MAHREEN

By HAERMEEBRAERH9900

1.5K 423 71

A Koda yaushe muna Jin labaran zama da kishiya Mai ban mamaki da ban al'ajabi....Labarin MAHREEN labari ne na... More

MAHREEN PAGE 1
MAHREEN PAGE 2
MAHREEN PAGE 3
MAHREEN PAGE 4
MAHREEN PAGE 5
MAHREEN PAGE 6
MAHREEN PAGE 7
MAHREEN PAGE 8
MAHREEN PAGE 9
MAHREEN PAGE 10
MAHREEN PAGE 11
MAHREEN PAGE 12
MAHREEN PAGE 13
MAHREEN PAGE 14
MAHREEN PAGE 15
MAHREEN PAGE 16
MAHREEN PAGE 17
MAHREEN PAGE 18
MAHREEN PAGE 19
MAHREEN PAGE 20
MAHREEN PAGE 21
MAHREEN PAGE 22
MAHREEN PAGE 23
MAHREEN PAGE 24
MAHREEN PAGE 26
MAHREEN
MAHREEN PAGE 27
MAHREEN PAGE 28
MAHREEN PAGE 29
MAHREEN PAGE 30
MAHREEN PAGE 31
MAHREEN PAGE 32
MAHREEN PAGE 33
MAHREEN PAGE 34
MAHREEN PAGE 35

MAHREEN PAGE 25

36 15 3
By HAERMEEBRAERH9900

💅   MAHREEN   💅





WRITTEN BY HAERMEEBRAERH






PAGE 25:



Machine ne ya ci burki a baya na da qarfin gaske, ina buɗe ido na a hankali sai na kula na bar kan hanya na fara hawa titi, mutumin har ya fara masifa sai ya kula da yanayi na, cikin rage faɗan da ya fara min ya ce,

"Ke Wagga lahiya ki ke kuwa?"

Nan da nan kuwa hawayen da nake ta maqalewa suka hau sauka da gudu, zafin su na qona kumatu na na durqusa na ɗauki jaka ta da ta fad'i na ci gaba da tafiya, biyo ni ya yi ya ce na hau ya kai ni gida,Na so na yi musu sai na ga Kabu kabu ne ko banda kuɗi zan iya tsayawa maqota na karba na biya na basu daga baya dan dai nera saba'in in Allah ya yarda ba zan rasa me ara min ba.

Komawa baya na yi na hau a hankali na sanar da shi Alieru qtrs za a kai ni,nan da nan kuwa ya dauki hanya sai unguwar mu, mu na isa na ce ya jira na dakko masa kuɗin shi ya ce min,

"Basshi d'ai" (barshi kawai)

Godiya na masa na shige cikin gida, ina shiga na yi wurgi da hijabi na na kwanta a qasan carpet na kunna standing fan dama ta saman a kunne take, kuka na buɗe baki da qarfi ina yi, saboda ciwon da ko ina na jiki na yake min, na yi kukan da ban taɓa yi ba a rayuwa ta ranar har se da bacci ya ɗauke ni,Ko juyi na yi sai na b'are baki na ci gaba da kuka na kafin wani baccin ya sake ɗauka ta.

Duk abin nan da ake na rashin lafiya ta ban taɓa qin yin girki ba, saboda Yah Maheer baya son cin wani abincin in ba nawa ba sai dai in lalurar hakan ta kama ya zama ba yanda zai yi to zai ci a wani wajen, se kuma in mun je gida, ko maqota ne suka kawo abinci baya ci, tin da na dawo garin ya dena cin abincin kowa.

Wata rana da jima wa ban mantawa mu na hira da Maman Ameerah a game da maza da ke cin abinci a ko ina, se na ke faɗin cewa shi baya da wannan halin gaskiya duk da ya kan ci amma se dole,cikin nuna jin haushi ta ce,

'Wa ya faɗa maki baya cin abincin waje?'

