MAHREEN

Oleh HAERMEEBRAERH9900

1.5K 423 71

A Koda yaushe muna Jin labaran zama da kishiya Mai ban mamaki da ban al'ajabi....Labarin MAHREEN labari ne na... Lebih Banyak

MAHREEN PAGE 1
MAHREEN PAGE 2
MAHREEN PAGE 3
MAHREEN PAGE 4
MAHREEN PAGE 5
MAHREEN PAGE 6
MAHREEN PAGE 7
MAHREEN PAGE 8
MAHREEN PAGE 9
MAHREEN PAGE 10
MAHREEN PAGE 11
MAHREEN PAGE 12
MAHREEN PAGE 13
MAHREEN PAGE 14
MAHREEN PAGE 15
MAHREEN PAGE 16
MAHREEN PAGE 18
MAHREEN PAGE 19
MAHREEN PAGE 20
MAHREEN PAGE 21
MAHREEN PAGE 22
MAHREEN PAGE 23
MAHREEN PAGE 24
MAHREEN PAGE 25
MAHREEN PAGE 26
MAHREEN
MAHREEN PAGE 27
MAHREEN PAGE 28
MAHREEN PAGE 29
MAHREEN PAGE 30
MAHREEN PAGE 31
MAHREEN PAGE 32
MAHREEN PAGE 33
MAHREEN PAGE 34
MAHREEN PAGE 35

MAHREEN PAGE 17

22 11 0
Oleh HAERMEEBRAERH9900

💅 MAHREEN 💅

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

PAGE 17

Hidimar bikin Kabeer qanin Yah Maheer da Ke bi masa ce ta kankama ba kama hannun yaro,duk Wani ayyukan girke- girken biki da duk wata hidima da ya kamata ace na sa hannu a ciki ban tsaya wata qiwa ko son jiki ba da ni ake yin komai, kuma ina aiki ne domin Allah ba dan ace wance ta na ta aiki ko ganin ido ba.

Abun da ke matuqar burge Ummahn su da ni kenan, wato rashin gudun aiki ,da rashin qiwa wajen aiki,ko da zan yi in dawo Ina ciwon jiki saboda rashin sabo da aikin yawa kamar nasu ba na qin yi zan shiga a yi komai da ni a tashi.

Bayan kammala biki an Kai amarya gidan ta da ke cikin garin Bauchi Wanda yake da dan tazara da gidammu, amma hakan be hana ni Kai musu ziyara ba bayan kwana biyu da yin bikin nasu.

A hankali muka fara shaquwa da Habibah matar Kabeer wadda ta girme ni a shekaru Kuma ta fini sanin kan duniya, da wannan sanin duniyar da ta fi ni da Kuma girme min da tai a shekaru ta yi amfani wajen Jana a jiki har na sakankance da ita na d'auke ta kamar 'yar uwar da muka fito gida d'aya.

Ta b'angaren Habibah kuwa yanda na ɗauke ta Sam ba haka ta ɗauke ni ba ashe, kallo na kawai take a matsayin tsanin da zata taka ta cimma burikan ta na mallakar dangin miji da Jan dangin miji a jikin ta, duk wata tambaya da za ta min akan kowa na gidan da zuciya d'aya nake zama na bata amsa, sannan da zuciya d'aya nake hira da ita, har ya zamana ba ma boye wa juna abubuwan da suka shafe mu, watarana naje gidan ta sai muka shirya sallar da zata fara a gidan miji za mu je Liman Katagum tare da ita, cikin sa'a sai ya zamana matar Isma'il ma zata je a lokacin ta na d'auke da tsohon cikin ta na fari.

