YADDA NA KE SO

By Dijen-sy

943 100 44

YADDA NA KE SO burin Ummi ta auri mijin novel ,Mai arziki ba ta son talauci ya rayuwa zata juyawa mata a sand... More

Shafi 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20
Page 21
Page 22
Page 23
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29

Page 7

28 4 1
By Dijen-sy

YADDA NA KE SO🌺

BY DIJENSY



Page 7


    Ummi sauri tayi ta shirya cikin riga da skirt ta yafa d'an mayafi ta fito parlour ta tarar da Baba zaune Mukhtar na daga gefe kan carpet suna dan yin magana kasa kasa ,itan ma rusunawa tayi ta gaishe da Baba ya amsa ,ta sunne kai ita a lallai innocent kuma hakan ba karamin tasiri yayi wa Baba ba ya ga kamar rikicin ta ya ragu tunda har ta iya durkasawa kas ta gaishesa ba irin da ba gaisuwar spring.

  
    Baba nasiha ya musu sosai musamman ita ,dukda ya sameta a hakan sai da ya sake jan kunnenta da ta dinga wa mijinta biyyaya idan yace bari ta bari ,baya son jin tsaiko sam.Yana magana ta jinjina Kai da amsawa da to Baba ,tashi tayi ganin ya gama ya shiga kitchen ta bude fridge exotic ta dakko ta sa a plate da cup sai ruwa ta kai masa Muhktar ta gefen ido yake kallonta ,kamar ba itan ba ashe ta san har ta dakko abu a kitchen haka? Ina ma zata dinga mutunci irin haka.

    Baba bai ma sha ba ruwan kawai ya dauka ya ce musu akan hanya yake  Abuja zai tafi ,nan Mukhtar ya raka shi har kofar gida Ummi ta tsaya daga kofar parlour tana ganin yadda Baban ya sha'ku da Mukhtar sai kace ma shine dan nasa juyawa tayi bayan ta amsa Allah ya kiyaye ta shiga dakinta "Munafuki sai wani kinibibi yake ma Baba ka wa kanka gata da baka ce komai a kaina ba da ka ga abu". Ummi ta fad'a tana cire mayafin ta mayar wardrobe.Zama tayi ta dakko wayarta ta hau danne dannenta , Muhktar da ya komo cikin gida ya ga ba ta parlour yasan daman hakan zatayi.

   ****

   Yau ranar Monday Mukhtar yayi shirin komawa aiki ,bai samu karyawa ba tea kawai ya sha ya shiga dakinta ya ga tana kwance da alama bacci take yayi tunanin kar ta tashi ta ga ba ya gidan kuma at least ya kamata ya sanar mata.Takawa yayi gaban gadon ya tapping pillow din idanunsa kan lips dinta a baccin ma sai ta turo baki wannan yarinya akwai rikici da ta'bara.Yayi tunani a rai.

   Sai a karo na biyu ta bude ido saurin mikewa tayi zaune tana kallonsa "Lafiya?"Ta tambaya cikin maganar bacci.

  "Zan fita aiki ,nace bari na fada miki yau zan koma aiki Incase kina son wani abu ga number na ki kirani"Ya fad'a Yana ajje mata takarda da number rubuce a jiki ta bi ta da ido sannan ta maida kallonta garesa.

   "Da ka rubuta ai ka ajje baka tashen Ina tsakiyar bacci ba now kaina ya dinga ciwo kenan".

  Sauke kafafunta tayi ta na mikewa ta tafi toilet abinta yana binta da ido daga ita sai riga vest da wandon bacci bai kai 'kauri ba.Ko a gefen silifas dinta ta rufo kofarta Muhktar ya girgiza kai ya fita daga d'akin cikeda tunani kala-kala.

   Tun da ta fito daga d'akin ,ta wuce kitchen wani dad'i ta ji ma da ya fitan zata sakata ta wala abinta.Yau dai tayi yunkurin girki don ta gaji da cin cereal da oat ,dankali ta fere ta soya tana Yi tana tsaki duk Mai ya ba fallatsa a cooker gas en Kai da Gani kasan ba ta saba ba,kwai ta fasa uku ta soya ta fito hada shayinta tayi ta ci tayi nak ta ajje plate din da ta bata sink ta komo parlour for the first time ta zauna don d'akin ta gaji dashi.