'Ba ina nufin ba ya cin abincin waje kwata kwata ba, in dai Ina nan ba ya cin abincin ko ina ya gwammace ya zauna da yunwa ko ya yi ta shan fruits, shi ya sa sanda ya fara zama a garin nan duk sanda ya je zan ga ya rame'

'Ai kuwa ya na cin nawa, kuma rama da ya yi ai saboda ciwon qodar da ya yi ne baki ga har baqi ya yi ba a lokacin,kuma haka ɗaliban shi mata za su dinga zuwa duba shi har abincin suke kawo masa, na kan ce Allah ya kiyaye kar su masa asiri tunda matan garin nan akwai shegen asiri in suka ga namiji su na so se ki ga budurwa ta kai shi wajen malami an asirice mata shi'

A lokacin nan na ji raina ya ɓaci wato a gaba na ne yake nuna ba ya son cin abincin kowa a bayan ido na se ya hau ci, ko da ya dawo na tare shi da maganar ina ta masifa, be ce min ci kan ki ba se da na gama sannan ya ce,

'Da ta faɗa maki ina cin abincin ta ta taba gani na da idon ta na ci abincin wani waje haka kawai ba dalili? Na tan ma saboda mijin ta na gayyata na ne kuma kin san babu kyau a gayyace ka cin abinci ka qi, ke kin ga shaida ai sanda ku ka zo bread ne se fresh milk da fruits su ne abinci na na kan kuma sai nama haka da kifi soyayye na ci, kuma da take maganar 'yan mata ba ɗalibai na bane, sannan ba sanadin na kwanta jinya suka zo duba ni ba? Yanda suka kai haka suke kwashewa tunda ba iya ci ma nake ba, kaiii wannan matar na rasa me yasa take so dole sai ta ja min masifa ina zaune lafiya da iyali na, sannan in banda abinki Zan zauna da yunwa ne idan na ji ina son cin wani abu ba bread ba ke da kan ki ki ke matsa min se na je na siya na ci, ra'ayi na ne bana so na ci wani abincin in ba naki ba, sannan kamawa take nake cin wani abincin idan ba nakin ba, ai komai dalili ne da shi ko? Dan Allah ki dena ɗaukan maganganun matar nan ba kowanne ne ke da amfani ba"

Yanda ya yi maganar ma ni se ya sanya ni dariya, sannan daga baya na gane ai duk abinda ya faɗa gaskiya ne zai kashe kan shi da yunwa ne in be ci abincin wani wajen ba a sanda bana nan? Hira muka ci gaba da yi ya na sanar da ni yanda zan dinga zama da mutane ba komai ne za a faɗa min in dinga dauka ba, wani burin shi ya hana ka zaman lafiya,a haka dai mukai ta hira kala kala har aka manta da zancen.

Ajiyar zuciya na sauke mai qarfi bayan na gama dogon tunani na,a daddafe na tashi na shiga kitchen na yi girki, taliya ce kawai na dafa dama ina da miya, se na yanka lemo da kankana na ajiye sannan na yi wanka na yi sallar la'asar da ta jima da wuce wa.

Wata riga ta na sanya wadda za a kira ta da net, Dan kuwa Shara Shara ce sosai, sai pant da na saka shi kaɗai, zaune nake ina shan iska Suwaidatu da ta dawo daga boko ina bacci ta yi shirin islamiyya ta tafi, dan ta makara sosai jira take dama na farka ta shirya ta tafi, nan take na tuna cewa BD na fa ya gabato December din nan zan cika shekara sha takwas cif-cif,murmushi ne ya kwace min, na hau murna,ni ma zan zama babba.

Maman Ameerah ce ta fito da daurin qirjin ta kamar kullum, zama ta yi a gefe na mu ka hau hira jefi jefi, cikin zumudi na ke sanar da ita cewar,

"Gobe fa BD dina,"

A d'age ta Kalle ni ta ce,

"Shekara nawa?"

"Inshaa Allahu gobe zan cika shekara sha takwaaaasss"

"Mtssswwwwww, ni na zaci ma kin kai ashirin ashe ke se yanzu ne zaki shekara sha takwas ɗin?"

