana yana cewa.."Haidar ya ka kira sunana kuma kayi shuru? Yi maganarka kofa a bude take nan wajen zaman sulhu ne da fahimtar juna ya kawo mu dan haka ba kai ba duk wanda yake da magana yayi maganarshi."

Share hawayenshi yayi dan ya rasa ta ina ma zai fara,amman yaji zai dauki duk wani wulakanci da cin mutuncin da duk zatayi mashi ba ita ba Koda kuwa su Bash ne bama kamar Bash yasan waye Bash a wajen zuciya,zai jure zai dauka fatan shi ta zama mallakinshi ya kuma rayu da ita *DA'IMAN ABADAN* ya nuna mata irin *ZAZZAFIYAR KAUNAR* da yake mata furzar da iskan bakinshi yayi yana kallon Baba Bishir yace."Baba daman so nike a k'ara bani dama a karo na biyu Ina son na auri Jidda dan na k'ara gyara zumincin da nayi *SANADIN* b'atawa, tabbas nasan ban cancanci haka daga gareku ba duba da irin abunda nayi amman duk da haka karda a kalli laifina a dai sake bani damar na gwada sa'a ta."

Tunda ya fara maganar AK yake kallonshi yana jin gabanshi yana faduwa,daman abunda ya guda kenan karda  ta dawo Haidar ya sake shigowa da bukatar aurenta,yana tsoron karda itama Jidda din ta amince da bukatar Haidar duba da *SANADIN SHI* ta bar gidan su,sanadin son shi ne silar shigarta duniya.. d'ago kanshi yayi yana saukewa saman fuskar Jidda da ta kura mashi ido tana sakar mashi murmushi kalar tausayi yayi mata tana dan kwabe fuska,turo baki tayi tana nuna mashi karda ya damu ita din ta shi ce, murmushi yayi mata yana sauraren Baba Bishir yaji mai zai ce akan maganar Haidar din.

Rintse idonshi Haidar yayi yana budewa gami da furzar da iska mai zafi a bakinshi,dan komai sukayi akan idon shine mai hakan kenan nufi?kar dai ace soyayya take da wannan guy din duba da irin kallon da yake mata, itama ga yanda take wani shagwabe mashi fuska, inalillahi yayi a zuciyarshi yana jin jikinshi yayi sanyi dan alamu sun nuna ba ma zai samu karbuwa a karo na biyu ba a wajen Jidda.

Murmushi Baba Bishir yayi yana cewa.."wanann kuma ai ba humurunmu bane Haidar wannan maganar tsakaninka da Jidda ne,kasan dai  mu bamuyi ma yaranmu auren dole balle kuma Jidda ba yarinya bace tasan abunda ke mata ciwo zata iya zab'a ma kanta mijin da take so take son rayuwa da shi *DA'IMAN ABADAN* dan haka idan kun sasanta kanku bamu da matsala idan kuma baku sasanta ba kuma sai ayi hakuri a rungumi qaddara."

D'aga Kai kawai Haidar yayi yana godiya yana da gudurin tinkarar Jidda komai zata yi mashi kuwa zai sanye har sai yaga ta zama matar shi... addu'a akayi kowa ya kama gaban shi duk da Haidar yaso yayi magana da Jidda amman bata bashi fuska ba sai dai yayi hakuri ya bar gidan akan zai dawo washe gari.

★★

*ABUJA 🥀*

D'ago shi Moha yayi yana kallon shi sai kuma ya hau share mashi hawayen yana mamakin kalar abun da yasa Najeeb kuka,kuka fa kuka wannan na hawaye rabon da yaga hawayen Najeeb tun rasu Baffah ,amman yau ga Najeeb nan yana kuka har da hawaye hawaye sosai ba kadan ba.
Bai hana shi ba amman yana dan bubbuga mashi bayan shi har yayi shuru yana sauke ajiyar zuciya sai kuma ya kalli Moha yana cewa.

"Na gaji sakinta kawai zan yi kowa ya huta."

Zaro ido waje Moha yayi yana girgiza mashi Kai sai kuma ya kure shi da ido yana son tabbatarwa shin wannan maganar da gaske daga cikin bakin Najeeb ta fito ko kuwa? Koda bai da lafiya ne? tabbas bai da lafiya da yana da lafiya tabbas ba zai tab'a furta wannan kalma ba.

Wai saki,saki fa?sakin ma wai Zulaihat yake cewa zai saka,Ina son da yake mata ya tafi?Ina kaunar take?duka duka yaushe akayi auren da har maganar saki zata fara shigowa?auren da ko wata shidda bai yi ba ake cewa za'a kashe shi?wanann wani irin laifi ne tayi mashi mai girma haka?

