YADDA NA KE SO

Von Dijen-sy

943 100 44

YADDA NA KE SO burin Ummi ta auri mijin novel ,Mai arziki ba ta son talauci ya rayuwa zata juyawa mata a sand... Mehr

Shafi 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20
Page 21
Page 22
Page 23
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29

Page 10

25 4 1
Von Dijen-sy


   YADDA NA KE SO🌺

   Page 10

By Dijensy

    Sabuwar waya ta gani fil a cikin kwakinta ba irin tata bace sai dai tana da kudi itama ,dagowa ta yi ta kallesa  fuskarta ba yabo ba fallasa "Nagode".Ta fad'a ya jinjina kai ta wuce d'aki ya bita da kallo.

    Sabon sim ta sa a ciki don bai ba ta wancen ba,ita dai wasai ta ke jinta tun da dai yaya ya ba ta kudi mai tsoka ga Kuma sabuwar waya zata dawo online.Ranar da farinciki ta kwana washegari da safe  wajen biyu da rabi na rana  sai ga Zainab.Ummin na kitchen ta ji sallama shaf ta manta da ta bawa mai wanki kaya bata rufe da a sauri ta fito daga kitchen din ta ga Zainab sai da ta kalleta da kyau ta gane inda ta santa ba yabo ba fallasa ta amsa gaisuwar tata Zainab ta zauna tana satar kallon parlorn.

    "Ya sunanki ma?"Ummi ta tambaya tana son tabbatarwa ko itance.

  "Zainab,Zainab ce Yaya Mukhtar ba ya nan?"Zainab din ta tambaya.

   "Baya nan ya fita aiki".Ummi ta amsa.

  "Au haka fa,daga school na ke nace bari na biyu".

  "Tohm sannunki".Ta fad'a Ummin tana tafiya kitchen,faranti ta dakko ruwa ta kawo mata ta ajje ta koma kitchen jiran miyarta ta kammala ba karamin sa a ta ci ba ta zo dai dai sanda Ummin ta yi girki don kame-kame ta ji ba zai riketa ba.Zubo mata tayi a plate ta kawo dinnning table ta ce ta zo ta ci , Zainab ta taso ta zauna Ummi ta zubo nata ta zauna adjacent da ita.

    Shiru ba mai cewa komai , Zainab duk wani move na Ummi ta tana kallo wani haushin Ummin a ranta take ji kawai Gani ta ke Bata dace da Muhktar ba , ita kuwa ba ta san tana Yi ba don idanunta kan wayarta.

   "Anty na koshi bari na Kai kitchen".Ta tambaya tana tashi Ummin ba ta ce komai ba ta shiga kitchen din tana ajjewa ,ta tsaya dube dube warmer ta vani kamar yadda ta yi tsammanin ta ga shinkafa ce ciki ta koma kan gas cooker ta bude tukunya a cikin sand'a maganin ta barbada cikin miyar ta juya ,tayi sauri ta fito.Ummi da ta gama ta mayar da nata plate din kitchen, Zainab parlor ta dawo ta zauna Ummi kuwa d'aki ta wuce  sai ga Muhktar din ya dawo wajen 3:30pn Ummi ta yi mamakin dawowarsa da wuri don wani lokacin ya na kaiwa Maghreb ma.Tun da dai har da abinci sai ta ga bari ta bashi for the first time fatanta dai ba zai ce mata this and that ba tunda ba sabawa ta yi ba.Ya zauna parlour ya ga ta fito da abinci a tray ,kafeta yayi da ido yana so ya tabbatar da abinda idanunsa ke gani ? Ummi ce yau take jera masa tray din abinci a gabansa?

   "Ga shi".Ta furta tana wucewa d'aki ya bita da ido yana dan mamaki ita kuma kunya ta ji kada yace ba ta saba masa ba sai yau ko don ta ga Zainab wacce gaisawa kawai sukai da ita ya tambayeta gidansu daga haka ba su sake magana ba tana dai zaune.

    Shinkafa da miya ce ,ya zuba a plate yana bude sauce din ya zuba akai don kamshi ta Yi kamshi ya Kai bakinsa maggi ya dan so yayi yawa amma dai ba laifi.Ya dan ci dayawa zuciyarsa cikede tunani wani sashe na zuciyarsa yana tuna masa da maganar Shafiu duk yadda akai  Ummi ta fara sauyawa.Koda ya gama ya tashi ya dauke kwanunkan  Zainab tayi saurin karba tana cewa bari ta je ta wanke ya bata ta tafi da shi.

    Danne danne ya soma a waya kusan minti 20 d cin abinci ya fara jin jikinsa ba dad'i sallahr asr yayi a gida ,a hankali ya ke jin cikinsa na ciwo kamar wasa tashi yayi daga kwance da yake a dakinsa ya fito   kitchen ya shiga ya sha ruwa ko zai samu sassauci ya dawo d'aki ya tafi ya ajje wayar bandaki ya shiga a tunaninsa ko baci cikin yayi ya ga dai ba anan matsalar ta ke ba fitowa yayi ya zauna wani irin daurewa cikin yake yi sosai yake jin ciwon har ya gagara tsayawa ya tamke cikin katamau.


