YADDA NA KE SO

By Dijen-sy

968 110 44

YADDA NA KE SO burin Ummi ta auri mijin novel ,Mai arziki ba ta son talauci ya rayuwa zata juyawa mata a sand... More

Shafi 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 21
Page 22
Page 23
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29

Page 20

40 1 0
By Dijen-sy

YADDA NA KE SO🌺

PAGE 20

   BY DIJENSY

       A wannan kwanakin ba abinda Zainab ta ke irin jiran ganin canji daga gun Mukhtar din,kwatsam ta wayi gari da alert na 50k ,ta duba ta ga shi ya turo mata ranar Yana gun aiki.Kafin ta kirasa ta masa godiya sai da ta fara kiran Salihan tana dariya tana labarta mata ,wani ajiyar zuciya Salihan ta sauke tana fadin "Lallai yarinya zata shigo hannu kenan".Ta fad'a a ranta tana gyara murya.

"Mai na fada miki ,aikinsa Yana Yi sai kinyi hakuri,50 k saura kudin gold dinki Ina fad'a miki yanzu kika fara ganin alkairai kawata.

  Zainab din Kai ta jinjina "Aikuwa gashi na fara bari na kirasa".Ta fad'a bayan ta katse Salihan ta bi wayar da ido "Au hakane? Ko kiransa ba tayi ba wawiyar kin ci Sa'a dai faduwa ta zo dai dai da zama ta kira Rod'as ta kwashe labari ta fad'a masa yayi ta dariya.

  "Lallai sa a ta bude,aikina na kyau".

  "Jira zami wani Dan lokaci zata sake nemar ka dole ,sai mu charge din ta kudi dayawa".

"Kanki a kwai oil mutuniyar ,haka za ai"

  Dariya  sukai  kafin suyi sallama a bangaren ta kira Mukhtar din Nan ta masa godiya yace ba komai duk wannan tunanin da take ita kadai ya bawa sai dai wani abu da bata sani ba Ummin ma ya bata daidai da natan shikuwa daman Yana da niyya tun sanda aka sayar da gonarsu ya ke son suma.
 
        Yau tana zaune kan gadon tayi baje baje da wasu tsoffin hotunansa da ta gani tana gyara wancen d'akin .Ko lura da shigowarsa ba tayi ba don a bude kofar ta ke ,ya tsaya ta bayanta Yana kallon abinda ta ta ke kallon pictures din ya shagaltar da ita don ya bayar kallo ne dukda ya ga ta rage sosai compare to da.

   Wani tsohon pic dinsa ya gani ta dago wanda sukai su uku ,shi da babansu da Mamanshi sannan shi Wanda bai wuce 2years.

  "Date of birth din yana baya".Ta ji muryarsa ta d'ago da mamaki ,sai tayi murmushi ta juya pic din baya ta ga an rubuta date ta juya tana sake kallon hoton ta dago ta Kuma kallon Mukhtar din kamar yasan mai take tambaya a ranta.

"Na ga kin 'kura masu ido kinsan waye a hoton?"

  "Kai ne mana kana dan karami".

   Murmushi yayi bayan ya zauna gefen gadon "Do I look like my self?"

  "Sosai ,banbancin hanci ne yanzu yafi tsaho".Ta furta tana murmushi wanda ya sa ya shafa hancin nasa yana murmushi.

  "A ina kika ga wannan?"

  "Na gyara d'akin can shine na gansu na zo ina kalla".Ta amsa.

  "Wayo ke kin boye naki ban taba ganinki ba kina baby?"

  Shiru tayi fuskanta na canjawa "Tun kafin aurena Ya Abdulbasit suka dauke pictures dinmu suka boye sabida kar ina gani ,a duk sanda na dakko na gani sai nayi kuka idan na ga Ammy".

  Hannunta ya riko cikeda lallaci "I understand,ciwone da bazai ta'ba gogewa ba  ,sanda na rasa mahaifiyata na shiga yanayi na maraici amma mutuwar mahaifina ta sanya na san rayuwa nasan waye ni ,duk wata dawainiya da yake Yi ta dawo kaina a lokacin ji nayi kamar kowa ya juya min baya ,rayuwa tayi Yi min zafi na rasa Wanda zan kaiwa kukana face ubangiji da ya halicceni ,you should be blessed you still have Baba as a father,kina da brothers and you have me".
 
