MAHREEN

By HAERMEEBRAERH9900

1.5K 423 71

A Koda yaushe muna Jin labaran zama da kishiya Mai ban mamaki da ban al'ajabi....Labarin MAHREEN labari ne na... More

MAHREEN PAGE 1
MAHREEN PAGE 2
MAHREEN PAGE 3
MAHREEN PAGE 4
MAHREEN PAGE 5
MAHREEN PAGE 6
MAHREEN PAGE 7
MAHREEN PAGE 8
MAHREEN PAGE 9
MAHREEN PAGE 10
MAHREEN PAGE 11
MAHREEN PAGE 12
MAHREEN PAGE 13
MAHREEN PAGE 14
MAHREEN PAGE 15
MAHREEN PAGE 16
MAHREEN PAGE 17
MAHREEN PAGE 18
MAHREEN PAGE 19
MAHREEN PAGE 20
MAHREEN PAGE 21
MAHREEN PAGE 22
MAHREEN PAGE 23
MAHREEN PAGE 24
MAHREEN PAGE 25
MAHREEN PAGE 26
MAHREEN
MAHREEN PAGE 27
MAHREEN PAGE 28
MAHREEN PAGE 29
MAHREEN PAGE 30
MAHREEN PAGE 32
MAHREEN PAGE 33
MAHREEN PAGE 34
MAHREEN PAGE 35

MAHREEN PAGE 31

27 9 2
By HAERMEEBRAERH9900

💅  MAHREEN  💅







WRITTEN BY HAERMEEBRAERH









PAGE 31:








Mun isa garin Kano da misalin uku da rabi na rana, gidan shiru saboda a  wannan lokacin 'yan biki basu fara zuwa ba, tunda sauran sati ɗaya da wasu kwanaki ne,kowa na can cikin gida, amarya ta tafi gidan qanwar Mama gyaran jiki can bawo road, sudanis ne sun iya gyaran jiki sosai, a hankali muka ja akwatin mu muka shiga gidan, a zato na bayan an gaisa za a d'akko maganar gobarar da mu kai dan a yi mana jaje, a lokacin na yi niyyar bayyana yanda abun ya faru saboda in da taimakon da za a yi mana a yi mana, amma duk wanda mu ka gaisa a gidan se na ga ba wanda ya damu da ya ji ya abun ya kasance.

Kayan jikin mu kawai sun isa shaidar sauyin rayuwar da muka samu, shiru na yi na hadiye abinda nake ji na tausayin kai na a cikin 'yan uwa, nima na faɗa hidimar biki tsundum, dama Yah Maheer ya bani dubu goma gudummawar biki, na bayar na riqe sauran dubu goma da ya ce na riqe a hannu na ko zan buqaci wani abun a ciki na je na yi qunshi aka yi wa Suwaidatu baqi da ja itama .

Mu na nan zaune duk wata hidima da za a yi ban ware kai na ba kamar yanda ba wanda ya ware ni, har zuwa ranar da Addah Babba ta zo gidan, na yi murna sosai da ganin ta itama ta yi murna sosai da gani na domin mun jima bamu haɗu ba, sai dai ta zo ba ta da lafiya ni na zauna kusa da ita har ranar da aka fara gudanar da bikin, bikin da ya tara dangi masu dimbin yawa da abokan arziqi, kamar yanda kowa ke kwalliya nima haka na sanya ɗaya daga cikin ɗinkin mu da Yakubu tsara mana, gaba ɗaya fitted gown ya min sai dai yanayin style din kowacce daban ne, se gashi na yi wani irin kyau me ban mamaki kamar wadda ta sanya kaya masu shegen tsada,duk inda na shiga sai an yaba kyan da na yi, ganin dangi da abokan arziqi sai ya mantar da ni duk Wani baqin ciki da damuwa da ke raina, hankali na ya kwanta na wannan lokacin, duk kuma inda amarya take ina nan biye kamar yanda ta min a biki na ta na kusa da ni koda yaushe nima haka na kasance a bikin ta se inda na ga be dace ace yayar amarya na wajen ba se na bar ta da qawayen ta.