  Kallo ta kunna a tv ta ja pillow ta shingida a kujerar ,sai wajen 12 ta tashi ta Yi wanka sannan ta sanya kaya jeans da shirt ta saka wanda ya kamata ta Yi kyau sosai ta rubbing powder ,zama tayi ta dinga selfie sai da ta yi ta gaji ta hakura.Anan ta samu na canja profile din Instagram,chat dinta ta duba ta ga Faruk online.

   'Ba magana 'Ta tura masa.

  Ta ke yayi reply "Nayi miki magana nace me? When kin riga da kin nunan iyaka ta'

  'Faruk bansan bayanin da zan ma ka yarda ba cewa bana son auren da Akai min ba ba yadda zanyi ne this is a week I swear ban taba hada makwanci da shi ba to even show you ba ya gabana bana son shi'

  Surprise emoji ya turo mata 'Dont fool me mana Ummi ,sai kace wani yaro zan dauki zancenki ke d'in?'

  'I swear Faruk ba karya nake ma ba ai promise  my pride is yours believe me baiyi komai dani ba'

  'show me your face'

  Video call ta kirasa ta na murmushi 'Ka Kalli idona if am lying '

  Zuba mata ido yayi kansa akan kirjinta da ya fito ta sama don shirt  din Mai budadden wuya ce sosai ya ce 'Na ji na yarda but what is the way out?'

  'Have you inform your parents?'Ta tambaya.

  Kai ya gida mata 'Daddy yace na bashi lokaci'
Murmushi ta Yi 'Ya school?'

  'Fine ya kike?'

  'Not fine ,na rasa me ke min dad'i all I know is that I miss you'

  Murmushi yayi Yana gyara kwanciya 'I Miss u too '

    Hira sosai sukai don ta fad'a masa ma ya fice so called husband din nata ,wajen zuhr ta tashi tayi sallah.Knocking ta ji a kofa ta fito ta bud'e wacce ta gani a tsaye ya sa ta tsalle ta rungumeta "My Yusrah bayanta kuwa Shaheeda ce ita ma ta je ta rungumeta "Mara mutunci kin ga dama kin zo?"

  Baki ta ta'be Shaheeda"Darajar Yusra ki ka ci yarinya".

  Shigowa sukai ciki suka zauna parlour tana ta murna suna tsokanarta da amarya ta ango.

   Tsaki tayi Shaheeda tace "Munafuka ga yadda kikai fresh kin wani da'me Allah sa bamu takura muku ba Ina mijin naki?"

  Harara ta watsa mata "Miji ne zai sa na tsuke bazan yi kwalliya don farincikin kai na ba? Ba ma ya nan ya fita ke fa ba wani fresh ki ma daina wannan tunanin Allah ya sawwake wlh ko gado bazan kwana da shi ba balle ma wani Abu ya hadani dashi".

  Baki Yusrah ta rife "Ummi me kika fad'a?"

  Baki ta ta'be "Mai kunnenki ya ji ,Yusrah kenan ke wasa kika dauki zance na ne? Wai kuwa kinsan tsanar da nayi masa? Ko zaa mutu bazan taba yarda dashi ba don ban dauke sa miji ba".

  Jinjina Kai Shaheeda tayi "Lallai Ummi baki da hankali amma ke da bakinki kike fad'ar haka".

  "Allah ya shiryeki Ummi wlh bazai dore ba wannan abin naki Ake zuwa dai shi ido zai cigaba da zuba miki aka ce?"Cewar Yusrah.

  "Tohm ya Yi min dole man na mani".Cewar Ummin.

  Tashi tayi "malamai ku tashi mu shiga d'aki ,mai kuka kawo min?"

"Gidan amarya muka zo kin ci uwar rainin wayo ma abinci muka zo ci na amarya".

"Abinci ? Ni fa ba na girki yau ne ma na dan yi dankali ga ragowa can wlh ,mu je kitchen din ku dafa abinda kuke so".

  Baki Yusrah ta rike "Mai mijin yake ci?"

