YADDA NA KE SO

By Dijen-sy

968 110 44

YADDA NA KE SO burin Ummi ta auri mijin novel ,Mai arziki ba ta son talauci ya rayuwa zata juyawa mata a sand... More

Shafi 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20
Page 21
Page 22
Page 23
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29

Page 5

27 4 1
By Dijen-sy

YADDA NA KE SO🌺

BY DIJENSY

Page 5

 
   "Nasiru asibiti zaka wuce ba gida ba".Baba ya fad'a ,kai tsaye asibitin ya kaisu suna zuwa ya zagaye bayan motar ya daka mata tsawa ta fito a tsorace tana gudun kar ya sake mata wani marin.Asibitin suka shiga ya ce a kai ta a mata gwajin 'kanjamau da duk wani disease da yake sexually transmitted don bai ma yadda ba ta ta'ba wani ala'ka da wani ba sannan yasa a auna ko tana da ciki.

  Tambayoyi me gwajin take mata ganin yadda hankalin ta yake a tashen har ma da wanda ya kawo ta.kadan take amsa mata idanunta na tsiyaya da hawaye.

  "Kina da aure ne?"
  Kai ta girgiza a ranta ta raya ga dukkan alamu fita take da samari ,ta jima d'akin gwajin tana mata aune aune har sai da ya isheta kafin ta fito aka ce su jira na yan mintina aka fito da results ya tabbatar bata dauke da komai ,suka tabbatar wa da Baba ma bata taba yin wata muamala ba sai a sannan yaji sanyi a ransa duk da da kyar ya yarda suka tafi daga asibitin .Tun da suka tafi har suka isa bai ce da ita komai ba ,suka shiga gidan ta gudu d'aki ya wuce wajen Nafisahn.

  "Mai yasa kika bar yarinyar nan fita?"

  Da mamaki ta dubesa "gidan kawarta tace zata ne fa".

  "Toh ta bi saurayi sun fita yawo na ganta ba dan ina nan ba Allah kadai yasan abinda zasu aikata yarinyarnan nema take tafi karfina dole na kawo maganin abinnan".Baba ya ke fad'a rai a bace.

  Da mamaki Anty Nafisa ta ke sauraransa ta na girgiza Kai "Ko dai mahaifin yaran za a wa magana?"

  'Yaro? Ina ruwana dashi? Shi yake bibiyarta ko ita ke kai kanta? Bani da wannan lokacin nasan me zanyi".Ya fad'a tare da yin kwafa ya fice harabar gidan.

   Abdulbasit ya nemo a waya ya daga ya sanar masa da abinda ya faru ya tabbatar masa duk hukuncin da ya dauka kar suyi blaming dinsa yayi iya yinsa kanwarsu bata jin magana sabida haka ga abinda ya yanke.

  Abdulbasit shiru yayi don hukuncin yake ga yayi tsauri sabida kanwar tasu duka nawa take za a ce za a mata aure,ko institute bata shiga ba.Ba yadda zai yi ya ja da Baban don yaga ransa ya baci ,a take Abdulbasit ya kira Ummin bayan sun gama waya da Baba sai dai taki dagawa tasan bata da gaskiya.

  
Dawowarsa kenan daga wajen aiki ko gida bai karasa ba bayan magrib ya tsaya gun mai shayi kamar kullum siyan indomie  kira ya shigowa wayarsa.

      "Alh Bashir" Ya gani rubuce ,gefe ya ja ya amsa bayan ya gaishesa yace "Mukhtar idan ba damuwa gobe asabar ina son ganinka a gidana ".

  Shiru yayi kafin ya ce "Tohm Baba Allah ya kaimu"

  Sallama sukai ya katse wayar Muhktar ya shiga tunani ma zai fad'a masa ko dai wata kyautar ce ,duk ya ji wani irin yana ganin kamar he is doing much.Yana amsan indomie sa ya wuce gida washegari da safe ya tafi gidan Baban anyi masa iso a sitting room daban ya samesa ya du'ka Kai cikin rissinawa  ya gaishesa ya sa ya dawo kujera ya zauna.