Tabbas akwai abunda tayi mashi wanda ya tsaya mashi a zuciya har yake b'ata mashi rai har da zubda hawaye ga kuma saki da yake cewa zai yi ,shi abun ya tsorata shi sosai da yaji kalmar saki tana fitowa a bakin Najeeb,dafa shi yayi yana cewa.

"Yaushe ka fara shaye-shaye ban sani ba.!?"

Murmushi mai ciwo Najeeb ya sakar ma Moha,baiyi mamaki ba dan Moha yayi mashi wannan tambayar,dan ya lura kamar yana mashi kallon wani mahaukaci mahaukaci dan kawai yace zai sake wanda bata son shi..furzar da iskan bakinshi yayi mai huci sosai yana cewa.

"Moha amfanin mai zama da wanda bata sonka?gayaman dadin mai zama da wanda take kallon kwayar idonka tana gaya maka bata sonka bama iyakar bata sonka ba harda cewa take bata kaunarka sanann kuma ta kalli idonka tace daman ba dan Allah ka aureta sai dan wata manufa ta daban."

Shuru yayi yana jinjinar da kanshi jikin kujerar da yake zaune yana tura hannunshi saman lips din shi ya shafa a hankali yanda yaji yana mashi zafi kadan,d'agowa yayi yana kallon Moha yace.

"Ba wannan ba baka isa da ita ba,baka isa ka sata ba balle kace daina ta daina bata jin kunya bata jin komai ta kalli idon mijinta tayi mashi tsawa ko kuma tayi mashi tsaki ta gaya mashi duk abunda ta gadama."

Murmushi yayi yana cigaba da cewa.."Moha ka sanni kasan halina kasan abunda zan yi da wanda ba zan iya ba tabbas nasan ka sani sai dai baka san zan iya rabuwa da ita ba duk a tunaninka,bari kaji wallahi da gaske nike sai na sake ta taje ta auri wanda take so dan ba zan iya daukar rashin kunya ba,karda azo ayi abun kunya na karya yarinyar mutane azo kuma ana wata magana ta daban kaga maganin ayi karda a fara."

Murmushi Moha yayi yana cewa.."naji duk uzurinka Najeeb amman duk da haka bai dace kalma marar dadi irin saki tana fitowa daga bakinka ba,tabbas bata kyauta ba ai ko da ce bakomai bai dace ta dunga cewa bata sonka ba saboda abun ma bai dace ba amman kasan yanda za'ayi.?"

Girgiza kai Najeeb yayi bai ce komai ba yana kallon Moha,gyara zaman shi Moha yayi yana surbar tea sai kuma ya ajiye yana cewa.

"Tana sonka fa sosai."

Wani kallo yayi ma Moha yana cewa.

"Sona kuma?yarinyar da ke kallo idona tace bata sona ita sai na sake ta kake cewa tana wani sona,taya Kai kasan tana sona.?"

"Come down my friend." Dariya Moha yayi yana cigaba da cewa.." maida wukar bari kaji dalili na na cewa haka." Tsaki kawai yayi bai ce mashi komai ba sai dai zarara mashi Ido da yayi yana sauraren shi,Shima Mohar bai damu kin mashi maganar da yayi ba ya cigaba da cewa.

"Zulaihat na sonka Najeeb kuma tana kaunarka dalilina na cewa haka Ina ganin tsantsar sonka a cikin idonta ta kwantar da hankalinta ta fahimci son da take maka ne ta kasa saboda kawai a ganinta kaima ba sonta kake ba and sai yau na ida tabbatar da tana sonka Najeeb."

"Yau kuma? Mai ka gani har ka tabbatar da tana sona.?"

"Yau tun da suka shigo office dina na fahimci tana cikin damuwa,sai dai ban tambaye ta ba amman Ina lure da duk wani motsinta har muka iso gida ta wuce gida muka shiga namu gidan,bayan mun huta nike tambayar Darling maiye matsalar kawarta maike damunta? Kasan mai tace man.?"

Girgiza kai kawai Najeeb yayi yana kallon Moha cigaba da cewa Moha yayi.

"Wai wata yarinya ce take sonka kuma kawarsu ce mai suna Khadija suna kiranta da suna Baby,tun ganin farko da yarinyar tayi maka taji tana sonka kuma sai ta gaya ma Zulaihat irin son da take maka, darling tace take ya nuna b'acin ranta a jiya kenan har taki yin lecture din da zasuyi bayan taka."