Ranar da aka yi dinner kuwa na sha kuka musamman da aka sanya Waqar Ameenah Ameenah 'yar Auta Ameenah Tauraruwar mata....na kasa dena kukan farin ciki a wannan lokacin ita kan ta amarya se da ta yi kuka ganin yanda wajen ya cika da dangin ta da masoyan ta.

Mu ne har azare mu ka raka amarya d'akin ta, Masha Allah gidan Ameenah ba qaramin kyau ya yi ba alhamdulillahi, kwanan mu ɗaya washegari mu ka kamo hanya mu ka koma Kano, daga nan muka je bauchi ziyara zuwa na gidan su Yah Maheer na ga tarbar da ta min dad'i domin kuwa duk sanda mutum ya maka alkhairi ka faɗa,sun nuna alhini da kuma jajanta min gobarar da mu ka yi sannan sun yi mana addu'ar neman tsari kar Allah ya maimaita mana shiga wannan mummunan hali a gaba, godiya na dinga musu har ina hawaye saboda na ji dad'in yanda su ka tuna kuma su ka jajanta mana ainun, kamar koda yaushe se da na dinga kai ziyara daga wannan gida na shiga na fita wancan ba hutawa, ranar qarshe da zan gama ziyara ne na je gidan Rasheedah babbar 'yar Yayar Yah Maheer wanda duk zuwan da zan yi sai na je gaishe ta kamar ibada, daga qarshe na je gidan Ruqayya qanwar Yah Maheer ɗin da suke Mama ɗaya, sai gidan Cousin din shi Ladidi mutuniyar kirki da son zumunci, bana manta wa ina Bauchi ta na yawan kawo min ziyara ta na so na tsakani da Allah.

Da yamma muka koma gida a gajiye,abinci muka ci na yi wanka sannan na sanar da su cewar gobe za mu tafi bauchi daga nan mu koma Kano inshaa Allahu.

A cikin daren Ummah ta sa aka je gidan Dada (Yayar su Yah Maheer babba) aka karbo daddawa da kuka da kubewa busasshiya da kanwa se albasa wanda tun zuwanmu ta aika kuɗi aka yi mana wannan dakan, na ji dad'i sosai na samu kayan na killace su a cikin kayan mu, sannan muka yi shirin bacci.

Da asuba bayan na yi sallah gari ya waye na yi sharar tsakar gida, na sa yara suka wanke banɗaki sannan muka ci abinci, da misalin tara da rabi na safe mun gama shirin tafiya Bauchi, har tasha yaran gidan suka raka mu, mu ka rabu cikin kewa da qaunar juna.

Gidan Husaini muka sauka bayan mun isa, mun samu tarba kadaran kadahan, da yamma lisss na shirya muka wuce gidan Addah Ummu na a can muka kwana washegari mu ka tafi Kano.

A hanya ina ta addu'ar samun iyaye na cikin walwalar su da lafiyar su tare da fatan Allah ya sa su nuna min soyayyar su da suke nuna min tun ina qarama, bana son yanda muka koma kamar baqi, ban da dogon burin sai sun taimaka mana dole amma ina da burin ganin mu tare kamar da mu na fara'a da annashuwa da juna musamman Babana,murmushin su da soyayyar su a gare ni ta fi kudi da duk wani abun duniya da zan samu, zan iya hakuri na ci gaba da rayuwa a gidan miji na a cikin halin samu da rashi ni dai su dena daure min fuska.

Ina addu'a ina hawaye har se da na rasa abinda zan roqa a wajen Allah sannan na samu hawaye na suka tsaya, ko kafin na isa Kano ido na sun yi luhu luhu, a haka mota ta tsaya a tasha mu ka samu taxi zuwa kabuga daga kabuga muka dau adaidaita sahu har gidan mu.