  "Ahnn Mukhtar ? dalilin da ya sa na kira ka ina so ka amsa min wata tambaya wacce ta shafeka ka da ka ji nauyi na ko wani abu a matsayin mahaifinka nake  ba wani boye boye tsakani na da kai hakane?".

  Kai ya jinjina Mukhtar Baba ya ce "Ya batun aure akwai wata da ka tsayar ne da niyyar aura ko kuwa babu?"

  Dimm ya yi na d'an lokaci kafin ya dago kad'an bai iya hada ido dashi ba ya girgiza kai "Babu".

  Kai ya jinjina Baban "Tahm zan baka mata Mukhtar ,zan aura maka 'yata Ummi ina so ka amince ka mun wannan alfarmar ".

Da ac a d'akin amma ya ji wani zufa na keto masa ,yanayi ya tsinci kansa da ba zai ce ga irin sa ba ,shi dai yasan har ga Allah baya sahun masu kudi ,talaka ne shi komai nashi a lissafe yake , yanzun ba ma shi da eligibility na yin aure ta ya zai aura masa yar sa da take yar gidan gata ta taso a daula? Bata saba da wahala ba da rayuwa irin ta sa ba anya anyi balance kuwa?

  "Zan samu ?"Baba ya sake tambaya don ya ji Mukhtar ya dauke wuta .

   Tsaka me wuya ya shiga sai dai bazai iya denying ma Baba ba domin ya na musu halacci yana ma kanyi ,baisan dai mai yake nufi dashi ba amma haka ya jin jina kai "Ba abinda zaka tambaya a gurina na gagara maka ". Muhktar ya fad'a cikin dauriya.

  "Alhamdulillah".

  "Bana son ka ji wani damuwa ,duk wani abu hidimu tn aure idan ka cire sadaki duka ala'ada ce da bidia sabida haka banson komai daga gurinka sadaki kawai ya isa ,akwai bikin Abdulbasit da ya rage sati biyu idan Allah ya yarda nake so a hada tare da naku,kana da gidan zama?"Ya tambaya

   Kai ya girgiza masa Baban ya ce "Ba wani abu ,ina da gida da zan iya baku ku zauna,bana so ka dasawa zuciyarka tunanin irin wacce yarinyar ka aura ,nan da ka ganni ba da arziki nayi aure ba zai da aka Yi gwagwarmaya Allah ya hore sabida haka kar ka ji komai zaman aure fahimtar juna  ce ,da hakuri da juriya.Yabawa da halinka ya sanya  ni neman wannan alfarmar Mukhtar".

   Addua ya yi masa da godiya Baban kafin ya tashi ya tafi,kamar bai da jini a jiki ya hau keke hular kan ma gagararsa tayi ya rufe face dinsa Yana jingina a kujera.Sam bai son issue irin wannan ,ba wai bai gode  bane yasan wannan gata ne  wanda har yayi yawa a baka aiki a baka mata sannan a baka gida?   Babbar matsalarsa yarinya ba bata son shi tana son shi Allahu aalamu? Duk wani abu da zai ja masa rainin baya son shi bacin duk da fadawa Baba da yayi bai da gida amm ya ce zai bashi ??? Baya son abinda zai zo ya biyo baya.

   Ya shiga gida ya ji ya kasa samin nutsuwa , Shafiu  ya kirawo gidan ya labarta masa kamar mafarki ya gani
"Abinda nake ji a gari yana faruwa daman har yanzu? Abokina Allah ne ya baka wlh ".Shafiu ya fad'a.

  Kai ya dago Muhktar"Shafiu hankali na ya kasa kwanciya fa ba wai abin wasa bane fa".

  "Alkairi ne in sha Allah ka da kayi mamaki akwai wani abu da yake tunkararka ne , nutsuwa zakai abokina kayi tunani  sannan kayi addua"

Kai kawai ya gid'a Shafiun yace "Mai ne plan naka toh yanzu?"

"Plan what ,2 weeks fa ni mai na tsara?"