Ko da na koma gida muna hira da Yah Maheer na sanar da shi sai ya ji dad'i da farin cikin yanda muka had'a kammu ni da matar qanin shi, nasiha ya dinga min akan yanda zan ci gaba da zama da kowa lafiya, sannan ya dinga yaba min akan qoqarin da nake na zama da kowa lafiya da nuna kulawa ta da soyayya ta zuwa ga 'yan uwan shi da iyayen shi, nuna masa na yi ai ba komai, nima ai haka yake son 'yan uwa na da iyaye na kamar nashi, dan haka dole na kula da nashi, muna hira Ina gyara akwatin mu na tafiya har na gama tsaf, kallo na ya yi ya yi murmushi sannan ya ce,

"Baby na ke da ki ke ta had'a kaya tin yauuu Se fa jibi ne tafiyar,ko tsabar kin matsu mu je gida inda zaki shiga dangi ki manta da ni?"

"Habaa ba haka bane, kasan akwai kayan Suwaidatu da zan had'a, shi yasa na fara da nawa, bana son yin abu a qurarren lokaci ka sani"

Langwab'e Kai ya yi kamar wani abun tausayi sannan ya ce,

"Allah sarki ni bawan Allah, yanzu in mun je gidan ma ganin ki wahala zai min, gashi na ce ki min tausa tin d'azu kin qi"

A gaskiyar magana tausa na daga abinda bana so a rayuwa, na farko ni ban San dad'in ta ba in ni ake wa, sannan in ni zan yi wa wani sai in ji ana soken hannaye qashi na Sukata, duk sanda na fad'i haka sai Yah Maheer ya ce Ina fad'a masa magana dan na ga ba shi da qiba, Kar na damu zai yi qiba ne sai ya wuce gori a waje na watarana.

Cikin nuna ni fa bana son yin wata tausa na qarasa gare shi na hau yi masa tausa, abokin shi ne ya kira shi a waya suka hau gaisawa, qarshe suka b'ige da hira,cikin sauri na yi amfani da wannan damar na je parlour na sa Suwaidatu d'ebo kayan ta da na goge mata na fara had'a mata tata jakar, takalman Yah Maheer na kwasa na sa a jaka na tsaya Ina kallon kayan namu Ina nishin gajiya, ta baya na na ji an tab'a wuyana, daga Jin haka ba sai na juya ba na San wanene, dan haka kawai sai na tsaya Ina sauraran me yake cewa haushi na shiga ta.

"Baby na dan Allah ki yi hakuri ki cire min kaya na ba da ni za ku tafi ba akwai wani aiki da ya taso daga baya zan biyo ku, I am so sorry darling Kar ki fushi dan na San ba Kya fushi," ya qarasa maganar shi cike da tsokana.

Cikin fushin kuwa na juya Ina kallon shi sannan na ce,

"Habaa dan Allah Husband sai da na gama had'a kaya kafff na kulle komai tafiya kawai nake Jira sannan zaka ce na warware ga kayan ka ba a sama suke ba ma, gaskiya ni dai ka bari in na je can zan cire Maka, and ni bana son wata darling Baba ma fa haka yake Kiran Mama da shi kana kirana darling kamar wata tsohuwa"

Dariya ya dinga yi sannan ya kama hannu na muka zauna a kujera mai cin mutum biyu, ya ce,

"To Baby na daga yau na dena Kiran ki da darling shi kenan? Kuma ai gani na yi Baba na ce maki darling yaran gidan ku ma wasu darling Mahreen suke ce maki....to yanzu daiii komai ya wuce zan je na cire kaya na in yaso se ki qara gyara inda ya b'aci ko?"

Ni dai ba haka na so ba, na so mun yi tafiyar ne tare fushin da nake kenan,ni bana son abinda zai na raba ni da shi na tsawon lokaci, shine dalilin da ya sa ko Kano zani asibiti yake raka ni, to amma wannan karon da alama hakan ba zata samu ba, dan haka washe baki na yi na nuna masa komai ya wuce zan cire masa kayan nashi sannan na masa addu'a da fatan alkhairi akan abinda za su yu d'in.