Ina zuwa kuwa na ga fa'idar addu'a nan take na tabbatar da cewa biki ne ya ɗauke min hankalin su ba wai sun daure min bane dan ba su son taimaka min kamar yanda zuciya ta ta raya min, ranar hira na sha a bangaren Baba kamar kar mu rabu, labarai kuwa na sha su har wanda ya na primary se da ya bani.

Washegari kuwa muka shirya da ni da shi mu ka dauki hanyar zuwa gaishe da Mahaifiyar shi daga nan mu ka je gidan Innata muka gaishe ta , mu ma je gidan qannen shi da ke danladi na sidi, da gidan Babban abokin shi, mu na tafe mu na hira kamar kar ranar ta qare, Baba ya yi yawo da ni sosai a gari duk kuma inda mu ka je se ya sanar da ni nan fa waje kaza ne, ko ya ce,

'Nan mun taba zuwa ni da wane, nan kuwa kin ga mu na yara daji ne, Ohhhh ki ga wajen nan haka ya dawo? Ikon Allah wato na kula Kano har ka gama rayuwar ka wani wajen ma ba za ka san akwai shi ba'

Ire-iren wannan labaran ne ya dinga gudana a tsakanin mu, alhamdulillahi ko da be tambayi maganar gobarar da mu kai ba ya wanke min duk wani quncin zuciya ta, na ji cewar har yanzu iyaye na na so na, ba wai yada ni suka yi ba saboda bani da shi, dama can me nake basu? Me nake da shi har da za su share ni dan ya qare? A koda yaushe a jikin su nake a maqale kamar jinjira, su ke yi min abubuwan da ba za su misaltu ba, tunawa na yi da yarinta ta yanda suka sha jinyar nakasa ta kuma har yanzu da girma na su na shan wahalar jinya ta da aljihun su da zuciyoyin su, tunda in banda lafiya ran su na quna saboda tausayi na.

Da leda niqi niqi muka koma gida Baba ya yi siyayyar kayan miya da kayan kwalama.

Nan da nan na sake kamar wani abu be taɓa faruwa ba, na yi kyau na murje a 'yan kwanakin, ba jimawa kuma mu ka fara shirin komawa garin Kebbi,inda Baba ya bani dubu ashirin, Mama ta bani biyar,sai Umma ta sai wa Suwaidatu biscuits da sweets, godiya muka dinga musu, washegari da asuba bayan na je gaishe da Baba ya min nasihar shi me ratsa zuciya da kwantar min da hankali tare da dasa min wani irin hakuri da tsoron Allah a cikin rai na,Baba ya sanar da ni cewar,

"Mahreen duk jarabawar da ki ka ga ta samu bawa daga Allah ne, ba wanda ya isa ya azurta ka ko ya talauta ka bayan Allah, da zaki san tarihin mahaifiyar ki da irin gidan da na auro ta da kuma wahalar da ta sha a cikin aure na da kin gane cewa ki na cikin ni'imar Allah, tabbas kema ki na d'and'ana jarabawar rayuwa,amma ki sani bayan wuya sai dad'i ki dinga duba ladan da za ki samu in ki ka yi ibadar ki daidai,kar ki duba girman wahalar ki ke sha ki duba girman wanda ki ke wa ibadar da kuma girman sakamakon da zai maki,me yasa na dage na dinga sai maku abinci kala kala? Dawa, gero, shinkafa 'yar Hausa, da sauran su? Duk dan ku koyi zama a kowanne situation ku ka samu kan ku ne, dan haka ki qara hakuri Allah na tare da ke, game da maganar rashin lafiyar ki kuma duk abinda ki ke so in dai na neman lafiyar ki ne ki tambaye ni ko nawa ne in ina da shi zan baki, in bani da shi zan nemi hanyar da ta dace na miki, ki riqe mijin ki da kyautatawa, ya na son ki, ya na ji dake ya na kuma kula da dukkan lamuran ki, dan haka kar ki gaza kema wajen nuna masa soyayyar ki, ki yawaita yi masa murmushin nan naki me kyau, hushiryar nan ta fito sosai, kar ki dinga bata rai ki na shan kunu, (ya gwada yanda nake yi in ina fushi😭😭kuka na ya qi tsayawa tunawa da wannan nasihohin ba zan taɓa manta su ba har abada jin su nake kamar yanzu ne Baba ke yi min su) ki riqe ibada dama can ke ba me wasa da ibadar ki bace Allah ya muku albarka, Allah ya kai ku lafiya ya baku zuri'a mai albarka, ki kara hakuri akan rashin haihuwa domin dama Allah ya ce a cikin Alqur'ani mai girma, 'Audhu billahi minasshaid'anirrajeem, Lillahi mulkussamawati wal'ardhi yakhluqu ma yasha'u, Yahabu liman yasha'u inasan wa Yahabu liman yasha'uzzukra, au yuzawwujihum zukranan wa inasan, wa yaj'alu man yasha'u aqima, innahu aleemun qadeer.' a takaice dai kamar yanda na sha faɗa maki Allah ne me azurta bawa da yara wasu ya basu mata zallah, wasu maza zallah wasu kuma ya haɗa masu mazan da mata, wasu ya bar su aqima,wanda ba su haihuwa, ki sa a ran ki duk yanda Allah ya yi ki shi ne daidai, shi ne kuma mafi alkhairi a gare ki,"