"Tohm ba yace zai baku gida ba ,mai ya rage lefe nw shi ma an yafe naka kai kai wamnan a sadaka aka ma aure"

Harararsa yayi "Be serious mana"?

  "Okay ,zakai event ne?"

   Kai ya girgiza "Event ana zaune kalau?"

  "Abokina  bansanka da tsoro ba fa kai da kake da dakiya akan aure duk ka razana ko tsoron auren kake ?"Ya fad'a da zolaya.

 
    Shiru yayi sai da ya bashi baki sosai ya samu relief tare suka sauka kasa wajen Umma ,suka fad'a mata ta hau jinnina Lamarin  ,a fili tace Allah ya tabbatar ya sa albarka  a ranta kuwa bata ji dad'i ba don akwai yar kanwarta da take masa sha'awa amma ya zatayi harkar manya ake yanzu dole ta ja baya da wancen batun yanzu su ci arzikin tare.

 

     Ummi a gida bata san wainar da A
Ake toyawa ba ,wuni tayi ta kasa fitowa sai da daddare ta zo ta dauko abinci ta ci ta koma miss calls din Faruk ta tarar sai sanna ya kirata ta shiga bayi ta amsa ,kuka ta fashe tana fad'a masa ya janyo mata  Babanta yayi fushi ta bashi labari har asibiti suka je hakuri yayi ta bata ya mata alkawairn idan dad dinsa ya zo nan da next month zai masa maganarta iyayensu su shiga tsakani nan da Nan taji nutsuwa ta zo mata ta kuma amince da hakan sukai sallama tayi kwanciyarta.

   Washegarin da safe wayar ya Abdulbasit ce ta tasheta ta ,da fad'a ya hauta ko da ta daga.

"Kinsan me kika jawa kanki? Baba aure zai miki kuma wlh ba ruwana kowa ya aura miki kar ki kuka "

   Tsaye ta mike "Aure ,wlh ba wanda zan aura idan ba Faruk ba yaya meyasa baza a tambayen wa nake so na? Sai kace rasa miji nayi?"

  Gigicewa tayi "Zaki ga meyasa baza,a tambayeki ba sanda kika fita uban wa kika tambaya?"

   Wayar ta katse ,tayi saurin kiransa ba bata lokaci. " Ba kya jin magana Ummi duk abi na jan magana kin iya shi "

  Hawaye taji ya zubo mata nasiha yayi ta mata yace zai kira Baban ya basa hakuri anjima ,ta tashi ta shiga bayi alwala tayi ta zo tayi sallah bayan ta idar taji knocking  a kofa ko da ta karasa kofa Baba ta gani da sauri tayi baya. Tana tsugunawa ta gaishe shi duk a tsorace take dashi.

   Yana tsaye yana binta da harara  jiyake kamar ya rufeta da duka idan ya tuna a yanayin da ya ganta yar karama da ta ita amma tasan duk irin wannan?

"Khadija duk iya kulawar da zan miki na miki ita ,kunen kashi da taurin Kai  ya Sanya har kike bin namiji ,tunda har hakane aure kike so ,ba za a Yi bikin Abdulbasit ba tare da an hada da naki ba".

  Dagowa ta yi da kuka ta kamo  kafagunsa tana magiya "Baba Dan girman Allah idan kana kaunar kaka da mahaifinka ka yi hakuri bazan kara ba kar ka min auren dole "

  "Kina da wanda kike so ne?"Ya tambaya.

Kai ta jinjina "Faruk baba wanda ka ganmu dashi Allah zai fadawa iyayensa".

Kai Baba ya girgiza yana janye kafarsa "Ko maza sun kare bazan aura miki dan iska ba Khadija ,wannan ba mijin aure bane wanda yake yunkurin yin Zina da yar wani wallahi bazaki taba auransa ba ko kukan jini zaki na riga da na gama magana aurenki ba dagawa nan da sati biyu karatune har PhD idan mijinki  ya bari kiyi zaki yi amma dai aure dole nayi miki kafin ki ja min abin kunya".