"Yarinyar ganin irin abunda Zulaihat tayi mata sai ta nuna ma Darling rashin jindadi nan darling ke gaya mata ai Kai mijinta ne."

Tsaki yayi yana cewa..."wannan maganar shine yasa ka gane da tana sona?maiye tayi anan da har zaka wani ce tana sona?yarinyar da yau din nan take gaya man bata sona na sake ta,Kai kuma kana man maganar jiya da ta zama past ya wuce ?

Dariya Moha yayi yana cewa..."ai kaji matsalarka saurin fushi ka bari na Kai karshe mana sai ka kwalishe ni yanda kake so,da dai ba sunanka Najeeb ba."

Murmushin gefen baki yayi yana cewa."okay Ina jinka Alhaji Muhammad K Abdullah." Dariya Moha yayi da yaga ya dan fara saukowa tunda har ya kira full name din shi,tabe baki yayi yana cewa..."Okay kana jina ko Alhaji Najeeb H Abdullah." Lumshe Ido kawai yayi yana murmushi dan ya kosa ya karasa jin shirmen Moha ko kuma yace tatsinniya.

Cigaba da cewa Moha yayi. "To da Zubaida ta gaya mata alaqarku sai tace amman ta cigaba da pretending din tana sonka a gabanta,shine fa yau ta Kara yin maganarka a gabanta har tana cewa ita zataje office tace tana sonka,kaga wannan dama ce da zaka gane shin tana sonka ko bata sonka."

Girgiza kai yayi yana cewa..."Taya kenan.?"

"Yauwa nawan yanzun dai Ina son ka fita sabgar Zulaihat ka daina yi mata magana idan ba ta kama dole ba,ka dunga shareta ka nuna baka san tana waje ba,ka daina zama a dunga inda ta zauna idan zaku je makaranta ba ruwanka da yi mata magana iyaka ka dauketa ka ajiye ta kawai."

Ajiyar zuciya yayi yana cigaba da cewa..."Sannan kuma ita wanann yarinyar Baby zaka bata dama kuna gaisawa amman a gaban Zulaihat ku nuna kuna soyayya,har waya ka dunga kiranta idan har Zulaihat tana wajen anan ne kawai zaka gane shin tana sonka ko bata sonka."

"Naji Moha amman kasan ban san raini kuma karda a shiga hakin yarinya daga soyayyar wasa ta maida ta ta gaske kaga kamar an cuceta fa,kuma ya zan gane tana sona idan har akayi abunda kace?Dan ni bukata ta kenan ta soni ta kaunace ni ta kula dani kamar jariri ta nuna man *ZAZZAFIYAR KAUNA* shine kawai bukata ta kasan dai yanda nike son ta wallahi ban iya rayuwa idan ba ta dan da ita nike son nayi rayuwa har *DA'IMAN ABADAN*

"Hakane Najeeb kishi,idan har ta nuna kishinta akan taraiyaika da Baby tabbas tana sonka dan in babu so babu kishi,idan har kuwa akwai so to dole akwai kishi Najeeb tanan ne kawai zaka gane tana sonka idan har tana kishinka and maganar Baby baka da matsala zan mata magana da kaina nasan ba zata yarda ta maida soyayyar ta gaske ba duba da irin son da take ma Zulaihat tana son suyi kawaice sosai da sosai,saboda haka take ta cire sonka a ranta dan ka kasance mijin Zulaihat fa."

Murmushi yayi yana cewa.."shikenan damuwa ta daman karda ta maida abun gaske na yarda da shawararka 100% Moha ,daman na fita a harkarta zan kuma k'ara fita ne duk abunda zai hadamu magana zan kiyaye shi in shaa Allah."
Yauwa Najeeb kayi magana idan har ka daure ka jure wallahi sai kaga riba a wannan plan din namu dan nima ban jindadin irin zaman da kuke yi da juna,kuma Kai ne *SANADIN* duk abunda ya faru ,ba yanda banyi da Kai ba akan ka dunga sakar ma Zulaihat fuska kana janta a jiki amman kak'i wai Kai karda ta rainaka ,ai shi so ba ruwanshi da wani raini a gani na dan haka Ina ji a jikina komai zai zo da sauki ya zama labari in shaa Allah."

"Allah yasa Moha,ai na gane kuskurena wallahi karka so kaji yanda sonta yake wahalar dani ,inasonta inakaunarta sosai da sosai." Bayan sun gama tautaunawa suka tashi duba da har tara na dare ya wuce kowa ya shiga gidan shi.