A ranar da za mu tafi na dinga jiran Habibah ta min maganar tafiya shiru, dan haka da muka gaji da Jira sai muka nufi tasha ko da muka je ashe su a motar gida za su tafi shi yasa bata min maganar tafiya ba tunda ba motar su bace,da samun labari sai muka shiga motar haya muka tafi ni da Suwaidatu, muna tashi motar bayan mu ma ta kusan cika ashe su Isma'il sun shige ta, dan haka gaba d'ayan mu sai muka isa kusan a tare, Yara kuwa aka hau murna kamar yanda suka saba wannan karon murnar ta zama biyu ga amarya ga Zaituna da tsohon ciki, haka muka tsaya sashen Yayan su Yah Maheer muka gaggaisa a tsaitsaye da su Maman Ummeeta sama sama, sannan muka shige sashen mu, muna shiga gidan Ummah da Mama suka taso su na mana lale maraba, sauran qannen Yah Maheer ma na yi mana maraba lale, gani na yi Ummah ta kama akwatin Habibah suka wuce suka yi d'akin Umman Mama ma ta ja na Zaituna suka yi d'aki Sai gani tsaye a tsakar gida zuruuu ba me Jan nawa akwatin Ina tsaye Ina tunanin shin me ya faru ne haka Sai ga Baba ya fito daga d'akin Shi babu riga saboda zafi da yake Ji, ya kama akwati na zai shigar min da Shi d'akin Ummah da sauri na kama na riqe na ce,

"Habaa Baba ka bari Zan Iya ja ba komai, na gode"

Suwaidatu na gani ta fito daga d'akin su bayan ta ajiye ta ta jakar, jiki ba kwari na ja akwati na na Kai d'aki a sannan ne Ummah ta hau min sannu da zuwa, na amsa mata Kamar ba abinda ya faru,cikin Ikon Allah kuma Sai na Ji bana jin zafin abinda ta yi d'azun,nan fa aka hau hidima da mu,hirace ta daban ta kuma musamman ke gudana tsakanin ta da Habibah ana jefa wa da ni sama sama, ko kuma in sanya kaina a ciki ko da ba a saka ni ba.

A haka muka kwana washegari muka yi wanka muka shirya dan zuwa ziyara, har gidan Addah Ummuna sai da muka je, mun sha yawo sosai na ziyara har sai da qafafun mu suka gaji Libus.

Ko da muka dawo gida da yamma lisss mun gaji, na shiga banɗaki na watsa ruwa na yi alwala, a inda na bar su suna hira da Ummah nan na same ta, dan haka se na musu sallama na wuce ciki na shirya sannan na tada sallah, Zaitunah na daki ita da su Suwaidatu suna tasu hirar Mama na kai wa Baba tuwon shi na dare.

Kafin na idar Habibah ta je ta yi alwala itama ta zo ta tada sallah,Ummah kuma ta fita tsakar gida dan su ci abinci da Mama se aka bar mu mu biyu a d'aki, hira muke ta zabgawa kamar wasu dad'add'un qawaye, muna tsaka da hira Kabeer  ya kira ta, ta kuwa kashe murya ta amsa sallamar shi, yanayin yanda take amsa wayar se ya bani kunya da sauri na kalli hanyar d'akin Baba wanda bamu da nisa da shi, da hannu na yi mata nuni da ta yi a hankali kar ya ji ta, domin shi mutum ne da baya maraba da irin wad'annan abubuwan, na kula yanayin yanda muke jin nauyin juna ni da Yah Maheer a cikin gidan ya na burge Baban, tinda a fili yanayin soyayyar mu, shaquwa, da kulawar mu yake amma bama bayyana wa ta yanda za a ga rashin kunyar mu.

