YADDA NA KE SO

By Dijen-sy

968 110 44

YADDA NA KE SO burin Ummi ta auri mijin novel ,Mai arziki ba ta son talauci ya rayuwa zata juyawa mata a sand... More

Shafi 1
Page 2
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20
Page 21
Page 22
Page 23
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29

Page 3

27 6 5
By Dijen-sy

  YADDA NA KE SO🌺




By Dijen-sy

https://chat.whatsapp.com/LWLjxERDFd1JbCeDRQ7XKO

Page 3

       Duk wani mai tausayi idan ya dubi halin da suka shiga sai ya tausaya musu kwana bakwai amma kamar yau Ammy ta rasu ,kowa na zaune parlor sunyi jungi jungi harda mahaifiyar Ammyn ,Anty Sa'a ce ta shigo ta zauna 'kasa gefen babar tasu ta dubeta "An tasheta ta ci abincin,?"

Kai Anty Sa'a ta girgiza "Umma yarinyarnan taki yin komai,idan anyi magana kuka take da haka numfashinta sai ya dauketa a kyaleta daga yanzu zuwa wani lokaci zata tashi ta ci da kanta.

   Allah sarki suka shiga yi a parlor ,gunjun kuka suka jiyo ,ashe Umar ne dawowarsa kenan daga makaranta sai yau ya samu dawowa.

Rikeshi suke yi daga waje amma ina ya rasa control ya shigo cikin parlor kamar ransa zai fita .

  "Kayi hakuri ba kuka zakai mata ba "Duka yan d'akin suka hau bada baki ,bayansa Abdul ne ya rikeshi yana basa baki ya tsuguna kusa da kakarsu kuka ta fashe dashi ta kasa jurewa kuma kukan da ta ga Umar din na yi.Duk cikin yaran ba wanda yayi kukan haka a maza.Ya jima a haka kafin ya ce "Ina Ummi?"

  Ita kawai ta fad'o masa wani tausayin junansu ya kama sa ya nufi d'akin ta ,kwance ya tarar da ita ta juya baya ko fuskarta ta rufe da hijab kawayenta ne sai cousins suna zaune sunyi shiru sai jan carbi ."Ummi"Ya kira sunanta yana Jan hannunta  ya d'ago ta  ta tashi zaune duk radadin da yake ji bai hanasa ya fahimci halin da take ciki ba ya tabbatar ya ninka nasa.

  D'ago da ita yayi tayi wani  shafal kamar karmami idanunta uwa skeleton dakyar take motsawa "Ummi kiyi magana,bazaki ce min komai ba".

 
  Fashewa tayi da kuka tana girgiza "Ku gaina fad'a min Ammy ta rasu  dan Allah ya isheni bana son ji."

  Jikinsa ta Fado ta hau kuka Yana Yi tana Yi ,Wanda ba Wanda bai zubda kwalla ba a d'akin Abdulbasit ya kasa jurewa ya fice don idan ma ya je taurin kan Umar ba tashi zai ya fita ba .

  Wannan mutuwa ba kadan ta dokesu ba sai da aka hada mata da addua aka samu sauki kamar zautacciya taki cin komai ,da sannu ta soma karbar tea tamkar raino haka Anty Sa'a ta ke sata a gaba har ta soma gajiya , Hafiz su suke sa ta a gaba sai ta ci tana musu kuka haka zasu tursasa mata sannan ta soma cin ,Baba ya musu nasiha sosai ya tarasu a parlour bayan sun mata addua ya jaddada musu ba a ja da hukuncin Allah tunda suke musulamai dole suyi hakuri da abinda ya samesu su rike kaddara ,kakarsu ma tayi musu sosai alhamdulillah sun samu relief.Satinsu biyu Baba ya sa su koma school  shima Abdulbasit ya koma aiki ba dan sun so ba haka suka koma ,Ummi kuwa ya yanke shawara ta bi Anty Sa a tunda itama tana da yara zasu so babarsu ta dawo tunda ta jima anan d'in ,duk abinda aka ce Ummi shi take yi ba musu ba uhm ba aa ba wani respond,sai da aka kwana biyu a hankali tawakkali na shigarta ta soma samun kanta ,waec ta matso kusa tun rasuwa bata sake zuwa ba sai ranar exam.

