DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUN...

By JameelarhSadiq

6.2K 234 122

labarin soyayya mai ciki da darussa iri iri mai masu tsayawa a zuci..masoyane suke nuna ma juna tsana marar a... More

ZAZZAFAR KAUNA 01-10
ZAZZAFAR KAUNA 11_20
ZAZZAFAR KAUNA 21-30
ZAZZAFAR KAUNA 31-40
ZAZZAFAR KAUNA 41-50
ZAZZAFAR KAUNA 51-60
ZAZZAFAR KAUNA 61-70
ZAZZAFAR KAUNA 71-80
ZAZZAFAR KAUNA 81-90
ZAZZAFAR KAUNA 101-110
ZAZZAFAR KAUNA 111-120
ZAZZAFAR KAUNA 121-130
ZAZZAFAR KAUNA 131-140
ZAZZAFAR KAUNA 141-150
ZAZZAFAR KAUNA 151-160
ZAZZAFAR KAUNA 161-180
ZAZZAFAR KAUNA 171-180
ZAZZAFAR KAUNA 181-190
ZAZZAFAR KAUNA
ZAZZAFAR KAUNA 201-210
ZAZZAFAR KAUNA 211-220
ZAZZAFAR KAUNA 221-230
ZAZZAFAR KAUNA 231-240
ZAZZAFAR KAUNA 241-250

ZAZZAFAR KAUNA 91-100

210 10 5
By JameelarhSadiq

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*91-100*

Koda suka shigo cikin gidan cizewa Jidda tayi tana kallon Ammie sai kuma ta rushe da kuka tana girgiza kai tace.."Ammie ba zan iya ba, i'cant ba zan iya shiga cikin gidan ba,nasan ko na shiga koroni Baba zai yi kuma ga dukan alamu yana gidan tunda yau weekend Dan Allah Ammie kiyi man rai mu koma karda mu shiga nidai tsoro nike ji."
Dakatawa Ammie tayi da yake daga Jidda sai ita suka shiga cikin gidan su kuma su AK suna tsaye kofar gida dan sai an basu izini zasu shigo...kallon Jiddarh Ammie tayi tana cewa.."haba mana Daughter karda kiyi haka please kiyi addu'a sannan kuma ki sama kanki dauriya da juriyar komai zaki tarar a gidan nan but Ina son na Kara tuna maki duk tsanani yana tare da sauki fa.

And kowa da tashi qaddara ke haka taki qaddarar take,kuma in shaa Allah Ina gaya maki komai zai zo da sauki ba abunda zai faru sai alkhari Jiddarh kwantar da hankalinki please." gyade mata kai kawai Jiddarh tayi sai kuma ta share hawayenta tana tafiya jikinta sai karma yake tana 'bari tana mazari kattttt haka take.
Bakin kofar da zata sadasu da parlo suka tsaya suna yin nocking,sai da sukayi sau biyu ana ukkun ne aka zo aka bude...wata yarinyace da bata wuce shekara 7 ba tazo ta bude kofar,Koda ta bude tsaye tayi tana kallonsu Jidda daga can cikin gida suka ji ana cewa.

"Wai Nana waye ne yana nocking kuma ba kije kin bude ba zaki bar mutun a tsaye.?"

Yarinyar da aka kira da Nana ta turo baki gaba cikin shagwaba tace..."Mama na bude fa wasu ne.".."okay kuma ba zaki shigo da su ba, shiyasa Dejarh ta fiki iya tarbar bak'i fa." Yanda Nana take sunburo baki zaka gane an shagwabe yarinyar ba sai an gaya maka ba,kuma kallo d'aya zaka yi mata ka san tana cikin hutu da jindadi tana samun kulawa ta mussaman.

Murmushi Ammie tayi tana cewa.." sannu yanmata." Ita dai Nana dan murmushi tayi tana cewa."ku shigo." murmushi Jidda tayi tana bin yarinyar da kallo,yanda ta girma ga kuma kyaun da Allah ya bata har ya zarta wanda ta san ta da shi...shiga suka yi suka samu waje suka zauna,ita dai Jidda a sanyaye take suna dai Zaune sai ga wata yarinyar ta fito tsawansu d'aya da ta farko.kuma kamarsu d'aya tana fitowa ta kalli su Jidda sai ta washe baki tana cewa.

