MAHREEN

By HAERMEEBRAERH9900

1.5K 423 71

A Koda yaushe muna Jin labaran zama da kishiya Mai ban mamaki da ban al'ajabi....Labarin MAHREEN labari ne na... More

MAHREEN PAGE 1
MAHREEN PAGE 2
MAHREEN PAGE 3
MAHREEN PAGE 4
MAHREEN PAGE 5
MAHREEN PAGE 6
MAHREEN PAGE 7
MAHREEN PAGE 8
MAHREEN PAGE 9
MAHREEN PAGE 10
MAHREEN PAGE 11
MAHREEN PAGE 12
MAHREEN PAGE 13
MAHREEN PAGE 14
MAHREEN PAGE 15
MAHREEN PAGE 16
MAHREEN PAGE 17
MAHREEN PAGE 18
MAHREEN PAGE 19
MAHREEN PAGE 20
MAHREEN PAGE 21
MAHREEN PAGE 22
MAHREEN PAGE 23
MAHREEN PAGE 24
MAHREEN PAGE 25
MAHREEN PAGE 26
MAHREEN
MAHREEN PAGE 27
MAHREEN PAGE 28
MAHREEN PAGE 29
MAHREEN PAGE 30
MAHREEN PAGE 31
MAHREEN PAGE 32
MAHREEN PAGE 33
MAHREEN PAGE 35

MAHREEN PAGE 34

42 7 2
By HAERMEEBRAERH9900

💅   MAHREEN  💅












WRITTEN BY HAERMEEBRAERH







*Mai so a sanya ta a group ɗin MAHREEN2 paid book ta min magana ta wannan No 09031416423*




PAGE 34:








Ina nan zaune se na tuna irin wannan abun ya taɓa faruwa da ni a Kano, wata shekarar da kawun Yah Maheer ya rasu(Baba dan Juma Allah ya masa rahama)ana ta'aziyya ciwo ya turniqe ni dole na zame jiki na koma gefe na kira Yah Maheer na sanar da shi zani asibiti, dubu goma sha takwas ya zaro ya bani tare da bani hakurin ba zai samu damar raka ni ba saboda mutane da ke zuwa musu ta'aziyya, nuna masa na yi babu komai amma can qasan rai na a tsorace nake, na riga na saba komai zan yi ya na biye shi ke min jagora bana son yin abu baya nan, se in dinga jin wani tsoro na shiga ta,haka na daure na tafi asibitin na bi dogon layi kafin na ga likita, bayan na gan shi ne ya rubuta min testes da za a min na jini guda uku na masa godiya na fita, wajen da ake biyan kudi na je na tadda mata jingim a wajen se gefe layin maza ne amma ba su da wani yawa,ina nan na bi layi na sakankance kuɗin hannu na zai ishe ni, har aka zo kai na, bayan sun karbi takarda ta su ka sanar da ni kudin dubu goma sha tara zan biya, ji na yi gaba na ya yanke ya fadi, domin kuwa kudin waje na dubu goma sha bakwai da dari takwas ne ya ragu na taɓa na yi kuɗin mota.

Sanye nake da niqabi sai na ji zufa ta wanken fuska, tini na fita daga layi na koma gefe ina tunanin makama, dan na tabbata ko na kira Yah Maheer d'aga masa hankali kawai zan yi,ni ba account No ba a lokacin balle a tura min na cire ta POS wa ma ya san da POS time din, sam ban san da zaman shi ba a duniya,na san ba shi ma da shi tunda na san aljihun shi, tunani na yi dama ni da Yah Shamsu muka saba zuwa Aminu Kano duk sanda na zo shi ke rako ni in dai ba da Yah Maheer ɗin na zo ba, yawancin likitocin ma da nake gani abokan Yah Shamsu ne, nan da nan na kira shi ina daga zaune a gefen wasu flowers, ya na dagawa na ji muryar shi sai kuka ya kama ni, cikin kuka na masa bayani rarrashi na ya yi sannan ya ce,

'Haba Mahreen ga Sadeeq a asibitin me makon ki neme shi ya baki kuɗin se ki zauna ki na kuka?'