    Baba ya sake jaddada mata tayi concentrate akan karatunta ,kawai jinsa take haka ta soma exam duk wanda ya santa a da sai yaji tausayinta.Kawayenta ke dan tallafa mata basa rabuwa da ita koyaushe suna son debe mata kewa.

    A kwana a tashi exam tayi nisa har sun kammala ba wani celebrate komai a sanyi lami ta dawo gida ta shige d'aki tana dakko hoton Ammy ta kura mata ido "Ammy yau Mommynki ta gama secondary zata haura wani matakin sai dai kin mata nisa Ina rokon Allah yasa kina aljannah nayi kewarki Ammy Ina son kasancewar dake".

Muryarta ya karye sai hawaye ranar tayi kuka sosai Anty Sa'a ta mata fad'a sosai tace duk sanda ta sake gani ta shige d'aki kuka sai ta kwace hotunan.Ta sa ta fitowa cikin yaran gida suyi hira , parlor take fitowa ta yi shiru idan Khalil ya kira suyi waya itama ba mai tsaho ba ta kashe gabadaya komai baya mata dad'i .

   Lokaci lokaci takan yi waya da Yan uwanta ya Umar kusan kullum ne.Yau ma kamar kullum tana zaune parlorn Anty Sa'a    ,gida ba wani dadi yake mata ba tayi missing gidansu ,ac and komai her room uwa uba Ammy idan ta tuna sai taji Kuma gidan ba zai mata dad'i ba.

      Sallama taji ta daga Kai ta ga Yusrah da Shaheeda wani sanyi taji ta Yi saurin mikewa tana musu sannu da zuwa ,d'aki ta shigar dasu suka gaisa take musu complain basa zuwa.

  "Ina Lubabatu Yusrah ta koma gidan nasu?"Ummi ta tambaya bayan sun gaisa .

Kai ta girgiza "Tana gaisheki ai mommy na Jin dadi aiki da ita tace zata zauna mata".

Murmushi tayi tace "Allah sarki luba nayi missing dinta in sha Allah zan zo kwanan nan".

  "Sai kin zo ".Cewar Yusrah.

Suka cigaba da hira ta ji dadin zuwansu sosai sun dade kafin suyi sallama da ita suka tafi.

  *****

    Daga toilet ya jiyo ringing waya ya fito ya san abokinsa Shafiu ne yazo daukansa don sunyi zasu fita .Sauri yayi ya shirya ya fito ,kafin nan ya sallemi Umma.

   "Sorry mutumina"Ya fad'a Yana hawa baburin suka hau titi Shafiu yace "Sai na tsaya mun Sha mai".

  Nan ya shiga gidan Mai suka parker, Muhktar ya sauka.

   Dai dai sannan Baba suka shigo da motarsu  nasirun ya fita bayan Baba ya bashi kudin ya fita ,kallon window yayi idanunsa suka sauka kan Muhktar.Wani mamaki ne ya kamasa ganin me kama da wani tsohon abokinsa da ya dade da  sani rayuwa kowa yayi nisa bai sake ganinsa ba tun rabuwar karshe.

  Sosai yake kare masa kallo ,halacci da ya masa ya sa Baba ya kasa hakura.Sauke glashin motar yayi don sake tabbatar wa, Nasiru ya kira ya ce ya je ya masa magana da wancen lokacin an gama zuba musu Mai har zai hau Nasiru ya tabo shi ya waiwayo.Nan ya fad'a masa alhajina na kiransa,dan cakewa yayi ya dubi Shafiu ya masa alama da yaje ya bi bayan Nasiru a dan rissine ya gaishe shi Baban ya yi murmushi 'Ikon Allah".

"Dan Allah dai dan gidan Sunusi danyaro ne?"

  Kai ya jinjina murmushi Baba ya fadada "Ma Sha Allah ga kama ,Ikon Allah kai dansa ne kenan"

"Eh dansa ne ni".

