MAHREEN

By HAERMEEBRAERH9900

1.5K 423 71

A Koda yaushe muna Jin labaran zama da kishiya Mai ban mamaki da ban al'ajabi....Labarin MAHREEN labari ne na... More

MAHREEN PAGE 1
MAHREEN PAGE 2
MAHREEN PAGE 3
MAHREEN PAGE 4
MAHREEN PAGE 5
MAHREEN PAGE 6
MAHREEN PAGE 7
MAHREEN PAGE 8
MAHREEN PAGE 10
MAHREEN PAGE 11
MAHREEN PAGE 12
MAHREEN PAGE 13
MAHREEN PAGE 14
MAHREEN PAGE 15
MAHREEN PAGE 16
MAHREEN PAGE 17
MAHREEN PAGE 18
MAHREEN PAGE 19
MAHREEN PAGE 20
MAHREEN PAGE 21
MAHREEN PAGE 22
MAHREEN PAGE 23
MAHREEN PAGE 24
MAHREEN PAGE 25
MAHREEN PAGE 26
MAHREEN
MAHREEN PAGE 27
MAHREEN PAGE 28
MAHREEN PAGE 29
MAHREEN PAGE 30
MAHREEN PAGE 31
MAHREEN PAGE 32
MAHREEN PAGE 33
MAHREEN PAGE 34
MAHREEN PAGE 35

MAHREEN PAGE 9

42 14 0
By HAERMEEBRAERH9900

💅  MAHREEN  💅







WRITTEN BY HAERMEEBRAERH






PAGE 9






Hannun ta da ta ke miqo min na bi da kallo, da sauri na riqe plate din da ta miqo min,idanun ta na qare min kallo fuskar ta d'auke da murmushi, nima murmushin na mayar mata ta ce,

"Ina kwana amarya?"

"Lafiya qlou alhamdulillah,"

"Masha Allahu, ga wannan ba yawa ku tab'a,"

"Thank you so much, this is more than enough, thank you"

"Ba komai,"

Juyawa ta yi zata koma d'akin ta, na bi bayan ta da kallo, Maimuna mace me mai jiki mai kyau masha Allah, bata da tsayi sannan bata da qiba, mazaunan da take da shi ne suka qarawa surar ta kyau, d'aki na na koma riqe da plate d'in a hannu na, bud'e wa na yi sai na ga indomie ce da kwai da dankalin turawa a gefe.

Ajiye wa na yi a qasa na masa bismillah akan ya sakko mu ci dan ni bana wasa da ciki na musamman in na ga abinda nake so, halin da nake ciki be sani jin ba zan ci abincin ba, kallon plate d'in Yah Maheer ya yi sannan ya ce,

"Ki ci kawai zan ci cincin da dubulan kar ki damu,"

Qoqarin tilasta masa nake ya ci sai ya kalle ni ya ce,

"Kar ki damu young lady i am not hungry, zan fita anjima sai in kawo maki kayan miya ki yi mana girkin rana, tinda kin ga ko mutanen kano ma basu tafi ba zasu sake dawowa, be kamata ace su zo ba abinci ba ko?"

"Hakane, Allah ya kaimu,"

Loma d'aya na kai baki na ina taunawa, dad'in abincin ya sanya ni lumshe ido, a duniya ina masifar son duk.wani abinci da aka sanya wa farin maggi shine dalilin da ya sa yana wahala in ci abincin da aka sanya wa farin maggi ban gane ba,mu gidan mu ba a cin farin maggi,dan haka nake matuqar qaunar cin shi, lokuta da dama abinci ko ba dad'i indai an saka farin maggi bana jin haushin cin shi ko waye ya dafa kuwa.

Hamdala na yi a qasan raina da Yah Maheer be ci ba, haka kawai na zo na yi girki ya ji be kai wannan dad'i ba?

Ina gama ci na miqe na tattare komai na gyara na share, sannan na kai masa ruwa a buta waje saboda zai yi sallar dhuha (walaha) ya na fita na dakko bedsheet d'ina da ya yaye a jiyan na bud'e qofa kamar mara gaskiya ina leqe, na shige kitchen d'ina na kama inda duk na ga be min ba na wanke, na yi masa muguwar matsa na yarfe, sannan na koma cikin d'akin da sauri na sake maida zanin gadon, ko da ya shigo ya ga zanin gadon har zai yi magana sai ya yi shiru ya na ta kallon shi, ni kuma na juya ina gyaran wardrobe na qarya dan komai a gyare yake, ban juyo ba se da na ji ya tada sallah sannan na yi wufff na bar d'akin na koma parlour na kwanta a kujera ta man rest da nake mugun son irin ta, se gashi an yi min ba tare da an san ma zab'i na ba,wannan karon se na ji bata burge ni ba wanda da a da ne na gan ta aka ce wannan taki ce ba qaramin tsallen murna zan yi ba da farin ciki.