"Inshaa Allahu Baba na gode, da yardar Allah zan yi dukkan abubuwan da ka lissafa min, kuma nima na sha faɗa maka ka dena damuwa akan rashin haihuwa ta, ni da kai na nake addu'a idan yara alkhairi ne a rayuwa ta da addini na da miji na Allah ya bani masu albarka idan babu alkhairi Allah ya qara mana hakuri da juriya, idan shi alkhairi ne a wajen shi ko ba da ni ba Allah ya bashi masu albarka, baba lokaci na tafiya kar na rasa motar farko"

Maganganu na sun shige shi sosai saboda ina ganin hawaye kwance a saman fuskar shi, a duk sanda za mu yi magana irin haka to tabbas za mu saka juna kuka, shi ya na fara nashi nan take ni kuma ina nan ina nawa a duk sanda na tuna maganganun shi, sallama na masa na kama hanyar komawa cikin gida.

Nan take ina tafiya na hau hasashen kalar hakurin da zan qara yi a rayuwa ta da  kalar kauda kan da zan ci gaba da yi a rayuwa ta akan duk wani abu da zai bata rai na ko ya dasan baqin ciki.

Tunawa da na baro hawaye na zuba a idon Baba sai ya sa jiki na sanyi, na miqe na yi wa mutanen gidan sallama  na aika Sa'id ya sanar da Baba na gama shirya wa, Baba ya dauki makullin mota ya ce na je waje gashi nan zuwa.

Ban san me ya tsaya yi ba har muka fitar da kayan mu wajen mota muna jiran shi, se daga baya Baban ya zo, da shi da Mama suka kai ni tasha, Baba ya ce gaba za a kama min ni ɗaya ba zai yu a samu a baya mu matsu ba,ko kuma ya biya mana kuɗin mutum uku a bar mana baya, haka kuwa akai nan take ya biya mana kuɗin mutum uku muka shige baya mu na daga masu hannu suka tafi, Mama na ta jaddada min na riqe addu'a na roqi Allah duk abinda nake so a halin tafiya Allah zai amsa ko ba jima ko ba dad'e,ina kuka muka rabu da iyaye na suka tafi, mu na nan zaune a tasha har kusan takwas na safe kafin motar ta cika mu kama hanyar Kebbi.

Tafiyar awanni bakwai ce ta kai mu garin na Kebbi, inda mu ka tarar da Yah Maheer da abokin shi na jiran mu a tasha, kayan mu suka dauka su ka sanya a bayan motar abokin shi sannan mu ka nufi gidan da muke zama, mu na zuwa na ga gidan ya sha gyara daidai iyawar namijin da be saba aiki ba,dariya na yi na wuce wanka na yi wanka da ruwan tap me dumi, ina fitowa na ga ya dakko mana holandia me strawberry, ruwa da abinci, zama mukai ina ci ina mamakin a ina ya samu abinci haka har da nama na san be iya girki ba, ko ashana da kyar yake kunna wa ya sa mana maganin sauro.