Wani irin b'acin rai na ji ya kama ni, saboda ina da wani hali na tsani tsaki, ita kuma halin ta kenan, bata iya minti ashirin bata zabga shi ba, ni Ko ba da ni akai tsaki ba se na ji ba daɗi balle ayi da ni, kallon ta na yi ni ma a d'age dan na fara mayar mata martanin rashin kyautatawar ta nima a hankali ba tare da na sani ba ma.

"To ai dama kowa da shekarun shi a duniya nima iya nawa kenan, kuma ina alfahari da hakan na ji dad'i da zan cika shekara sha takwas Alhamdulillahi "

Surutai ta dinga yi ta kama hanya ta shige d'akin ta, mamaki ne ya kama ni menene na faɗa a cika shekara sha takwas? Da kai na na furta,

"Allah ya qara kema, me shegen surutun tsiya, komai se kin faɗa ai gashi nan"

Miqe wa na yi da kyar na shige nawa gidan raina a bace, da dare na zaci Yah Maheer ya manta da BD na, se na hau hira a fakaice ina fadan date of birth ɗina, ya na ji na be ce komai ba, haushi ya kama ni, saboda ni fa na ɗauki cika ta shekara sha takwas babban abu, ni ina ta BD ɗina shi ya na ta lafiya ta, dan rashin lafiyar da nake ba ta boyu a idon shi ba, sannan na sanar da shi ko map reading exam ban tsaya na qarasa ba gida na dawo, dan haka a dame yake, what if na zo ban samu na ci Geography ba da dai sauran tunane tunanen nan su suka haɗe masa suka hana shi kula ni.

Ina nan ina kumbura baki ya wuce masallaci sallahr Isha'i,ko da ya dawo na yi wanka na fito da katifa parlour,na yi readyn yin bacci, ina nan daga kwance mu na ta hirar gida dan kuwa ya ce da sallah can za mu je mu yi sallah,har qarfe sha biyu bacci ya qi dauka ta, kuma yau mu ne zamu kwana ba wuta se asuba a kawo, kamar jira suke kuwa  ina kwance kawai se dif an ɗauke wuta, wani irin kuka ne ya tokare min wuta saboda na san yau ba zan bacci ba, banda ma rashin baccin da zan yi ciwon da qurajen nan za su hau yi min ba kaɗan bane domin dama ranar an kod'a rana.

Lallashi na Yah Maheer ya hau yi, ya ja maficin da ke gaba na ya hau yi min firfita, ni dai shiru kawai na yi bahaushe ya ce da babu gwanda ba dad'i amma kam bana wani jin firfitar nan, kula da hakan ne ya sa ya ce min,

"Baby na ki qara hakuri, na san zaki ta jin maqota sun kunna inji mu kuma shiru, ga AC a kowanne gida akwai ta amma mu shiru, inshaa Allahu watarana zan sa maki AC zafi ba zai dinga damun ki ba, zan kuma sai maki gen in ba wuta kawai se mu kunna gen ɗin mu mu kunna Acn mu mu sha ko?"

D'aga masa kai na yi a shagwab'e saboda da salon lallashin yake min magana kamar ana ririta ɗan yaron da ba a so ya yi rikici,a qarshe qofar parlour muka fita muka zauna ya shimfid'a abun sallah ya kwanta, nan da nan kuwa bacci ya ɗauke shi, saboda ya gaji,ni kuma yanda na ga rana haka na ga dare saboda ba ma zan iya baccin ba.

Washegari kuwa bayan Yah Maheer ya dawo daga masallaci sai na ji shiru be min addu'a ba, be taya ni murnar cika shekara sha takwas ba, se na hau fushi ina kumbura baki, nan take na tuna sanda na cika shekara sha bakwai a gidan shi lokacin mu na Bauchi, siyayyar kayan kwalama dangin zaqi da na fi so ya yi min,sannan da sassafe ya tura min message zazzafa da addu'o'i a ciki, me yasa wannan karon be min ba, fushin babu gaira babu dalili na hau yi, ina gama komai qarfe tara da rabi Baba ya kira ni, su na a tare da Mama, Waqar da mama ke min tun ina yarinya ta hau yi min,sannan ta min ta BD sannan ta min addu'a sosai Baba ma ya yi min addu'a sosai na dinga jin dad'i tare da yi musu godiya (Har yau in Mama na nishad'i mu kai waya to fa zata rangad'a min waqa ta tin ta yarinta, kusan duk haka take mana)