Numfashi nake ta fitarwa saboda sabon zazzab'in da ya ke son sake rufe ni, ina kwance na ji sallamar Yah Maheer ya fito cikin shirin fita, ya ce min bari ya je ya dawo, in 'yan kano sun zo na sanar da shi ya dawo su yi sallama zai je ya samu Yaya Babba a samo motar da za su koma har kano a cikin ta, na ce masa to.

Qasan raina kuwa har na gama yanke hukuncin binsu in koma gidan mu na fasa zaman anan ni,bani da lafiya ba zan zauna ba, ni dai kawai kome za a yi sai an koma da ni a wannan ranar.

Ko minti biyar be yi ba da fita sai ga 'yan uwa na sun zo inda daga nan ba inda za suje za a wuce da su kano, cikin murna na je na tarbe su ina ta farin ciki, na shiga d'aki kamar wadda zata d'akko wani abu, na d'auki akwati na madaidaici da aka d'ora a saman wardrobe na zuba kaya na a ciki sannan na zuge, na ajiye a gefe, na dauki ledar kazar da ban ci ba jiya da sauran lemo na fita da shi,sannan na koma na deb'i kayan gara da yawa na sake fita da shi, Goggonaye na ne wato qannen babana ne su uku suka zo daga baya kowaccen su ta ci kwalliya, Goggo Bilki, Aunty Jummai, Aunty Ameenah (matar qanin babana)da Aunty Iyannan, can kitchen d'ina kuma Yayar mu ce da sauran qannen babana su Shafa, ina zaune wajen su Yayar mu ta ce,

"Ki tashi ki je wajen aunties din ki mana ki gaishe su,"

Ta kula da yanda gaba d'aya nake jin jiki dan haka da ido kawai take bi na har na fita parlour na tadda su su na zaune a kujerun da suka cika parlourn, da ido suke bina bayan na gaishe su, ina fidda nishi kad'an kad'an, Aunty Jummai ce ta ce,

"Wannan nishin da ki ke yi kamar kin yi gudu fa?"

Ji na yi ido na ya kawo ruwa, saboda ni kad'ai na san ya nake ji a wannan lokacin, gaba d'aya jiki na ciwo yake, cikin qoqarin daidaita murya ta na ce mata,

"Banda lafiya ne, zazzab'i nake ji"

Kallon junan su suka yi, na ga sun yi murmushi, can se Aunty Bilki ta ce,

"Ai ya kamata ki sha magani, amma ki ta nishi haka se kace wadda tai gudu,ina shi Maheer d'in?"

"Na sha magani....ya fita wajen Yaya Babba,amma ya ce na kira shi in kun zo"

"To shikenan ki je ki kira shi"

Da kyar na miqe na fara takawa zan fita se na ji suna magana qasa qasa, (ehe bana mantawa na ji ku sarai😂) gaba na yi abu na na dakko waya ta na fad'a masa zuwan su, ya sanar da ni cewar sun had'u da Yaya babba gasu ma tare a waje, na kashe wayata.

Ina komawa wajen su Yayata na zauna muna hira can muka jiyo muryar Yaya Babba da Yah Maheer sun shigo, ina jin muryar Yayana na fita da saurin da zan iya na je gare shi ya rungume ni, se hawaye ya balle min Yah Maheer kuwa ciki ya shiga su gaisa da su Goggo da Yayarmu, cikin kukan shagwab'a na ce wa yayan mu,

"Yayah zan bi ku dan Allah mu koma bana son zama anan"

"Subhanallahi ke da aka kawo ki gidan mijin ki gidan da ake fatan mutuwa ce zata raba ku amma kice wai zaki bi mu? Ai ba haka ake yi ba,"

"Ni dai na fasa zama zan bi ku ni na ma had'a kaya na"

"Tirqashi....to kin ga ki yi hakuri ba haka ake yi ba, duk macen da ki ka ga an mata aure an kai ta gidan miji ba a fatan abinda zai raba ta da gidan daga mutuwa sai zuwa unguwa, dan haka ki yi hakuri Allah ya miki albarka ya baku zaman lafiya da zuri'a mai albarka, amma saboda hankalin ki ya kwanta ni ina nan a gari zan kai sati d'aya Kafin na koma zan sake zuwa wajen ki, in baki sauya ra'ayin ki ba sai mu koma tare kin ji?"