  "Idan ba damuwa zaka iya kwatanta min gidan naku don kuwa ina son ganinsan".

  Shiru ya danyi kafin yace "Ai ya jima da rasuwa".

Baba ya rintse ido "Allah yajikansa da rahama Allah ya yi baza mu hadu ba kenan,tohm kuna ina yanzun?"

  Fad'a masa yayi Muhktar Baba yace "Ka ga na cikaka da tambaya ko ,aminina ne ,mahaifinka mutumin kirki ne ya min halacci a rayuwa da bazan iya mantawa ba ,idan ba damuwa ka kaini gidan naku".

  Kai ya jinjina Muhktar ya sami abokin nasa "Abokina ka ga wata sabuwar".

Labarta masa yayi a takaice ya ce toh shi zai barsa kawai don yana da mahinmanci fitar ta sa  da zai Yi ,sabida haka Muhktar ya shiga motar a ransa muma yana jin  d'ari-d'ari amma dai ya wanke zuciyarsa da fatan ba cutuwa a ciki yadda zamani ya lalace.

  Har kofar gida ya kaisa a hanya ne yake fad' masa alkairan  mahaifin nasa  ya masa.

  "Tare muka taso da babanka munyi secondary tare ,a sannan mahaifiyata bata da lafiya babanka akwai neman kudi Allah sarki ,har tsokanarsa muke sanda babata ta kwanta a ciwo  kudin da yake tarawa a asusu kaf ya bani na nema mata lafiya a sannan duka iyayenmu basu da karfin shi kansa yana da bukatar kudi amma haka ya sadaukar min da wannan damar Allah da ikonsa ta samu sauki mahaifiyata kafin daga baya lokaci yayi, bayan wani lokaci  suka tashi daga kusa da inda muke ,a sannan nikuma mahaifina ya daukeni munje kauye, munyi gonna dawowata ban sami Sunusi ba sai aka ce sun tashi a sannan ba wani abin communication na rasa yadda zan na samesa sai daga baya ashe shikuma ya tafi Maiduguri neman kudi nikuma na sami scholarship kasar uk tunda a sannan dukanmu min kammala sakandare kaji yadda muka rabu dashi".

 
  Murmushi yayi Muhktar "Allah sarki shekararsa kusan 3 da rasuwa yanzu".

"Allah akbar,Allah rahama masa".

  "Yanzu sai mahaifiyarku?"

  "Allah ya mata rasuwa kusan shekara 18 da wucewa ta rigashi".

"Allah sarki".

  "Sai matar Baban tamu da kannena". Mukhtar ya fad'a.

  Kai ya girgiza cike da jimami ,bayan sun iso ya fito  ya masa iso bayan ya sanar da Umman suka gaisa ya ga yaran ba karamin sha'awa suka bashi ba ,mutuwar Ammy ya sa ya ji dama suna da yaran da suka fi haka.

   Zuwan Baba alkairi ya zame musu ,Bai tafi ya barsu haka ba sai da ya musu kyakykyawar kyauta ,bayan sun fito waje da kyar ya amsa Mukhtar ya tambayesa wani matakin yake na karatu ya fad'a masa ,da Kuma sana ar da yake ya jinjina Kai number sa ya amsa yace zai taba sa sukai sallama Yana godiya.bayan ya tafi baba Muhktar ya furzar da iskar farinciki "Allah Mai bayarwa ,ka amsamini addua ta".

100k Baba ya bashi ,take ya lissafe mai zai yi dasu ,zai siya musu abinci ya biya kudin aikin d'an Rasheeda sannan kuma ragowar sai cika ya sake generator Cafe dinsu don Shafiu ne ya siya musu da dadewa.kuma Shafiu na bada gudmawa sosai kasancewar dawainiyar da yake bata Kai ta Muhktar a gidansu ba don yana da yayi maza ba shi ke kuka da gidansu ba.

  Ranar farinciki ya cika Muhktar ranar Abbansu ya sha addua kam ta silarsa sun samu abu dukda baya raye.

   ★★★

Baba kai tsaye gidan Anty Sa'a yayi ,bayan sun gaisa Ummi ta fito ta gaida Baban nata.

