DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUN...

By JameelarhSadiq

6.2K 234 122

labarin soyayya mai ciki da darussa iri iri mai masu tsayawa a zuci..masoyane suke nuna ma juna tsana marar a... More

ZAZZAFAR KAUNA 01-10
ZAZZAFAR KAUNA 11_20
ZAZZAFAR KAUNA 21-30
ZAZZAFAR KAUNA 31-40
ZAZZAFAR KAUNA 41-50
ZAZZAFAR KAUNA 51-60
ZAZZAFAR KAUNA 61-70
ZAZZAFAR KAUNA 81-90
ZAZZAFAR KAUNA 91-100
ZAZZAFAR KAUNA 101-110
ZAZZAFAR KAUNA 111-120
ZAZZAFAR KAUNA 121-130
ZAZZAFAR KAUNA 131-140
ZAZZAFAR KAUNA 141-150
ZAZZAFAR KAUNA 151-160
ZAZZAFAR KAUNA 161-180
ZAZZAFAR KAUNA 171-180
ZAZZAFAR KAUNA 181-190
ZAZZAFAR KAUNA
ZAZZAFAR KAUNA 201-210
ZAZZAFAR KAUNA 211-220
ZAZZAFAR KAUNA 221-230
ZAZZAFAR KAUNA 231-240
ZAZZAFAR KAUNA 241-250

ZAZZAFAR KAUNA 71-80

257 13 4
By JameelarhSadiq

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*71-80*

"Dallah can Malama maza koma inda kika fito ki chanza dressing din ki." Kallon kanta ta dunga yi daga sama har k'asa sai kuma ta kalli gefe da gefe ko zata hango makusar shigar tata da yake cewa wai ta chanza....ganin bata ga aibun shigar ba ta mai da kallonta kanshi tana cewa.."Mai kuma wannan shigar tayi da har zaka wani ce na chanza ta.?" Cikin rashin kunya da fitsara tayi mashi maganar.

Kwafe ta yayi da ido kawai bace mata komai ba,sai ma mamakin karfin halinta da rashin kunyarta yake da kuma rashin tsoron Allah,in ba rashin tsoron Allah ba maiye ace tana matar aure ta dauki wannan gayun na kece raini ta kuma fita,bayan inda zata akwai maza mazan da ba maharramanta ba, tabbas ya yarda bata da hankali.

Ganin yanda yayi banza da ita ya kuma dauke kai ya maida ga tv sai ranta ya b'aci sosai wato  ga mahaukaciya tai ta yi ko? Ko kuma karya uwar haushi tai tayi,kwafa kawai tayi ta juya fuuuu ta shiga room din ta tsaki yayi yana bin ta da kallo yana cewa

"Stupid."

Can sai gata ta fito ta daura ma kayan hijab har kasa sai wani kumbure fuska take tazo gaban shi ta tsaya kam..sai da  ya mula ya sha iska ya d'ago yana kallonta daga k'asa har sama tsaki yayi yana cewa.

"Ai da saura."

Turo baki tayi tana Kara kallon jikinta ganin hijab ce to mai ye kuma sauran,nan ma fuuuu ta Kara juya ta shiga room ba'a dad'e ba ta fito sai wani kumburi take kamar yeast.

Kashe kallon yayi yana kallon fuskar yanda take turmuke sai wani busar kamshi take ganin ta wanke fuskar ba sauran kwaliya ko digo a sama ga kuma hijab da ta saka har kasa sai yaji dan dama dama duk da dai da son samune to ba inda zataje balle har wani gardin kwato ya kalle mashi mata.

Tashi yayi yana yin gaba bai ce mata komai ba..bin bayanshi tayi sai kumbura take tana hawa shiga mota yayi yana worming din motar yana kallonta..ganin bata da niyar shiga ya dannan ma gateman horn yana niyar ficewarshi ganin da gaske yake tafiya zai yi ya barta ya ta bude bayan mota ta shige sai wani cin magani take.

Ko kallonta bai yi ba ya danna hancin motarshi ya ficewarshi daga gida ,yanda yake ba motar wuta sai kayi tunanin garin baki d'aya zasu bari,dan ba d'aga ma motar yake ba wuta yake bata dan so yake kafin 30mn ta ida tayi mashi a cikin school.