"Assshhh"Ya furta Yana runtse ido ganin ba haza ya dauko wayarsa ya kira Shafiu yazo ya ce gashinan zuwa.Kafin Yan mintina Muhktar ya kasa control ya fadi a kasan carpet na d'akin yana matagugu.Ummi tana d'aki ta sanya earpiece ba ta jiyo komai ba ta nisa cikin kallo.

    Knocking din da aka yi ne ya sanya  Zainab ta shi ta je ta bude ta ga Shafiu ya soma tambayarta Muhktar din ta yu kamar ba ta gane ba ya ce Ina Ummin?

  D'akin Ummi ta nufa  gabanta na faduwa ta tura kofar dayake Ummi na kallon wajen ta ga shigowarta ta zare earpiece d'aya  Zainab ta ce "Anty wani ya zo yana kiranki".

  Fitowa ta yi ta ganshi itama ba saninsa ta yi ba  "Ina Muhktar din ya kirani cikinsa na ciwo?"

    Cikeda rashin fahimta Ummi ta dubesa ganin alamar ba ta hane ba ya sa shi kiran wayarsa suka ji ringing baa daga ba Ummi ta nufi d'akin kwance ta ganshi ya mugun galabaita kamar baya motsi , Shafiu yana biye da ita da gudu ya karasa gun abokin nasa Yana riko shi "Innalillahi Muhktar me ya faru? Ummi me ya samesa?"

  Waro ido ta ke yi ta rasa ma ya za tayi ta girgiza kai  ta yi"Wlh ban sani ba sai yanzun".

   "Wannan ba zai iya ma hawa baburin ba".Cewar Shafiun l.

  Ta juya tana nufar dakinta ta dauko wayarta Baba ta shiga kira baya dagawa ta kira Abdulbasit su kadai ta ke da numbersu a ka yana dagawa ta fad'a masa ,ya ce zai kira Nasiru Nan da Nan ya kirasa ya sa ya zo gidan aka tafi da Muhktar asibiti.

    Ana kaishi emergency suka shiga dashi , Zainab ta shiga kiran Umman ta fad'a musu halin da ake ciki su ka taho Umma da Huda.Bayan doctor ya fito ya tambaya matarsa aka nuna Ummi kai ya girgiza ya dubi Shafiu sanan ya kalli Umma.

  "Guba ya ci a abinci ya akai hakan ta faru?".

   Gabadayansu poster sukai ba ma Ummin da tambaya ta fito daga bakinta "Ta Yaya?"

"Mu zaki tambaya ? Ko mu ne muke zama da mijin naki?"Umma ta tambaya Shafiu ya hau girgiza cike da rashin yarda kai yo ko jikinsa kunne  ne ai ba zai yarda ba Ummin  ba shi da ya San ba son Muhktar din ta ke ba.

 
   "Mai kika basa Ummi?"Shafiu ya tambaya Umma ta soma "Nasan komai Ummi ki fad'a mana mai kika bawa Muhktar a abinci?"

  "Ke Zainab kina gidan abin ya faru ki fad'a mana?"Shafiun ya Kalli Zainab.

  Kai ta shiga girgizawa tana diri diri "Nasan dai ta zubo ma Yaya abinci daga Nan ya tashi ya shiga d'aki.

Kankance idanu Shafiu yayi "Really,matar da ba ta masa girki ? Yau ta soma bashi abinci shine har da guba?"

  Salallami Umma ta fara yi Zainab tana ta ya ta "Kuma ni wlh ta bani abincin amma ban Yi komai ba ,kenan shi kadai ta saka wa? Innalillahi wainna ilaihirajiun ".

  Nasiru ya na kallonsa he can't believe Ummi abin nata ya Kai haka sun shiga uku Baba zai kashe yarinyarnan muddin ya ji.Kuka Ummi ta soma yi ta ma rasa ina bakinta ya tafi don ta kasa magana ta durkusa wajen Nasiru "Don girman Allah idan kana kaunar Allah Nasiru kar ka fad'awa Baba wlh zai iya kasheni ,baba idan ya ji wlh sai ya kasheni don Allah wlh ban Yi masa komai ba".

   Wani salatin Umma  ta saki Zainab zuciyarta ta faranta wani dad'i taji kamar ta yi ihu da kyae ta boye farincikinta ta shiga zubar da hawaye "wannan wani irin balai' ne?"

   "Ai wlh dole mu dau mataki bazaki kashe shi ba wlh ,Kai Shafiu wace iriyar rayuwa Muhktar yake da Ummin ni ban sani ba?"

  "Nikaina ba komai ya ke fad'a min ba Umma Amma dai nasani tun da suke Ummi ba ta taba yi masa abinci ba Kuma Yana fad'a min ba son auren ta ke ba".