"Khady ba dai wata matsala ko? Kina cin abinci ko?"

Kai ta gida yace haka ake so "An gama jarabawa kuma ,bazaki dan wani entrepreneur ba kafin result ya fito?"

   Kai ta girgiza "A a baba ni dai ba yanzu ba".

  Kai ya jinjina tom "ki huta yanzu kafin muga gaba ,a dai dinga sallah kinji ko da addua ana sa Ammy ciki kin ji ko?"

Kai ta jinjina "Ki dauka nan gidane kinji bana son shigewa d'aki komai da kika ga suna yi ki dinga shiga cikinsu yan uwanki ne".

  Kai ta jinjina a kasan zuciyarta kuwa tana jin bazata iya ba ko yanzun ma ta gaji da su gabadaya yawansu ma bai mata ba cimar da komai ma.Kawai hakuri take abubuwa su lafa ita da za a maida ta gida kurum su zauna da Lubabatu.
  
 
   "Ni zan wuce idan kina bukatar wani abu ki kira ni ko yayanki kinji ko?"

Kai ta jinjina ya tashi a tsakar gidan ya lalo kudi 50k ya bawa Anty Sa'a yace sa yi cefane tana ta rafka godiya bayan kayan abinci da ya dire musu ,ita kam zuwan Ummi gidan ya zame mata alkairi waca waca suke jinsu  duk da da dinma ya na taimaka musu amma yanzu ya karu sosai.

    D'aki tayi shigewarta ta hau danna waya ta ji haushi  bai ba kudi ba shikuwa baya son bata ta da kudi tana karamarta.Ya Abdul zata kira tace ya sa mata kudi a account nata.Tasan yanzu duk abinda take so shi suke mata.

 
  Chat ta ga ya shigo wayarta a IG ance hello ,ta bude profile din ta ga picture wani farin guy ya jingina jikin mota da black kaya ta duba ta ce hi.

  "Y kke?"

  "Lafy and u?"

  "Fine girl ,baki gane ni ba ko?"

  "Yep".Ta amsa.

"Okay ,I have been following your post na ga kin burgeni sosai just want us to be friends".

  Tabe baki tayi ta sake komawa ,hotunansa ta gani na post  ,agogon hannunsa ta gani ta duba takalmi ta ga dai masu tsada ne sai ta duba motar ma "What if ba tashi ba?"

     "I need more clarification".

"By the time muka fara sanin juna , you will know me well"

  "You can check my profile details".

  Dubawa ta sake Yi nan ta ga sunansa ,ko da ta cigaba da bibiya ta fahimci  dan babban gida ne ,komawa tayi suka cigaba  da chat Bata Ankara ba time Yana ta shigewa , ya burgeta sosai ganin ya tambayeta kan Ammynta a profile da yaga ta sa RIJF  yayi mata gaisuwa  ,da video call ma ya kira ta 'ki amsawa ganin background din d'akin da take Bai Yi ba ba ta son ta kwafsa, sai can dare sukai sallama ta ajje wayar ta kwanta.

  Bacci tayi cikeda mafarkin saurayi fari me agogo wai gashi har sun saba da juna sun fita dating, asubah taji ana kira ya sa ta bude ido ta mike.Kusan tunda Ammy ta rasu Bata taba bacci na yau ba ,wasai  taji zuciyarta ta je tayi alwala ta zo tayi sallah ta koma gado bacci ba ita ta tashi ba sai after 10 , message dinsa ta fara cin karo har hudu na kalamai masu sanyaya ruhu tayi murmushi kafin ta hau reply ta tashi.

  Koda ta yi brush ta dawo ta zauna ,chat suka cigaba da yi  ,ji ta Yi ta  kosa Yusrah ko Shaheeda su zo ta nuna musu kodayake bata baci ba group ta shiga ta sender musu picx dinsa "Yayi?"