"Sannunku da zuwa." K'arasa isowa tayi gabansu tana kallon Jidda sai da tayi minti biyar tana kallon Jidda sai ta saka yatsanta a cikin dimples dinta tana cewa.

"Kina da kyau Ina son dimples dinki irin nawa."

Murmushi kawai Jidda tayi tana yin kasa da kanta sai goge hawaye take,maida kallonta wajen Ammie tayi tana cewa.."Kema kina da kyau." Shafa kanta Ammie tayi tana cewa."Allah yayi maki albarka." Dariya Dejarh tayi tana barin wajen direct kitchen ta nufa tana cewa..'Mama ki zo kiga wasu masu kyau a parlo." K'arasa juye abincin tayi a cikin warmers tana kallon Dejarh tana murmushi tace.

"Saurin da nike kenan na fito naga su waye Dejarh,maza dauke warmers din ki fara Kai su dinning kafin Babanku ya dawo ko.?" dariya yarinyar tayi tana fitowa daga kitchen tace.."Mama tace ga tanan fitowa ku dan K'ara hakuri." Sai kuma ta kalli Nana tana cewa.."Nana ki taso mu ida kwaso kayan mu kawo dinning." Tashi Nana tayi tana shiga kitchen dan taimakawa yar'uwarta.

Anan Jidda ta k'ara banbance Nana da Dejarh ita Nana miskilace sab'anin ita Dejarh da take da son mutane da kuma yawan magana,bayan sun gama jera dinning din suka dawo parlo suna duba homework din su kwabe fuska Nana tayi tana cewa.

"Ni ban gane nan ba Dejarh karda Uncle Bash ya dawo yayi man fad'a,yi man kinji please." Waro Ido Dejarh tayi tana cewa."kin manta yana gane note dina da naki kina son nayi yayi bulala  ko.?"

Girgiza kai Nana tayi tana cewa..okay yi man spelling sai na dunga rubutawa please." D'aga Kai tayi tana gaya mata tana rubutawa gwanin burgewa,suna cikin homework Mama ta fito tana sauri tace.

"Bayin Allah kuyi hakuri na barku zauna da yake kun tada na kusa karasa girkin ne shiyasa ga yaran nan ba wayau ne dasu ba..ba komai suka iya ba balle na bar masu." Ko kadan Mama bata lura da Jidda ba da yake tayi k'asa da kanta tana kukan zuci tun da Mama ta fito.

Ajiye masu ruwa Mama tayi tana murmushi dai dan bata gane Ammie ba,karfin hali kawai tayi tana ajiye mata ruwan da ta fito dashi daga kitchen,amman ita dai sai taji gabanta yana faduwa balle duniyar nan da tazo karshe babu amana da yarda a cikinta.

Mama na kokarin yin magana Baba ya banko kofa ya shigo ko sallama babu haka ya tsaya a gaban Ammie yana mata wani kallo can ya nuna mata kofa cikin fushi yace..."Maza ku tashi ku bar man gida,karda na sake ganinku a cikin gidana har abada idan kuma ta kuskuren sake shigo man gida wallahi wallahi sai nayi mata abunda har ta mutu ba zata tab'a mantawa da ni ba."

Kuka Jidda ta rushe da shi tana d'ago kanta,da sauri Mama taja baya tana innalillahi wa'innalaihirajiun can kuma ta durkushe a wajen tana rushewa da wani irin kuka...wata irin tsawa Baba ya buga masu yana nuna mata kofa yana cewa.."Zaki fita ko sai na tsine maki albarka." Tashi Ammie tayi tana cewa .."Haba Kai ko Alhaji Abdullahi abi komai a sannu komai sai yazo da sauki amman fushi da tsunuwa ba naka bane,ai nasa farinciki zakayi da godema Allah dawowar ta gareku ba tsinuwa ba."

D'aga mata hannu Baba yayi yana cewa.."Baiwar Allah cikin girma da arziki tin ban Kai bango ba ku fitar man daga gida, Jiddarh dai ce ko?tuni na sallama ma duniya ita na barta da duniyar da ta zab'a,dan ni tuni na fiddata daga cikin 'ya'yana dan haka karki sake dangantani da ita."