Tsoroce take dan ba abunda take tsoro a rayuwarta sama da tsawa sai kuma gudun mota,tana tsoron aita falla gudu da ita a cikin mota kamar rai din biyu ne ba d'aya ba , shiyasa bata cika hud'a da mota ba..ta gwanmace ta hau naped itama naped din bata yarda aita falla gudu da ita ba dan hankalinta baya kwanciya har sai taga ta sauka sanann.

Ganin gudun ba mai karewa bane, ta rintse idon ta har bata san adadi ba haka ma salati tayi shi yafi cikin kwando wani taka burki da yayi yana yin reserve duk a lokaci guda bata san lokacin da tayi tsale ba ta koma gaban mota tana makurewa waje d'aya.

Hawayene kawai taji suna zubo mata sai kuma addu'a da ta kamayi tana Allah Allah taga sun isa makarantar saboda a rude take sai taga makarantar tayi mata nisa sosai.

Babu inda baya karma a jikinta tsabar tsoro,lura da situation din da take ciki da yayi sai ya kara ma motar wuta dan yaji dadi da yaga ta firgice daman ta Kai shi makura ta Kai shi karshe dan rashin kunyarta ta isheshi over and over ma.

Ga kuma drive  da ta mai dashi dan wulakanci da rashin kunya daman yace ba zai ce ta dawo gaba ba,dan bata Kai wanann matsayin ba da zai tsaya yana gaya mata wai ta dawo gaba,kenan ya damu da ita kuma ya damu da mai dashi drive da tayi.

Yanzun gashi da kanta ta dawo gaba ba dan Allah ba,ganin yanda yake sharara gudu da ita ga wata daff da yazo yin overtaking zai wuce bata san lokacin da ta rushe da kuka ba tana cewa.

"Dan Allah kayi hakuri Sir,kar da ka kashe ni wallahi ban shirya mutuwa yanzun ba."

Cikin kuka tayi maganar a gigice tayi mashi maganar tana hade hannunta waje d'aya,shi dariya ma ta bashi sai dai bai yarda ko murmusawa yayi ba balle har yayi dariyar duk da ta bashi dariya to the extent,wai bata shirya mutuwa ba daman ita mutuwa sai an shirya mata take zuwa kenan?tabbas yarinyar nan ya k'ara yarda har yanzun da sauranta.

Yarinta da rashin hankali suna dawainiya da ita,daman matsalar auren yarinya kenan sai kayi hakuri ka Kai zuciya nisa dan ka dunga ganin shirme da hauka kenan iri iri.

Ko kallonta baiyi ba balle ya nuna yaji tana wani abu wai shi magana,kuma bai fasa kokarin ganin ya Kai inda yake son zuwa kafin 9am tayi dan komai ya faru ai itace sila itace ta b'ata masu lokaci bayan sai da yaje har bakin kofar room ya gaya mata ta shirya da wuri karda ta tab'a mashi lokaci amman duk a banza a wofi dan fadin baiyi amfani ba.

Tunda har fad'a mata tayi sauri ta shirya akan lokaci baiyi amfani ba ,ko kuma yace bata ji ba saboda kunnenta na k'ashi ne to shima ba zaiji magiyarta ba kuma bai saurareta ba Koda kuwa zatayi kukan jini bana hawaye ba.

Kuka take bill haki da gaskiya tana bashi hakuri iyakar kokarinta ,ganin bai da niyar rage gudun ta kalle shi tace..."Sir dan Allah ka saukeni anan zan samu taxi ta karasa dani." Yanda tayi mashi maganar ne a laddace da kwantar murya ya bashi mamaki.wato da yake taga mutuwa shiyasa take mashi biyaiya kamar ba itace bace take mashi duk rashin kunyar da ta gadama ba tsaki kawai yaja yana mamakin halin mata.

Su dai mata komai nasu daban yake ba komai suke dan Allah ba komai sai sunyi mashi riya da yaudara wai shi Zulaihat take ma magana cikin sanyi da natsuwa ta koma mashi Zulaihat din da ya sani a baya ba ta yanzun ba,ta koma wata so silent  har wani sinne kai take tana kukan da ta rabu da yin shi girgiza kai kawai yayi yana mai shan wata kwana tafiya kadan yayi ya iso bakin gate din school din.