Hakan da ya fad'a ne ya sanyaya raina, sai na ji hawayena sun rage gudu, kafin ma ya qarasa shiga ciki an fara danna masu horn akan su fita a wuce, fita suka dinga yi muna sallama a bakin hanya, ganin Yayar mu zata fita se na rungume ta ina kuka, cikin dakewa ta ce,

"Ki yi hakuri Mahreen ke da ga ki ga Addah Ummun ki da Addah Firdausn ki? Ki zaman ki lafiya da maqociyar ki me kirki kin ji Allah ya miki albarka"

Ko ameen d'in ma na kasa furtawa, haka qannen babana suma suka wuce dik aka barni ina tsaye a jikin qofar gidan ina hango su a mota, na jima a wajen ban koma ciki ba ina ta kuka, ina juya wa zan koma ciki muka yi ido hud'u da Yah Maheer da ke tsaye ya na kallo na shima cikin tausayawa, hanya ya bani na wuce ina jin matsanancin haushin raba ni da 'yan uwa na da gidammu da ya yi aka kawo ni wata uwa duniya.

D'aki na shige na kwanta ina numfashin zazzab'in da ya sake rufe ni rufff, magani ya sake bani na karb'a da kyar, ina nan zaune ya na ta jera min sannu se ga qanin shi da abokan shi sun zo, shi yake bi wa Yah Maheer d'in, fita ya yi wajen su Palrour suka hau gaisawa, cike da jarumta na fito nima sanye da hijabi, da plate din da na zuba kayan gara akai na je muka gaisa na ajiye masu plate d'in sannan na miqa masu ruwan shan da ke a cikin jug tin wanda na kaiwa su Goggo na.

Godiya suka min na zauna a gefe suna hira ina yaqe,dan bana so zuwan farko su ga ban girmama su ba, se da na ji sun fara personal hirar gida na tashi na basu waje na koma d'aki na kwanta.

Da daren ranar ma Addah ce ta bamu abinci bayan na cika leda da kayan gara na miqa mata, sannan na deb'i mafitai da plates da qananan cups da aka raba a biki da yayar mu ta min dabarar zuwa da su ta ce ina ba wa baqi in sun zo, dikkan su an saka sticker na auren mu jiki,ta yi min godiya sosai sannan na fad'a mata suna na ta fad'an nata ta ce amma an fi kiran ta da Addah.

********************************

Cikin kwanaki uku na samu wata iriyar kulawa da lele da shagwab'awa wajen Yah Maheer ta yanda da ana tauna ruwa na tabbata da zai tauna min tsabar yanda yake lele na,a sannan kuma na gano Yaya Babba wayo ya yi min ya gudu ba sake dawowa ze yi ba, a lokacin ne nima na ga matuqar wautata da shirme na, dama ta yaya iyaye na za su b'ata lokacin su su aurar da ni a kawo ni sannan a maida ni kamar auren 'yar tsana?

Tini na fawwala wa Allah lamura na na saki zuciya ta na hau bautar aure, a rana ta hud'u Yah Maheer ya aiki qanin shi mai suna Kabeer ya yo mana siyayya, inda ya had'o min da farin maggi, murna a waje na kamar na taka rawa, irin gani yau a gidana ni kad'ai zan amfani da farin Maggi da Baba ke hanawa.

Yah Maheer kuwa d'an gidan Baba ne, ko a hira ya ji Baba baya son abu, har yanzu da muke tare shekara da shekaru to fa ba za a yi wannan abun ba,dan haka ko da ya kyalla ido ya ga Ajino Moto sai ya d'auke shi cikin kayan ya ce banda wannan kar a sake siyowa da shi, duk naci da magiya da shagwab'a ta be sa ya bar min ba, qarshe sai na karba na ce to ya bani na ba wa Maimunah tinda su suna amfani da shi.

Wannan shine dalilin da ya sa ya nesanta da cin abincin da suka kawo, ni kuma se ya zame mani blessing, dan kuwa Maimuna gwana ce wajen iya girki ta yanda ko ba ajino in ta yi girki ya na masifar dad'i,balle kuma ta na saka mutumi na.