Abun mamaki Koda ya dawo zaune ya taddata parlo ta bugu tagumi tana kallon tv,sai dai sam ba fahimtar abunda ake a tvn ba take kawai tana Kallon ne,ga books da ta ture gefe ga dukan alamu karatu tayi ,cikiciki yayi sallama yana shigowa d'agowa tayi tana ansawa sai kallonshi take kamar maison cewa wani abu,inda take bai kalla ba ya shige room din shi da yake ba yunwa yake ji ba balle ya nemi abinci.

Sauke ajiyar zuciya tayi tana jin wani sanyi da ta ganshi tashi tayi tana kashe kayan kallon ta taitara books dinta ta kashe gloves ta shige room daman bacci take ji rashin dawowar shi ne yasa bata shiga ta kwanta ba,haka kawai take jin kamar yana wajen budurwa dan bai tab'a kaiwa irin wannan lokacin ba sai yau.

Wanka tayi ta shirya ta kwanta sai dai baccin ya gagari idonta sai tunane tunane take ,tashi tayi zaune tana dafe kanta da yake mata ciwo mai hakan ke nufi?kodan ta gaya mashi gaskiya yake wannan d'agin shoulder din?kallonta fa baiyi sai kace wata dodo?chabb wai ita Najeeb yake ma haka,Koda yake ai sakinta zaiyi nan da wata biyar shiyasa yake mata haka daman ba sonta yake ba yana da wanda yake so ga dukan alamu daga wajenta ma yake yanzun ,tunda baici abinci ba duk yau tana sane da shi kuma ya dawo bai nemi abincin ba ya kwanta idan ba zance yaje wajen budurwarshi ba aka bashi Ina ya ciyo abinci....Kishi yasa bata hasaso gidansu ba ko kuma gidan Moha gidan kawai budurwa zuciyarta ta bata yaje yaci abinci.

★★

*GUSAU 🥀*

Kwaliya taci cikin wani lace pink mai ratsin army green,ba karamin kyau laces din yayi mata ba ga kuma kwaliya da tayi har jan baki ta shafa kuma yayi mata kyau da yake ba yab'a shi tayi ba,dai dai ta saka shi kuma ba karamin
kyau yayi mata ba.

Murza daurin dan kwalinta tayi mai V-shape tayi mashi see me ,tana fashe jikinta da turare masu tsada da dadin kamshi ,daukar wayarta tayi tana karanta text din da ya turo mata murmushi tayi tana tura mashi..."Inasonka Ina kaunarka nima Choco-milo,Beb Kaine mafarkina Kaine farincikina kuma kaine nike fatan kasance da shi har *DA'IMAN ABADAN* Kaine nike fatan ka kasance mijina na kula da kai na nuna maka *ZAZZAFIYAR KAUNA* ka kula dani ka mallaman zuciyarka rayuwata Ina kewarka sosai ka gaida man da Ammie ta ." Tura mashi text din tayi tana fitowa parlo kallo d'aya tayi mashi ta dauke kanta tana dukawa tayi ma Nana kiss a kumatu tana kallonta tace.

"Nana ba zaki je gidan Momy Wasi ba ke.?"

D'aga mata kai yarinyar tayi tana kamo hannunta tayi mata kiss tace..."Mami ni banji dadi...ba kaina ciwo yake ba kuma Uncle Bash yace zaizo ya kaine hospital." Dafa kan tayi tana cewa.."Ayya sorry Sweetheart bari na jira Yaya Bash sai mu tafi tare hospital din ko.?" Girgiza kai yarinyar tayi tana cewa.."Uhmm!ku tafi kawai ai daga hospital din sai nace ya kawo ni gidan Momy din ko.?" Murmushi kawai tayi tana shiga room din Mama dan ganin wainar da Dejarh take toyawa da har yanzun bata fito ba,ita har ta fito amman ita bata fitowa ba.

Iskewa tayi yarinyar tasha kwaliya sai daura dankwali take ,ta kasa yanda zatayi ma dankwalin ya zauna a kanta tsaye tayi a gabanta tana kallon yarinyar kamar wata babbar mace idan yaran suna abu, duka duka yanzun suke da shekara takwas amman idan suna wani abu baka cewa shekararsu kenan,mika mata hannu tayi tana cewa .

"Kawo na d'aura maki dan kwalin."