 
    Kuka ta hau yi tana ihu kamar ranta zai fita sai ga Anty Nafisa da gudu ta je ta rikota tana magiya ta roka mata Baba tayi shiru ,ba karamin tausayi ta bata ba don duk tayi laushi ko kallo ma kyau Baba ya ki Yi balle ta ga fuskar rokarsa.

  Ya Abdulbasit ta hau kira switch off don bata san irin fad'an da Baba ya masa ba a waya  sanda ya kira ya rokesa,shi yasa ma ya kashe don kar ta kirasa sun san halin Baban nasu idan yayi fushi baya jin Ammy kadai ce iya ta dawo  dashi shi gashi bata nan.Tana ji tana gani ya fice daga gidan ta koma daki tana ruzgar kuka ,don ya mata kashedi   ta sake ta fad'awa wani ma kamar tana tona asirin kanta ne kowa zai san mai ta yi kuma hakan ba zai saka ya fasa ba....

★★★

  Kwance Yusrah ta tarar da ita sanda ta shiga d'akin nata,wayarta na gefenta ta dauka ko bacci ta ke Koda ta zagaya ta ga idanunta biyu ba don ta kifta ba da ca zatayi a mace ta ke.Zama tayi kusa da ita ta riko siririn hannunta don ta rame sosai.

  "Ummi".Yusrah ta kira.

   Ba ta ce komai ba ta cigaba da magana "Ki yi wa kanki gata Ummi ki tashi ki Yi rayuwa ki amsheta a yadda ta zo kin kuwa ga yadda kika koma kamar wata zombie? illata kanki fa kike Yi duba ki ga cikinki a wani shafile haba Ummi,ko ma mene Bai ci a ce kina haka ba nasan is not easy Amma Yakamata ki rage wannan abun yayi yawa ko rasuwar Ammy ba ki haka ba".

  Gani tayi ta rufe fuska ta fashe da kuka wanda ya sa Yusrah yin shiru ta soma ba ta hakuri da ta san anbaton Ammy zai ja haka da ba tayi ba.Da kyar ta samu Ummin ta tsagaita ta sa ta tashi zaune tana share hawaye.

  "Yusrah mutuwata a yanzu ta fi min zaman cikin duniya wannan rayuwa Ina ji a jikina bazan iya ba ,ko iya rayuwar gidannan a yanzu is hell balle har na je gidan wani namiji da ba dangin iya ban san irin shi ba ma balle kalarsa no matter how handsome Yusrah bazan iya rayuwa da kowa ba banda Faruk,kaunarsa ta ratsa zuciyata bazan zama da wani ba ko kad'an".

  Kai Yusrah ta jinjina aiki ja "Ummi ,bikinki fa kwana uku ya rage?"

  "Ko yau aka daura aurena raayina ba zai sauya ba Yusrah ,bana son aurennan bana son wanda zan aura na tsanase fi ya da mutuwa ina tausayawa rayuwarsa da ya bi son zuciya sai ya aureni kowa yashe shi na rantse miki ya shigo babban babin ba'kincikin rayuwa in dai har ya za'bi zama da ni a matsayin mata shi da farinciki har abada".

Furucinta bai wa Yusrah dad'i ba ita kam da Baba ya hakura ya bar batun aurannan da da yadda zatayi ta rikeshi da ta yi don tana gudun abinda zai biyo baya zallar kiyayya take gani a fuskar kawar tata Kuma ba yanzu ta santa da hali irin haka ba muddin ta dora maka karan tsana za ta iya yin komai na ganin ta 'bata maka ko da kuwa ita ma zata cutu.

    Turo kofar akayi ta ga amaryar Baba ce ,babban bagco ta gani mai aikinta Habiba ta shigo mata dashi kamshi ya karade d'akin , turaren humra ne da ma na wuta kala kala cikin robobi masu yawa tana ta fito dasu.

    "Yusrah ki ta ya ta za'ba ga sunan samples ne wanda ta za'ba shi za a kawo mata"Anty Nafisa ta fad'a kafin ta fita ga dukkan alamu itace zata siya mata turaren , Yusrah kam ta dubeta.