  Ta shagala da chat ba ita ta ankara ba sai 12 ,ta fito cikinta ya fara kuka ta fito waje ta samu Anty Sa'a a parlour da Yara sun jima da breakfast ta gaisheta a sukwane "Ummi sai yanzu ? Haka kike wai da bacci tun dazu Yara suke lekawa sai suga bacci kikai ga abincinki can a kitchen".Ta fad'a Ummi ta wuce ,ta duba plate ta ga wainar flour ce ,sai faten wake gefe da kunun gyada.

'Kut' ta furta a ranta ,ya ma Yi sanyi Kai ta girgiza.

'Inaaaa bazai yiwu ba wlh dole na koma gidanmu mene wanann kamar hancin kare ? Ga miya ce ko wake uwa wani gudawar yara?"

Tsaki tayi ta fito da iya kunun Anty Sa'a tace "Baki ga wainar bane?"

Kai ta girgiza na koshi ya isa wanann".

Ta wuce d'aki ta bita da ido'Lallae yarinyar dole na gyara miki zama Ina miki magana kina juyan keya kina cikin gidannan sai dai ki bacci ko tashi ki ci  ? Rabia ta sangarta ki"' Anty Sa'a ta fad'a a rai.

 
  *****

    Muhktar bayan tafiyar Baba ankai sati biyu kafin ya ga kirasna sukai waya bayan sun gaisa yace masa aikine ya Sha kansa ya tambayesa gidan kowa lafy Sannan yace ya turo masa da CV nashi ,wani dadi ya kama Mukhtar ba Jira ya tura masa cv ya ce zai tabo shi.

  Farinciki ya cikasa daman bai jima da idar da sallah ba ya daga hannu ya soma addua Allah ya datar dashi ya samu aiki Mmai tsoka.Baba yana gama waya dashi ya kira wani a waya ya mashi magana yana da d'a da yake son a bashi offer aiki ,abinka da harkar manya da hanya ba jira ba bata lokaci ,ko sati biyu ba ai ba ,Baba ya kirasa yace zai hadasa da wani zai je interview wacce kawai za ayita ne don confirm aiki ya gama samuwa sai dai lafiyar yi.

   Duba da iyalin gidan yasa bai samar masa a Abujan ba yace a barshi a Kano ,sabida haka aka bashi aiki babban maaikata.Shafiu ya fara wa albishir sannan Ummansu tayi murna sosai taji dad'i don shine bangon jinginarta bata da yadda zatayi bata da mai karfi a yan uwanta dole ta ja shi a jiki idan ba haka ba tayi asara shiyasa take yin kokarinta ta nuna musu so idan ta duba itace me kananin Yara tayi sake to kuwa cutuwa zatai.

    Da dan kudin da yake dashi yayi sadaka mai kauri ,kuma ya godewa  ubangiji ya tabbatar yinsa ne ya sa ya kawo abokin babansa cikin rayuwarsa.

   Dole ya karkade kayansa da takalmi ya karo kayan sawa ya soma zuwa aiki ,sai ya jiyewa abokinsa Shafiu sha'awa amma dai komai nada lokaci shima Allah bashi rabonsa.

  
★★★

Bangaren Ummi kuwa tuni sunyi nisa da mutumin ta Faruk ,har soyayya ta fara shiga tsakani kullum tana makale da waya ba fashi,gashi turo mata kudi yake kamar abin banza yanzu ita fita ce matsalarta Yana ta tambayarta fita sai ta masa karya yace yazo taki kar ya raina gidan da take da dai gidansu ne.Ko hoto idan yace tayi masa ko video call sai ta tabbatar ta samu background da bazai sa ta kwafsa ba sannan take yi.

    Yau dai ta dau alwashin sai ta fita sun hadu ,karya tayi wa Anty Sa'a tace zata je gidan su Yusrah Bata son hanata tun yanzu ta fara Gani ko ta takura tunda dai Bata taba fita ba yasa tace to.

  Bata tambayeta transport ba don tana da kudi ,ba don kar Nasiru yayi mata munafunci ba da shi zata sa ya kaita.

  Unguwarsu ta je Kai tsaye ,ta kira Faruk tace masa tana gida ta shirya yazo.