Ganin ba fa zai min maganar shekarun da na qara ba kawai se na tafi gidan Maman Aminu, nai zama na, anan ne Amina ta kai ni gidan wata mata da ke unguwar, bayan mun gaisa ne take tambayar ina ne gidana na yi mata kwatance, bata gane ba, Amina ta ce mata, ni matar Malam Maheer ce ai, gidan mu daya da Maman Ameerah, mamaki ne ya kama ta, ta ce,

"Auuu dama da gaske da mutane a gidan bayan ita Maman Ameerah? Ai na sha zuwa da dare in na ga haske sai in ce mata anan matar Malam Maheer take sai ta ce ah ah,ba kowa su kadai ne a gidan,ashe qarya ne, ai ko inshaa Allahu duk na zo zan zo a gaisa,"

Haka muka ci gaba da hira sama sama daga baya na koma gida, bayan na koma ne wata 'yar ajin mu ta zo me suna Asma'u wasagu take sanar da ni randa na tafi fa Mr. Joseph sa wa ya yi a taimaka min wajen yin map reading saboda an sanar da shi banda lafiya ne ya sa na tafi, hamdala na dinga yi ga Allah ina sakewa, sannan na ce in yana da rabon musulunta Allah ya sa ya musulunta.

Bayan tafiyar ta da 'yan mintina ne na ji waya ta ta yi qara alamun saqo ya shiga ciki, ɗauka na yi dan in ga wanda ya tura saqon, sunan Yah Maheer ne ya bayyana cikin tura baki kamar ya na gani na na buɗe, kalaman da na karanta se da suka sanya ni zubar da hawaye, addu'o'in da ya min sun raunata zuciya ta sosai, ina tsaka da kukan farin ciki wani message din ya shigo, katin waya ne na dari biyar,kafin in kwashe in loda a waya ta ya kira ni.

"Hayyakillah ya habibty"

Wani irin farin ciki ne ya kama ni har da tsalle na,

"Wato ashe kyale ni ka yi ko ka na sane ka qi kula ni, ni ma to Yau ba zan kula ka ba"

"Tooo da wa nake magana yanzu?"

"Da dodo"

"Dan Allah ya yi hakuri kar ya firgita ni, babyna na kusan dawowa me ki ka dafa ne yunwa na ke ji"

"Ni ba abinda na dafa yanzu dai nake so na yi girkin saboda na san se bayan Isha'i za ka dawo tunda yau ka na da 4-6 lecture"

"Hakane to kin san yanda za ai ki yi girkin kaɗan tunda kin ga zafi ne kar ya kwana ya lalace"

"Inshaa Allahu haka zan yi se ka dawo, Allah ya bada Sa'a, Allah kai ma ya yi maka dukkan abinda ka roqa min a wajen shi har ma da qari"

"Ameeen mar'atussalihaaa se na dawo"

Bayan ya kashe waya ne na ji wani kwarin guiwa, ban ɗora girki ba kuwa se da shida na yamma ta yi dan na san se bayan magrib zai dawo, shinkafa da fa dika na yi ta sha zogale gidan Maman Aminu na samo ga albasa se qamshi take,da busasshen kifi na yi amfani dan ni na fi son in dai dafa duka zan na sa kifi na fi ci sosai.

Kankana na wanke na yanka na cire wa kwallaye na yanka ta qanana, na zuba madara da sugar dan kuwa ita kaɗai nake da a wannan lokacin, sai ruwan da ba wani sanyi sosai, ina girki ina gyaran gida da jiki na, dan haka sai kammala komai da na yi ya yi daidai da bugawar agogo qarfe takwas na dare, ina Yah Maheer ya tsaya? Me ya sa be dawo da wuri ba? Daurin dankwali na da na kafa na taɓa dan so nake na burge shi saboda addu'o'in da ya min da kalaman qaunar da ya zuba min amma fa fisabillahi na takura, na jima rabon da na saka atampa gashi ba wuta mu za a kawo wa da sha biyun dare yau.