Da niqabi na na goge majinar da ke tarara a hanci na saboda kuka na ce,

'Ba zan iya kiran shi ba, ni bani ma da No shi dan Allah ka kira ka faɗa Masa'

'Akan me ba zaki iya faɗa masa ba? Bari na turo maki No shi dole ki masa magana sanda ba na nan wa zai taimaka maki a asibitin da ya wuce shi?'

Ya Shamsu ba mutum ne mai faɗa ba dan haka yanzu ma cikin lallashi yake nuna min Yah Sadeeq din dai ya kamata na nema hakan ne ya fi dacewa.

Wani sabon kukan ne ya kwace min, nan da nan zazzabin da na ke fama da shi ya qaru, a duniya bana son roqon kowa, bana son na nemi taimako wajen kowa in ba Allah ba, ko Yah Maheer da muke tare ban san in ta ce masa bani bani ba, gashi dai ba na sana'a a wancan lokacin, amma duk abinda ya bani alhamdulillah wanda be ban ba ba na tambaya se idan abun amfanin gida ne da dole sai na tambaye shi kamar su Omo sabulu da sauran su, ko ina jin shagwaba na ce ya siyo min kayan zaqi da na ke mutuwar son sha.

Yah Sadeeq Family friend din mu ne,tare suka taso da Yah Shamsu,abokai ne ko na ce aminai ne, iyayen mu maza abokai ne sosai, dan haka mun ɗauke su a matsayin yayun mu, suma gidan su sun dauke mu a matsayin 'yan uwan su,ni dai ban ji wani comfort na in kira shi na tambaye shi dubu biyu ba se nake jin zai ce na yi roqo.

No shi ce ta shigo waya ta Yah Shamsu ya turo min, ina nan zaune ina shawarar ko gida ma zani ne abu na mu riqe sauran kudin zai mana amfani in mun tashi komawa Bauchin tunda koda yaushe matsala daya ake nuna min, kuma an kasa bani maganin da zai min amfani, ina tsaka da tunanin nan se ga kiran Yah Sadeeq ya shigo wayata, ina dauka na yi sallama, ya amsa cikin yanayin saurin maganar shi ya hau min faɗan ashe ban dauke shi yayana ba,yana asibitin ina neman kuɗi se na kira Shamsu da ma baya gari, to shi ze zo ya kawo min kuɗin? Hakuri na bashi sannan ya ce ya hakura, in je bakin kitchen na asibitin na jira shi, na amsa da toh, nan take na tafi ina share hawaye na ta cikin niqabi na samu waje a bakin kitchen na zauna ina ta duban hanya, a zato na daga ward din da yake aiki zai fito ya tadda ni anan, da yake wajen nasu da nisa, ashe already ya na cikin ma kitchen ɗin ya na jira na, ina nan zaune kusan tsahon minti ashirin da wani abu, shiru ni ban kira ba shi be kira ba, can se na ji an buɗe qofar kitchen ɗin na sake kallon wanda zai fito a karo na ba adadi dan tun zamana a wajen na ke kallon masu shige da fice, ga qamshin abinci da chips na ta dukan hanci na, Yah Sadeeq na gani cikin kayan shi na likitoci ya na tsaye ya na kallo na, da sauri na miqe tsaye ya zo inda nake ya sa hannu a aljihun shi ya dakko kudin ya miqa min sannan ya ce,

'Tun d'azu ina zaune ina jiran ki kira ni na zo na baki kuɗin amma shiru ke ki na zaune ashe ki na shan iska abun ki'

Cikin jin kunya na bashi hakuri na ce,

'Ka yi hakuri banda kati ne na zaci in ka zo zaka kira ni se na sanar da kai na zo'

'Its ok, yanzu ki duba dubu biyun ta ishe ki ko?'

'Eh na gode Allah ya saka da alkhairi '

'kin tabbata ta ishe ki?'

'Eh ta ishe ni na gode sosai Yaya'

'Humm matsa nan ai baki ɗauke ni yayan ba, tunda se da aka kira ni ke ba zaki iya fadan matsalar ki ba, ki na da na mota?'