Dai dai inda aka tana dar mashi dan ajiye motarshi yayi parking yana duba time,tara saura minti biyar yana da 10mn dan yana bad'a 5mn daman kafin ya shiga lecture venue daman shi haka yake ko kallonta bai yi ba ya had'a laptop din shi da wayoyinshi ya bude ya fito.

Ta godema Allah yafi sau ba adadi da taga sun iso lafiya zufa kam ta tasha ta har ta gode Allah ga ciwon kai da take ji sama sama,sauke ajiyar zuciya tayi tana goge fuskarta bag dinta ta dauka tana fitowa.

Had'a ido sukayi ta turo mashi baki tana magana k'asa k'asa ta kama gabanta tana Allah ya saka mata kusan kasheta da yayi daman can ba sonta yake ba shiyasa yaso ya kashe ta Allah yayi saving dinta.

Murmushi yayi yana bin ta da kallo komai nata burgeshi yake,wata sa'ar rashin kunyarta na bashi dariya kuma tana mata kyau, k'asa motsi yayi yana kallonta yana jin yanda sonta da kaunarta suke zagaye duka alhahirin jikinshi .

Tafiya take cikin natsuwa kamar ba ita bace ta murgada mashi baki ba,ganin lokaci na tafiya ya nufi office dan idan har ya biye ma zuciyarshi to zai iya kwana nan tsaye yana kallonta bai gaji ba.

Bayan ya shiga office wayoyinshi kawai ya ajiye yana dauko projected din a zaiyi using da ita a wajen lecture din ya dauko hanya...kamar yanda ya saba haka ya shigo fuskarnan tamau babu fara'a ko kadan a samanta.

Kallo d'aya zaka yi mashi kaji shaskarshi da tsoronshi ya shigeka dan wannan shine haduwarshi da ta farko dasu duba da shi sabon malamine a makarantar ,amman yanda ya shigo masu yasa kowa ya kama kanshi yasha jinin jikinshi.

Duk mai wata tsohuwar rashin kunya da kuma tabbata sun kama kansu dan basu ga wajen wasa ba a wajen Dr Najeeb,balle har suyi mashi,matan class din kowa sai woow suke cewa suna Masha Allah dan ba karamin kyau yayi ba.

Dan ga kwarjini da haibar da yayi kuma ba kamaramin kyau tsuke fuskar tayi mashi ba,bayan ya gama had'a projected din ya maido hankalinshi a kansu sai da ya kare masu kallon yaga attitude din su sanann yayi gyaran murya ya fara cewa.

"Silence."

Duk da ba wata magana suke ba tun sanda ya shigo hall din ya dauki shuru kamar anyi mutuwa,Koda suna magana to a hankali sound din maganar take fitowa tana shiga kunnenshi da yake Allah ya azurta Najeeb da baiwar ji.

Bayan hall din ya Kara yin shuru fiye da baya ya dauki maker ya rubuta sunan shi saman whiteboard din wato *DR NAJEEB H ABDULLAHI* abunda ya rubuta kenan ya waigo yana kallon class din yayi gyaran murya ya fara yin abin da ya kawo shi.

Koyawa yake amman hankalinshi yana kanta yana jindadin yanda take natsuwa a duk lokacin da yake lecture wanann attitude din har da shi ya Kara jin son ta kasance matar shi dan yana son mace wanda ta san ciwon kanta da abun da take.

Yana cikin basu darashi wayar wata a cikin hall ta dauki ruri,take yayi shuru yana kallon inda sound din yake fitowa,kamar wasa sai ga wanda ake Kiran wayar tana kokarin yin picking din call din wata uwar tsawa ya buga mata yana cewa.

"Heyyyy you are very stupid."