Ai kuwa ina nan zaune har tara ta yi na ɗora hannu na zan tuge dankwalin se muka ji qarar buɗe gate, murgud'a baki na yi na ce,

"Haaaa Allah ya temake ka da se dai ka zo ka ga wannan cinyayyen gashin nawa da quraje suka cinye"

Sallamar shi ya yi cikin sanyin shi sannan ya shiga parlour,miqe wa na yi da sauri ganin ledoji a hannun shi,karba zan yi ya girgiza mun kai alamar in barshi, se da mu ka yi sannu da zuwan mu da muka saba na musamman sannan na ja baya ya wuce ni zuwa bed room din mu nan take na taka na bishi.

A gado ya baje ya na maida numfashi, da alamun gajiya da yunwa a tattare da shi sosai, cikin tausaya wa na hau matsa masa qafafun shi sannan na ce,

"Sannu Yah Maheer ɗina, ka gaji ko? Mu je na taya ka wanka, se ka ci abinci, ko kuma abincin zaka fara ci?"

Idanun shi lumshe ya ce,

"Bari na fara wankan,dan in na ci abinci ba zan iya ba bacci zan yi na san"

Wanka na tafi na taya shi bayan na rufe qofar da zata sada mutum da parlour da banɗaki saboda kar Suwaidatu ta gani.

Mu na fitowa na haɗa masa abinci, nan take ya ce,

"Ba ki duba abinda na kawo ba ko?"

Ni dai na ji qamshin abubuwan kwad'ai tunda na san ina da kwad'ai ba se an fadan ba ma, jan ledojin na hau yi kayan kwalama ne kuwa sosai a ciki da kuma gasassun kaji biyu manya se lemon exotic da qananan cup cakes,tsalle na yi na d'ale shi ina ta murna sannan na hau yi masa godiya da addu'a, se da na gama murna ta sannan ya ce,

"Kar fa ki ga na siyo wadannan abubuwa ki zaci ina supporting wai bikin zagayowar ranar haihuwa,ah ah na miki ne dan kyautatawa, dan kar ki saba da wai duk ranar zagayowar haihuwar ki sai na ce maki happy birthday Shi yasa na jinkirta ban maki ba, so ki sa a ran ki ko da BD ko babu in ina da shi zan kyautata maki kuma zan maki addu'a sannan in banda shi za mu ci gaba da hakuri da rayuwa kin ji ko?"

Kai na daga na yi masa godiya, Suwaidatu ta yi bacci dan haka aje mata nata na yi na ce gobe sun haɗu, gajiya na yi da daurin dankwalin kai na se na Kalle shi nace,

"Ka ga kwalliya ta?"

"Eh Masha Allah kin yi kyau duk da cewa ke ɗin kyakkyawa ce ko ba wanka ba guga"

Dariya mu ka yi a tare sannan na ce,

"Ka ga daurin dankwali na ya yi kyau?"

"Sosai ma ai in ki ka kafa gwaggwaro sai mutum ya zaci kun haɗa dangi da yarabawa nan kuwa tsabar kwarewa ce kawai"

Dariya muka dinga yi sosai saboda yanda yake maganar na san ya san me nake shirin yi,ai kuwa tuni na sa hannu na tuje daurin na ce,

"Washhh Allah na na gaji, yau na yi qoqari na jima da daurin nan a ka"

"Ni da na san cire wa za ki yi, shi yasa ki ke ta wannan shan kwanar"