  "Babarsa ta kawo masa na kwana uku ,Yana hada tea yasha da indomie matsalarsa ce ba ta wa ba duk ya ga zai iya ne".

  Kai kawai suke jinjinawa , kitchen din ma da suka shiga suka ga wanke wanke a sink "Wanann din wa kika barwa?"Shaheeda ta fad'a.

"Ku na barwa idan ba za ku min ba kudaina tambaya".

  "Lubabatu za mu kawo miki kawai". Yusrah ta furta.

  "Ni banson me aiki ai ba zama na zo Yi ba ba Kuma girki nazo masa ba ,Kuma wlh kar Wanda kuka fadawa Kuna dai kina ku dauki abinda zaku girka ku ci ko kuma ku ja bakinki kuyi shiru"?

   Basu kuma magana ba ,fried rice sukai suka suya kaza sukai chicken pepper ,har rawar jiki take suna gamawa ta zuba ta ci don ta dade ba ta ga lafiyayyan abinci ba haka.Ranar wuni sukai daf da zasu tafi Muhktar ya dawo a parlor suka gaisa dashi ko sannu da zuwa ba tayi ba ta raka su har gate suka tafi ta dawo bata samesa parlour ba ta zauna abinta wanka yayi ya fito ya tarar da ita.

   "Ba magana Amarya".

   Kallonta ta mayar kan tv "Kawayenki ne baki fad'a min zasu zo ba"Ya sake magana.

  Kallo shi tayi "Au sai na nemi izini zasu shigo?"

  Kai ya girgiza "Ba haka nake nufi ba but ai da mun tanardar musu wani abun".

  "Sun gode".Ta furta kamar an mata dole.

  Kewayowa yayi ya zauna gefenta tayi saurin mikewa ya riko hannunta ta koma "Mene hakan ka sake ni".

  "Tohm ki tsaya ki sauraren".

  Kai ta kawar tana cika tana batsewa  fa fuzge hannunta ta koma ta zauna "Calm down ba fad'a bane ,magana zami".

  "Ke yanzu kina Jin dadin wannan abun da kike? Irin zaman da muke tare? Ba fa Makiya bane mu maaurata ne"

  Kai ta jinjina "Indai baka son abinda nake ma kayi abinda zai hana faruwar hakan".

"Amma kinsan bazai yiwu ba ,abune wanda bazan taba Yi ba komai Zaki min Ummi aurenki na riga da nayi stop decieving yourself stop second thought face the reality Ummi ba yadda kika daukeni nake ba ,wlh duk macen da ta kasance da ni zata ji dad'i kuma zan faranta mata indai kulawa kike so sai kin ture , iya karfina da abinda nake dashi zan miki "

  "Dan Allah ka daina maganganun nan don ba shiga ta suke ba,ba kyautatawa ba kome zaka min ba zan taba zaman aure da kai ba".

   "Mai kike so toh?"

  "Ka bani takarda ta".

"In na baki Ina Zaki?"

 "Ba damuwarka bace".

"Damuwar matata ta shafen dole na tambaya ".

  Mikewa tayi ya sake damke mata hannu "Rest your case Ummi mu zauna lafiya".

  "Har abada,ka cika ni".This time around da fad'a tayi maganar.

  Sakinta yayi ta tashi ta tafi d'aki tana Jin haushin rike mata hannu da yayi "Dan iska"Ta furta tana goge hannun.

  Kitchen ta shiga abincin da suka rage a flask ya gani ya Gani a ransa yayi tunanin ashe shi kadai ne bazata girkawa ba.Abincin ya duba ya zuba ya ci ya koma d'aki Yana tunanin yadda rayuwa zata kasance da irin wannan zaman nasu.


 

Tun sannan bata sake fitowa parlour ba idan Yana nan kullum haushinsa na karuwa gunta ,tun sanda su Yusrah suka zo bai Kuma cin abinci mai suna abinci a gidan ba sai dai yaci a waje.Da ya Gane sai ya ke ci daga waje idan ya shigo cikinsa a cike sai dai ya zauna time din bacci yayi ya kwanta duk yadda ya so su daidaita da ita ta ki ba ta fahimcesa ba ma balle ya bullo mata da wani aza room stuff marabarsa da wanda bai aure ba canjin gida ban da haka ba abinda ya sauya kuma ya kasa fadawa kowa damuwarsa....