Zaqewar da ta yi se ya dinga sa ni jin kunya, amma ita ko a jikin ta dan na kula ta d'au hakan a wayewa, da na dame ta da yi mata nuni da ta yi a hankali se ta fita bayan d'akuna wanda se da na yi danasanin damun ta akan tai a hankali da na yi, domin kuwa kamar a gaban kowa take yin magana, cikin b'acin rai kuwa Baba ya buga tsaki ya yi maganganu wanda ban ji me ya fad'a ba, kunya sai ta baibaye ni na Ji kamar da ni ake, Ko da ta gama ta dawo se ta hau bani labarin wayar tasu, na so na sanar da ita yanda Baba be ji dad'in yanda take waya ba se na kasa na ja baki na na yi shiru.

A haka muna hira da Habibahn Yah Maheer ya kira ni,na amsa wayata cikin kulawa kar na yi abinda zai sake sanya Baba yin fad'a, ko ya yi tsaki kamar yanda ya yi d'azun, ba mu wani jima ba muka yi sallama da juna na yi sallar isha'i na yi shirin kwanciya, na riga na gama bajewa a gado zan kwanta na bar space inda Habibah zata kwanta itama tunda zai ishe mu, sai jin Ummah na yi ta ce,

"Mahreen na ce ga shimfid'a se ki kwanta ni bari na yada tabarma a tsakar gida ke kuma Habibah se ki hau gadon"

Da sauri Habibah ta ce,

"Ahh Ummah ta yi kwanciyar ta ni zan kwanta anan ɗin, babu komai"

Ina jin su suna ja in ja takaici ya hana ni magana, ni dai da fari Ummah ta san bana son kwanciyar qasa, ciwon jiki take saka ni, tunawa na yi da farkon zuwa na garin yanda aka bar min gadon na kwanta har se da washegari da kaina na yada katifa qasa na kwanta, tun daga nan da ta gane kwanciyar qasa ciwon jiki take saka ni nake kwana a gado in na zo shine yau ake so na dawo qasa bayan gadon ze ishe mu ba sai na sauka ba, jin Habibah ta ce za ta kwanta a qasan ne ya sa na dena tura baki, dan na qudurta ba zan kwanta a qasa ba ko me za a ce.

Ina nan kwance bacci ya garere ni sakamakon wani irin tari da ya dame ni, tin Ina Yi a hankali har abu ya ci tura na tashi zaune na dinga yin shi,kanzil ba wanda ya ce mun, haka na yi ta tari har baccin wahala ya ɗauke ni.

Ashe ina can yawon bacci cikin dare ciwon Baba ya tashi ban sani ba, da asuba bayan na yi sallah na gaishe da Ummah se na bi lafiyar gado zan koma bacci, dan dama haka muke yi, se gari ya waye muke sake gaishe ta a kuma gaida Baba da Mama da mutanen sauran sashen.

Gaba d'ayan su sun zaci na koma bacci, cikin qasa da murya sai Ummah ta ce wa Habibah,

"Ki yi sauri ki je ki gaishe da Baban su jiya jikin shi ya tashi be ji dad'i ba akan shi muka kwana"

Cikin jimanta lamarin Habibah ta ce

"Subhanallahi me ya same shi? "

"Yi sauri ki je ki gaishe shi kafin ta tashi ki dawo"

Habibah na sanye cikin dogon hijabin ta ruwan coffee bana taɓa mantawa ta miqe ta nufi d'akin Baba,durqusawa ta yi ta ce,

"Assalamu alaikum"

A hankali Baba ya amsa mata sallamar ta, sannan ta sake cewa,

"Ya jikin Baba? Ashe jiya baka ji dad'i ba? Allah ya qara lafiya, ai ban sani ba se daz......"

"Tashi ki ban waje, na ce da sauqi......."

Ban sake kasa kunne dan jin qarashen maganar Baba ba tsabar dariya da nake ta yi daga nan inda nake a kwance, gashi bana so su san dariya nake tinda su a tunanin su bacci nake, cikin jimami Habibah ta dawo ta zauna a kujera, ita da Ummahn suna sake jimanta maganar rashin lafiyan Baba, na san za a rina tinda ba yau nake da Baba ba, na riga na sani in dai ya yi rashin lafiya baya son hayaniya,tin Ina dariyar su har baccin gaske ya ɗauke ni.