'ka yi hakuri inshaa Allah zan kiyaye, ina da na mota na gode'

Sallama mu ka yi ya wuce nima na koma wajen da na bari lokacin wata arniya ce a gaba na shige gaban ta zan miqa kuɗi ta zaburo za ta hau min masifa akan na wuce layi na daga niqabi  na na zuba mata jajayen ido na da suka gaji da kuka ina mata wani mugun kallo, domin na tsani dama yanda arna ke baro qasar su su zo su na mana gadara da masifa a namu qasar, jira nake ta ci gaba da masifar na wanke ta ta uwa ta uba dan a wuya nake, se nurse ta leqo ta ce su barni akan layi nake zuwa na yi na dawo, se arniya ta fara,

'Ohhh sorry Ma'am'

Banza na yi da ita na miqa kuɗi aka bani receipt na tafi wajen diban jinin,ina zuwa na ga wata 'yar uwar mu ke diban jinin wanda ko ita zan iya tambayar kudin ta bani, kawai se muka hau hira ta na ta dariya dan ta san za a yi drama wajen  diban jini na se ta hana kowa ya dauka ta zo ta dinga lallashi na da ban hakuri sannan ta diba ina ta sharben kuka abu na,dariya suka dinga min dan duk dakin diban jinin na fi su qiba yan siri  siri ne su ba wasu masu qiba ba, daga baya nima kunya ta kama ni, na dake abu na,ana ganawa na wuce gida da sauran canjin dari takwas ɗina.

Har na gama tunanin abinda ya faru a garin Kano Yah Maheer be zo ba, shawara na yanke kawai zan koma gida tunda lokaci ma ya kusan tafiya bana jin za su min test din a yau se dai gobe.

Fitowa na yi ina tattaki da kyar ni kadai na san me nake ji a jiki na a wannan lokacin, ina tafe ina tasbihi ga Allah wanda ya azurta ni da jinya ya ke kankare min zunubai, na yi nisa na kusan zuwa gate se na hango Yah Maheer a dayan bangaren ya na shiga asibitin, komawa na yi dan be kula da ni ba, wajen da ake aje abun hawa na bishi ya na juyowa ya ganni, duk na fita hayyaci na, ido na ya faɗa ya zurma,tausayi na ne ya kama shi idan shi ya kada ya yi jawur, hannu na ya kama ya na bani hakuri, har sai da ya bani mamaki, na ce,

"Wannan hakurin na menene?"

"Na komai ne Baby na, ki qara hakuri Allah ya na tare da masu hakuri kin ji?"

Daga masa kai na yi sannan mu ka tafi inda zai biya kudi,se da ya gama komai sannan ya ce mu je, ina biye da shi ina tambayar shi inda ya sami kuɗi ya na sanar da ni, tausayi ya bani ban ce komai ba a rai na se na dinga yi masa addu'a ina roqon Allah ya bashi ikon biyan bashin da ya ci, a zuciya ta ina ganin duk jinya ta ta hana shi tara abun arziqi a rayuwa ko ɗan filin nan na zamani bashi da shi balle gida.

Har muka isa ina tunani kala kala, ni ce mutum ta ukun qarshe da suka ce za su yi mana a yau saura su yi hakuri se gobe se kuma in an Kawo na  emergency.

Yah Maheer ji ya yi an ce ya je ya suyi condom da hand gloves,mamakin me za a yi da condom ya hau yi, amma dai ya wuce ya tafi siyowa, tunda nake ban taɓa ganin Condom ba ido da ido na ga yanda ake bude shi se ranar, sanda za a min test su biyu ne a dakin kawai mace da namiji ba a barin namiji shi kaɗai.

Ba bata lokaci na hau gadon aka hau yi min test din ana yi ina kuka, saboda daga macen har namijin arna ne, tunani nake shin mata basa iya yin wannan test sai maza? Ina matasan mu ne ? Yanzu ba a karatu se dai a hau social media, yanzu ba a maida hankali a yi karatu dan kishin kai da kishin mata sai dan kuɗin da za a samu da dai mutanen mu sun yi qoqari wajen yin karatu dan addini da kishin mata kuma gashi tsufa suke tafiya suke, next generation ya za a yi kenan? tun daga nan na qudirta da yardar Allah se na zama midwife dan in dinga taimakawa mata 'yan uwa na.