  "Allah sarki baiwar Allah,Ummi dan Allah ki za'ba ko ya ne ,matarnan tana da kirki kime kin sa a ki godewa Allah tana tsaya miki dukda ma kina mata abubuwa ki zabi ko guda uku ne".

   In ba don tana son turaren ba da kamshi ba abinda zai sa ta yarda ta dauka da kuma maganar Yusrah.

"Ki zabar min".Cewar Ummi.

  Yusrah tana budewa tana jin kamshin ta ce "Amma dai kina shan abinda Anty Sa'a ta aiko muki?"

  Baki ta ta'be "Da can din ni 'kazama ce ko kuwa ca kai bana kula da jikina?"

"Aa wai wannan ai na musamman ne Hajiya Ummi na wanda yace ba kya tsafta wannan shima wani gyaran ne".

    "Toh kuwa ba zan yi ba indai don wani gardi ne".

Kai ta girgiza Yusrah tayi concentrate akan abinda take yi kafin ta sa Ummi ta zagi dan mutane.Masu kamshi ta za'ba mata ta fad'awa Anty Nafyn sabida haka ta aika aka kawo irinsu dayawa ta kashe mata kudi kan turarukan amma Ummi ko godiya.Gani take a yanzu kowa makiyinta ne tunda dai sun kasa sawa Baba ya janye , Abdulbasit tun jiya yana gari amma kamar ba exist dinsa kowa ta dauke masa wuta daga ita sai halinta sai Yusrah Amma Shaheeda kam tayi zuciya da lamarin  Ummi ta ajje gefe don kanta idan ta koma mata sai suyi kawancen don baran baran sukai sabida ta ce tayi hakuri da abinda Baba ya za'ba mata ta ma gode Allah ba a cikin abokansa masu aure aka bata ba.

  Wajajen asr Yusrah ta tashi tafiya gida ,a waje ta tarar da Ya Abdulbasit nan ya hada mata card admit din dinner yace ta raba ma friends dinsu da zasu gayyata don ya San Ummi ba lallai bane don ba wanda take fadawa za ai bikinta.Hatta dinkunan kayanta da Baban ya basa kudi ya saya mata shi ya kai mata wajen tailor dinta aka dinka ya kawo mata ko kula kayan ba tayi ba ko kayan d'aki ma sai Anty Nafy ce ta zabar mata Akai furnishing gidan ba abinda take participating na auren.Abdulbasit yake ta nasan shirin shi da amaryarsa ,Umar da Hafiz sun dawo gida ana e gobe biki Umar ya kammala karatunsa , Hafiz kuwa sun kammala exam zasu shiga level 2 bikinnan da za ai yasa shi zuwa.

    
    *Ranar Aure*

    Zaune yake cikin motar da zasu tafi daurin auren shi da abokinsa Abdool wanda yake wajen aiki d'aya dashi yanzun ,gidan baya sauran abokan arziki ne sai uku , Mukhtar ya sha ado ya fito a angonsa babbar rigar ta yi fitting dinshi farar shadda ce zanen aikin aka  yi color coffee brown ,da hula ta yi matching da aikin.Yanayin da yake jinsa Bai san ko haka sauran suke ji ba shi dai ba ya tunanin farinciki yake Yi dari bisa dari kallon abokan nasa kawai yake amma hankalinsa ba ya tare da duk abinda suke cewa.Wayarsa ce tayi ringing ya ga Shafiu ne ya amsa nan yake tambayar sa ko ya karasa wajen daurin auren yace masa suna hanya , Shafiun ya tabbatar masa da komai ma reception ya yi ready yanzun wajen daurin auren zai tafi idan suka kammala sai su koma reception godiya yayi masa kafin su katse kiran.
    
   Abokan arziki da yan uwa sun hallara taro yayi jamaa bugu da 'kari daurin auren duka biyu ne zasi yi shi ,an d'aura auren Abdulbasit da Amaryarsa Hafsat sai Muhktar da amaryarsa Khadija (Ummi) akan sadaki dubu 100k aka shafa fatiha aka Yi hotuna aka wuce reception ta bangaren Muhktar shi ma Abdulbasit suka wuce nasu.