Se da na shaqi bacci na son raina sannan na farka, na je na yi brush na wanke fuska ta sannan na ajiye brush dina a jaka ta a lokacin Habibah bacci take bata farka ba, dan haka se na sa hijabi na na je qofar dakin Baba na durqusa na gaishe shi ya amsa cikin sakewar fuska tare da tambaya ta ya jiki na dan ya ji ina ta tari da alama mura ke son kama ni,godiya na masa da kulawar shi a gare ni sannan na miqe na je na sake gaida Ummah da Mama, nan take Ummah ta ce,

"Ki jira Habibah ta farka se ku shiga cikin gida ku yi gaisuwa tare"

Murmushi na yi na ce mata

"Toh Ummah "

Shara na fara yi kafin ta farka har na gama ta na bacci,ina tsaka da wanke wanke ta farka, ni ban san ta farka ba se da ta yi brush ta shiga ta ajiye brush ɗin ta fito, sai na ga Ummah na nuna mata hanyar tafiya sashen Baffanin Yah Maheer dan ta je ta yi gaisuwa,sai na yi kamar ban gani ba, Zaituna ce ta fito matar Isma'il da runtumemen cikin ta ta zauna a kusa da inda ake wanke wanke ta dinga kwakule kasar ginin wajen ta na sha, saboda daɗin ta take ji, a haka muna zaune ina kallon ikon Allah Habibah zata je gaisuwar ba da ni ba ko kuwa yaya? Ina kallon ta kuwa ta yi gaba zuwa gaishe gaishe, ni kuma na yi kamar ban gani ba na qarasa wanke wanken na tashi na wanke jiki na, ta na dawowa muka haɗu muka gaisa da junan mu sannan ta wuce daki na tafi tawa gaisuwar.

Kwana biyu tsakani aka yi bikin qaramar sallah cike da nishad'i da annashuwa washegarin sallah Isma'il ya ɗauki matar shi suka koma bauchi, ni da Habiba kuwa mu na nan tukunna bamu tafi ba, dangi ana ta kawo mana kayayyakin qauye, su kuka, albasa, yaji, daddawa, kubewa, kayan miya danye da busasshe sai citta da kayan kamshi da sauran su, duk wata albasa da kayan miya da aka kawo sai a baza su su sha iska dan kar su lalace kafin mu tashi tafiya.

Bayan sallah da kwana uku kuwa Abubakar ya zo ganin gida shima mu kuma muna shirin komawa da yamma, nan fa aka jawo kayayyakin da aka bamu aka hau rabo, tin da na ga yanda ake rabon be min ba se na ɗauki littafin addu'o'i na na hau karanta wa, Suwaidatu na can an gama haɗa mata kayan ta ta na ta kuka bata so ta koma, duk sai na yi ta jin rai na babu dad'i, ina nan zaune ina tunanin shin me ke saka yarinyar nan kuka ne haka duk sanda muka zo za mu koma Bauchi kamar wadda ake yi wa wani mugun abun se na ga Ummah ta kwashi kayan miya me yawa ta zuba a na gaban Habibah suka kalli juna akai murmushi,ni ɗin ma murmushin na yi a raina ina ayyana cewar,

'Ohhh ni Mahreen Ina ganin duniya yau, mu da muke mu biyar shine ake karawa mutum biyu,Allah ya kyauta'

Ta na gama rabawa se cewa ta yi,

"Mahreen ɗauki naki"

Cikin nuna halin ban damu da abinda kuke aikatawa ba duk da na gani na ce,

"Ahhh ba komai Ummah a daukar mana kowanne"