  "Subhallah" ta cigaba da yi "Shafiu matsa na duba yaronnan Allah yasa bata kasheshi ba".Umma ta fada likita ya tafi tuni ya barsu gun.

   "Ko me zan masa bazan taba sa mishi guba abinci ba  ba wlh sharri ne ni ban san komai ba akai".

  Umma tana wucewa suka barta anan Nasiru ya hau gargad'a mata "Ummi me kike tunani ,ko ban fadawa Baba ba sai ya sani sai sun fad'a masa".

  Kuka ta fashe dashi tana kiran ya Abdulbasit ya ji ta soma kuka tana rantsuwa sai da ya mata tsawa ta nutsu ta soma labarta masa
  "Yaya wlh ban Saka masa guba ba bansan meya faru ba"

"Ki yi shiru ki daina kuka muddin kinsan ba ke ce ba mai zai tayar miki da hankali?"

   Kai ta jinjina"Na bari amma ka fad'awa Baba ni ban sa masa magani a abinci ba".

   Nan ya tabbatar mata da zai kira Baban ya fad'a masa ta ajje wayar tana share hawaye ta kasa shiga sai kallon kofar d'akin da ta ke yi .Umma nurse ta sa su fita su bashi gu kafin ya Dan dawo  hayyacinsa don masifa take tayi a cikin d'akin can waje ta fito da wayar Muhktar din karama ,Kai tsaya ta lalubo number baba duk abinda ake yi Ummi ba ta sani ba don sun fito sun wuce waje suna binta da harara.Umma Yana dagawa Baban ta soma zayyane masa a rikice ya shiga bata hakuri don ko wuka aka ce Ummi ta caka masa zai yarda ,ya ce ta kirasa anjima idan ya farfado Muhktar din amma tayi hakuri baya kasar.

     Abdulbasit ya shiga zabgawa kira a sannan Abdulbasit Yana ta jiransa yaji on another call ,ko da ya dauka ya shiga labarta masa.

  '"Ka ji abinda kanwarka ta Yi ko? Ka ji ko? Kisa take son farawa Wallahil Azeem ta fito daga gidan Muhktar bazata dawo gidana ba ,nima wataran zata iya kasheni".

   Kai ya shiga girgizawa Yana son fahimtar da Baba ya ki ma barinsa magana daga baya katse wayar yayi da fad'a.

   Wajen awa  daya da rabi kafin Muhktar ya farfado ,idanunsa har ya fad'a yayi wuri wuri daga kwance yake ganinu Umman suna ta rafka masa sannu nai ga fuskar da ya tashi daga mafarkinta ba.

      "Sannu Mukhtar,sannu".Umma ta fad'a ya dubesa Shafiu "Sannu,ya kake Jin jikin naka?".

    Kai ya jinjina yaji muryar Umman "Babanta ya ce na kira ka idan ka farfado ,gashi ga Alh Bashir din ".Umman ta fad'a tana mika masa kunne.

  "Ka fad'a masa da kanka abinda ya faru don na gaji".

  Da mamaki yake kallon Umman "Na ce me ,Umma?"Ya fad'a a galabaice.

  "Poison ta sanya .aka a abinci Muhktar baka da hankali ne ko me? Auren dole ne? Kai bakasani ba ko me tunda kake da ita ta taba baka abinci?"

  Wahalallan numfashi yayi yana girgiza kai "Umma ki katse wayar please me sa kuka fadawa Baban?"

  "Sabida shikadai zai iya da yarsa wannan wahalar ba da mu ba wlh ka tashi ba don abokinka ba sai dai ka mutu tana d'aki ta sanya earpiece kukan mutuwar taka ma ba dadin sa zata ji ba wannan yar iskar yarinyar".

   Idanu ya rintse yayi luf  kiran ya kare Baban bai daga ba ,tunanin Allah kadai yasan badakalar da akai yake ,ko ina ma Ummin ta yi?

   

       *Mu je zuwa ,labarin YADDA NA KE SO yanzu ya fara wasa farin girki ,sai dai ina so ku sani zan dakata sabida sallah idan bayan sallah Allah ya kaimu zan cigaba da post,ayi sallah lafiya yan uwa*


Dijensy

     

  

 
  
 
    
  

Weiterlesen

Das wird dir gefallen

177K 6.5K 81
Not many people understood 12 year old Jessica, as a person and an individual. That doesn't include, however, her older sister, who Jessica adores w...
379K 13K 53
Anhay Sharma:- Cold business tycoon who is only sweet for his family. He is handsome as hell but loves to stay away from love life. His female employ...
300K 21.8K 26
Avantika Aadish Rajawat Aadi, with his fiery nature, adds intensity and excitement to their relationship, igniting a spark in Avni. Avni, like the ca...
The lost triplets Von Rebecca

Aktuelle Literatur

1.7M 55.5K 75
Alexander, James and Skye were triplets. They were stolen from their family at the age of 4. The family searched for them day and night never giving...