 

    ***

    Nan gidan su Mukhtar su ma yan uwa duk sun hallara ,sunyi shigar kayansu masu kyau suna haka ango ya shigo suka yiyyi hotuna ,Bai Yi yunkurin ma zuwa gidan su Ummi ba kamar yasan ba hadin kai zata bayar ba Ummi da take gida a yanzu  fuskarnan ba walwala musamman da ta ji an daura.Lace ta sanya lemon green ,ba makeup ko na kwabo a fuskarta ,banda kakarta ta Yi fad'a da bazata fito sarari ba sai da tayi kamar zata doketa sannan ta fito don Goggo tana goyon bayan aurennan dukda sunan ta ta ci ba ta son halayen Ummin ba ta shagwaba kuma jika irin yadda wasu suke yi.

     
    Har ranta ba San gaisuwarnan take ba kowa yazo sai a ce ta je su gaisa kamar ta tsuduma ihu , dad'i ta ji ganin har 2:30 ba ta ji an ce ga ango da abokansa ba sabida haka ta koma daki,sai a sannan ta sake shawara baza ta je dinner ba kamar yadda suka lallaba ta aminta a baya yanzun ta fasa,yin duniya da roko Anty Nafisa ta zo itanma Bata ji maganar tata ba Yusrah ta shiga halin innalillahi duk uban kashe kudin da sukai na sittira ,ga itama natan dinkin wannan wace iriyar yarinya ce?

       Shaheeda da ranta ya baci tace ita dai sai ta je ,mai kwalliya ta zo ta musu lokacin ta ma shige bayi ta kullo don sun isheta da magiya,jiki a sanyaye Yusrah da ta shirya ba karamin kyau sukai ba kamar ta rufe Ummi da duka haka ta fita da ba'kin cikin abinda ta musu,su kadai suka je dinner su Ya Abdulbasit ya kirata ya fi sau a kirga Umar da Hafiz sunyi sun gaji da zaginta ta ma ki fitowa daga toilet din suka tafi a kufule.

   Wayarta tayi ta buga game duk dan ta kore haushin da ke damunta a zatonta zata dan ji sanyi sai dai ba wani sauki ,jin gidan shiru ya sa ta fitowa d'akin ta zauna gado.Sai to 12 sannan suka gama dinner ,basu biyo ta gidan ba kowacce ta wuce gida , washegari aka kai amarya da yamma ,matar Abdulbasit kuwa aka wuce da ita Abuja da wuri suka tafi.Komin fushin da Yusrah zatayi bata iya rufe ido ta ma Ummi yadda ta so ,sabida haka ta je dai ta banda Shaheeda da ta yi fushi da ita dukda tana jin kewar kawar tata,sai wajen 9pm ango ya shigo abokansa uku suka rako shi ,addua suka gabatar ba wani hira aka tattauna ba yo ina ma kawayen? Yusrah ce kawai, Nasiru shi ya tafi da Yusrah gida yana jiranta a wajen tun dazu,kafin tafiyarta dai sai da ta roketa da ta taimaka ta nutsu kar tayi hali iri nata Kai kawai Ummi ta gid'a alamar assurance bazata yi ba sukai sallama ko gezau Ummi Yusrah ce ma take ji kamar kwalla ta zubo mata,bayan tafiyar su ya rage ango da amaryarsa......




Dijensy
 
  

Continue Reading

You'll Also Like

126K 7.1K 44
When she wants to go to her dad's house as she was missing them!! Her husband who was searching online how to "stop your wife from going away from yo...
259K 4.3K 62
This is an unofficial fan-made English translation of We are...āļ„āļ·āļ­āđ€āļĢāļēāļĢāļąāļāļāļąāļ™ (We are... we are in love). Please do not re-translate to any other langu...
728K 16.2K 67
Two girls are exchanged at birth and are given to the wrong mothers and after 13 years the truth comes out Rosabella Rossi is different from her sist...
500K 36.7K 38
Avantika Aadish Rajawat Aadi, with his fiery nature, adds intensity and excitement to their relationship, igniting a spark in Avni. Avni, like the ca...