Ai kuwa nan da nan aka kwashe wa Habiba kayan miyan gaban ta a kwali, busassun kayan miya kamar su kuka kub'ewa da sauran su aka mata ledar su daban suma, duk ina zaune ina kallon ikon Allah, hadari ne ya taso sosai, ga zafi ana ta zubawa, cikin sauri ta d'ebi nata ta tafi, mu kuma Yah Maheer ya yi waya ya ce mu jira in Abubakar ya gama gaishe da mutanen gida gobe da safe mu dawo tare, ba haka na so ba, dan kuwa raina b'ace yake da abubuwan da aka yi min, haka na danne ba dan na so ba, Baba ya kula da duk abinda ya ke faruwa, dan haka sai ya dinga min hira sama sama, na kuwa ji daɗin hakan sosai, cikin wata hikima ta Ubangiji ina yada fitila gefen kujera zan d'auki tabarma sai na ga kwalin da aka totsarawa Habibah kayan miya da yawa a ciki a gabana ta manta da shi saboda sauri.

Abubakar ne ya dauka ya kalla ya yi dariya sannan ya ce,

"Ba rabo ba"

Umma na jin haka ta hau salati ta na nuna baqin cikin manta kwalin da akai, nan da nan Baba ya ce a fitar da kayan miyan a baza su kafin gobe sai a kai musu, haka kuwa aka yi, aka baza su gefen namu da dama tunda aka ce ga kason mu ban kwashe ba se da Yah Maheer ya ce zamu sake kwana sannan na baza shi.

Qarshe dai har da muka koma Bauchi kayan miyan rabon mu ya koma dan kuwa bata je ta ɗauka ba.

Haka na dinga ganin banbanci ina mamakin me zai sa a banbanta tsakani na da ita tunda dukan mu d'aya muke, har se da watarana na samu cikakken bayani da tarihin Yah Maheer a bakin shi.

*Wanene Yah Maheer?*

Shine Babban d'a a maza a wajen Malam Mahmuda da kuma Malama Zainab, mahaifiyar Yah Maheer ta rasu a wajen haihuwar qanwar shi Ruqayyah wannan shi ne dalilin da ya sa riqon shi ya dawo wajen Ummah, ita ya sani a matsayin mahaifiyar shi, ta yi masa riqo riqo irin na amana, ta yanda bata banbanta shi da yaran da ta haifa ba, kowa ita ya sani a matsayin mahaifiyar shi.

Mahaifin Yah Maheer na matuqar son shi da qaunar shi, ta yanda duk wani abu da ya danganci shi ya na ɗaukar shi da mahimmanci, a nan na gano cewa ko da Baba na so na na musamman to soyayyar Yah Maheer ta shafe ni.

Yah Maheer ya bani labarin gidan Gurama da nake zuwa gaishe su in mun je Liman Katagum nan ne gidan su Mahaifiyar shi, kakanni shi na wajen mahaifiya sun rasu sai qanin mahaifiyar shi da suke uwa ɗaya uba ɗaya da kuma qannen ta da suke uba ɗaya kawai se cousins ɗin mahaifiyar tashi ne suka rage a gidan.

Ko da na gama jin wannan tarihi kafff sai kawai zuciya ta ta ba wa Ummah uzuri akan abinda ta yi a matsayin murna da farin cikin ganin surukar ta ta ɓangaren Kabeer, sannan na tuna baya nima fa lokacin zuwa na ta yi min wannan tarbar wadda ta sa ban taɓa ɗaukar ta a wani matsayin da ya wuce mahaifiya ga Yah Maheer ba.

Dan haka sai na danne abinda ya faru na binne shi a raina ban sanar da shi komai ba, muka ci gaba da murnar dawowa ta gida lafiya.

Ana haka wataranar Laraba Yah Maheer be koma aiki ba muka karbi baquncin qanwar Yah Maheer wato Sadiya (Allah Ubangiji ya gafarta maki ya yafe maki dukkan kurakuran ki ya raya abinda ki ka bari), Abida ta zo da tsohon ciki a jikin ta a wancan lokacin, haihuwa ko yau ko gobe, cikin sauri na dora ruwan yin ɗan wake dan na ji labarin itama ta na son shi kamar Yah Maheer, ina can kitchen Ina kwab'in ɗan wake na bar ta da yayun ta su yi hirar zumunci.