Kuka ta fashe dashi tana cewa.  "A'a Baba karda kayi man haka,kayi hakuri ka tsaya ka saurari uzirina  wallahi Baba ba zan sake ba dan Allah Baba karda kayi man haka."Tsaki Baba yayi yana shiga wani daki,da belt ya fito a hannunshi yayo kan Jiddarh ya fara zabga mata a jiki,ganin yanda yake bugunta kamar ba shi bane ya haifeta yasa Mama ta shiga tsakaninsu tana bankade Baba tana kare Jidda tayi mata rumfa tana cewa.

"Kashe ta zaka yi Abdullahi.?"

Kuka Mama ta fashe da shi tana cewa.."wallahi ba zan zuba maka ido ba ina kallo ka kashe man ita ba." Nunata da yatsa Baba yayi cikin fushi yana cewa.."Aisha maza ki ban waje." Banza Mama tayi mashi tana Kara shigar da Jidda jikinta tana kuka Jidda na kuka haka ma Ammie,ida shigowa su Dad sukayi saboda izinin shigowa da Bash yayi masu,da sun ki shigowa tunda Baba yace karda su shigo mashi gida,amman Yaya Bash yace su dai shigo ai shi yace su shigo karda su damu da duk furicin da Baba yayi masu yana cikin fushi ne shiyasa.

Wani kallo Baba yayi mata yana cewa.."magana fa nike maki Aisha,ni nan Abdullahi nace ki matsa ki ban waje na koya man wanann yarinyar hankali."

Kin matsawa Mama tayi sai ma cewa da tayi.."babu inda zani matsa wallahi sai da ka koya mana hankalin tare,amman ka sani ba zan matsa ko nan da nan ba,haba mana bawan Allah Kai da zaka yi murna dawowarta gida ka gode ma Allah da maido mana da hankalinta har ya karkarto ya dawo gida,hannunka baya tab'a rubewa ka yanke."

Tsaki Baba yayi yana lallata masu belt su dukansu ya had'e yaita zabga masu ganin abun ba mai karewa bane Bash da Muhd suka shiga suna kallon Baba cikin takaici da b'acin rai da Kuma zuciya da ta kawo Yaya Bash wuya ya kalli Baba yana cewa.

"Bugun ya isa haka Baba,ka sani wannan abun da kake ba hanya ce ka dauko wanda zata bulle da Kai ba,gaya man dadin da kakeji kana dukan mahaifiyarmu a gaban idonmu a gaban bakuwar fuska.?"

Kallonshi Baba yayi yana cewa.."Dan Ubanka ni zaka gaya ma magana.?" "Ai ba gaya magana bace gaskiya ce na gaya maka, yarinya ta dawo gida maimakon muyi murnar dawowarta sai kuma akashin haka,bayan bamu da guri da fata sai na Allah ya dawo mana da ita gida cikin koshin lafiya haba mana Baba jininka ce fa kake ma wannan tozararci , tabbas tayi laifi dan laifi amman tun da ta dawo kuma tace ta tuba ba shikenan komai ya wuce ba."

Janyo kwalarshi Baba yayi yana wasga mashi mari cikin zafin rai da kunnar rai yace.."bai wuce ba dan ubanka nace bai wuce ba ubana kuma sai ta bar man gida,Kaine dai kake wata addu'ar Allah ya baiyanata amman ni ban yin wata addu'a..addu'ar da nike kullun Allah ya nisantata daga garemu ya cire mata wani gida dan bani bukatarta na bar ma duniya.

"Idan Kai baka bukatarta Abdullahi ni nan uwarta Ina bukatarta komai ta zama kuwa,kai ko da da 'ya'ya ta dawo man da kuma ciki a jikinta wallahi sai na ansheta na kula da ita tun da daman ba wani yayi man nakudarta ba, ni kadai nasan wahalar da nasha kafin na samaita ni nan nasan zafinta tunda nasha wahala kafin Allah ya bani ita nasan zafin haihuwarta."

Shuru Baba yayi yana kallonsu zuciyarshi cika fal da mamakinsu,wato hade mashi Kai zasuyi kenan?har shi Aisha take kallon kwayar idonshi tana gaya mashi magana?shi take gaya mashi bai san ciwon Jidda ba,bai san zafinta ba akan gaskiyarshi.

Dan ya nuna rashin amincewarshi da dawowa cikinsu zasu nuna mashi b'acin rainsu a fili ,kallon fuskar kowa yake a cikinsu yana kallon reaction din kowa,shi dai Muhd baice komai ba saboda magana ba cika damunshi tayi ba,amman kana kallonshi zaka ga zallar b'acin rai a fuskarshi ,dan wani irin kallo yake ma Baba wanda ya kasa gane fassarar kallon.