Murmushi ya yi ya ce,

"Ki adana tambayoyin ki se kun huta zan baki labari"

"To ai hikenan Allah ya kai mu mu huta din"

Nan na hau bashi labarin bikin Ameenah qawar shi, dan duk qanne na sun fi yin wasa da tsokanar juna daga ita sai Auta Jiddah,bayan mun gama da cin abinci ne na shiga daki dan na sauya kaya na, ina shiga kamar tare muke da shi ya rungume ni sosai ya na sauke ajiyar zuciya tare da faɗin,

"Alhamdulillahi na gode wa Allah da ya dawo min da fitilar gida na lafiya"

"Hummmm ai kai dai ka ga bone Husband, wai ko kunya baka ji ba ka kira Mama ka na ce mata gidan ya maka duhu na dawo, habaa ai a zato na ba zaka iya faɗa wa mama wannan maganar ba"

Kama baki ya yi ya na mamaki na,

"Me na yi to? Gulma ko sata da na baki kunya?"

A hankali ya kama hannaye na da nake qoqarin jan rigar da na sanya qasa, ya kalli cikin idanuwa na ya ce,

"Ki na nufin abinda na faɗa ba gaskiya bane? Kin kuwa san yanda ki ke a rayuwa ta? Ba zaki gane ba, amma yau zan sanar da ke wani sirri da ke zuciya ta, wanda ban taɓa faɗa maki ba, Baby na ke ce farin cikin rayuwa ta, mutane na ce wa ke/kai ne farin cikin rai na a baki, ni ina faɗa maki ne har cikin rai na,ke kadai ke bani nishad'i da cikakken farin ciki, to kin ga kuwa rashin ki dole rayuwa ta ta zama cikin duhu, in shiga qunci shi ne ma'anar gidan ya min duhu"

Ba qaramin tasiri maganganun shi suka yi a zuciya ta ba, na yarda da kalaman shi, na yarda da abinda ya ce duba da yanda ya rame' ya yi duhu, ya yi aski amma gaba ɗaya fuskar shi ta zurma Suwaidatu ta riga ta san in mun shiga daki ta bar mu mu kebe ba tare da ta shiga ta dame mu ba, wannan dalilin ne ya sanya mu sake jiki da junan mu har sai da aka kira la'asar sannan muka fito,wanka mu ka yi sannan ya ja mu Sallah tunda ya makara ba lallai ya samu sallah a masallaci ba.

A nan parlour mu ka ci gaba da hira har bacci ya damu Suwaidatu ta shiga daki ta bar mu zaune a parlour, ashe rabon mu sha wahala ne ya hana mu bin ta mu kwanta baki daya..........

*Assalamualaikum mutanen kwarai masu albarka, kar ku manta ku fara shirin siyan part two na wannan Novel da zarar an kammala part one din shi...Thank you for all ur support and love....Allah ya bar mu tare har aljannah*

Continue Reading

You'll Also Like

262K 25.6K 62
Ryan and Aaruhi The story of two innocent hearts and their pious love. The story of one sided love. The story of heartbreak. The story of longing a...
3.1M 70.1K 81
Diana is an 18 year old girl about to start her senior year until she bumps into a woman at the bookstore who has quite the personality. The woman ta...
1.4M 34.8K 47
When young Diovanna is framed for something she didn't do and is sent off to a "boarding school" she feels abandoned and betrayed. But one thing was...
3.6M 291K 96
RANKED #1 CUTE #1 COMEDY-ROMANCE #2 YOUNG ADULT #2 BOLLYWOOD #2 LOVE AT FIRST SIGHT #3 PASSION #7 COMEDY-DRAMA #9 LOVE P.S - Do let me know if you...