MAHREEN PAGE 20

43 11 7
                                    

💅   MAHREEN   💅

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH



PAGE 20:

"Ahh Nafeesah ke ce ki ke tafe? Bismillah shigo ciki"

"Wallahi Aunty ni ce ke tafe da yamma, na zo na ɗebe miki kewa dan ke yanzu gwauruwa ce,"

Dariya muka yi a tare, muka shige parlour muka zauna, ruwa na buɗe fridge na dakko mata na ajiye, sannan muka fara gaisawa tare da taɓa hira.

Bamu tashi ba sai da aka kira magariba, muka yi alwala muka yi sallah, sai na duba abincin mu na ga ba zai isa ba mu ci da daren, wake na dafa na qara a shinkafar sannan na zuba wa kowa, mu kuma na haɗa mana baki ɗaya muka zauna muka ci ana ci gaba da hira, da dare ya yi muka sake dunguma daki na muka kwanta,kafin bacci ma hira Nafeesatu tai ta yi min game da auren ta da ya gabato,har daga qarshe ta ce,

"Ni fa aunty zuwa na yi ki koya min yanda zan yi girke girke masu dad'i da yanda zan kula da gida na"

"Ikon Allah ni ɗin me na iya da zan koyar?"

"Ke kuwa ki ka iya Aunty dan Allah ki koya min abubuwa masu amfani,ni fa ko kunna risho da haɗa shi ban iya ba"

"Aiki ja kenan, to shi kenan Allah ya kaimu ya bani ikon koya maki abun alkhairi"

Haka muka kwana da safe na yi mana wainar flour da na sanya wa kayan haɗi sosai har da lawashin albasa, muka ci muka kora da baqin shayi, bayan mun gama ne muna zaune na dinga koya mata abinci kala kala da yanda zata kula da gidan ta, da sauran duk abinda na sani dai wanda be gagara ba, da rana da za mu yi girki kuwa se na kwance risho gaba daya na nuna mata yanda ake haɗa shi, sannan na sake kwance wa na ce ta haɗa, ta kuwa haɗa shi daidai yanda ya kamata, bata wani jima ba kwanan ta uku ta tafi ta koma LK.

Kafin Yah Maheer ya dawo aka yi auren Nafeesah inda aka ajiye ta anan garin Liman Katagum,mijin ta ma ɗan uwa ne dan haka auren dangi suma suka yi.

*****************************

Zaɓe ya gabato, rikicin siyasa da na qabilanci na ta wakana a kowacce jaha, a wannan shekarar ta 2011 ne Baba Buhari ya qara fitowa neman takarar shugaban qasar Nigeria inda yawancin mutanen Arewa suka fito qwan su da kwarkwatar su suna so ya zama shugaban qasa tare da wasu qalilan daga kudu,ta wani bangaren kuma sam sam Baba Buharin be yi musu ba ba sa qaunar mulkin shi saboda tarihin shi da suka samu wajen iyayen su, mutanen kudancin Nigeria kuwa wasun su na qin shi ne saboda qabilanci b'angaranci da wariya saboda addini da ba d'aya ba.

A wannan lokaci garin Bauchi na ɗaya daga cikin garuruwan da aka dinga samun rikici har ta kai wasu sun rasa gidajen su da 'yan uwan su.

Mu kuma da muke gida mu na zaune cikin tashin hankali da taraddadin abubuwan da ke ta faruwa, a lokacin Yaron Maimunah ya fara zama sosai, mazaje na qofar gida ana ta tattauna halin da qasa ke ciki, wata 'yar ajin su Hauwa'u ce ta wuce dauke da qullin kaya akan ta tana kuka, tausayin ta duk ya kama mu Hauwa'u ta je ta same ta ta mata magana tare da jajanta mata abinda ya faru da su gidan su an qona dole su bar wajen.

Suwaidatu kuka Hauwa'u Kuka, Hauwa'u fad'i take dan Allah in ara Mata waya ta kira Baban ta ta ji ina yake, fatan ta Allah ya sa baya shago, (Chemist ɗin shi).

Ni kuwa da wauta yanayin yanda duk suka rud'e suka rikice sai ya dinga bani dariya na dinga dariya ina tsokanar su, Maimunah kuka take ta na tambayar ko ya 'yan uwan ta suke? In ta kalli d'an ta sai ta ce,

"Hummm yaro ka zo duniya a lokacin da ake rikici a cikin ta,"

Suwaidatu ce ta Kalle ni ta ce,

"Aunty ni Kashi nake ji, kamar na gudawa nake ji"

MAHREEN Место, где живут истории. Откройте их для себя