Tin ina amarya Yah Maheer da abokan shi da ke zuwa gaishe mu suke yabo da tsananin son girki na, har kyautar kud'i sukan min ko kuma yabo da addu'a.

Zuwan Alhaji Younusa na farko gidan mu na kai masa abinci jellop rice ya so ya qi ci saboda a qoshe ya zo, amma a cewar shi kawai yanda ya ga shinkafar ya yi kyau a plate da qamshin ne ya yi inviting din shi har ya ci, da ya ci kuwa sai da ya hau zuba santi ya na comment akai kamar irin a makarantar nuna bajintar girke girke.

"A gaskiya Maheer ka yi dacen matar aure, gata saliha, gata me kyau, gata me addini, 'yar gidan mutunci sannan ta iya girki, ka san a dafadikan shinkafa ake gane mace ta iya girki ko bata iya ba, ta dafa ta ta yi kyau da dad'i gishiri be yawa ba, maggi be yawa ba, kuma ba a zabga mata mai ko yaji ba, sannan gashi ta dahu daidai bata yi cikin shege ba,(tsimburum-burum) gaskiya dole na ce maki job well done amarya, Allah ya yi albarka"

Wani irin dad'i da farin ciki na dinga ji, kawai se na tuna Babana yanda yake yawan yabon girki na addu'a na yi masa cikin raina sannan na miqe na shige d'aki na bar su tare, kafin na shiga na ji sun yi magana qasa qasa sun tafa an fashe da dariya.

A raina na ce,

'Oho ai dama Yah Maheer d'in nan da ya ga abokan shi sai an yi gulma ta an tafa ake jin dad'i Allah ya shirye ku'
Na murgud'a d'an baki na sannan na yi murmushi na wuce ciki na rufe qofa ta.

Wata na d'aya a gidan aure na ga baqi kala-kala, kar ku manta Bauchi shine inda dangin mahaifi na suke ta b'angaren uba,dan haka ta ko ina ganin baqi nake, b'angare daya kuma muna waya da mutanen gida akai akai, da yayu na da ke cikin garin.

Yau ma kamar kullum ina kwance bayan na kammala aiki na, sanye nake da wata riga fara mara hannu guda, hannu dayan kuma guntu ne ko damtse na be rufe ba, sai makeken tambarin heart a jiki wanda aka rubuta I LOVE YOU a qasan heart d'in rigar ga zauna a saman qirji na sa kyau ta qara bayyanar da su, sai na d'aura wani zani na materil me kama da skirt irin me fad'in nan sosai ta qasa ta sama ya kama mutum,Baba ne ya siyo mana ni da su Addah Ummu inda daf da biki na ya qaro min da wata riga da yake kiran ta rigar amare, dan kuwa sak irin ta amare ce amma purple.

Kai na a gyare yake na tsaga tsakiyar shi na kwantar da shi ya yi kyau sosai, ina ta rubuce rubuce a wani d'an qaramin littafi na, domin Allah ya zuba min son yin rubutu,tin a da can, haka nan zan qirqiri magana mai ma'ana na rubuta na ajiye a littafi, ina tsaka da rubutun na ji muryoyi na tashi a tsakar gida ana ta hayaniya sosai, tashi na yi na jawo hijabi na da ke saman qofar d'aki na a koda yaushe saboda baqi na zira na idasa fita,mata na gani sama da biyar suna tambayar nan ne gidan D'an azumi?Addah ta ce ba nan bane, dan ba da haka ta san sunan shi ba, wata dattijuwa ta kafe ta ce nan ne, saboda nan aka musu kwatance,ko da na leqa sai qanwar Yah Maheer da ni ban san ta a fuska ba amma na san ta a waya ta ce,

"Goggo nan ne, ga ma Mahreen d'in can, kama suke da Ummu" (Ta san Addah Ummu tinda ta kan je kano gidan Kawun su)

Baki na washe alamar na san su tinda sun nuna sun san ni suma, shiga suka yi na wuce gaba muka je parlour, suka zazzauna, na zauna a qasa a gefen kujera na hau gaishe su, anan ne na ji wata ta na ta tsokana ta da 'yar qauye se na gane akwai wasa a tsakanin mu, ni dai ban tanka ba ina dai ta murmushi, da sauri na je na deb'o musu abinci,dama na dafa shinkafa da miya da kifi  na had'a musu da kayan gara da ruwan sha na ya ka musu lemon da ya rage bamu sha ba, se na basu waje dan su ci na koma d'aki.