Ana gamawa jini ya ɓalle min sai da su kan su suka tsorata, audiga matar ta bani ta ce in saka,nan take na samu audigar na saka ban iya amfani da audiga zalla ba se jinin ya dinga bin qafa ta, hankalin su a tashe matar ta yi min dabara da kan ta ta yanda jinin zai tsaya iya audigar sannan ta ce mu je se ranar Monday za a karbi result.

Ina fitowa muka haɗa ido da Yah Maheer se kuka ya kwace min, nan take na dinga yin shi kuwa ba bata lokaci, da kyar ya iya lallash na muka fita zuwa wajen machine ɗin mu, na hau muka wuce gida.

Daidai da pad da zan amfani da shi babu sai wani qaramin towel da muke goge jiki fari qal na yanka biyu na yi amfani da shi, ranar wuni na yi a daki ina jinyar jiki na da zuciya ta.

Na tabbata qarfin tawakkali ne ya sa ban kira na shiga uku na lalace ba a ranar nan saboda yanda na shiga damuwa da kuma yanda nake jin tsananin ciwo a jiki na.

Haka na dinga fama da jinya har Monday muka je mu ka karbi result mu ka kai wa likita same treatment da aka saba min tun farkon zuwa na asibiti shi aka sake min, na gaji da shan antibiotics kala kala, daga me sani amai, se me saka ni na dena cin abinci saboda warin shi se wanda ko zufa na yi se na ji warin shi, haka na daure na gama shan maganin.

Waya muka yi da mama nake bata labarin abinda ya faru, se ta ce na ɗauki ruwa a cup na karanta Fatiha qafa bakwai na shanye inshaa Allah jinin zai tsaya kuma zan ji sauqi.

Nan take kuwa na ɗauki ruwa a cup na yi addu'a na shanye, na ji daɗin jiki na amma jini be dauke ba, har sai da na jera kwanaki ina yi ba fashi, se Allah ya taimake ni jinin ya ɗauke.

Shawara mama suka yi da Baba akan ya kamata na je Islamic center inda ake ruqya a min ruqya ko akwai matsalar jinnu a lamari na, ban san an yi ba amma sun tsaida shawarar duk sanda na je Kano za a kai ni Islamic center dan neman magani.

Rana ta qarshe da na je ganin likita a wajen zaman jiran shi na sha sanyin AC saboda layi ya zo kai na ni ce daf da AC, dan haka tun anan na fara tari, ban wani damu ba a zato na normal mura zan yi,bayan na gama da ganin likita na tsaya a shago na sayi Tom Tom na wuce gida.

Ina zuwa na tadda Yah Maheer na jira na ya bani kyakkyawan albishir...............

To jama'a na gaji se zuwa gobe ko jibi inshaa Allahu.

Continue Reading

You'll Also Like

4.1M 169K 63
The story of Abeer Singh Rathore and Chandni Sharma continue.............. when Destiny bond two strangers in holy bond accidentally โฃ๏ธ Cover credit...
261K 25.6K 62
Ryan and Aaruhi The story of two innocent hearts and their pious love. The story of one sided love. The story of heartbreak. The story of longing a...
923K 55.1K 49
๐ˆ๐ง ๐ญ๐ก๐ž ๐“๐š๐ง๐ ๐ฅ๐ž๐ ๐ฐ๐ž๐›๐ฌ ๐จ๐Ÿ ๐‡๐ž๐š๐ซ๐ญ๐ฌ, ๐š๐ง๐ ๐ฉ๐ฎ๐ซ๐ฌ๐ฎ๐ข๐ญ ๐จ๐Ÿ ๐“๐ซ๐ฎ๐ญ๐ก๐ฌ, ๐‹๐จ๐ฏ๐ž ๐ฐ๐ž๐š๐ฏ๐ž๐ฌ ๐ข๐ญ๐ฌ ๐ฆ๐ž๐ฌ๐ฆ๐ž๐ซ๐ข๐ณ๐ข๐ง๐  ๏ฟฝ...
859K 71.7K 34
"Excuse me!! How dare you to talk to me like this?? Do you know who I am?" He roared at Vanika in loud voice pointing his index finger towards her. "...