Sulaiman kuwa hawayene a fuskarshi sai zuba suke ya kasa hanasu zubowa shi kuwa Humaid idanuwnshi jajir suke ya kuma kama hannun Jidda yana murzawa alamar lailashi kenan,sannan Usman shima yana kusa da Mama yana share mata hawayenta amman ko inda Baba yake bai yarda ya kalla ba,mai hakan ke nufi?

Tambayar da yake yi ma kanshi kenan,wato dai yaran nan duka ba wanda yake bayanshi sun nuna mashi sunfi son uwarsu da yar'uwarsu a kanshi,tabbas zai nuna masu gidan shi ne kuma ba wanda yake tsoro a cikinsu tunda dai shine dai silar zuwansu duniya.

Ajiye belt din hannunshi yayi yana nuna masu kofa yace cikin fushi.."ku sake ta nace ta bar man gida." Yanda yayi maganar with serious yasa Mama itama cin serious din tana cewa.."zata bar maka gida Abdullahi kamar yanda ka bukata tunda daman ai gidan ba nata bane kuma ba nawa bane tabbas gidan ba na kowa bane sai naka,amman ka sani kafata kafar Jidda ba zan tab'a barinta ta koma inda ta fito ba."

Murmushi takaici Baba yayi yana kallonta yana mamakin Karfin halinta yace.."haka kika ce ko Aisha." Komai bata ce mashi ba ta kama hannun Jiddah ta shiga room dinta da ita can sai gata ta fito rike da trolly sai kuma ta kamo su Nana tana cewa.

"Ai magana tazo karshe Abdullahi gidane dai zamu bar maka tunda haka kake bukata ba shikenan ba.?" Shi dai Baba shuru yayi bai sake cewa komai ba,amman duk jikinshi yayi sanyi dan tunda ya auri Mama bata tab'a yin yaji ba balle azo ga saki .

Amman yau wai ita take cewa zata bar mashi gida dan kawai ya fadi gaskiyarshi tabbas ba zai hanata yanke hukuncin da taga ya fiye mata kamar yanda shima ba zata hanashi daukar hukunci ba akan Jidda tun da ba fin shi son Jidda din tayi ba.

Yana tsaye yana kallon Bash ya dauko kayan su Nana suka bude kofa suka fita,da Ido kawai ya bisu dan dukansu bin bayan mahaifiyarsu sukayi ba wanda ya tsaya...itama Ammie bin bayan su tayi aka bar Baba daga shi sai Dad da AK,bayan sun fice Baba ya zauna saman sofa yana dafe kanshi abun duniya ya damaishi.

Dafashi Dad yayi yana cewa.."Haba Alhaji a gaskiya banji dadin abunda ya faru ba,ai idan rai ya b'aci hankali baya gushewa fissabillahi ko kadan banyi tunanin abun nan zai faru ba,haba mana ai hannuka baya rebewa ka yanke Alhaji."

Shi dai Baba shuru kawai yayi bai ce komai ba sai ma kallon Dad kawai da yake yi,dan wani irin abune ya tokare mashi zuciya ba haka yayi tunani ba,yasa Mama zata goya mashi baya akan hukuncin da ya yanke ma Jidda.

Yasa ta cire ta a zuciyarta kamar yanda take gaya mashi ashe duk fadi take,maiye amfanin Jidda a cikinsu yarinyar da ta watsa mashi k'asa a Ido,yarinyar da ya bata yarda 100% yarinyar da yake jinta a cikin rainshi sama da sauran y'ay'anshi,amman rana d'aya ta kunyata tashi ta tozartashi a gari.

Tasa ya zama abun nuna da Ido da baki har da hannun,ta sa yaji komai na duniya ya fice mashi yarinyar da tasa yaji gwanma mutuwa da zaman duniya,ita ai shedace akan halin da ya shiga ta Sanadin tafiyar yarinyar wani irin nemane bai mata ba,kamar yayi hauka haka ya koma Ashe duk a banza yayi ,kuma shine za'a juya mashi baya dan kawai ya fadi gaskiyarshi.

Kallon Dad yayi yana sauke ajiyar zuciya yace.