Ina kwance ina ci gaba da rubutu na qanwar shi ta shigo saboda ta na fama da tsananin ciwon kai, nan take sanar da ni ita ce Abidah da muke waya sanda ina gida,hira muka dinga yi kamar dama mun san juna,har Yah Maheer ya dawo, suka hau hira, ta na masa magana akan matsalar ta, ya na nuna ba wani aljanu dan dai ya kwantar mata da hankali ta dena sa damuwa a ranta, se bayan ya fita ne ta yi murmushi ta ce,

"Kin san Ustazai shi se ya nuna ba wani aljanu ko sihiri in kama addu'o'i in yarda komai ya same ni daga Allah ne"

"Allah sarki, ai maganar shi gaskiya ne ke dai ki ta addu'a Allah ya baki lafiya"

"Hummm Ameen to, wato kin bi bayan mijin ki ko?"

Dariya na yi cike da jin kunya na sauka a gado zan maida hijabi na se ta ga shigar da ke jiki na, salati ta saka se da ta tsorata ni, sannan ta ce,

"Lallai ana nan ana rikita d'an uwa na"

Da sauri na fice a d'akin ina dariya, a raina ina ayyana

'A shigar qananan kaya na me ki ka gani baiwar Allah?'

Ko da na shiga na ga sun ci abincin amma ita cousin d'in shi Ramatu bata ci ba, ashe ita da Abidahn  ba su cin kifi ne, ita Ramatu haka take, ita kuma Abidah saboda cikin da ke jikin ta ne a lokacin, se na ji babu dad'i nan take na ce zan dafa masu wani abun ko da taliya ne, suka qi amincewa suka ce tafiya ma za su yi za su koma can garin mu wato Liman katagum driver da ya kawo su na jiran su, dan haka har bakin.qofar gidan na raka su bayan na debar masu kayan gara na hada da plates dan na ga mafitan sun kusan qarewa shi yasa ban basu ba suna da yawa.

Bayan tafiyar su muka koma ciki yana qara yi min bayanin su, ashe mutanen gidan su ne da qanwar baban shi da suke uwa d'aya uba d'aya da baban shi,hamdala na dinga yi da na dora hijabi a saman riga ta basu ga komai ba.

Mu na shiga na cire hijabi na na rataye idanu Yah Maheer ya qura min kamar be tab'a ganin abinda ya burge shi a duniya ba sama da ni, da sauri na dau littafi na da nake rubutu a ciki zan fita ya kuwa sa qafa ya tokare qofar ya rufe........

Nima na zare hannu na a rubuta sirrin masoyan....

Mutanen k'warai masu albarka in an karanta sai a dangwala min yatsa a star din nan hilis...sannan a Yi sharing da abukkai....se a zuba sharhi saboda shine taki na... love 💕 all.

Continue Reading

You'll Also Like

3.6M 291K 96
RANKED #1 CUTE #1 COMEDY-ROMANCE #2 YOUNG ADULT #2 BOLLYWOOD #2 LOVE AT FIRST SIGHT #3 PASSION #7 COMEDY-DRAMA #9 LOVE P.S - Do let me know if you...
446K 26.1K 43
The story continues to unfold, with secrets unraveling and new dangers lurking in the shadows. The Chauhan family must stay united and face the chall...
1.5M 132K 45
✫ 𝐁𝐨𝐨𝐤 𝐎𝐧𝐞 𝐈𝐧 𝐑𝐚𝐭𝐡𝐨𝐫𝐞 𝐆𝐞𝐧'𝐬 𝐋𝐨𝐯𝐞 𝐒𝐚𝐠𝐚 𝐒𝐞𝐫𝐢𝐞𝐬 ⁎⁎⁎⁎⁎⁎⁎⁎⁎⁎⁎ She is shy He is outspoken She is clumsy He is graceful...
142K 7.7K 40
𝐁𝐎𝐎𝐊 𝐎𝐍𝐄 𝐎𝐅 𝐓𝐇𝐄𝐈𝐑 𝐅𝐀𝐈𝐓𝐇 𝐒𝐄𝐑𝐈𝐄𝐒 Aarohi and Siddharth's tale began unexpectedly at her brother's wedding. Their connection spa...