Yanda ta buga tsawar yana wulla mata wata uwar harara sai da kowa na cikin hall din ya rude ya sha jinin jikinshi,tsoro ya baiyana a saman fuskar kawo a saman students din..ba kamar yarinyar da yayi ma tsawar, dan sakin wayar tayi bata sani ba tsabar firgici da gigicewa...ran shi ya kai kololuwa wajen b'aci wanann wani irin sakarcine?ya yana cikin koya masu abunda zai amfane su nan gaba amman take kokarin daukar waya kamar ba a cikin class take ba,tabbas bai daukar wannan rainin bai san rainin a rayuwarshi sam.

Tsaki yaja tana nuna mata kofa yace.

"Oooya get out."

Yanda yayi maganar babu wasa balle annurin rahama a saman fuskar yasa yarinyar ta taitara bag din ta ,ta dauko wayata ta nufi hanyar fita,dan dakatawa tayi tana cewa.

"Sorry Sir."

Tsaki yayi yana cewa.

"Get out,before i slap ur dating face useless."

Kwabe fuska yarinyar tayi tana ficewa daga hall din har da guntun hawayenta tana jin nadamar tsayawa bashi hakuri da bai ci mata wannan mutunci ba.

Bayan fitarta ya buga tsaki ya cigaba da abunda ya tarasu ko 15mn ba'ayi ba sai ga wata yar'gayu tasha kamshi sai buga yanka take tana yauki ta shigo cikin hall,kallon time yayi yaga 10:05 wato anyi 1hr da fara lecture sannan ta gardamar zuwa.

Kawai kasa ce mata komai yayi yana mai kwafa ya bita da Ido kawai yana son yaga karshen rashin kunyarta, aikuwa yaya abunda ya isheshi dan yarinyar ko kallon shi bata yi ba ta samu waje ta zauna...sai da ya bari ta zauna ya buga mata wata uwar tsawa wanda tafi wanda ya buga ma mai waya yana mai cewa.

Get off and get out."

Tsaye yarinyar tayi tana kallonshi yanda ya sakar mata da wata harara yasa ta Sabi jikkarta tana ficewa tana mamakin wannan wani irin malami ne Allah ya hadasu mai masifar bala'i,ga shi da kyau amman mutunci bai isheshi ba dai.

Ita dai Zulaihat batayi mamakin abunda yayi ba dan zai iya yin wanda yafi wanda yayi masu ma indai Dr Najeeb ne ya disga mutun a cikin mutane bai dauke shi aiki ba a wajen shi.

Sanin hali yasa ta kama kanta ta nuna bama ta tab'a ganin shi ba kamar yanda shima tun da ya fara bai kalli inda take ba a zahiri ammam a badili hankalin shi kaf yana wajen ta dan yafi gane abunda yake koya masu inda yana kallonta.

Bayan ya gama aka fara yi mashi tambayoyi yana bada ansa sai kuma ya fara jefo questions da kan shi yake pointing din wanda zai yi mashi answering din question...wani question yayi mai zafi sosai yayi masu sai da jin kowa ya dauke a class din saboda da zafin question din yan maganganu suka fara tashi  a hall din dan murmushi yayi dan yana sane yayi question din daman.

Kuma yasan da wuya a samu wanda yasan question din saboda tuni  akayi masu topic din da yayi tambayar kan shi dan tun level two ake yin topic din kuma yanzun su da suke three hundred level suke ,Wanda suke daukar karatun da mahinmamci ne kawai ba zasu manta ba and kuma bai sani ba ko anma koya masu tunda bashi yayi masu course din ba a level two yana kano.

Yatsa da daura a saman baki yana cewa..."Silence." Shuru akayi ana kallonshi sake maimaita tambayar yayi shuru wajen yayi suna kallon iKon Allah dan su basu tab'a jin irin wannan tambayar ba ma sun dai san suna topic din amman basu samu damar yin shi ba.

Ganin ba mai niyar tashi ya bashi ansa yayi pointing din Zulaihat yana cewa.." Hi Stand up." Gabanta wani irin faduwa yayi rass haka gabanta ya fadi,take taji hawaye suna kulle idonta wato shi dai bai da gurin da ya wuce yaci mutuncinta a cikin mutane.

Bayan ita tsoron magana take a cikin mutane kuma yasan da haka dan ya tab'a tadata da suna kano yayi mata wani question ta san ansar amman ta kasa badawa saboda idanun  yan class da suka tsura mata...sai dai ya gama balbaleta da ruwan rashin mutunci da wulakanci sannan yace ta zauna sai da tayi kuka a lokacin dan ba karamin disgi yayi mata.