  Hawayen da ta ke rike wa ne ya tsiyayo ta ji ta kasa jurewa ta tsinci kanta a Mukhtar din Wanda ya rasa uba da uwa ita Ammy ta rasa Amma ji take kamar ta rasa bangaren na jikinta toh ina ga ance yau ta wayi gari ba Baba Yan uwanta ba bu su ?

  Matsawa tayi daf da shi tana d'ora kanta a kafadarsa ya tallafo bayanta Yana jingina ta a kirjinsa.

  "I promise to take care of you har karshen numfashi na ,amanar Baba ce bazan taba ya da ke ba Ummi your dad has done a lot to me which I can't forget you're blessed to have him a matsayin mahaifi,I am here for you too anything you want I am here for you talk to me always available for you".

  Hannayenta biyu ta sanya tana kewaye su a bayansa wani irin yanayi ta tsinci kanta matsayinsa a ranta tana jin sa fiya da na koyaushe ,a lallai maganganunsa sun sa ta ji tausayin rayuwarsa duk da halin da ya shiga he is still strong,a duk lokutan da ta dinga kuntata masa Daman da wannan damuwar a ransa? Mukhtar Yana bukatar kulawa ,Yana bukatar mace da zata kasance masa hasken idanuya ta share masa nasa hawayen na zuciya.

  Wannan tunanin ta ke tayi a ranta tayi luf a jikinsa ,wani irin yanayi Mai dad'i ya tsinci kansa Ina ma zasu dawwama a haka Yana Jin dadi yadda Ummi ta ke improving a zamantakewar ta su.Kiran wayar Zainab ne ya katse musu zantukansu na zuci ,hannunsa daya ya yi amfani yana zurawa a aljihu ya dakko wayar ya kara a kunne bayan ya daga ,har lokacin Ummi tana jikinsa kamshin turarensa yana ta tafiyar da ita shauki  ba ta taba tsammanin zata ji wani abu gameda Mukhtar din ba haka,ji ta ke ina ma su kwana a haka kawai iya hakan she felt secure and safe.

     Cikin wata iriyar murya Zainab din ta furta "Yaya ka zo bani da lafiya fa".

  "Me ya sameki?"Ya tambaya hakan ya sa Ummi dan dagowa ,ba ta ji me akace a wayar ba ta dai ji ya ce "Tohm Gani"

Hakan ya sa ta tabbatar Zainab ce ,wani Abu ta ji ya dunkule mata Mai ya sa sai a wannan lokacin zata katse musu....

Bata karasa ba taji muryarsa "Ina zuwa ,bari na duba gun Zainab ta ce Bata Jin dadi".

  Tashi tayi tana jinjina kai yace "Ko zamu je tare muga me ke damunta?"

  Kai ta girgiza "Ka je zan zo bari na dauke wannan zan shiga toilet am pressed ".

  Kai ya jinjina Yana mikewa ya fita ta kwashe hotunan tana jin wani kishi ,tana tambaya a ranta ko meke damun Zainab din???

  A zaune ya sameta ta jingina Kai da gadon tana rike ciki yayi sauri ya karaso "Zainab me ya faru ? "

  "Amai na yi cikin ba dad'i daga cin indomie fa sai amai".

  Sannu ya hau yi mata Yana taimaka mata ta tashi ya zaunar da ita kan gadon "Tohm mu je asibiti mana?"

Kai ta girgiza "Tea kawai zan sha ban jin zazzabi".

  "Sai ana jin zazzabi Ake Shan magani ?"

"Amai ne kawai da gajiya nake ji ,tea din dai zan sha".

   "Mint tea? Ko Lipton?"

  Kai ta jinjina"Mint din zai fi".

Kitchen din ya fito ya hada mata sannan ya dawo ta karba ta Sha , paracetamol ya bata ta sha ta ce ta dan ji dama dama.Da maghrib tayi ya je masallaci sallah ya dawo ya shiga dubata tunda yaga jikin nata da sauki Kuma Ummi ta ajje masa abinci a dining ya ce mata zai tafi Kai kawai ta jinjina "Tsoro ma ni nake ji ko zaka kira min Hameeda ta zo ?"