   Ummi a bangaren ta kullum sai tayi waya da Faruk ,idan tayi hoto ta tura masa ba abinda ya dameta soyayyarsu suke Yi hakan Yana rage mata kewa.Tayi waya da Ya Abdulbasit shi din ma kira yayi ,sau daya ta kira Anty Sa'a sun gaisa ta tabbatar mata suna lafiya shikenan Anty Nafisa ta kirata itama.

★★★

   Tun a jiya da daddare Umma ta kira da ta ke fad'a masa Yara za su zo gidan sa,ya amsa da toh sai dai bai san ya zai Yi da waccen yarinyar ba.Daman weekend ba aiki ko da ya tashi kamar kullum bayan yayi  wanka ya fito dakinta ,ya sameta tana sauya zanin gadon dakinta ita ba ta yarda ba aiki take sai haki take bata saba ba gajiya tayi da ganinsa yasa zata sauya don da ba abinda zai sa ta wani dakko aiki.Ko shara iya dakinta take yi , Muhktar ke yin sharar duka gidan wajen compound ya sa almajiri ya share musu bandakinsa da na parlour ma shi ke wankewa idan ya samu time weekend.

     "Ummi".Ya kirata ta dago kai tana kallonsa lokacin take d'ame bedsheet din.

"Yau 'kannena za su zo".

  "Ina da damuwa ne?"Ta furta.

    Takowa yayi  inda ta ke "Baki da ita amma ni Ina da ,ko ba komai kannena ne please ki ajje duk bacin ranki ki yi shi a kaina daga ni sai ke dan Allah karki huce haushina akansu , please I am pleading ,need this favor from you".
   
   Shiru tayi yace "Zan iya samu?"

   "Mai kake so na musu tukunna ma wai?"

  "Wannan abincin me dad'i da kikaiwa freinds dinki idan zasu samu a musu sai ma na taya ki".

  Murmushi tayi "Na musu ko sukai abinsu ,su sukai kayansu Kuma ma da kake maganar kawayena are you comparing them with my friends?"

  Kai ya girgiza "Ko kadan just assist and treat them good".

  "Ni bazan iya dora tukunya ba ,idan kana son su ci abinci you can place order for them su zo su ci".

  Shiru yayi kafin ya ce "Is ok hakan ma yayi ,I will do so can you promise to treat them nice?"

"Ni da nace maka dukansu zan ko mene ka dauken Mukhtar?"Ta fad'a.

  "No kawai attitude ne banson su gani su san halin da muke ciki".

  "Naji".Ta fad'a.

  "So help me  ina yakamata na siyo musu?"

  Fada masa gun abinci tayi me tsada sannan ta ce "Ina son ice cream ka ta hon dashi".

  Murmushi yayi ya ce "Tohm sai na dawo".

  Ba ta ce ko Allah ya kiyaye ba ya fita ta Yi tsaki "Mara zuciya".Ta furta.

_Readers ba kwa min comment,ba Kuma kwa voting_

Dijensy
 
 

Continue Reading

You'll Also Like

142K 6.9K 28
Hooked onto drugs, no family, no guidance or sanity until she met HIM. Cover Creds: @Triceynexttdoor โค๏ธ -BLICKY.
60.5K 1.4K 35
โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€ you got me down on my knees it's getting harder to breathe out . . . โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€ ๐‘ฐ๐‘ต ๐‘พ๐‘ฏ๐‘ฐ๐‘ช๐‘ฏ . . . ๐œ๐ก๐ซ๐ข๐ฌ ๐ฌ๐ญ๐ฎ๐ซ๐ง๐ข๐จ๐ฅ๐จ ha...
1.7M 55.5K 75
Alexander, James and Skye were triplets. They were stolen from their family at the age of 4. The family searched for them day and night never giving...
333K 10K 81
(Fixed/Fan-TL) Top idol group Stardust, whose members disappear like dust. The group that used to have seven members ends with four members... "Is...