Kin tashi tayi duk da had'a idon da sukayi amman sai ta maida kanta k'asa tana wasa da yatsan hannunta gabanta sai bugawa rass yake,sai addu'a take Allah yasa ya tada wata tunda bai ambaci sunanta ba ,kuma ai daman ba kowa ya santa ba a class din banda Zubaida tun da wannan ne zuwansu na farko.

Murmushin gefe baki ya saki dan yasan tabbas tasan ansar amman kuma tsoronta na banza ba zai barta ta iya bada ansar ba,kuma dolenta yau ta tashi ta bada ansa tun da ta sani bai ga amfanin sanin nata ba,tunda ba zata gaya ma wasu ba su karu da ita.

Hadda Zubaida yasan ta san ansar amman ba ansarta yake bukata ba ,ta Zulaihat din yake bukata dan yasan ita Zubaida idan har ya tadata zata tashi ta bada ansar duk da itama tana da tsoro amman bata kai Zulaihat ba.

D'ago kanta tayi sai caraf suka had'a ido da shi marairaice mashi fuska tayi tana mai dan turo mashi baki,girgiza mata kai yayi yana nuna mata da ta tashi ta bada ansar tun da ta sani, langwabar da Kai tayi gefe tana nuna mashi yawan mutunen wajen ba zata iya magana a gabansu ba,shima langwabar da kan yayi yana nuna mata ta tashi karda ta yarda ya Kara yi mata magana a karo na biyu .

Hawaye ne suka zubo mata tana sharewa dan tasan halinshi tun da har yace sai ta tashi gwanma kawai ta tashi tun bai wulakanta ta ba,kallon Zubaida tayi sai ta sakar mata murmushi tana nuna mata da ta tashi,duk ita ta lura da maganar kuramen da sukayi wanda bayan ita da ta saka masu Ido ba wanda zai ce ga abun da sukayi tun da ba wanda yasan alaqarsu da ita balle a saka masu Ido.

A hankali ta mike tana wasa da yatsun hannunta jikinta sai kirme yake tsabar tsoro,caaaaa haka idon kowa ya dawo kanta haka taji idanun a samanta ,duk da idonun yan class din da take ji suna kallonta.

Amman hakan bai hana taji kaifin Idonshi a kanta ba,a takure take sai da ta lumshe Ido ta bude tana kafe shi da Ido tana mashi kallon k'asa k'asa kallon baka kyauta man ba kuma baka yi man adalci ba,ta lura yau sau biyu yana cin ta winning daman ya saka ta kuka a hanyar su ta zuwa.

Kuma yanzun gashi ya tadata a cikin mutane wai tayi magana bayan yasan ba iyawa zatayi ba,gyaran murya yayi yana Kara maimaita mata question din cikin rawar murya ta fara answering din question din d'aga mata hannu yayi yana cewa.

"Wait."

Tsayawa tayi tana kallonshi gabanta na faduwa karda ace ba tayi answer din dai dai ba?daman ta dade da wuce wajen tun first semester dinsu 200l yayi masu shi,kuma the some question yayi a lokacin kuma ita ya tada yace sai ta bada ansa.

Da ki badawa yayi mata zagin asara da wulakanci iyakar san ran shi ya zaunar da ita kuma bai bada ansar ba ya gama gabanshi cikin fushi da takaicinta,washe gari da ya dawo bayan ya gama lecture ya Kara tadata yayi mata question din dakyal ta ba dashi a hakan ma bai ga tayi kokarinta ba sai da yayi mata fad'a akan tsoronta yace ta zauna,ji tayi yace.

"Introduction your self."

Dan kasa tayi da kanta sai kuma a hankali cikin rawar murya tace.."My name is Zulaihatu Aminu." Dan shuru tayi sai kuma ta cigaba da ansa tambayar ta tashi tana gamawa har ta zauna ya kuma ta data yana ce mata.
"Zulaihatu prove ur answer."
Zaro mashi Ido tayi tana turo baki gami da marairaice mashi fuska tana mashi kalar tausayi,shima yanda tayi yayi mata yana nuna mata tana b'ata masu lokaci tayi abunda ya dace ko kuma ya fiddota kan step.