  Ba Jira Yana rawar Kai ya zo ganin babe ,haka ya shigo unguwar ya sameta a kofar gidan Nasu tana addua kar wani ya gansu tasan baba dai baya gari.

  Wining glass yayi ta ga shine cikeda murmushi ta karasa ta bude gidan gaba ta shiga ya ja mota suka tafi.

   Eatery suka wuce suna ta hira kasancewar farkon haduwa ne tana ta dan Jin nauyi sai ta ga a zahiri ma ya fi mata kyau da kwarjini.

  "Ba don Ina driving ba saki a gaba zan nayi ta kalla".

  Murmushi tayi ya sake kallonta "Those lips omo..."Ya fad'a Yana shafa lips dinsa tayi rolling eye.

"Pretty demsel kinyi kyau a fili sosai "
  "Kai ma haka".Ta amsa.

  "Really?"

  Parking yayi suka karasa ciki bayan sun zauna yasa aka musu order abinci aka cika gabansu kamar kayan banza ,ba iya ci zasi duka ba ta na son irin hakan dole ai respect dinsu Bata son kalar tsiya.Da gani Yana da hannu ta Yi murmushi a hankali take ci a gayance ya dauki drinks ya mika mata a baki a kunyace ta dubesa ya daga mata gira domin kar ta bashi haushi ko ya ga ta gaza ta bude baki ya bata tasha.

     Bayan sun kammala sun danyi picx sannan suka tashi ,ice cream ya kaita suka siya dayawa aka shigo mota ya dubeta bayan ya jingina Kai da kujera .

"Babe kamar kar ki tafi ,har na far missing naki".Ya fad'a murya a shagwabe taji wani iri saurin dauke ido tayi banda tayi control kanta ji tayi kamar fa fad'a jikinsa 'Astagfurillah ' ta furta a rai.

  "Don't worry zamu na waya".Ta fadan

"No ni ba waya ba nafison muna haduwa Ina Jin kamshin masoyiya".

  "Yanzu dai time yana tafiya muyi mu je".

  Kai ya jinjina ya soma driving hannunsa ta ga yaya kamo hannunta ta kasa kwacewa ya rike ta kam yana tuki da dayan.

  "Ni naji ma bana son komawa school ,zance na fasa Dady ya min aure".

Murmushi tayi ya dubeta "Baby ki saki jikinka nine fa sai wani makalewa kike "Ya fad'a Yana sake Jan hannunta jikinsa kamar zai Dora a kirjinsa  Sam she is not enjoying tana Jin ba dai dai bane Amma San burgewa ya hanata ta kwace hannunta.

  Ice cream din duka ya Bata yace ko zata kira mai gadi ya shigar mata tayi karya tace yayi tafiya an masa rasuwa ,bye ta masa waving ya tafi tayi saurin fitowa ta ga me keke ta tarar ta shiga sai gidan Anty Sa'a.

   Koda ta shigo karya tayi tace daddyn su Yusrah ya siyo musu ya bata ta kawo ta bawa yaran Anty Sa'a sai tsalle suke dad'i yazo.Anty Sa'a dai kallonta take don ba yarinya bace karyar bata gamsu da ita ba ,ta ya wannan uban ice cream din ace wai bata akai shi bashida yara? Ko kuwa kudin hauka ne?

  

  Hmmm wannan lamarin Ummi ko zai dore? Toh ya batun Muhktar ya samu aiki ko zai dawo da Safnar shi ???_

Dijen-sy

 

Continue Reading

You'll Also Like

Cecilia By Anastasia

General Fiction

88.9K 2.5K 37
Cecilia's father, a well-known and successful lawyer, was tired of her problems. Tired of the issues she had been causing for the family and it's nam...
634K 29.3K 68
[NEEDS HEAVY EDITING] Adaa and Isha Malhotra. The famous sisters of Bikaner. Their father, one of the most successful businessman of the city. With l...
108K 5.5K 30
If you knew what it felt like to have your entire life upended, that was exactly what Isabelle felt like right at this moment. From finding out you h...
125K 7K 44
When she wants to go to her dad's house as she was missing them!! Her husband who was searching online how to "stop your wife from going away from yo...