"Rabu dasu Alhaji,fushinsu na banzane zasu gaji su daina ne,amman abunda na sani Kulu ba zata tab'a zaman gidan nan ba."

Girgiza kai Dad yayi yana cewa.."ai kuskurene Babba Alhaji Abdullahi idan har kace Kulu ba zata zauna maka gida ba,to idan ka koreta Ina kake son taje.?"

Tsaki Baban yayi cikin tafasar zuciya yace.."daman can da ta gudu yawan tazubar dinta ni na sama mata inda zata je?Dan haka ni ba damuwa ta bace idan ta tashi taje duk inda zata je ba ruwana saboda yanzun ban had'a komai da ita ba tuni na yafeta daga cikin y'ay'ana."

Fahimtar da har yanzun yana cikin fushi yasa Dad kallon AK yana cewa.

"Son tashi muje mun dawo zuwa anjima."

Cikin mutuwar jiki AK ya tashi yana kallon Baba cikin kwantar da murya yana cewa.."Allah ya baka hakuri Baba,dan Allah ka yafe mata wallahi Jidda mutuniyar kirki ce ka zauna kayi tunani ka kuma tuna amanace Allah ya baka zaibtambayeka ranar gobe kiyama and ana ma Allah laifi mumuna kuma arokeshi yafiya kuma ya yafe Baba."

Yana gama fadin haka ya juya ya fita yana share hawayen shi dan sam bai ji dadin abunda ya faru ba,duk da su dukansu suna da gaskiya Baba yana da damar da zai nuna b'acin rainshi amman ba irin haka ba,itama Mama tana da damar da zata fad'i abunda ke ranta sai dai ayi hakuri kawai.

Har suka fita Baba baice masu komai ba sai ma ido kawai da ya bisu dashi yana nazarin maganarsu,dan maganar AK ta dan fara sauko da shi ya fara control din fushin shi har yana son ya samu sararin yin tunani.

★★

Tun da suka baro gidan Baba ba inda suka yi ma tsinke sai gidan Yaya Muhd dake G.R.A da yake yayi aure yana auren wata kawar Meenat,shima Yaya Bash yayi aure ga gidan shi ga na Yaya Muhd,Humaid kuwa an sanya mashi biki bai fi saura wata biyu a daura mashi aure ba,dukansu a unguwa d'aya suke da gidaje kuma neighbors din juna ne dan har sun fara kewaye gidanje suna son suyi gate d'aya idan ka shigo first gate kuma ka shiga main gate din ka.

Koda suka sauka a gidan Yaya Muhd babban parlon gidan suka yada zango,tin a mota Jidda take kuka kamar ranta zai fita komai na duniya ya fice mata a rai bata son komai duba da abunda Baba yayi mata kamar bashi bane ya haifeta...gaskiya abun yayi mata ciwo sosai bata tab'a tunanin Baba zai yi mata haka ba Koda kuwa a mafarki ne.

Zaune suke su duka sunyi shuru ba abunda ke tashi a parlon sai kukan Jidda tsaki Yaya Bash yayi yana buga mata tsawa yana cewa.."kukan uban mai kike yi mana dan ubanki?Zaki yi mana shuru ko sai nazo na karasa cin ubanki a wajen nan yanzun nan."

Rufe bakinta da hannu tayi tana share hawayenta tsaki ya kuma saki yana cewa..."Ai Kinga abunda ya faru ko? Ai ba wanda ya janyo wanann masifar  sai ke Kulu,ban san yaushe kika zama sakarai marar tunani ba,Ina hankalinki da tunaninki ya tafi? dadin mai kika ji da kika watsa mana k'asa a ido.?"

Shuru tayi bata ce komai ba cigaba da cewa yayi.."tabbas dole Baba yayi maki abunda yayi maki Jidda,dan a kanki sai da zumincinmu ya tarwatse akan ki sai da Baba ya kwanta akan gadon asibiti saboda kiranki da suna karuwa dasu ke yi a cikin family,akan ki muka daina motsi mai karfi saboda da mun motsa sai anyi mana gori,a kanki muka cire kanmu daga cikin family muka koma bamu hudd'a da kowa saboda guje ma gori da ake mana,kinji dadin haka ai ko Kulu? hankalinki ya kwanta ko Kulu.?"