Cigaba da bayanin yanda topic din yake baki d'aya..sai da tayi ma topic din pieces ta bude shi ta gaya masu komai a cikin..sosai yan class din suka gane sai tabi suke mata dan daman ba sani sukayi ba dan ba'a tab'a koya masu ba sai kuma gashi sun samu a wajen ta.

Tabbas ya jingina ma kanshi ya kuma ga kokarin kanshi ya Kai zuciyarshi nesa dan daurewa kawai yayi ya sata wannan aikin..lura da yayi basu san komai ba akan topic din kuma ya na da amfani su sani.

Rashin sanin ba karamin ila bane yana mamakin wasu malaman da son kansu da k'uya da yayi masu yawa,kawai su koya ma dalibansu abu shi ke masu wahala amman sun iya cin kudin albashir bayan sai da sukayi alkwarin zasu yi aikinsu akan gaskiya da amana kafin aka basu aikin.

Amfanin mai rotion din zai yi masu?bai ga amfanin rotion ba gwanma kawai ka zauna ka sa tsoron Allah a zuciyarka ka koya yanda ya dace dai dai kokarinka.

Yana jin rad'adin kishin kallon mashi mata da ake kuma yana jin zafin yanda gardawa suke sauraren voice din ta har suna mata tambaya inda basu gane ba.

Saukin shi d'aya ma hijab ce har kasa a jikinta kuma babu kwaliyar komai a fuskarta shine dama damar da abun sai yayi mashi yawa da zafin da rad'adin kishin yayi mashi yawa fiye sosai.... murmushi kawai yake yana kallon yanda rawar murya tana wani sinna kai,kamar ba sabuwar Zulaihat har shi ba mai taken taibata da rashin kunya iri iri.

Bayan ta gama yasa ta zauna shima ya Kara yi masu bayanin da ya dace sannan ya gaya mashi roles and regulations din shi sai da kowa ya k'ara girmama lamarin tsaurinshi da miskilancin shi har da qaddararshi ma.

Dan yanda yake fadin dokokinshi cikin Isa da gadara yake fad'a masu,kuma yana nuna masu dole su bi idan kuma basu bi ba to dai dai yake da zamaninsu bai da case da suyi obey ko kar da suyi shi dai ya gaya masu ya fita hakinsu.

Bayan ya gama fadi ya taitara kayanshi yana shirin dauka captain yazo dan ansa ya Kai mashi office ga mamakin yan class din sai yace baya so,shi bai son ana zo mashi office Koda captain ne idan bashi ya bukaci hakan ba kuma karda ya damu zai iya dauka da kan shi tun da daman shi ya taho dasu da kan shi ba wani ya kama mashi.

Yanda yayi maganar with so serious babu wasa a cikin sanann ya kama gabanshi kamar yan class din suna jiran ya fita nan aka fara magana akan halinshi kowa ya tsorata a class din wata fine Beb ce a kusa da Zulaihat da ta isheta da surutu tunda ya fita tana nuna mata yanda take tsorace da halin Najeeb murmushi yanmatar tayi tana kallon Zulaihat tace.

Comments nd vote pls

*AMATULLAH DATA SERVICES*

*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350

9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500

VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank

08160508316 for call or whatsapp

Share pls✓

Continue Reading

You'll Also Like

2.4K 224 27
Wannan ne littafi na na farko,Allah sa inyi abin arziki your comments and likes will be appreciated 😅 Life is full of ups and downs,when we think...
13.1K 433 56
labari ne data kafu aka kadara🙇🙇 Kubiyoni ku ji yanda LabariDr. Essha Ahmad zata Kaya da Young Tycoon Namji Mai ji dankashi Aliyu Umar Tycooon 💃...
29.4K 864 23
Labarin Yarinyar da ta tashi a tsakanin yayyenta maza, da suke shirye da aikata ko menene saboda ita, ba ta san tsoro ba, rashin ji ya kaita ga haɗuw...
31.3K 1.4K 9
Story of a young blind Fulani girl👸🏻