Makale kafad'a tayi tana cewa.."A'a Mami na kusa gamawa fa." Samun bakin gado tayi ta zauna tana kallon Mama tace.."Ina wuni Mama.?" "Lafiya lau,fatan dai Kinga bakonki zaune a parlo ko.?" Dan turo baki tayi tana cewa ." Mama dan Allah nidai nidai." Dakuwa Mama tayi mata tana cewa.."kedai mai?maza tashi kije ku gaisa kafin ta gama daurin dan kwali." Tashi tayi tana cewa.."Ni wallahi ko ganin shi ban son yi Mama ,ya dace ya fahimci haka ya fita daga sabgata yaje yaji da matar shi haba mana."

Tsaki kawai Mama tayi tana cewa.."sai kiyi duk abunda kika yi Niya tunda ba'a isa dake ba shikenan ko.?" Tashi tayi tana nufar hanyar fita tace ."Yi hakuri Mama ba zan sake ba." ", A'a Kulu kima sake mana daga gaisawa shine zai zama aiki ko Karan hauka ya cijeni wallahi ba zan ba Haidar aurenki ba,idan baki kulashi zasu ce ana wulakanta masu d'a kin san dai yanda iyayenshi suke da tsegumin tsiya ni kuma ban san wannan tsegumin." Fita kawai tayi tana zama parlo ta kalle shi tana cewa.

"Barka dai Yaya Haidar."

Murmushi yayi yana cewa.."Jiddah kinyi kyau sosai har inajin kishin ki fita da wannan kwaliyar haka wani ya kalle man ke." Murtuke fuskarta take tana mashi wani kallo tace..."Allah ko.?" D'aga mata kai yayi yana cewa.."kwarai kuwa Jidda,dan har yanzun sonki yana nan bai rage ba sai ma karuwa da yake Jidda ban san wani irin so nike maki ba Jidda please by my wife."

Tashi tayi tana kallon agogo tace..."kaga ni nan fita zan yi sai anjima Allah ya huce gajiya Yaya Haidar." Shima tashi yayi yana cewa.."okay ba damuwa bari na saukeku ko.?" Murmushi tayi tana girgiza kai tace.."Aa bar shi nagode sosai...Allah ya bar zuminci."  "Haba mana Jidda dan Allah ki barni na kaiku mana ba gidan Auwal bane ai ba wani nisa ke da akwai ba."

Yaya Bash ne ya shigo yana kallonshi can dai ya mika mashi hannu suka gaisa ya shiga ya gaida Mama ya fito da Dejarh,tashi Jidda tayi tana bin bayan Bash,shima Haidar din biyo bayan su yayi yana cewa.

"Haba mana Jidda ki daina yi man haka mana,nine fa PP dinki.waigowa tayi tana kallonshi sai kawai tayi murmushi tana cewa.."nagode sosai fa Yaya Haidar amman Yaya Bash zai Kaimu." Har zai yi magana Bash ya katse shi yana cewa.."kije ya sauke ki mana daman ai ba hanyarmu d'aya ba da zaki ce ni zan kaiki." Dan turo baki tayi tana kallon Yaya Bash ya shiga mota ya tafiyarsu ya barsu nan tsaye...can kuma ta turo baki ta nufi motar Haidar murmushi yayi yana bin ta da kallo can ya nufa motar ya bude mata ta shiga ya kulle sannan ya zagaya Shima ya shiga yana fita daga gidan.

*Gsky ku dunga yi kuna taimakon yar'baiwar Allah kuma sayen Data🥰*

*Akwai Data available masoya akwai ko wane network kuma cikin rahusa 270 1GB ko wane network,banda 9Mobile shi  300 1GB*

*Zaki biya kudin data idan kina bukata ta wannan account din 8160508316 Jamila Bello Abubakar Opay bank,08160508316 for call or whatsapp*

Share pls✓

Fortsæt med at læse

You'll Also Like

2.3K 100 16
wannan sanyin illa zaiyi miki acancikin ki, ai ita mace da ɗumi aka santa, ai ballagaza ita ke illata ƙanta da ƙanta sai sanyi ya kamaki kizo kisani...
1.7M 95.2K 87
Daksh singh chauhan - the crowned prince and future king of Jodhpur is a multi billionaire and the CEO of Ratore group. He is highly honored and resp...
45K 2.8K 46
Na kasa fahimta da gasgata abinda zuciyata ke ayyana mini a kansa, SO ne ko BIRGEWA?. Komai nasa birgeni yake, ban taɓa ji ko ganin wanda ya haɗa abu...
29.5K 865 23
Labarin Yarinyar da ta tashi a tsakanin yayyenta maza, da suke shirye da aikata ko menene saboda ita, ba ta san tsoro ba, rashin ji ya kaita ga haɗuw...