  "Hameeda kuma ? In kinsan kina Jin wani Abu ki fad'a mu je asibiti but me Hameeda zata miki da baza mi miki ba ? Ki taso ki fito parkourn tunda zaman d'akin ba dad'i".

  "Kace abinci zaka ci idan na ji kamshin abincin amai zan ka dai je idan ka ci ka dawo please ka ji?"

  Kallonta kawai yayi ,ya ce Allah Kara sauki ya fita ta tashi zaune "Zaki ga abu ai yarinya da ni kike zancen".Ta furta tana tuna dazun da ta fito zata d'akin Ummin don bata san ya dawo ba ta hangesu a cikin d'akin suna Shan soyayya har mamaki tayi ashe Ummin munafuka ce a haka kamar bata kula da lamarin Mukhtar din ??

   Koda ya je ta zuba masa take tamabayarsa jikin Zainab din yace da sauki ,plate daya suka ci abincin ta ke fad'a masa bikin Yusrahn ya matso kusa ya ke mata maganar Mai zata bata gudumawa tace itama shawara ta ke.

    "Ki yi mata souvenir toh ? Can you?"

  Murmushi tayi idea yayi sai dai Mai zata Yi?

  "Like ,cup ,some kind of dai duk irin abubuwan rabawa dinnan a dinner think about it".

Kai ta jinjina "Yes yayi I will think about it".

"Idan kinyi tell me we see how much it will cost".

  Kai ta jinjina tana tunanin ba dai biya mata zai ba ? Is it not too much kamar ba rannan ya bata 50k ba.

"Tunanin Mai kike?"

  Kai ta girgiza "Ba komai".

  "Allah sa ba Kya son magana sosai , anything da yake damunki let me know".

  Da toh ta amsa bayan sun gama ta tattare kwanunkan,har lokacin isha yayi ya fita Koda ya dawo sai da ya sake duba Zainab din ,Ummin ta shigo a sannan ta mata ya jiki ,ta koma d'akinta sai after 9 Mukhtar ya shigo d'akin Zainab a hakan ma ba ta so ba ta bayar ko zai ce zai kwana nan dole ta kirkiro abu don ta ga alamar Ummin nan ta karkashi zatayi mata.

   ***

 
      Washegari da safe bayan ya shigo dubata ya tarar ta shirya nan take fad'a masa zata bisa ya sauketa asibiti don jiya da tsakar dare ta sake yin amai ya ce toh.Tare suka fita nan ta ga ashe yanzu Ummin itama tana masa girki ya tafi dashi ,wani abun da ya sake bata haushi package din Ummi yafi nata kyau.Kin yarda tayi su shiga tare ta ce ya tafi aikinsa kar ya makara ya ga ta dage ya wucewarsa tana ganin bullewar motarsa ta fito daga asibitin ta kira Salihan.

"Kawata Ina wannan kawar taki da kike fadamin tana aikin asibiti Nana Maryam Hospital? "

"Mene?"Salihan ta tambaya.

"Ina son ki hada mu da ita , please so nake ta taimakan da wani abu ,ko kudi ne zan bada".
 
Nan ta fad'a mata abinda ta ke bukata  Salihan ta kirata ,da farko Bata amince ba sai da ta ji zata bata kudi 15k ta yarda.

   Ba tare da ta shiga asibitin ba gidansu ta tafi ta kwashi hirarta sai wajen zuhr ta koma gida sanda sukai waya dashi ta fad'a masa ta baro asibiti amma tana son biyawa gida yace toh ,wajen zuhr ta kira Saliha ta tabbatar mata ya zama ready ,nan ta ke gidansu ta karbi sakon ta bata 20k din  Salihan ce ta cinye 5k din 15 ke ta tura ma yarinyar.

     Zaune take cikin dan sahun tana jujjuya takardar , murmushi tayi tana hasko yadda Mukhtar din zai yi.Tana kitchen ta ji ana knocking Ummi ,ajje abinda ta ke yi tayi ta taho bud'e kofar Zainab ta gani haka kawai ta ganta fuska sake sai sakin murmushi take ,Ummin ta ce."Ya jikin?"