Girgiza kai kawai take tana share hawayenta,cikin kuka Mama ta cigaba da cewa.."laifin mai nayi maki mai zafi Kulu da zaki saka man da haka?maiyasa? maiyasa kika iya guduwa daga gidan ubanki kika koma inda baki da kowa Kulu.?"

Kuka ta sake rushewa da shi tana cewa.."duk kuyi hakuri ku yafe man tabbas nasan ni mai laifi ce a wajen ku, kuma bani da bakin da zan baku hakuri dan nasan  na kunsa maku bakin ciki sai dai ku sani a lokacin harda rashin wayau da hankali suka sa na bar gida ba tare da tunanin komai ba."

D'ago kanta tayi tana share hawayenta ta cigaba da cewa. "Na bar gida ne saboda da ba zan iya rayuwa babu Yaya Haidar ba,a lokacin inajin zan iya mutuwa idan har bai aure ni ba,Ina jin a lokacin ba zan iya ruyuwa da wani bayan shi ba ,da shi nike son na rayu har *DA'IMAN ABADAN* shiyasa na yanke ma kaina hukuncin bari gida kuma ina addu'ar Allah yasa na mutu ko na huta sai dai Kash kana naka Allah kuma na nashi ,Dan Allah kuyi hakuri."

Duk abunda ake Yaya Muhd baiyi magana ba sai yanzun ya kalli Jidda yana cewa..."tabbas kinyi disappointed dina kuma baki kyauta ba Jidda Haidar din banza Haidar din wofi mai akayi akayi wani Haidar da har zaki tafi ki barmu?mutumin da yace baya aurenki saboda qaddara ta fad'a maki ba wanda tafi karfi qaddara ke taki qaddarar haka take Kulu,amman ki sani kinyi kuskure da har kika bar gida saboda da soyayya, bayan shi bai damu da tafiyarki ba ana cikin tashin hankalin tafiyarki yayi aurenshi Kinga daman can ba sonki yake ba,da ace yana sonki da duk baiyi haka ba.'

Cikin kuka Kulu tace..."kamar yanda ya cireni a zuciyarshi nima haka na cire shi kuma Ina bakin cikin abunda na aikata akan son wanda bai sona bai damu dani ba tir da mai hali irin nawa."

Sosai sukayi mata fad'a sanann sukayi ma Ammie godiya sosai,a gidan Yaya Muhd suka kwana da Mama cewa tayi zasu kwana a gidan Humaid sai Yaya Muhd ya hana yace kawai su kwana gidanshi tun da akwai waje.

Washe gari bayan sun tashi sunyi breakfast suna bata labarin fad'an da Baba yayi da Baban Yaya Haidar akan yana cewa haka nan akayi ma d'anshi wulakanci dan yace mata karuwa ashe dai ba karya yake ba tun da gashi ta nuna halinta...sun gaya mata yanda family ya kasu gida biyu wasu sunce bai kyauta ba wasu kuwa sun ce ai gaskiya ya fad'a...sun gaya mata irin halin da Yaya Auwal da Wasi suka shiga akan tafiyarta har sai da Wasi tayi miscarriage saboda tashin hankalin da ta shiga na guduwar tata,suna cikin fira Baba ya kira Yaya Muhd yake tambayarshi Ina su Mama suka tafi nan yace suna gidanshi,cewa Baba yayi to gashi nan tafe gidan nashi zasuyi magana.

*AMATULLAH DATA SERVICES*

*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350

9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500

VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank

08160508316 for call or whatsapp fa

Continue Reading

You'll Also Like

1.6M 98.4K 39
"You all must have heard that a ray of light is definitely visible in the darkness which takes us towards light. But what if instead of light the dev...
38.8K 2K 19
Labarin sanyayyar tacacciyar soyayyar ruhi biyu.. Wanda akai wa auren dole da juna, Amman basu san da hakan ba. Shin ya zaman nasu zai kaya idan suka...
7.2K 254 12
_Duniya makaranta a lokacin da wasu suke shiganta a lokacin ne wasu ke barinta,wasu na zuwa Duniya wasu kuma na barin Duniya, Rayuwa kamar shafin lit...
3.1M 253K 96
RANKED #1 CUTE #1 COMEDY-ROMANCE #2 YOUNG ADULT #2 BOLLYWOOD #2 LOVE AT FIRST SIGHT #3 PASSION #7 COMEDY-DRAMA #9 LOVE P.S - Do let me know if you...