Haka muka kwana cikin farin ciki, sai na ji duk wasu ciwukan da nake ji sun min sauqi saboda farin cikin da Yah Maheer ke bani, hamdala na dinga yi ina gode wa Allah mai kowa me komai wanda yake yaye wa mutum baqin ciki ta hanyoyi da dama, idan ya jarabce ka da rashin wani abun ta wani ɓangaren sai ya jarabce ka da samu ta wani bangaren, ko ya yalwata maka ya sanya ka farin ciki ta wani fannin, dan haka na tabbatar da cewa Allah ya jarabce ni da ciwo tun ina qarama ta, se ya bani iyaye na gari masu tausayi na da 'yan uwa masu qauna ta, bayan na girma na fita daga qarqashin kulawar su se ya haɗa ki da miji na gari mai tsananin so na da qauna ta tare da kulawa da ni,shi din 4 in 1 ne, shi ne uwa ta uba na kuma 'yan uwa na da ke nesa da ni sannan kuma miji na.

Duk irin gwagwarmayar da nake sha ta rayuwa mutane da dama ba su hango wannan illa gatan da nake samu wajen Yah Maheer shi ke tsone masu ido, shi kawai ake so a dakushe min ko ta wacce hanya ba tare da ni na sani ba, domin ban taɓa kwana da kowa da mugun nufi ba a rai na, sannan ban taɓa tashi da kowa da mugun nufi ba a raina.

***************************

Bayan sati biyu muna zaune da dare tsakanin magariba da isha'i, daren ranar anata kod'a zafi Maman Ameerah da iyalan ta na tsakar gida su na shan iska, ni kuma da nawa iyalan mu na qunshe a cikin gida mu na shan zafi saboda ba ma so mu fita gaba ɗaya a cakud'e abun be yi tsari ba dan na san da mijin ta ya dawo anan zai kwanta,Yah Maheer kuwa ba zai bari mu zauna ga mu ga su ba se ya ce in aka kawo wuta fa? Shi baya so, ina zaune se na ji yo muryoyin mutane a tsakar gida alamun an yi baqi, ina nan zaune shiruuu ina ta aikin firfita a raina ina fatan su kawo wuta dan mu ne da wutar sha biyu na dare, zuwa a asuba,gashi Yah Maheer na masallaci be dawo ba, sallama na ji an yi min a qofar parlour na, jinkiri na ɗan yi kafin na tashi zaune na amsa, mayafin da nake daurawa na gyara saboda ni bana daura zanin atampa se dai mayafai da na mayar zani dan sun fi fitar da shape me kyau a jikin mace, ba za ka zauna ka yi kamar wani ɗan qauye ba.

A bakin qofa muka haɗu na tsaya ina mamakin ganin su............

*Mutanen kwarai masu albarka in an karanta a dannan min star hilis sannan a yi sharing saboda wanda basu karanta ba su antayo ayi da su..ina maraba da comments ɗin ku, amma a yi hakuri banda zafafawa domin wannan labari na gaskiya ne kamar yanda na sanar da ku tun farko...Thank you my fiful*

Continue Reading

You'll Also Like

280K 32.3K 81
#Book-2 of Hidden Marriage Series. πŸ”₯❀️ This book is the continuation/sequel of the first book "Hidden Marriage - Amazing Husband." If you guys have...
1.3M 67.6K 59
π’πœπžπ§π­ 𝐨𝐟 π‹π¨π―πžγ€’ππ² π₯𝐨𝐯𝐞 𝐭𝐑𝐞 𝐬𝐞𝐫𝐒𝐞𝐬 γ€ˆπ›π¨π¨π€ 1〉 π‘Άπ’‘π’‘π’π’”π’Šπ’•π’†π’” 𝒂𝒓𝒆 𝒇𝒂𝒕𝒆𝒅 𝒕𝒐 𝒂𝒕𝒕𝒓𝒂𝒄𝒕 ✰|| 𝑺𝒕𝒆𝒍𝒍𝒂 𝑴�...
585K 48.7K 23
Indian Chronicles Book III My Husband, My Tyrant. When Peace Becomes Suffocation. Jahnvi Khanna has everything in her life, a supporting family, a hi...
3.1M 70.1K 81
Diana is an 18 year old girl about to start her senior year until she bumps into a woman at the bookstore who has quite the personality. The woman ta...