  "Da sauki ,jika kam da sauki".Ta fad'a tana murmusawa Ummi dai ba ta gane wannan murmushin ba ta tafi ta koma kitchen.

    Zainab din ce zata rike kwana ,ta Yi wanka ta fesa turare cikin wata army green doguwar riga mara hannu.Gurasa ta siyo miya kawai tayi ta turarata ta sanya a flask ,tana jiran dawowarsa wajen 6 Mukhtar ya dawo,ya ga jikin nata da sauki ya tambayeta tace Yan magunguna suka bata kawai.Abincinsa ta hado masa sai wani food warmer ta Sanya takardar a ciki ta rufe ta kai ta ajje yace "Sai da kikai girki ke da baki da lafiya?"

  "Ba wani abu mai wuya bane fa"?

   Bude warmer gurasan ya fara yi sai ta miya dayar ya Kai hannu Yana so yake mene bacin wa'annan ya ga paper yasa ya dubeta da wani weird look? Ta saki murmushi ya Kai idanunsa ga paper yana budewa ya ga abinda ke ciki.Murmushi ya saki daman zuciyarsa ta bashi hakan ganin hakan ya tabbatar masa da zaton sa ,wow she is pregnant with babynsa? Yau shine zai kasance Baba?

   "Surprised?!"

   Murmushi yayi yana jinjina kai hakoransa na fitowa,wani irin dad'i Zainab ta ji ina ma gaske ne ?

    Hannunta ya rike Yana Kai hannunsa cikinta ya shafa "Shine ke wahalar damu haka daman?"

  Baki ta dan turo "Ita dai ".

  Gira ya dage "Ohh tun yanzu ,tohm saurin mai kike zaki gani shine ba ita ba just wait and see,Allah ya Sanya alkairi ya bamu masu alkairi ameen how many month".

Gira ta daga "Weeks dai ,ya Mukhtar 3weeks".

  Kai ya jinjina "Shine kike mana laulayi haka".

Kai ta langabe "Ka ga kuwa a gida akai abinda na ke so na kasa ci miyarnan ma da kyar na iya yinta banson kamshin tattasai".

"Ayya sorry uhmm,haka abin ya ke Allah ya Kara miki lafiyar jurewa ya bamu masu albarka congratulations".

     Da ameen ta amsa  ta soma serving dinsa yace ta bari kar ta ce masa cikinta ya murda yana tsokanarta tayi dariya.

   Ba ta san mai isa ba yau ta damu da sauraran conversation dinsu ,ta na kitchen ta kasa fitowa duk jikinta ya Yi sanyi tun daga farkon hirar ta su har kashe ta ji Zainab din cikine da ita ,komawa tayi ta jingina da locker tana tunanin tata bangaren anya ba ta yi ganganci ba kuwa? Muryar da Mukhtar din ta ji Yana yi kadai ya isheta ta fahimci yana alfahari da cikin wani irin danasani ne ya kamata sai ma da ta tunanin idan maganin ya hanata daukan ciki ya zatayi ? Ita da take da kishiya yanzu Zainab na mata iya shege what if ta haihu fa? Dole hankalin Mukhtar ya karkata gareta ita da yaranta?

  "Innalillahi".Ta furta ta tana Jin haushin kanta na yanke shawara ba tayi tunanin gaba ba......

Dijensy
   

 

Continue Reading

You'll Also Like

109K 8.1K 64
ရယ်စေ၊ မောစေ အသက်ရှည်စေ ဟာသနှော၍ ရယ်မောပျော်ရွှင်စေရန်အလို့ငှာ လုလင်မောင်မောင်(ပစ်တိုင်းထောင်) နေမင်းပုည(ရွှေဒင်္ဂါး) (Own Creation) Starting Date...
220K 19.3K 27
Maybe sometimes love needs a second chance because it was not ready for the first time 🥀... Ekansh Malohtra a youngest buisness tycoon (28).. A man...
16.3K 1.1K 36
"You were magnificent, Satoru Gojo. I will never forget you for as long as I live." Satoru Gojo laid there, bisected in half, as if the universe itse...
141K 14.4K 17
[Sequel of 'MY SUBCONSCIOUS DESIRE'] Once again, a tale of desire and respect Once again, a tale of Rathod and family bond A multi-couple story. F...