Ban koma ba se da na kammala ɗan wake na yi miyar attaruhu da yaji albasa da kifi, na tsame taliyar da na dafa saboda su a Bauchi sukan haɗa taliyar da ɗan wake, ta wani ɓangaren na dafa taliyar ne saboda ni, dan bana cin ɗan wake sosai se dai sama sama.

Se da na ajiye wa Yah Maheer nashi da duk abinda ya kamata sannan Suwaidatu ta kai wa Abubakar nashi ta ɗauki nata sannan na dakko mana namu ni da Abidah.

Bismillah mu ka yi muka fara cin abincin, bana manta wa tsabar yanda abincin ya mata dad'i se da yawu ya zuba a bakin ta duk da ta cika bakin ta da ɗan wake, tsokanar ta na dinga yi ta na kare kan ta da cewar,

"Ba dole na zubo da yawu ba tunda kin iya girki, da baki iya ba se na kawo wa Yayah wata ya qara da ita"

Haka muka gama cin abinci cikin raha da barkwanci suka gama hira da 'yan uwan ta sannan Abubakar ya dakko machine ya gyara daidai yanda za ta iya hawa, kallon fuskar Abubakar na yi na ga yanda ya bata rai, sai na ji wani irin yanayi ya shige ni wanda na kasa tantance shi, haka Abidah ta hau machine ɗin nan ya tuqa ta suka tafi.

A zato na gidan ta zai maida ta se dai ban sani ba a she ba gida suka nufa ba wani wajen suka wuce............

*Mutanen kwarai masu albarka in an karanta a dannan min star hilis sannan a yi sharing saboda wanda basu karanta ba su antayo ayi da su..ina maraba da comments ɗin ku, amma a yi hakuri banda zafafawa domin wannan labari na gaskiya ne kamar yanda na sanar da ku tun farko...Thank you my fiful*

Lanjutkan Membaca

Kamu Akan Menyukai Ini

1.4M 34.9K 47
When young Diovanna is framed for something she didn't do and is sent off to a "boarding school" she feels abandoned and betrayed. But one thing was...
3.6M 291K 96
RANKED #1 CUTE #1 COMEDY-ROMANCE #2 YOUNG ADULT #2 BOLLYWOOD #2 LOVE AT FIRST SIGHT #3 PASSION #7 COMEDY-DRAMA #9 LOVE P.S - Do let me know if you...
1.5M 133K 45
✫ 𝐁𝐨𝐨𝐀 𝐎𝐧𝐞 𝐈𝐧 π‘πšπ­π‘π¨π«πž π†πžπ§'𝐬 π‹π¨π―πž π’πšπ πš π’πžπ«π’πžπ¬ ⁎⁎⁎⁎⁎⁎⁎⁎⁎⁎⁎ She is shy He is outspoken She is clumsy He is graceful...
280K 16.2K 17
"α€˜α€±α€Έα€α€Όα€Άα€€α€œα€¬α€•α€Όα€±α€¬α€α€šα€Ί α€„α€œα€»α€Ύα€„α€Ία€œα€Ύα€―α€•α€Ία€žα€½α€¬α€Έα€œα€­α€―α€·α€α€²α€·.... α€™α€Ÿα€―α€α€Ία€›α€•α€«α€˜α€°α€Έα€—α€»α€¬...... ကျွန်တော် α€”α€Ύα€œα€―α€Άα€Έα€žα€¬α€Έα€€ α€žα€°α€·α€”α€¬α€™α€Šα€Ία€œα€±α€Έα€€α€Όα€½α€±α€€α€»α€α€¬α€•α€«.... α€€α€»α€½α€”α€Ία€α€±α€¬α€Ία€›α€„α€Ία€α€―α€”α€Ία€žα€Άα€α€½α€±α€€...